Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Tsintacciya by Nimcyluv sarauta

“Tsundum” sautin Amon faɗawarsa cikin kogin ya bada, kafin kuma wasu manyan ƙwayaye su fara firfitowa alamar wanda ya shiga cikin ruwan yana fidda numfashi.

Malam ne ya sauke Ajjiyar zuciya tsoro duk ya cika masa zuciya, Musamman like Md Adnan did! Yay Wani good jum before he fall in to the river.

Cikin damuwa Malam ya kalli Drive yace “Yadai iya ruwan sosai ko? Nasan Adnanu gwamma shi da ɗan uwansa, bana son rasa rai biyu a lokaci guda, Akeela nada matuƙar muhimmaci a rayuwata haka Adnanu.”

Shiru Driver yay domin like serious bai san komai ba amma dai yasan Adnan na yawan shiga wani ruwa.

Isiya ne yace “Uhm yadai iya ruwan ko?” Kallonsu driver yay kafin yace.

“Not sure! Amma Ƙaramin Mai gida yana shiga swwiming pool sosai yana son wasan ruwa, ta takalmin taya, amma dai ruwa kamar wannan bana da tabbacin yana shigarsa”

Malam ya kalli ruwan yace.

“Allah ka taimaka ni, ka duba lamarin wannan yaran”

Juyawa Driver yay yace “bari na kira taimakon kwanakwana incase”

Wajan motar ya nufa ya ɗauki Wayarsa tare da fara shiga goggle yana duba yadda zai samu impormation na ma’aikatan mafi kusa da garin.

Md Adnan wani numfashi yaja mai wahala yana jin yadda numfashin nasa ke wata fisga kamar zai bari ƙirjinsa.

A hankali kuma ya ɗaga hannunsa zuwa sama kafin ya ware legs ɗinsa, idanunsa dake a rufe ya buɗe yana kumbura bakinsa tare da fidda numfashi.

Girman ruwan da yadda yaga ruwa yay bala’in firgitar sa.

Cikin sauri kuma yay baya da hannunsu yana ware ƙafa tare da fara nutsu cikin ruwan yana ninƙaya, ya ɗauki good 10minutes yana duban Akeela amma babu ita, yana ƙoƙarin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana jin wani reshe na baƙin ruwan daya riƙe mata riƙa.

Hijab ɗin jikinta tuni ya zame yay gaba, gudun ya ƙara yana cimma ta yana gab da zuwa inda take wata igiyar ruwa ta riƙesa cikin kuma rashin Sa’a Wani irin ruwa mai yawan gaske ya tawo cure guda.

Wani kalan ware idanu Md Adnan yay kafin yay wani yunƙuri na guduwa ruwan yay gaba dashi ji kake “Shuuuuuu” sautin gudan ruwan ya bayar.

Dawo Driven yay yana faɗin “na kira, in sha Allah dukkan su noting will happen to them” Cikin damuwa Malam yace “Amma ko motsi babu, ji yadda ruwa ke gudu tsoro ya kamani sosai” “aifa da tsoro mutane har biyu ga wannan bawan Allan da gani bai saba da wahala ba” cewar Sunusi yana mai ƙara leƙawa cikin kogin.

A can cikin motar Md Adnan Wayarsa ce take ta ringing kira na wajan uku kenan amma babu respond! A hankali motar da fara shigewa wani matashi ya fara knocking Ƙofar motar hannunsa riƙe da wayarsa yana ƙara danna number Md Adnan yana mamakin abinda ya tsayar da shi har yanzu bai ƙarasu ba gashi lokaci na tafiya.

Daga cikin motar wani mutum ne mai kimanin shekaru 32 a duniya, yana zaune a back seat idanunsa maƙale da wani farin glass na haɗaɗɗun goyon nan.

Sanye yake da wata fitinanniyar Double breasted suit dark Maroon. Gashin kan nan nashi yay kwance har wuya daga gaba ya kwanto, sai ƙyalli yake yasha Ginger Geminal Oil hair.

Kakkauran laɓɓansa pink irin yirr ɗin nan lokacin zuwa lokacin yana taune su like his punishing kansa, fari ne tass irin farin nan da kai tsaye ba zaka iya tantance na wani ƙasa ko kuma jinsi ba, yana da kyau sosai looking soo damn sexcy and hot!

Irin manyan mutanan ne masu tashe da zamani irin definition of classic masu fama da mahaukacin kuɗi na halak.

Idanunsa ya janye daga kan haɗaɗɗiyar ƙaramar Apple system ɗinsa yana maida idanunsa Submariner Rolex ganin lokacin yaja ya ɗan saki siririn tsaki.

Deep down kuma zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi, like something bad gonna happen to him.

Irin mutanan ne da wahala ka fahimci sauyin fuskarsa, farin ciki da damuwa baya sanyawa kaga sauyi a saman fuskarsa.

Yana da kamilalliyar fuska mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa abu guda ke sauya masa tunani yaji ana masa ihu a saman kansa, ko kuma yaga anci zarafin wani ɗan Adam.

Zame system ɗin yay tare da ajjiye ta a gefensa, cikin nutsuwa ya fara juyawa laɓɓansa yana motsawa a hankali.

A taushashe sautin fitar amon muryarsa ke tashi yana faɗin.

“Asstagafirullah, Walahamdulillah, Wallahu Akbar” shine Amon kalaman dake fita a bakinsa.

A karo na wajan huɗu P.a dake tsaye daga baƙin ƙofar ya ƙara Knocking ƙofar, taɓe baki yay kafin ya ɗaga hannunsa tare da danna glass ɗin motar yay ƙasa.

P.a ne ya kalli mutumin cikin motar yace.

“5times ina kiran number Md amma no answer”

A karo na farko bayan sauke glass motar  Dr. ABDUL-HAKEEM BUKAR BELLO ya ɗaga idanunsa tare da kallon P.a idanunsa kawai ya juya da sauri P.a yace.

“Ok lemme try it”

Ya faɗa yana ƙara danna number Md Adnan, kafin kuma gently ya miƙa hannunsa ya buɗe murfin motar, kamar bai so haka Dr A.b ya fito da ƙafarsa kafin kuma ya fito daga motar baki.

Lumshe idanunsa yay saboda iskar ƙasa da ƙamshin sabbin shukokin da akai da suke dukan hancinsa.

Yana da tsayi da faɗi jikinsa a murɗe yake ga wani faɗin ƙirji da yake dashi (Physique chest) bayyanar ƙwayar idanunsa a yanzu ya tabbatar cewa shi ɗin (Half-caste) ruwa biyu kenan.

Zare jacket ɗin yay ya saƙala a hannunsa yana mai sassauta necktie ɗin wuyansa.

“Sir har yanzu ga, gashi mun tara mutane sun taro mu kawai suke jira”

Taɓe baki yay walking slowly ya nufi wani ma dai-dai cin waje da aka gyara yay ta tass ga kujerar da aka sanya masa.

Maida wayar P.a yay zuwa aljihunsa yana mai mamakin abinda ya hana Md Adnan ɗaga wayar da kuma mamakin rashin ƙarasuwar sa is anything okay Babu damuwa ai rashin sanin dalilin shine damuwar.

Waje Dr A.b ya samu wanda wasu jama’ar suke kiransa da AKEEM ya zauna yana mai sassauta haɗewar fuskarsa saboda ganin duk manya ne a wajan wanda shekarunsu, suka ja ainun.

Cikin mutunci ya buɗe bakinsa a nutsu yace “Assalamu alaikum warahamatullah”

Gaba ɗaya mutanan suka amsa masa kafin yay Shiru yin shirun nasa ne kuma yasa P.a dake gefensa a tsaye yace.

Al’amarin ya girmi tunanin su Malam tashin hankali sosai ya bayyana akan fuskarsa yasan yadda ƙaninsa Bukar Bello ke bala’in son yaran nasa fiye da komai na rayuwarsa, yanayin komai saboda dasu ya hakan salwantar da nasa farin cikin just to see them happy, yaya zai kasance idan wani abu ya faru da Md Adnan? Wannan dalilin yasa baya barin su ko’ina sai companies ɗinsu da gida ko kuma ƙasar waje, he cares about his children yana mutuwan son su, ko zazzaɓin su baya jurewa musamman Mai sunan kawonsu.

Driver Md Adnan ne yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un yanzu mene zance da Babban mai gida eh? Dan Allah? Yau warning ɗina akan na kula da driving ɗin Md Adnan ya kula dashi amma gashi shine ma yace ya shiga ruwan ƙilan dai yama kashe sa idan yaji labarin haka, domin yasan baƙar zuciyarsa.

Malam ne yace “Ubangijin sammai da ƙassai ya kawo mana ɗauki, Wannan wanne irin tashin hankali ne eh?”

Ya faɗa hawaye na zubu masa.

Kafin kace wani abu tuni mutane sun taro wajan yara da manya, a dai-dai lokacin ne kuma motar kwanakwana ta ƙarasu suna zuwa suka fara aikin su nan da nan suka shiga cikin ruwan, sama da mintuna talatin babu Md Adnan babu Akeela.

Tuni Driver ya fara kuka yana faɗin “shikenan wallahi na shiga uku wajan Babban mai gida, eh ina laifin ƴar kazar da nake ci na kwana katifa mai taushi ha banɗaki kamar ma kwanci, suttura kala-kala, eh? Duk banga haka ba ga ɗan ilimi dana samu na kan iya jin turanci ko yaya ne amma yanzu na tura masu ɗa cikin ruwa i can’t forgive myself if anything happens to Ƙaramin Mai gida”

Wayarsa dake ƙara ya duba ganin sunan Alhaji yasa ya ɗaga jiki na rawa yace.

“Yallaɓai” gyara zama Alhaji Bukar Bello yay saman kujera hannunsa ɗauke da Mug yana shan coffee, yana sanye cikin Arabian Jallabiya mai taushi da laushi a ƙalla zai kai shekaru 63 amma jikinsa sam bai nuna ba, kyawunsa na samartaka na nan.

Cikin ɗan sakin fuska yace “Bala” da sauri Driven yace “Na’am Yay.. Yallaɓai” ya ƙare maganar muryarsa na rawa, gaban Abbu ne ya faɗi haka kawai yaji zuciyarsa na tsinkewa cikin ƙasa da murya yace.

“Bala where is my friends?” Shiru Bala driver yay yana zare idanu jin haka yasa Abbu miƙewa tsaye tare da goya hannunsa a baya a kaushashe Muryar nan babu wasa yace “Bala yarana” jin haka yasa Bala fashewa da kuka yace.

“Tsautsayi da kauɗin harshe, Allah na tuba ka yafan…,” Da sauri Abbu ya katse sa da faɗin “heeyyy Bala this is the last time da zan tambaye ke where is my friends? Ina cute  two kids ɗina? Suna ina Eh Bala?”

Haɗiye kukan Bala yay kafin yace.

“Yallaɓai Ƙaramin Mai gida ne ya shiga ruwa kuma…” Gaba ɗaya ya faɗa masa abinda ke faruwa. Tun kafin ya gama jikin Abbu ya hau rawa idanunsa suka Kaɗa ganin yana ƙoƙarin faɗuwa yasa da sauri matarsa mai suna Hajiya Ayusher suna ce mata Ummi tayi saurin miƙewa yana ganin ta ya faɗa jikinta ya rungome ta sosai jikinsa na wani irin rawa bakinsa na ɓari yace “My Adnan My Friends ya rana Ayushertu” ya faɗa yana ƙara matseta a jikinsa.

Jikin Bala Driver na rawa hannunsa wanda yake riƙe da wayar ya riƙe sosai yana faɗin “kai,kai! Ka tsaya mana wallahi yallaɓai bani da laifi idan ka kuran ina zan dinga cin shinkafa? Ina zan dinga cin naman nan naku mai daɗi da romo? Innalillahi wayyooo Ni Bala na shige su”

Shiru yaji babu maganar Abbu sai Ummi dake faɗin “Subuhanallah, Abbu Meke faruwa da yaran namu? Didi! Didi! Mami” ta shiga kiran sunan mutane.

Da sauri Bala ya koma wajan kogin har yanzu babu wani labari, ɗaya daga cikin ma’aikatan ne ya fito jikinsa duk ya jiƙe da ruwa.

Da sauri Malam yau wajansa yana faɗin “Yaya! Wa aka fara cirowa” girgiza ma’aikacin yay yana sharce ruwan fuskarsa yace “till now babu wanda muka gani, ruwa ne yake da ambaliya daga ƙasa, Amma we’re still searching in sha Allah za’a same su”

Shiru kawai Malam yay tare da neman waje ya zauna yana ta sauke ajjiyar zuciya.

A hankali p.a ɗin ya kalli mutanan wajan yace “Kamar yadda kuka sani, kai ya waye lokaci yazo wanda ba sai munce dole sai gwamnati ta taimaka mana Sannan za muyi wani abun ba, ko zamu jira gwamnati at least we have to…” Gyaran Murya Akeem yay da sauri P.a yace “Yes sir” kallonsu yay yace “kuyi hqr bakina yana juye zuwa wani harshe daban, yana da kyau mu fahimci cewa idan muka ce sai mun jira gwamnati Tabbas zamu mutu babu mallaki komai na rayuwa ba, idan nace komai ina nufin, Ilimi both buko da Arabic, ƴan ci, ƴanci na nufin ka samawa kanka abinda babu wanda zai wulaƙanta ka, babu wanda zai kanka yace dan Meye ne kai Wannan? Ka zama komai kai updating kanka daga old version zuwa latest version something new haka” shiru yay yana kallon yadda Akeem ya yatsuna fuska kafin ya ɗura da faɗin “mun samu saƙon ku daga office ɗin mu dake   AKEEM BETTER FARMING INSTITUDE A.B.I na samu sanarwar daga wajan H.o.d Ni kuma na faɗawa Md Adnan, Md ya faɗawa C.E.O na wannan makaranta zance maku ne ko ma’aikata? Bama duba messages ɗin da bana e-mail bane, amma muhimmacin garin da kuma albarkatun noma da muke dashi a wannan garin me albarka Sir Akeem kuma Dr Abdul-hakeem Bukar Bello C.e.o of Akeem better farming institute yace a shirya tafiya kafin yace fara gabatar da aikinsa da Za’ai a channel ɗin M.hausa dake GOtv and DStv yanzu muna son ɗaya daga cikin ku ya faɗa mana matsalar ku”

Wani babban kuma mai ɗan shekaru ya miƙe bayan yay godiya ne ya ɗura da faɗin.

“A kullum muna fuskantar barazana daga wajan manyan mutane wanda suka tsoratar damu da faɗin sunayen su”

Akeem da idanunsa ke ƙasa yana zuciyarsa na tsalle kamar zata faso ƙirjinsa ta fito saboda faɗuwar gaba ya ɗaga idanunsa ya kalli mutumin kamar bazai magana ba sai kuma yace “Uhm” yana faɗin hakan yay shiru da sauri kuma P.a ya miƙa masa gorar ganin yana shafa ƙirjinsa cikin ƙasa da murya cike da tsoro mutumin yace.

“Sunce mu bar masu gonakin mu akan kuɗi dubu ɗari biyar biyar ga dukkan mutumin daya sanya hannunsa a kan takardar, za suyi ma’aikata, da farko Bamu san wacce kalar ma’aikata bace, yaran mu masu tashi sune abin tsoro, mun yarda da noma, kuma itace arziƙin mu da dukkan wanda yake ƙasar Nigeria, Noma toshan arziƙin mu kuma kwanciyar hankalinmu mu manoma, wasu nayiwa noma kallon wani abu nada ban amma da ace mutum zai san amfanin noma da kuma ribarta to hatta samarin da suke da kwalin jami’a tabbas zasu ajjiye dugun buri su tawo gona domin yin Noma, babu buƙatar kuɗi gonakin mu muke buƙata, ƙauyen dake gaban namu sun amince bisa shawara dana masu har Abin yake neman juyewa zuwa tashin hankali, shine yasa muke neman taimako daga gareka ka shiga wannan lamarin muna buƙatar gonakin mu” ya faɗa yana haɗe hannayensa waje guda, ganin hakan yasa gaba ɗaya mutanan wajan suka miƙe suna haɗa hannayensu waje guda.

Da sauri Akeem ya miƙe yana fidda numfashi domin baya ƙaunar wani babba ya duƙa masa.

Wata haɗaɗɗan jotter da pen P.a ya bawa Akeem cikin sauri ya fara rubutu mai cike da tsari daga ƙarshe ya rubuta.

           From Akeem better farming institute

              To

    marasa tsoran Allah masu son ci da gumin wasu

      Sign Abb hero

Yana gama rubutawa ya miƙawa P.A idanunsa ƙasa dan bai so ake ganinsa kafin a hankali cikin fitar wata Amon murya irin golden voice ɗin nan yace.

“Ku ɗauka ku Alhalin Abdul-hakeem Bukar Bello ne, babu abinda zai samu lafiyar ku, Alhalin ku, duniyoyin ku” yana faɗin hakan ya juya walking slowly irin tafiyar nan mai ɗaukan hankali.

Cikin sauri kuma a ransa ya furta “Adnan” da sauri ya nufi mota ganin hakan yasa P.a yabi bayansa motar ya shiga kana yana da gudu hankalinsa gaba ɗaya yay kan ɗan uwansa yana mutuwar son ganin nasa, he Loves him yafi son komai zai faru ya same su tare.

Wayar Md Adnan ya kira amma babu answer hakan yasa Murya can ƙasa yace.

“Uhm p.a drive faster”

Gudu ya ƙara suna zuwa dai-dai wajan taron jama’a Bala driver na ɗaga kiran Akeem ganin sunan Blood yasa Bala ya shiga uku.

Bai tsaya jiran jin abinda Bala zai faɗa ba, da sauri p.a ya fito daga motar yana buɗewa Akeem murfin motar, kai tsaye idanun Akeem ya sauka akan Baffansu.

Da sauri Malam ya miƙe ganin Mai sunan kawonsu yace.

“Kaga abinda ya faru ko? Daga zuwan Adnanu ya haɗu da aljalinsa” da wani irin kallo Akeem yabi Malam yama kasa gane mene sauke faɗa.

Ka kaff Malam ya bawa Akeem labarin abinda ya faru, nan da nan fuskarsa tai jajirrr saboda tashin hankali amma ko kaɗan babu wani alamar tashin hankalin cikin ƙwayar idanunsa saboda shegen shanye abune dashi a rai.

Zame jikinsa yay daga wajan Malam kai tsaye wajan ruwan ya nufa Malam na faɗin “A’a Mai sunan kawo kada mu rasaka dan Allah ka tsaya..” kafin ya gama magana tuni Akeem ya faɗa cikin kogin nutsu ya fara cikin ruwan cike da ƙwarewa yake sarrafa ruwan tamkar dai wanda ya san kanshi babu jimawa idanunsa ya sauka akan wani Abu mai duhu, cikin sauri yay wajan yana zuwa yaga mace saƙale jikin reshe ƙarasawa yay wajanta yana mai ɗan ƙara ware idanunsa ganin babu Md Adnan babu Labarinsa wani iri tsoro ya kamasa cikin damuwar ya nufi wajan yarinyar yana zuwa yay wani irin…..

<< Tsintacciya 1

3 thoughts on “Tsintacciya 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×