Kusan Ayatullah ya duba duk hotel ɗin ya ke zaton zai ga Yarinyar bai ganta ba, wannan ya sanya ya kuma yadda tabbas yarin yar nan ba mutun ba ce kawai dan ta ga kwana biyu ya maida da hankalin sa kan karatun sa ya cire ta a ransa shi ne take son dole sai ta kuma dawowa cikin rayuwar sa ta hana shi sukuni da wannan tunanin ya fitar da neman yarin yar daga jadawalin sa.
Faruk na kwance kamar kullum Ummu na goge masa jiki da towel bin ta kawai yake da ido ya rasa wannan wacce irin kaddara ce haka gashi dai ga abar sonsa sai dai babu lafiya shi a yanzu bama kansa ya ke tausayi ba sai ita kwata kwata kansa ya kulle ya kasa yin tunanin abin da ya da ce.
A hankula ya ce, “Ummu” ta dago daga goge masa kafar da take ta ce “Na’am Mijin Ummu jiki ya yi” Hawaye na kokarin zubo kasa masa ada ba sunan da yake son jin ta an ba ce shi da shi irin mijin Ummu sai dai ayanzu yanajin aransa jin daɗin sunan ko zama mijin ta tamkar rashin adalci ne gare ta a yanzu yanajin a ransa shi ɗin bai cancanci zama mijin ta ba katse masa tunani ta yi da faɗin mijin ya ɗago kwayar idon sa ya ɗora su akanta dan yanzu su kaɗai ke motsi a jikin sa.
Murmushi ya yi kawai kin san dai ina son ki ko itama murmushin ta yi ta dawi dedai kansa ta rungume kan dan shi kadai ta fahimci in an taɓa yana iya fahimta, ta jima a haka kafin ta shanye kukan ta dan kwata kwata bata son ta karyar masa da zuciya na yin kuka a gaban sa.
Kusan daƙiƙu masu yawa kafin ta koma ta cigaba da goge masa jikin tana masa hira a haka har ya samu ya yi bacci a hankula ta bar ɗakin inda ta saba zama ta nufa kanma ta ƙarasa kuka ya kwace mata.
Shima ɗin Faruk ɗin yana jin fitar ta hawayen da yake riƙewa suka biyo kuncin sa a hankula ya buɗe idanun sa ya juya bisa hanyar fita dan ganin ko tana dawowa.
Kuka ta ke sosai kusan tun farkawar Faruk bata kuma kuka irin na yau ba, a yanzu batasan ma taka mai mai kukan mai take ba duda tasan ba zai wu ce na tausayin mijin na ta ba.
Sallama taji an mata bata ɗauki murya ba wannan yasa ta goge hawayen ta a hankali ta ɗago ta kalli matashin da ke tsaye sanye yake da bakaken kaya sai farar rigar likita a jikin sa Dogo ne sosai kusan zai yi tsayin Faruk din ta kusan ma suna yana yi sai dai Faruk ya fishi haske bai yi kama da ba ture ba sai dai yana yin sa ya yi mata kama da ba bahaushe bane, tunanin amsar da zata bashi ta fara yi da turanci ita da ba wani gwanewa ta yi wajen turancin ba, kamar yasan mai ta ke tunani a hankali cikin nutsuwa ya ce, “zan iya zama?” Ya faɗa mamaki ne ya kamata.
Ba tare da ta bashi amsa ba ta matsa gefe wannan ya bashi damar zama, “Kar kiyi mamaki in ban tambaye ki dalilin kukan ki ba dan nasan wanda ya baro garin su zuwa neman lafiya wata kasar ba abin mamaki ba ne dan an ganshi yana kuka,” Mamakin ta ne ya karu Hausa yake rai rai da alamu bahaushe ne usul.
“Sunana Ayatullah na san ki ko.” Ya faɗa yana kallon ta, girgiza kai ta yi, “A’a baka sanni ba zuwa nan kasar na farko kenan.” Murmushi ya yi ai ba anan nake nufin nasan ki ɗin ba a Nigeria.” Shiru ta yi sai ta yuwu duk da dai banji ni ce ta kuma faɗe a ƙagare.
“Na ta kura miki ko karki damu yanzu zan ta fi ni nasan ki ne a asibitin tara na Kano wataran kin kai yara asibiti.” Shiru ta yi tana tunani, “Watakil ni ɗin ce.” Ta faɗa a takaice.
“Ke ce ma, yanzu waye bai da lafiya?” Kuka tasa ba tare da ta bashi amsa ba da sauri ya ce “Am sorry bawai ina nufin ɓata miki rai ba,” Girgiza kai ta yi “Mijina ne bai da lafiya.” Ta kuma faɗe gami da rushewa da kuka.
Dafe kai ya yi abu buyu ke masa yawo aka kukan da ta ke da kuma kalmar miji ya ma kasa bata hakuri ko lallashin ta shi kansa a yanzu lallashin yake bukata shiru kawai ya yi yana sauraron kukan ta har ta gama sannan ta miƙe, “Ka yi hakuri dan Allah.” “Girgiza kai ya yi kar ki damu insha Allahu Allah zai bashi lafiya ku cigaba da masa addu’a kinji.” “To na gode.” Kawai ta ce ta miƙe tabar gun.
Binta ya yi da kallo mai ke son samuna ya faɗa ta ya ma za’ai haka matar aure ba of all female in the world sai mallakin wani zuciyar sa zata so, ada bai yadda cewar son yarin yar ya ke ba sai kwana biyu nan da ya ganta a asibiti kullun daga ne sa yake tsayawa ya kalle ta yau kukan da take ne ya rinjaye shi zuwa inda ta ke.
Ummu kuwa ɗakin Faruk ta nufa a hankula take tafiya har ta isa lifter ɗin da zata sada ta da VIP section ɗin da Faruk din nata yake.
Daga zirin glass ɗin kofar ɗakin tana iya hango Dady da Mami zaune yayin da kunnen ta ya jiyo mata shesshekar kuka turus ta yi ta tsaya ba tare da ta tura ƙofar ɗakin ba jiyo muryar Faruk da ta yi yana faɗin wannan ita ce kawai mafita Dady.
“Amma Faruk kanajin zaka iya jurewa ga rashin lafiya ga kuma rabuwa da wadda kake so.” Muryar Mami taji na faɗin haka har yanzu bata fahimci mai suke magana a kai ba sai da ta kuma jiyo Faruk na faɗin.
“Ko da bazan jure ba hakan ba zai sa in cutar da ita ba kunaji abinda likitoci suka ce tun asali garin kaini asibiti masu ɗagani sun yi kuskure bazan warke ba ko mai gashin da akayi ta yaya zan rufe ido in ce zan zauna da ita, ita din yarinya ce tana buƙatar namiji yanzu ta fara rayuwa dole in mata adalci ina sonta anma ina tsoron hukuncin da Allah zaimin na barin ta da aure na doke in sawwake mata wannan nauyin.” Ya faɗa gami da rushewa da kuka.
Mai kuke tunanin zai faru?