Tana shiga Umar ya shigo niƙi niƙi da kaya wai gashi, da hanzari ta ce maza mayar masa, “Ai ya tafi” Umar ya ce.
Karɓa kawai ta yi ta miƙa ɗaki gami da dawowa dan ci gaba da wankinta. Kairiya da ta shigo ne yass Ummu ta watsa mata harara “Malama baki iya sallama ba.”
“Nafa yi sallama yaya ji ne bakiyi ba,” “Eh ai bazan ji ba tunda na kurmance.”
Komawa Khairiyya ta yi batare da ta ce komai ba tayo sallama, “Assalamu alaikum,” gabaki ɗaya suka amsa sannan ta dubi yayar ta su, “Yaya na dawo.” kamin Ummu ta ce wani abu ta ce da hajiya “Hajiya na dawo.”
Ummu ce ta ce, “Ina kika tsaya,” “Wallahi yaya yanzu aka tashe mu.” “Cewa na yi ki rantse eyye?”
Wuri wuri Khairiyya ta yi da ido dan tasan halin ummu duk da cewar yayar su ce sai dai suna shashkar ta tamkar yadda ɗa ke shakkar mahaifiyar sa. Tambayar ki nake kinyi shiru Ummu ta kuma faɗe.
“Wallahi yaya ba ƙarya nake ba yanzu aka tashi” girgiza kai kawai Ummu ta yi har ta cigaba da wankin inda Khairiyya ta yi ɗaki ta ce “Khairiyya.”
Da hanzari Khairiyya ta juyo ta ce “Kin tabbata yanzu aka taso?” Cikin sauri ta ce, “Wallahi yaya ba karya nake ba.”
“Ai shikenan amman dai kullum ina faɗa muku kuji tsoron Allah ku rike maraicinku. Ki je ki cire kayan ki zo ki tayani wankin nan.”
*****
Tun zuwan Faruk bai kuma zuwa ba yau kwana wajen huɗu kenan duk Ummu ta damu ita kanta har mamakin yadda ta damu da shi bacin ba wani sabo suka yi ba.
Tana mamakin yadda take jin indai har shine zata iya yadda ta yi aure duk da cewar tana tunanin ƴan ƙannenta.
Tun ɗazu ta kasa bacci hirarsu dashi take ta tunowa zumbur ta tashi zaune daga kwanciyar data yi ledar da tunda taso ta aje bata kuma bi takanta ba wato wadda ya bata ta janyo.
A hankula ta hau buɗewa dan karta tashi ƴan biyu dan Muhammad nauyin bacci ne da shi in ba huɗu tayi ba ya tashi shan koko baya ko motsi in ta kwantar da shi.
Alawowi ne masu tsada sai kwalin waya samsumg juya wayar ta hau yi duk da cewar bata san kan wayoyi ba anman idanunta da kyan wayar sun sa tasan mai tsada ce.
Ta kusa minti biyar tana juya wayar kamin zuciyarta ta angizata ta buɗe kwalin.
Da alamu ansa wayar acaji sai dai kana gani kasan sabuwa ce dan ko ledar sama ba’a ɗaye ba.
A hankula ta kunna yayin da tahau dube dube babu komai akai bata fi minti biyu da kunnawa bs kira ya shigo.
Ido kawai ta bi da wayar har kiran yakatse kamar tare suke wani kiran ya shigo a hankula ta ɗaga da sallamarta Assalamu alaikum rana ta farko kenan da zamu ce Ummu ta taɓa ɗaga waya kuma cikin dare.
Ta ɗayan ɓangaren sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya amsa sallamar. Faruk kenan tun zuwansa gidan su Ummi tafiyar gaggawa ta sameshi dole ya tafi duk da zuciyarsa da ruhinsa tattare yake da yarinyar da shi da kansa mamakin yadda ya mato kan karamar yarinya yake.
Shi ne sai yau kika ga damar duba kyautar tawa ko ya faɗa a shagwaɓance yadda ya yi maganar duk sai ya bata kunya.
Ummu mutun ce mai kunya da rashin son magana sai dai Faruk ɗan duniya ne da yasan salo salo na tafi da mata tuni ya yi amfani da salon sa wanda yasa duk rashin son maganar Ummu sai da ta biye masa.
Da kyar ya haƙura yabarta ta yi bacci dan shi inta shi ne ta yi ta magana yana ɗaya daga abinda yake so da ita shine sanyin muryarta gata kuma Allah ya mata hikimar zance kamar kamar me.
*****
Cikin ƴan watannin da Ummu ta yi da Faruk tuni ta gama kamuwa da sonsa ga wata shakkarsa da take kai ka ce matar sa ce dan ko kaɗan bata kaucewa maganarsa.
Tuni sun gama tsara batun aurensu dan kuwa har batun ƙannenta yasan dasu inda kuma ya amince zai zame musu uba kamar yadda ta zame su uwa wannan yasa Ummu ta ƙara sonsa girmansa ya kuma ƙaruwa a idanunta.
Abu ɗaya ke bata haushi dashi shine wayarsa ko yaushe yana duba waya ita faɗan da take masa ma shi ne idonsa anman ko zuwa gida ya yi kamin ta fito sai ta yi magana da karfi ko ta ɗan taɓa shi hankalin sa zai dawo gareta dan ya lula duniyar waya.
Suna zaune suna hira yana shan lemon da ta yi masa wanda yake masifar so dan kusan duk sanda zaizo sai yasa ta masa dan yana masa daɗi.
Ya ce “Albishirinki” ta ce “Goro jiya Abbanmu ya dawo na masa magana ya amince shida Momi sun ce ma kawai in aka ɗaura auren sai mu tare a gida sabida su Muhd.” Daɗi ya cika Ummu ji take tamkar ta rungume shi sai dai ina ba wannan damar tama kasa magana sai murmushi take zubawa.
Lalle ma yarinyar nan shikena faɗa miki magana zaki hau taƙe ko kajika tsaya kaga yau zan nuna ma ina cikin farin ciki.
Hannu tasa ta ɗauki wayarsa, let have selfie ta ce,
Burin Faruk ne kamar yadda tasani suyi selfie tare kullum sai ta ce ina sai babban abu ya zo. “Buɗemin” Ta ce, nuna mata fuskarsa yai alamar face lock ne ta haska yasa not recognize yace ok “Three full zero” tana sawa waya ta buɗe inda video ɗin da ya tsayar ta ci gaba.
Sakin wayar da Ummu ta yi ne ya tuna masa da yaufa asirin sa ya tonu wato porn video ɗin da ya kan kallo Ummu ta fito ya sa pause suka hau hira shi ta gani.
Girgiza kai kawai Ummu ta yi ta suri Muhd daga cinyar sa ta yi cikin gida inda ya hau kwala mata kira ina ta yi ciki.
Ranta a ɓace ta shiga gida tama kasa yin tunanin da yake dai dai. Wayar ta da ke hannunta ce ta hau ruri alamar kira, tasan Faruk ne kashe wayar ma ta yi baki ɗaya takai ta ɗaki ta aje cikin kayanta.
Aikinta ta cigaba yayin sauran ƴan uwanta keta hira. Shiko faruk iska ya kaima naushi, cike da takaici inda ya ɗan mari goshinsa, ya jima agurin kamin ya iya tafiya gida, ba tare da sanin me zaiyi ba.
Koda dare ya yi kasa bacci Faruk ya yi ransa fal tunanin Ummu, tare da kewar muryarta dan ya riga ya saba jin sanyayyiyar muryarta, dan kullum dare kamin su kwanta sai sun sha hira.
Wayarsa dake yashe saman gado ya kai hannu ya ɗauka, inda ya hau kiran Ummu da yai saving da Abokiyar rayuwata.
Sai dai kamar ɗazun wayar a kashe take. Ya Allah, ya faɗa inda ya miƙe yana kaikawo a ɗakin nasa, cike da tunanin yadda zai shawo kan abin, mai zai faɗa mata yake tunani, sai dai kamar an toshe masa kwakwalwa ya kasa tunani mai anfani.
Kamar Faruk, Ummu kasa bacci ta yi itama bayan ta gama komai, mai makon ta kwanta sai ta hau nin ke kayan da suke daman a ninke suke.
Koda ta gama wayar ta da ke gefe tajawo ta hau kallo kamar ta kunna sabida yadda take kewar muryar Faruk anman zuciyarta ta haneta.
Haka ta maida wayar ta koma gefen da ƴan biyu suke ta gyara musu kwanciya, ta koma ta kwanta duk da cewar idanun nata a bushe suke kamas babu alamun bacci a tattare da su.
Abinda yafi tsaya mata shine wato tun farko ko yaushe da take ganin Faruk na maida hankali a waya abin da yake kenan, ada tayi zaton ko chatting yake ashe kafi chat matsala yake.
Batasan sanda Bacci ya ɗauke ta ba, sai kukan Muhammad ta ji, wato ya tashi shan kokon sa lokacin ana kiraye kirayen sallah na farko.
Sai da ta bashi kokon ya shanye, sannan ta mai da shi ya koma Bacci, maimakon ta koma bacci kayan fanke ta fara haɗawa dan yanzu shida ma ta fara suya, dan ana ciniki sosai ya bunƙasa, tun kan su buɗe ƙofa ake fara zuwa, tuni ƙullin ya tashi, komai ta kai soro inda ta dawo cikin gida dan ɗora abincin kari na ƴan makaranta su Aisha.
Kamar yadda ta saba bayan sunyi sallah ta ɗora mai dan toya musu nasu fanken, inda su kuma suka koma bacci sai shidan ta tashe su.
Yau komai take yinsa kawai take, duk da batajin yanzun zata iya auren Faruk, anman tana jinjina rayuwarta babu shi, sabida yadda take jinsa aranta ta sani tana sonsa sai dai ba irin mutumin da take fatan ya zama abokin rayuwar ta bane, dan batajin zai iya yima ƙannen ta da yaran da zasu haifa isasshiyar tarbiya.
Kusan da sassafen Faruk ya shirya koma gun aiki bai je ba, sai gidansu Ummu, tana zuba fanke ta hange shi sai da gabanta ya faɗi ta daure tamkar bata ganshi ba.
Yayi kyau sosai ga haiba da ya ƙara, kamar ko yaushe manyan kaya ne ajikinsa wanda suka amshe shi.
Bai yi gangancin matsawa ba, daga nesa ya tsaya dan yasan bata wuce tara da zummar da zarar ta tashi sai ya ƙarasa.
Ilai kuwa tana gamawa yana ƙoƙarin ƙarasawa, ta yi gida da sauri sai su Usaina ne suka zo suka shigar da kayan, jigum yayi kawai ya jima a gun kamin ya koma motarsa dan barin gun.
Kai tsaye office ɗin Umar ya wuce ya yi sa’a baya komai hakan yasa sakataren sa ya masa iso ya shiga.
“To lafiya dai na ganka kamar an jefoka?” Umar ya tambaya.
“Bari kawai Umar ina cikin wani hali wallahi,” nan ya bashi labarin duk abinda ya faru. Dariya Umar ya sa, “kace Allah ne yaso ta, ta gane tun yanzu kaga sai ka ƙara gaba tunda dai nasan ba dena kallon abinka zakai ba.
Haɗe rai Faruk ya yi “Kaga Malam banson iskanci ni nace maka bazan dena ba, and wallahi ka dena min maganar rabuwa, na faɗa ma san yarinyar nan nake ba sha’awa ba aurenta zanyi.”
“To na ji yanzu ni me kake son in maka?” Umar ya tambaya yana kallon Faruk.
“Yawwa ɗan gari yanzu kai magana, so nake kaje ka bata haƙuri, ka tsaran ita ta amince kuskurene kasa ta dinga ɗaukan wayata.”
“Na ji zanje but sai kamin rantsuwa tsakani da Allah ka ke sonta aurenta za ka yi, dan bazai yiwu inje in shawo kanta ba ƙarshe kaje ka ɓata musu yarinya laifin araba mana.”
Tsaki Faruk ya yi in da zan lalata ta da tuni ban yi ba, bana fatan inzama silar gurɓacewar rayuwar Ummu Hani, ita ɗin sonta ajini na yake, burina ta zama uwar ƴaƴa na ta yaya zanyi gangancin ɓata uwa ga yara na?”
“Tom shikenan zanje duk da dai naji ka ne, nasan halinka in kana buƙatar abu gun mace ka iya shirga ƙarya.”
Shiru kawai Faruk ya yi yayin da Umar ke yi masa tsiya, wai duk tsala tsalan ƴan matan da yake buri, da masu sonsa ya ƙare a ƙaramar ƴarinya baƙa kuma.
Sai yanma Umar ya shirya bayan ya dawo daga aiki ya huta ya yi gidan su Ummu.
Koda ya aika cewa ta yi bata nan, sai da ya kuma aika yaro ya ce ace mata ba Faruk bane Umar ne.
Kamar bazata fito ba dan batason wani abu ya haɗata Faruk sai kuma ta canja shawara bayan ta yi wani tunani.
A kintse take kamar koyaushe mayafi kawai ta yafa ta yi waje…