Skip to content
Part 7 of 60 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Sai da tayi magana, tunda farko, tun sanda ta ga yanayin Tahir din akan Sa’adatu, me tace mata?

“Ba soyayya muke ba Amma.”

Da tayi mata magana akan duk da haka taja baya da Tahir din kuma sai ta amsa da,

“Da gaske Amma, ba soyayya mukeyi ba, dana fada miki.”

Da ya fara yi mata kyautukan da kowannen su yake rubuce da kalmar da idan aka cigaba da hadawa zasu tashi soyayya, ta sake yin magana sai Sa’adatu ta hadota dashi, ya zo ya lankwashe kafafuwan shi a gabanta, ya kalleta da idanuwan shi masu dauke da tarin kwarjini, ya bude bakin shi cikin sanyin muryar shi yana daureta da jijiyoyin jikinta, har saida taji bata kyauta ba da ta hana Sa’adatu amsar kyautar da yayi mata, bata kyauta ba da take kallon shi a matsayin dan Asabe ba nata ba, bata kyauta ba da taji bambanci tsakanin shi da Abdallah, shisa ta dauki ido ta saka musu. Karya takeyi dai idan tace zuciyarta bata doka ta kara dokawa ba lokacin da Sa’adatu tace mata Tahir yace yana sonta, da ta juya kuma saita nufi gidan Anty Khadi, saboda bata da abokiyar shawarar da take tunanin zata fahimceta sama da Anty Khadi din. Su Nabila duk wanda zata nema murna zaiyi da wannan maganar, zasu nuna mata yanda Asabe zatayi hargaginta ta hakura ne kawai.

Sai jikinta ya kara sanyi da zantukan Anty Khadi.

“Na fahimci daga inda tsoronki yake fitowa Abida, ki yarda dani, nasan ya irin auren nan yake kasancewa duk da banyi irin shi ba, amman darare nawa muka raba daga ni harke muna kuka akan matsalar Hajiya…babu uwar da zata so ‘yarta ta shiga irin wannan matsalar, musamman ma ke da kika san me kika Hadiya.”

Numfashi mai nauyi Abida ta ja, ko zata kwana ta yini tana bada labarinta da dangin miji kowa fa hasashe zaiyi, sai wanda ya taba tsintar kanshi a irin rayuwar da tayi ne zai fahimceta. A lokacin gani takeyi lokaci zai tafi da kaso mai girma na tsanar da sukayi mata, musamman idan ta zage damtse wajen kyautata musu. Wani sashe na zuciyarta kuma ya dinga gaya mata sai me? Ba dai Habibu na sonta kamar ya dauketa akai yayi yawo da ita ba? Kiyayyar da sukeyi matan fa yasa kafa ya tura baya ya daukota ya ajiye a gaba, soyayyar shi kawai ta isheta, bayan auren da ta dandani kulawar shi, ta kuma tabbatar soyayyar da sukayi a waje kamar cikin cokali ce, ta yanzun kuma bokiti-bokiti, sai ta kara godewa Allah da ya mallaka mata shi. Ta kuma gyara zama a gidan shi tana ganin da gaske kiyayyar mahaifiyar shi ba wani abu bace da ya kamata ta daga hankalinta akai.

Sai da Hajiya ta fara yi musu dirar mikiya da sanyin safiya tana daga musu hankali, tayi na farko, tayi na biyu, tayi na uku, lokacin da lissafi ya fara bacewa Abida sai ya hada mata da wannan tunanin na cewa soyayyar Habibu kawai ta isheta, in dai shi yana sonta, kiyayyar dangin shi bakomai bace ba. Da ta fara haihuwa, ta ga yanda wannan kiyayyar ta tsallako kan ‘ya’yan nata, sai jikinta ya kara sanyaya, ta kara gane ashe abubuwan da suke haduwa su sa aure ya cika, soyayya bama a sahun farko take ba. Wani sashe ce kawai da wasu ranakun ake wayar gari ma a nemeta a rasa.

“Sai dai ki duba, duk wannan abin, kin taba dana sanin auren Habibu?”

Anty Khadi ta datse mata tunanin da takeyi da wannan tambayar da ta sake fisgar tunaninta zuwa kyawawan halayen Habibu, tarin kaunar shi da kyautatawar da bata taba yankewa a tsakaninsu ba sai da numfashin shi ya kare. Ko yanzun aka dauki ranta, aka sake dawo mata dashi a duniyar da Habibu yake, zuciyarta ba zata taba barinta ta huta ba saita nemo shi, ko da kuwa duka duniya zasu taru su kita, bama iya dangin shi ba kawai.

“Ki rabu da Asabe, ki bisu da addu’a kawai, in da alkhairi Allah ya tabbatar mana, duk da daga nesa na taba ganin Tahir din nan, wallahi naga natsuwa a tare dashi.”

Kai Abida ta jinjina.

“Yana ma da natsuwar Anty, kawai ina tsoron Asabe ne, ko da take gidan nan ba shiri suka cika yi da Sa’adatu ba, kin dai san halinta da neman magana, ta mayar da Asabe kamar kakarta, duk yanda zata sosa mata rai ta sani, tun ina fadan harna gaji na kyaleta, kuma kin dai san yanda ta tsaneni.”

Dariya Anty Khadi ta yi.

“Ke dai kin cika tsoro wallahi…ai Sa’adatun ma itace dai-dai da halin Asabe.”

Murmushin karfin hali Abida tayi, bawai dan zuciyarta ta natsu ba, ba kuma dan bata yaba da halayen Tahir ba, yaro ne da kowacce Uwa zata so ace ya kasance mijin ‘yarta, saboda nagartar shi da sanin ya kamata. Ba ta san tashin hankali ne tun asali, duk wani abu da ta san zai bata mata rai ko ya daga mata hankali gudun shi takeyi da gasken gaske. Ta dai amsa Anty Khadi ne, ta dawo gida, sai dai yanda takeyin komai da sanyin jiki zaka fahimci tana tare da damuwa, har Sa’adatu ma ta kula da hakan. Bata san me ya kamata tace mata bane, itama tana tare da tata damuwar, tunani ne cunkushe da kanta, duka akan Tahir din, sunyi waya kamar yanda yace mata zasuyi, ya sake fada mata yana sonta, ya kuma dora mata da tana da lokacin duk da take bukata kafin ta bashi amsa. Sai dai ta dauka zai bata fili ne tayi tunani, sai ya sama musu wasu sababbin al’adun akan kiran karfe takwas din daya kirkirar musu.

Da an idar da sallar asuba saiya kirata, ranar farko ta dauka ne da faduwar gaba, sai muryar shi ta rantsa kunnuwanta tana kara saka sanyin asubar lullubeta tare da na muryar tashi, yanda ta fito a sirance kuma da wani irin amo saiya sakata sake jingina bayanta da bangon da take jingine dashi a inda ta idar da sallah tana yin azkar.

“Kinyi azkar din safe?”

Ya furta kalmar azkar din kamar shi ya kirkira, kamar kuma ba Hausa bace yaren da harshen shi ya fara nakalta, ta daga kai tana dorawa da,

“Shi nakeyi naga ka kira.”

Sai da yayi hamma daga dayan bangaren yana sauke numfashi a kunnenta, yana kuma tashin wani abu da bata san yana tare da ita ba sannan yace,

“Kiyi karatun Qur’ani idan kin idar, ko shafi daya ne. Zanji muryarki ne daman…”

Ko bayan ta sauke wayar daga kunnenta, sai ta tsinci kanta da kura mata ido kamar Tahir zai fito ta cikinta, ko makaranta da taje sai da kawayenta sukaita tambayarta abinda yake damunta saboda tayi sanyi kamar ba ita ba. Malamai biyu suka tambayeta ko bata da lafiya, karshe tace kanta ne yake ciwo dan su sama mata lafiya. Da ta dawo gida tana kunna wayarta sakon shine ya fara shigowa.

“Ina ta tunaninki, nasan kina makaranta, in kin dawo kuma akwai Islamiyya.”

Ba wasu kalaman soyayya bane, ta dai karanta yafi a kirga tana rasa abinda take ji. Saiya zamana kamar Tahir din yana duba, duk sanda zata samu sararin yin wani tunanin da baya ciki sai ya kira wayarta, ko ya tura mata da sakon text yana dawo mata da tunanin shi cikin kanta. Ba zatace kuma tun ranar ya sake furta mata wata kalma ta so ba, bata san ko ita bace take karanta so a duk wani karamin abu da zaiyi mata yanzun. Sai da suka shafe sati hudu a haka sannan ma ta saka shi a idanuwanta, kafafuwanta har hardewa sukeyi sanda ta fita. Yana tsaye a kofar gidan, da wani yadi ruwan toka da ta kiyasta laushin shi da idanuwanta. Yayi mata kyau fiye da duk wasu ranaku da ta taba ganin shi, sai taji bugun zuciyarta ya karu, da ta gaishe dashi, muryarta a raunane ta fito, daya amsa sai ta rasa me zatace masa, shirun daya gifta yana dauke duk wani sauti na abinda yake faruwa a kusa dasu. Kamar babu hada hadar mutane a unguwar, kamar daga ita sai shine kawai.

“Dan nace ki dauki duk lokacin da zai isheki shine kike ta wahalar dani ko Sa’adatu? Dan Allah ki bani amsa ko zan samu salama…”

Numfashi ta ja tana fitarwa a hankali.

“Me zance? Bayan baka bani lokacin ba Yaa Tahir, inajin kamar duk wani motsi da zanyi da kai a ciki.”

Ta fadi da dukkan gaskiyarta, tana saka murmushi ya kwace masa.

“Waye yace daman ina so kiyi motsin da bana cikin shi?”

Ita tayi murmushin wannan karin, wata kunyar shi na saukar mata. Yayi kokari sosai, ya jata da hira, ta kuma biye masa, lokacin da sukayi sallama ta koma gida, da ace wani zai tambayeta me suka tattauna ba zata iya bada cikakkiyar amsa ba, in da dai za’a sauya tambayar zuwa abinda take ji, zata amsa da kalma daya ne tak.

“Nishadi”

Wani irin nishadi da bata taba tsintar kanta a cikin shi ba. Duk tsokanar da Fa’iza ta dinga yi mata dariya kawai ta dingayi. Har saida suka kwanta ne tukunna Fa’iza tace mata,

“Kiyi isthikhara Sa’adatu, kiyi addu’a sosai, ki nemi zabin Allah.”

Ita wannan tunanin ma baizo mata ba sam, shisa take jin dadin zama da Fa’iza saboda irin wannan abubuwan, ko ba zakayi ba zata tunasar da kai.

“Kinga tunanin ma baizo mun ba, In shaa Allah zanyi.”

Fa’iza bata manta ba, karfe uku da rabi na dare ta tasheta, da kyar ma ta iya mikewa, sai da ta dauki lokaci zaune akan katifa, lokacin har Fa’iza ta kabbara sallar da ta zame mata jiki, ko lokuttan da bata sallah inka tashi zaka ganta a zaune, ta saka earpiece tana sauraron karatun Qur’ani, idan tace mata,

“Waike kina period dinma ba zaki kwanta kiyi bacci ba.”

Zatayi murmushi ne ta amsa da,

“Ko na kwanta ma ba baccin zanyi ba, juye-juye zanta yi.”

Sa’adatu ta dauka babu mai yawan ibadar Abida, ta dauka Abida ce kawai take wuni hidimar gida, kuma ta tashi cikin dare neman lahira, sai da taga Fa’iza yanzun. Haka ta jera kwanaki bakwai tana sallar nafila da kuma neman zabin Allah akan maganarta da Tahir, sai ta samu wata irin nutsuwa ta ban mamaki, duk da idan ta kalle shi bata iya hana kanta hasaso irin rayuwar da zata samu a gidan shi, tana da burika masu yawa, idan ta kalli Tahir kuma sai ta kasa ganin cikar duka wadannan burikan nata tare dashi. Shisa addu’ar da tayi ba karamin natsuwa ta sama mata ba, tunanin yana nan a ranta, taraddadin ne dai ta nema ta rasa. Musamman kuma da Saurayin Nana wato Mustafa yayi maganar yana son turo manyan shi, sai rabin hankalinta ya karkata wajen tunanin yanda bikin da ko tsayar dashi ba’ayi ba zai kasance.

Abida ta wanke kafafuwanta har gidan Asabe ta sanar da ita, duk da labarine da yayi ma Asaben dadi, amman sam Abida bata ji dadin tarbar da ta samu ba, shisa duk abubuwan da aka kawo mata ruwa kawai ta sha, tace mata zata wuce dan taje ta sanar da su Anty Talatu suma, tunda ko da Habibu yake raye, ba wasu shakikan ‘yan uwa maza yake dasu ba, sai sunje an sanar da dangi, tukunna suke zuwa,

“To ki gaishe dasu, idan na samu lokaci zanzo sai mu zauna muyi magana sosai.”

Asabe tace mata, ko arzikin rakiya bakin kofa bata samu ba, ko da ta fita sai kallon gidan takeyi tana karawa, daman gidaje irin wadannan sai dai ta wuce su a hanya, in ba dan Asabe ba watakila da bata da rabon shiga cikin irinsu, daula kam Asabe ta sameta, gashi nan ma ta nuna a jikinta daga suttura har ma yanayi, farar fatar nan ta kara murjewa. Har kasan ran Abida kuma tayi mata murna da fatan karin zaman lafiya mai dorewa. Bata ga hararar da Asabe ta watsa mata ba kafin ta fita, daman a wuya take da ita, sani ne kawai batayi ba, ace har yanzun daga Sadiya har Nana babu wanda ya tako inda take? Saboda Abida ta shanye su, gara ma Abdallah zatace ya kirata sau daya ya gaisheta, muryar shi can kasan makoshi kamar wanda aka tursasa shisa ta kasa yi masa mitar da tayi niyya. Sai dai ita ta kira shi taji lafiyar su. Mustafa kuma ai ta san dashi dama tuntuni, tunda Nana kusan ta kori kowa, shi kadai take saurare.

Abubuwa ne suka hadu suka sha mata kai, duk wasu yan kudadenta da take adanawa ta mikawa Uwani an karbo mata taimakon da take ganin ya zame mata kudinka a bola, tunda bata ga amfanin da sukayi mata ba. Idan tayi magana kuma sai Uwani tace mata.

“Abinda nake ta fada miki kenan ai, shi kanshi Malam yace ba’a zaune yake ba, in ba babban aiki akayi akan shi ba da wahala yaci, kudi zaki saki sosai fa Asabe.”

Har sai da sukayi sama da Uwani ranar.

“Wanne kudi kuma? Ke kanki kinsan banda su, wanda nake ta adanawa ne na fiddo na mika miki, gashi nan bukata bata biya ba, kuma kudin ba dawowa zasuyi ba.”

Sai Uwani taji haushi, da yake su duka ba hakuri ne dasu ba, nan suka dinga gayawa juna maganganu, Uwani ta dauki jakarta tayi gaba rai a bace, kusan wata daya basuyi magana ba, kafin Uwanin ta kirata suka shirya. Sai dai ko da wasu kudine suka shigo hannun Asabe bata jin zata sake mikawa Uwani tunda dai bata ga abinda wannan bin Malaman yayi mata ba, ita tunda farko ma zuciyarta sam bata kwanta ba. Yanzun ga maganar auren nan da take ta hasashe hartazo kuma bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba. Haka ta dinga juyi har dare, sai dai batayi kwauron baki ba, da yake Alhaji Salihu na wajenta, da tayi masa tayin abinci yace in da farfesu dai ta zuba masa ta hada masa da ruwan Lipton. Da ya gama ci ta kauda kwanonin saita koma tana zama a gefen shi.

“Hajiyata ya akayi ne?”

Dariya ta yi,

“Wannan Hajiya Allah dai ya datar dani.”

Dariyar ya yi shima, da alama yana cikin yanayi mai dadi yau.

“Ki cigaba da addu’a, kika sani ko bana harda ke a ciki?”

Zuciyarta taji ta doka, ta kara dokawa, jikinta har rawa ya fara yi, yana da arzikin da zai kaita ta sani, amman ko a hasashe bata taba lissafi da wannan ba.

“Allah ya amince to ya karo arziki mai albarka.”

Ya amsa, ita kuma tayi saurin dorawa da,

“Daman yarinyar wajena ce yau akazo akace wanda yake zuwa wajenta yayi magana zai tura manyan shi, to shine nace zan fada maka dan inje inji ya shirye-shiryen zai kasance, dan karsu saka lokaci kadan.”

Kallonta yayi sosai.

“Wanne irin kuma kar a saka lokaci kadan? Nifa bana so inga anja lokacin aure wallahi.”

Dan murmushi ta yi.

“Alhaji auren talaka idan ba’a ja shi ba ya za’ayi? Ko masu iyaye a raye ma ya aka kare da hidimar biki, balle kuma ita marainiya da ni mai hidimar ban ajiye ba banba wani ajiya ba.”

Gyara zama yayi, harga Allah mantawa yakeyi tana da wasu yara, sai yaji bai kyauta ba. Tunda marayu ne, ko ba komai akwai kudin da yakan ware dan yin sadaka da taimakawa masu karamin karfi, balle ita tunda sukai auren bata taba yi masa maganar yaran ba sai yau, ya kamata ace yayi kara ya taimaka musu, lokacin da yake neman auren nata, tayi masa maganar su, bai mata karya ba, dan bai ga dalilin da zaisa yara manya kamar wadannan suzo su jibge masa a gida ba. Sam bashida wannan ra’ayin, amman har ranshi yayi niyyar lokaci zuwa lokaci ya dinga taimaka musu tunda tace masa akwai inda zasu zauna. Hidimar shi ce da yawa, saiya manta.

“Ba zai gagara ba In shaa Allah, idan an saka lokacin ke dai ki fada mun kawai, yaushe kike so kije? Zan sa a kawo kayan abinci sai ki tafar musu dashi su kara, zan baki kudi ma da zaki basu saboda hidimar makaranta da dan abinda ba za’a rasa ba.”

Yanda tayi shiru tana wasa da yatsunta sai ya kara sakashi jin wani iri, musamman da ta dago ya hangi kwalla cikin fararen idanuwanta.

“Nagode Alhaji, Nagode kwarai. Allah ya kara arziki.”

Sai duk yaji rashin kyautawar da yayi. Dan haka daya mike, naira dubu goma cif haka ya kirga ya bata. Sosai ta dinga juya kudin tare da maganar da yayi yana sakata tunanin me yasa tayi asarar kudadenta? Me yasa ta biyewa Uwani ta dinga bankada masa rubutu da magunguna a abinci, inda ya kamata kuma fa? Sai tace me? Yanzun ga abinda take nema din nan da asirin baiyi mata ba, shi da kanshi ya dauka ya bata. Washegari wajen karfe uku sai ga sako ya aiko dashi, buhun shinkafa babba guda daya, taliya, macaroni, couscous, harda jarkar mai. Yace kuma ta shirya sai aje a kaita, inta gama abinda takeyi ta kira a koma a dauketa, kar dai ta kai Magriba. A shirye take, mayafi kawai ta dauka, tunda ba ita bace da girki ranar, ta dai kara dibar nama ne, na kaza da kuma na rago, harda kifi, tunda tasan kara kawo mata za’ayi, ita kuma ba iya cinyewa takeyi ba.

Da ta shiga motar, saita tsinci kanta da yi masa kwatancen Bachirawa, duk yanda taki jinin Abida, ta san babu wanda ya cancanci duka wannan kayan sama da ita, in zata fadi gaskiya ma ai bata san cinsu da shansu ba yanzun, Abidar dai ce. Sai tayi mamakin yanda Sadiya ta rugo ta fada jikinta, ita kanta Nana bakinta yaki rufuwa, kewarta da basu san sunyi ba ta danne su, itama sai murmushi takeyi, ganinsu cikin kyakkyawan yanayi, Sadiya tasa ta fita waje ta cewa direban daya kawota ya shigo mata da kayayyakin ciki. Abida kuwa da take alwalar la’asar, tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, har aka gama shigo da kayan tsaf, tukunna ne ma tayiwa Asaben sannu da zuwa tana ce mata su shiga daga ciki. Da bayanannen mamaki Abida take kallonta da tace mata duka kayan abincin nan nasu ne, mijinta ne yace a kawo musu.

Ta bude bakinta yafi a kirga tana mayarwa ta rufe saboda batasan me ya kamata tace ba, godiya? Ta wacce siga? Abincin wata nawa ne can take gani, rabonsu da buhun shinkafa tun rasuwar Habibu da aka aiko musu dashi daga gidansu Asiya. Shima wajen zaman makoki aka dafe shi.

“Na rasa abinda zance ne Asabe…Allah ya kara arziki ya saka da alkhairi.”

Abida ta fadi muryarta na rawa.

“Nice bansan me zance ba, wata nawa kike ta fama da su…muyi sallah, naga har kinyi alwala ko…nima bari inje inyi.”

Cewar Asabe tana mikewa, ko da ta fita, sai Nana a tsakar gidan tana zuba ruwa a buta, ganin Asabe yasa ta mika mata butar tana daukar wata.

“Nana ya kuke?”

Da murmushi ta amsa da.

“Wallahi lafiya kalua.”

Itama Asabe murmushin ne a fuskarta.

“Shine ko kuzo inda nake ko? Kun watsar dani dan na kara aure.”

Dan sun kuyar da kai Nana tayi.

“Ba haka bane Mama, lokaci ne bama samu, kinga ga makaranta, gashi kuma muna kamawa Amma ayyukan gidan, zamu zo In Shaa Allah.”

Sai wani abu da Asabe bata san menene ba yayi mata tsaye a wuya, wani abu da yafi kama da kishin kusancin Abida da yaranta. Batace komai ba, sai ta daura alwala ta shige dakin Abida, inda ta samu harta shimfida mata darduma a gefe, ita tana dayan gefen tana sallah. Itama sallar ta gabatar, sai da duka suka idar sannan tayi mata maganar bikin, tace ta fada ma su Anty Talatu, idan an tsayar da ranar da zasu turo zatayi waya ta fada mata, da kanta kuma ta mike ta fita, ta tura mata su Nana, tasan ba zasu rasa abinda zasu tattauna ba, ita kanta Asaben taji dadi, kudin da Alhaji Salihu ya batane ta raba biyu, dan haka ta zaro dubu biyar tana mikawa Nana data karba da fadin.

“Me za’ayi dasu?”

Sai Asabe tayi murmushi.

“Naku ne, ku ajiye a wajenku ko da zaku bukaci wani abin…”

Kafin ma Nana tayi magana Sadiya ta rigata.

“Ai da kin ba Amma, idan muna bukata kawai sai mu karba a wajenta, kudin makaranta ne daman, kuma tana bamu in zamu je.”

Kai Nana take jinjinawa cikin yarda da maganar Sadiya.

“Da gaske ne Mama, da kin ba Amma da hannunki, ko dan ba damuwa, nima sai in bata ta kara cikin hidimar gida kawai.”

Kallonsu kawai Asabe take yi, wannan abin na dazun yana kara girma.

“In baku kudi, kuna ce mun dana ba Abida, ku bakwa bukata kuke nufi kome? Ko baku ga kayan abincin dana zo dashi bane ba, ita na damkawa, tare da yaranta da ita kanta za’aci, kuma saboda ku na kawo.”

Sanin hali yasa basu sake cewa komai ba, tayi fadanta ta mike tana dorawa da.

“Ku kuka sani, ku dai san uwa daban ce, ba zaku taba sauyani da Abida ba…”

Suma kuma babu wannan a ransu, Abida dai tana da kima da daraja mai girmane a idanuwansu, saboda ko lokacin da Asabe take gidanma bata taba nuna bambanci tsakaninsu da su Sa’adatu ba. Tijarar Asabe bata taba sakata ta sauya musu fuska ba, da hankalinsu, sunsan bakowa bane zai rikesu yanda Abida take rike dasu yanzun, ko da kuwa Asabe tana biyanta lada ne. Har waje suka rakata, sai lokacin ne kuma ta ga Sa’adatu da tayi alwala tun wajen uku da wani abu ta shige daki ta saka earpiece tana kallo a waya, shisa bata maji shigowar Asabe ba, ko yanzun ta idar da sallah ne ta saka uniform din Islamiyya, sai ta fito jin muryar Asaben da suke sallama da Abida.

“Ina wuni.”

Ta furta.

“Da kina gidan?”

Cewar Asabe a madadin amsa gaisuwar da Sa’adatu tayi mata, sai ta ga kamar ciki-ciki ma Sa’adatun ta amsata, shisa jininta bai hadu dana yarinyar ba saboda rashin kunyarta, juyawa Sa’adatu tayi tana shigewa daki, saboda Tahir ta fito, da ba dan shi ba, zatayi zamanta ne, idan Abida tayi mata fada daga baya sai tace bataji zuwan Asaben ba, ta saka earpiece a kunnenta, kuma saboda Tahir, da sai ta hayakata tunda kwana biyu bata ji fadanta ba. Kamar yanda su Nana sukayi niyya, suna raka Asabe suka dawo, taje ta mikawa Abida kudin tana fadin.

“Amma ga wannan a kara a hidimar gida, Mama ce ta bamu wai ko zamu siyi wani abu, to ba abinda muke bukata.”

Kallonta Abida ta yi.

“Ai ba za’ayi haka ba Nana, kunce ba abinda kuke bukata?”

Kai Nana take girgizawa tunda Abida ta fara Magana.

“Babu fa Amma, dan Allah ki karba.”

Sai ta karba, da niyyar zata adana, tunda ga maganar auren Nana data taso, ba za’a rasa abinda za’a sai mata ba, ko da tukunya ce kuwa. Da wannan tunanin a ranta har Abdallah ya dawo, ta nuna masa kayan abincin da Asabe ta kawo musu tana dorawa da,

“Kaga idan an fara siyar fa jarabawar share fagen nan, kazo ka siyo Abdallah, kudin abincin, zamu kwana biyu ba mu siyi abinci ba, kudin nake so mu adana, watakila kadan zamu kara kudin makarantarka na shekarar farko.”

Kallonta Abdallah yakeyi, yana mamakinta, yana jinjina yanda take kallon shi kamar daga jikinta ya fito, yanda take da buri akan rayuwar shi fiye da Asabe, ko na rana daya Asabe bata kara daga masa maganar karatun shi ba tun rasuwar Habibu, banda Abida, da duk wani motsi da zaiyi saitayi magana kan yanda take son ganin ya cigaba da karatun nan da ya jima da cire ranshi akai. Amman yanzun kam zaiyi karatun nan, ko da a kafa zai dinga shafawa makarantar yana dawowa a kafa, zaiyi karatun nan yayi kokarin ganin ya gina rayuwar shi harma ya tallafi kannen shi.

“In shaa Allah, da an fara siyarwa zanje in siya Amma…”

Kai ta jinjina, daga kasan zuciyarta take fatan yayi karatun nan, karatun kuma ya zame masa madogara, bata son rayuwar shi ta kare a wahale, inda Habibu na raye zaiyi tsaye yaga yayi karatu ko dan kasancewar shi da namiji kwalli da yake dashi, kuma ko halayen Abdallah sun isa su sa kaso rayuwar shi ta inganta. Ko daya mike so yake yayi mata maganar Nana, yasan babu wanda zai suke dashi da zai tallafa musu wajen kayan daki, sai yaga kamar da Asabe ya kamata ya fara yin wannan maganar. Abinda bai sani ba shine Abida ma tana son yi masa maganar, bata so dai ya zamana katangar da zata sake shiga tsakanin shi da karatun, kuma ta kira su Nabila ta fada musu, Amira da tafi kowa ma sai da tayi mata kuka a wayar.

“Da Abba na da rai fa yanzun tunanin gudummuwa kawai zamuyi Amma, yanzun mune da tunanin yanda zamu fitar da ‘yar uwar mu kunya, rayuwa kenan.”

Itama sai taji zuciyarta tayi mata nauyi, Nabila kuwa tana gaya mata za’ayi maganar auren Nana bayan hamdala saita dora da,

“Amma kice asusu ya kamani, mu manyan yayye ai dole muyi babban motsi.”

Maryam kuwa tace mata akwai kayan kitchen din da take siye duk idan ta samu sarari tana ajiye daman saboda Nanar da kuma Sa’adatu, duk na wanda Allah ya fara kawowa. Ta san ko tashin Habibu akayi a kabarin shi aka hasko masa su zaiyi alfahari dasu, zaiga bata tankwabe kokarin shi na ganin kan yaran a hade ba, sun kuma taso cikin son taimakawa juna.

Mutuwa ta dauke musu Habibu.

Sai dai ya bar yaran da duk wanda zaka duba sai kaga zanen halin Habibu ko da guda dayane a tare dashi.

<< Tsakaninmu 6Tsakaninmu 8 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×