Haka suka taho suna zancan me yasa ta makara tace” Mashin din mu ne ya lalace a hanya shiyasa” tace “ ina Husna”? Nafisa tace” sai anjima zata shigo tace cikinta ne ta tashi ba dadi” ayyah Allah ya kara lafiya “Widad ta fada” dai dai nan suka zo office din suka ce” ki shiga muna nan da kinji wani abu ki kwallara kara mu kira mutane” duk yadda Widad take cikin rashin dadi sai da tayi murmushi tace “ tohm”.
Tana shiga tai sallama ya ansa ta tsaya cak tana jiran abunda zai fada ya dago da glass dinsa a ido. . .