Skip to content
Part 37 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Aisha tashin hankalin ta kullum karuwa yake musan man yau da wanda tasa su dunga biyar Ayatullah din suka turo mata da hoton sa da matar tasa haushi ne ma ya kamata ganin yarin yar da ya aura gata karamar yarinya gata kucaka dan ita kam gani tayi ya cuceta da ya auro wannan bakar yarin yar wannan in kawayen ta da fans din ta suka gani ai sai su mata dariya duk cikarta da ajin ta ace mijin ta ya barta kan wannan, ita dai bata ga kyau a yarinyar ba.

Ana gama shooting ta fito daga gurin a burkicen da take a haka ta yi niyyar tafiya Kano Balkisa ce ta hau yi mata faɗa, “haba Aisha ai sai ki bamu kunya yanzu fisabilillahi in yan blog da fans suka ganki a haka ai sai su yaɗa kin haukace.” Hararar ta Aisha ta yi “to su yi ko me zasu yi ma masana’antar da nake shirin bari mene dan an yi maganar tsohuwar jaruwama.” dafata Balkisa ta yi, “Eh duda haka anma dan Allah ko danni da ban shirin barin ta ba ki daure ki je ki shirya kinji Aminiyas.” Tsaki Aisha ta yi gami da kwafa shikenan ta shige ɗaki har lokacin ranta kuna yake.

Kai tsaye daga hotel din da sukai aikin film din filin jirgi suka rankaya a jirgin ma Aisha mita kawai take ji take tamkar taje ta buge Captain din ita taja  jirgin. Suna isa Kano kai tsaye centre din da ake bikin su Ummu suka wuce dan tana da information din komai na bikin, masu gadin gurin ne suka hana su shiga Bakisa na buɗe fuskar ta suka hau murmushi ah ranke dade kune Aishan ma buɗe fuskar ta yi nan suka ruɗe dan mutane sun fi son Aisha sun kuma fi son ganin ta, Aisha ce ta ce bikin cousin ɗina ake mun kuma manta da katin mu, murmushi Mai gadin yayi banda abin nayi zato sunan da mutane suka san ta dashi kenan sabida shine Film ɗin ta na farko ai fuskarki ma gate pass ce Allah ya sanya Alkairi bata ce Amin ba ta shige ciki hasalima a ciki cewa tayi Allah dai ya tarwatsa auren nan ita bata taɓa ganin bikin da aka wani daura aure kan ayi shagalin biki ba.

Tuni ido yai gun Aisha mutane na faman murnar ganin yar film har wasu na kokarin hoto, yayin da ita kuwa Aishan haushi ne ya kuma cikata hango Ummu hani suna raɗa da Ayatullah, ta kuma raina yarinyar data ganta a yanzu suda cewar yanzun tafi a hoto kyau anma ita tasan tafi yarinyar nan komai tafi karfin kishi da Bahaushiyar mace sai dai Balarabiya. A fusace ta matsa gurin tako dago ummu hani sai dai ta kasa taso ta tsaye dan ummun bata miki ba sai cikin zafin nama ta wankawa Ummu mari tana faɗin ke wacece yau she aka yi ki da zaki aurar min miji, sam ummu bata yi zaton Ayatullah Saurayi bane duda basu taɓa maganar ba dan hirar duniya kawai suke haka kuma ita a rayuwar ta tun mutuwar iyayen su ta maida hankali gurin neman kuɗi bata kallo batasan wasu celebrities ba dan haka har cikin ranta kawai wannan din matar Ayatu ce take kishi wannan yasa ta rasa abinyi ta dafe kunci kawai.

A fusace Ayatullah ya mike ya kwashe ta da mari har sau biyu tako dafe gun tana harar Ummu gami da jijjiga cikin fushi Ayatullah ya ce ke wacce irin shasha shace maras hankali da zaki zo har gurin shagalin bikin yarinya ki ce zaki mareta, cikin tsiwa da ko in kula ɗin marin ta ce Ayatu ni kake cewa shashasha? An faɗa din da ke mece in ba jaka dabba… Ummu ce ta dafe masa baki a’a mijin Ummu bansan ka da zagi ba ka kyale antinnan tamu kishi ke damun ta, Haushi ne ya cika Aisha wato ma Anti me yarinyar nan take nufi ni tsohuwa ce ko me.

Bazan kyaleta ba wallahi ba wata yar iska da zata zo ta cimun mutunci nida matata babu ita ya fada yana huci lokacin yana kokarin dauko wayar sa sa zummar kirawo police, yayun Ayatullah ne suka matso kusa sun san shi da zafin rai Mardiyya ta amshe wayar insa su Anti murja suka janye Aisha dakyar. Hakuri kawai yake bawa Ummu yana shafa mata kuncin yana faɗin anma dai ba zafi ko dariya ta yi ina wani zafi a mari ɗaya dama baka kulata ba wallahi. Girgiza kai yayi kawai ya watsar da batun Aisha din.

Cikin wasu ƴan mintinan da basu biyar ba har batun ya karaɓɗe social media kowa na faɗar albarkacin bakinsa kan abinda Aisha tayi ɗin yayin da wasu ke zagin Ummu suna faɗin tayi snatching ɗin saurayin Aisha yayin da wasu ke cewa karshan tama asiri ta masa dan taga mutun mai kyau in ba haka ba me zaiyi da ita ai ya fita kyau da komai, kaɗan ke faɗin ai babu namiji na gari da zai zaɓi mace irin Aisha duk kyanta.

Lokacin da ake fitar da Aisha yayi dai dai da parker motar su Faruk a harabar gun ba wani dogon bayani aka barsu suka shige dan kuɗi Anti Ummi ta miƙawa mai gadin Dady shi yake tura Faruk ɗin a kan kujerar sa, Sanye yake cikin kananan kaya dan ko tsayawa a shirya shi bai ba dan ya ƙagu yaga yaran nasa da har sun fara tafiya bai san dasu ba, suna shiga da Ummu ya fara tozali zaune kusa da wani kuma wai matsayin amaryar wani abu biyu ne suka taso masa kishi da tausayin kansa sam ɗazun ya manta da cewar ya yima kansa alƙawarin fita daga rayuwar Ummu fita ta har aba to yanzu me nazo yi, ɗagowa ya yi ya dubi Dady yace dan Allah dady mu koma na fasa ganin nasu.

Girgiza kai Dady yavyi sabida me ai tunda munzo kawai mu karasa kuka yasa mu koma Dady in muka je bamuyima Ummu adalci ba na bar mata yaran, ganin yana kuka da tunawa da dady yayi ko ya hankalin sa ya tashi jikin sa rikicewa yake yasa Dady ya juya, Ummu dake zaune ranta babu daɗi taga shigowar su dady ta kuma ganshi taga na kujerar anma sai take tunanin anya ba gizo bane har ta basa ta mike lokacin da taga sun juya ta bisu a baya Ayatullah ya bita da sauri tsoron ko abinda Aisha ta mata ne ya tunzura ta riƙo tan da yayi ta baya yasa ta dan daga murya ta ce Faruk..

Dady yaji haka ma Faruk Sai dai Dady na tsoron abinda zai samu Faruk in suka tsaya gaba yayi da sauri yayin da Ummu hani ta dubi Ayatullah dan girman Allah ka barni Baban su Umar na gani, tsoro ne ya kama Ayatullah shidai yasan tsohon mijin ta mutuwa ya yi amma yadda yaga ta yi yasa shi faɗin shikenan muje tom muje tare. Anti Ummi da ta hango mahaifin na su da Faruk da hanzari ka karasa Abba mai ya faru kunga yaran kuwa muje kawai in munje gida kyaji komai batai musu ba ta mara musu baya.

Koda Su Ummu u suka fito harabar gun  nemar Faruk da Dady tayi ta rasa ita dai tasan tabbas ba gizo suka mata ba tsahon minti kamat ɗaya ta jiyo da hanzari ko me ta tuna oho ta kamo hannun Ayatullah dan Allah kamin alfarma ka kaini gidan su Faruk dan Allah, a nutse ya ce Ummu ki daure ki nutsu bafa su kika gani ba, girgiza kai ta hauyi dan Allah ka min alfarmar nan, bikin fa… Kan ya karasa ta kuma katse shi da cewa dan Allah. Nunfashi ya furzar ba tare da dogon tunani ba ya ce muje motar sa suka nufa suka bar gun.

Kai tsaye gidan su Faruk suka nufa kusan kamar tare suke dan gudu sosai Ayatullah ya yi cikin sa’a kuwa Faruk na falo ba’a tura shi ɗaki ba lokacin da suka iso gidan, cikin kuka Ummu hani ta karasa gunsa tana faɗin Faruk kaine dama kana raye shike ka gujemu nida yaranka ka mana adalci kenan kukan ta kuma fashewa dashi gami ga dora kanta jikin keken nasa tana rusar kuka mai tsuka zuciya.

Ayatullah ji yake tamkar ya karasa ya rarrashe ta kukan nata har cikin ransa yayin da shi kuwa Faruk dauriyar da yake ce ya kasa hawayen da yake rikewa ne suka fara zarya a fuskarsa yau ga Ummu da wani mijin bashi ba, yau ga Ummu na kuka duk yadda zaiyi bazai iya ɗaya hannun sa ya share mata hawaye ba, ranar da ya guji gani kenan ya gwammaci ace ya mutu da ya ganta.

Cikin hanzari Ummu ta mike tayi gurin Ayatullah hannunsa ta riko tayi kasa cikin yanayi na roko tafara faɗin dan Allah Ayatu ka taimaka ka dubi girman Allah ka sakeni ni mijina nake so, kome ta tuna ta miƙe koda yake bai sakeni ba dama koda munje kotu cewa zatayi in zaɓa toni shi nake so shi na zaɓa, girgiza kai Ayatullah ya hau yi Ummu karki mun haka dan Allah, in kika zaɓi wani na bakimun adalci ba.

******

A can wurin biki kuwa bayan an fidda Aisha tana ta sirfa masifa yan uwan Ayatullah ne suka hauta da masifa ta zo ta bata musu biki da tana sonsa ta gudu ta ki auren sa Umman ta dake gun bikin ce ta zo ta shigar mata dakyar manya suka sa suka bar gun bikin yayin da  Umman Aisha din keta faman kunfar bakin wallahi yaran sai sun yi dana sanin ci musu mutunci da sukai kai tsaye gida taja Aisha da ke faman kukan wai an cuce ta dan me za’a wa Ayatullah aure bayan ansan suna soyayya.

A gida Kawu na kwance yana jin Radio matar tasa da diyar tasa suka iso sai faman faɗa umman take hankali ta she yake tambayar lafiya mai ya faru cike da zafi take faɗa masa ƴaƴan wan sa ne  suka ci musu mutunci a fusace ya miƙe sabida me mai kuka musu sai a lokacin ya kula da Aisha Umma ta ce wai dan Aisha tazo gun bikin tana faɗin ita ba’a kyauta mata ba an aurar da mijin ta.

Ajiyar zuciya yayi au ai dole suyi mata koma mene badai ta zaɓi shahara ba sai ta je ta auri shaharar, kuka umma tasa yanzu kaima Malam abinda zaka ce kenan yar kace fa yanzu in duniya taji jinin ka yaki auren ta wa kake tunanin zai aure ta, shiru yayi shikenan gobe zanje in samu shi yayan a daura musu auren in yaso tazo a ta biyu.

Kwabe fuska tayi ni wallahi bazan zauna da kishiya ba kafin Malam ya bada amsa Umma taja ta ciki tana faɗin to sai aka ce miki zaman zakiyi da ita kedai adaura din yadda na zauna ni ɗaya kena ke ɗaya zaki zauna.

A gurin biki kam an nemi ango da amarya an rasa kan kace mene wannan biki ya watse yan uwan ango suka nufi gidan da ango zasu tare zaton su ko tafiyar su sukai can sai dai gidan ba alamun anma zo shi a satin nan, suma su Aisha sai gida suka nufa dan zaton su Ummu ko can tafi sai dai gan yadda suka baro shi a kulle ahakan suka barshi.

Hankali ya tashi ga Faruk karami da Muhammad sai kuka suke wayar Ummu bata shiga kiran wayar gidan su Ayatullah sukai nama basa nan tuni hankali ya tashi dan zaton mutane ko Aisha ce tasa aka sace Amarya da ango, yayin da Aisha ke gida suna kitsa yadda zata mallake Ayatullah tuni batin ta sa ce Amarya da ango ya kuma yaɗuwa a social media cikin wasu lokacin da baifi awa ɗaya da yaɗuwar zuwan ta gun bikin ba sam bata da masaniyar meke wakana wayar ta da ake ta kira yasa ta ɗauka duda ba ɗabi’ar ta bane daga waya cikin faɗa take faɗin wai mene Muryar ɗan jaridar taji yana faɗin yawwa Hajiya Aisha zamuso jin ta bakin ki shin da gaske ne ke kika sace tsohon sairayin da budurwar da zai aura.

Zumbur ta miƙe wanne tsohon saurayin nawa kuma ta faɗa aɗan ɓacin rai, wanda ɗazun kika je kika rikitarwa biki, cikin fushi take faɗin ni wallahi na tsani sharri naku na ƴan jarida sabida mene zanje sa ce shi mtsss taja tsaki kafin ta kashe wayar, mita ta hau yi tana faɗin ni matsalata da mutane sharri wallahi yanzu inba inkancin banza ba  ta ina zan sace wani ma bare wanda nake so, Umma ce ta riƙo hannun ta kinga kyale so zo kiji.

Malam yana zaune inda su Umma suka barshi motar yan sanda ta faka a kofar gidan yan uwan Ayatullah ne suka fito cikin mutunci suka gaida shi Babbar yayar su Ayatullah din ce ta fara bayani dama kawu Aisha ce ɗazun tazo ta hargitsa bikin Ayatu hakan bai ishe ce ta ba sai da ta sa aka sace shi harda matar tasa, salati kawu yasa yanzu cin mutuncin naku da kukai mana bai isa ba shine har sai kun kawo hukuma wato dole sai kun nuna min ban isa ba ko.

Girgiza kai Anti Maryam ta yi no wallahi kawu ba haka bane kowa yasan Aisha zatayi abinda muka ce dan haka muka zo in ta faɗi inda suke shikenan, police ɗin ce ta matso kusa kaga dattijo aiki muka zo ba ɓata lokaci ba tana ina? Masifa ya hau yi ko ta kansa basu ba yan sanda matan suka shiga ciki.

Sosai Umma taji tsoro dan ita kam ta tsani sabgar yan sanda rantsuwa ta hau yiwa su Anti Maryam wallahi tunda suka tawo Aisha bata fita ba kuma bata kira kowa ba, dakyar su Anti Maryam sukai convincing ɗin police ɗin suka tafi ba tare da A’isha ba dan cewa sukai dole sai sun tafi da ita tunda ita ce suspect mafi karfi.

Kan su Anti Maryam su fito kawu ya wuce gidan yayan nasa rai a bace yana zuwa ya hau kuka shikam an tozarta shi ace shi ƴaƴan cikin sa zasu ɗaukowa police, Abba ya yi ta faɗa dan shi baima san sun je gidan ba ya cewa kawu yayi hakuri zasu zo shima su bashi hakuri kuma tinda abin nasu haka ne tunda Aisha ɗin ta dawo gobe jibi ran juma’a za’a ɗaura mata auren da Ayatullah ɗin yaga ta tsiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 36Ummu Hani 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×