Skip to content
Part 24 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Mama na kira muka gaisa ta ce jiya ta yi ta kira na ba ta shiga na ce ƙila network ne.

Na kira Lubna da Hassana da Aunty Ya gana suma duk complain ɗin ɗaya ne.

Na gama wayar ya miƙo mini hannunsa

ya ce mu je mu yi break past kai na girgiza na ce ni a ƙoshe nake ya ce to in raka shi ban son ko ganin su Amal amma na bi shi a tsaye jikin ƙofar da za ta sa da ka da Main parlor dukkan su suke tsaye kowacce da shigar nasara kai a buɗe ya sha gyara feak dukka ya ba su suna gaishe shi Amal da Suhaima suka yi saurin sanya shi tsakiya suka wuce na bi su a baya, sai na ji ba daɗi yau da Dina ba ta ce mini sannun da ta saba ba ashe wai ita ma ta ji haushi da aka ba ni ɗakin Mamansu, sun riga sun mamaye kusa da shi sai na zauna kujerar da ke gefen Dina don ita ta zauna wadda ke fuskantar sa su kuma suka sanya shi tsakiya suna hirar su har ya kammala ina kallon abin da suke cin turawa manya na faɗi a hankali, agogonsa ya kalla ya ce fita zai yi ni ya kalla ya yi maganar sai na yi saurin tashi dukkan su cin magani suka yi suka ce mishi sai ya dawo muka fita.

Tare da Iliya Direba aka zo kuma shi zai ci gaba da jan shi, ya gaishe ni cikin girmamawa Bashir Lema ya buɗe motar ya shiga bai rufe ba ya zuro ƙafarsa ɗaya waje ya ce  “Ki turo list na abin da kike so wanda za ki dinga ci, za a kawo miki.”

Na ɗaga mishi kai, ya shigar da ƙafar na rufe mishi ƙofar ya ce “thanks.  Ya ɗaga mini hannu ban yi murmushin da na saba yi mishi ba na juya.

Kallo ɗaya na yi ma su Suhaima na kauda kaina dariya na ji sun kece da ita suna maganar ji wata riga kalli wani dressing sai su kwashe da dariya da na shiga bedroom ɗina na zura ma kaina ido a madubi ban ga ƙauyanci ko kalar gidadawa a dressing ɗina ko ina yin na ‘yan ƙauye sai da ta yi dariya ta ce wane irin na yan ƙauye? Ke ma kin san yadda kike shan kallo idan har ba ki zunduma hijabin nan naki ba har ƙasa.”

Na ce “Ba wannan ba, kayan da nake sanyawa ya suke mayar da ni? Ta ce “Wai me ya faru ban gane tambayoyin nan ba ?

 Na ba ta labarin dariyar da su Amal ke yi ma dressing ɗina mummunan tsaki ta ja “Oh ke dama maganar waɗannan kika tsaya biye ma wa?

“Na ce “To na ga su ɗin wayayyu ne ƙarshen ta ina kwafsawa ni ce ban sani ba.”

Ta ƙara jan wani tsakin  “Wayayyu ko ‘yan  iska ki yi sabgarki kawai ki manta da su duk tsiya dole su gan ki da ubansu kina da damar da duk yadda suka kai ga tsiyatakun yana son su kin sha gaban su ke ce z… Wayar na katse ina girgiza kai don na san ɓaro ta za ta yi.

Knockin na ji ana yi na tashi na buɗe Easter ce sai da ta gaishe ni ta shaida mini ta zo gyara mini wuri ne na ce ta bar shi kawai, godiya ta yi ta juya na kulle ƙofar na koma.

Data na kunna na shiga facebook wani posting da na gani zauren fiqhu sun yi ya ja hankalina bayani ne kan salatut duha da falalarta take na ɗaukar ma kaina zan kasance cikin masu yin ta matuƙar ina da lafiya.

Alwala na miƙe na je na yi bayan na sallame na yi addu’o’i na karanta Alkur’ani mai girma zuciyata na ji ta daɗa yin sanyi daga sauran ɓacin ran da ya yi  mini ragowa.

Na tuɓe hijab ɗin na adana shi  na zauna na zura ma TV da ke aiki ido ita na yi ta kallo har na samu wayarsa dariya yake mini kan list din da na tura mishi ya ce ashe in yi shirin cin abinci don yana son abincin gargajiya zaman Turai ya sa ya haƙura sai idan ya zo, ya ce mini sai yamma zai dawo tare da kayan.

Muka ajiye waya ƙarfe uku cikina ya matsa mini da neman hakkinsa ba ni da zaɓi fita na yi suna zaune a Main parlor sanin ba abin da zan samu a kitchen na nufi dinning area na buɗe kwanuka jallof ce ta shinkafa da ta ji ganye sai kaza na ɗiba daidai yadda zan ci na zuba na zauna salaf na ji da ya sa ni ajiye cokalin na yi jugum ina kallon agbincin  shar-shar gwanin

ban sha’awa a ido a ido tuna yaji da Aunty Larai ta aiko mini cikin tsarabar da ta haɗa mini ta sa na tashi, kitchen ɗin na koma na fara duba kayana da safe ban gan su ba har na fara tunanin inda suka watsar mini da su, a wata drawer na gan su daɗi ya kama ni ko banza zan dinga dama kunun gyaɗa ina sha na ciro yajin na mayar da kayan na fita.

Inda na tashi na zauna na zuba yajin na ci abincin gwanin daɗi sai da na ƙoshi na tsiyaya lemo na sha na tashi na ƙara wuce su suna dararrakinsu da zantukan su na iya shege a kaina.

Kaɗaici ya sa na yi ta kiran waya daga Haj zuwa su Baba Isah Aunty Larai Aunty Ya gana.

Yamma liƙis na sake wanka da kwalliya cikin riga da skirt ta material na rufe kaina da ƙaramin veil takalmi flat ne a ƙafata ina tsaye jikin window na hango shigowar motarsa na fita a gaban idona motar ta tsaya ina naɗe da hannayena sai da Direban ya fito ya zagaya ya buɗe Gate shiru da na gani bai fito ba na matsa na buɗe ƙofar, takardu ne akan ƙafarsa yana dubawa murmushi ya tada kai ya yi mini na mayar masa sai ya miƙo mini hannu na kwashe takardun kan ƙafar ta sa sai na miƙa masa ɗayan hannun ya kama ya fito, feck ya ba ni a kunci ya tambaye ni yadda na wuni na ce lafiya muka wuce ciki.

Yadda suka saba tahowa tarar sa yau zaman su suka yi hannu kawai suka ɗaga mishi Amal da Suhaima Dina da ta taso ta tare shi ya riƙe ta a gefen sa ni dai da na ga ya kama hanyar zuwa inda suke tsayawa na yi ya isa duk ya ba su feck sannan ya dawo inda nake muka tafi ciki.

Sai da ya kintsa ya ce mu je na ga kayan da aka kawo mini muka fita kitchen ɗin muka shiga ta cikin sa kofar store take muka shiga  na duba komai na ce ya yi muka dawo kitchen ɗin kalolin nama da dama akwai ya ce zan iya amfani da su na ce to, ya ce  to me za ki yi mana yanzu?

Fuska na ɓata na ce yanzu namijin nan zai shigo ina ciki yana ciki.

Ya matso inda nake  “Ki yi aikinki yana nashi ba ruwansa da ke .

A raina na ce Kash!  Don ni so nake ya gane muhimmancin addini kullum ina cikin tunanin yadda zan ɓullo mishi ya fahimci koyarwar addini ya jingine ɗabiun yahudu da nasara.

“Ki yi aikinki Baby daga ba ki son na shi da an samu mai aikin shi kenan.”

Na ce “Ka bar mai aikin zan dinga yi kaina”

Ya ce “Kin tabbatar za ki iya? Na ɗaga mishi kai ya ce “Good.”

Nan ya fita ya bar ni ina ta tunanin me zan mishi in burge shi na ga da daddare bai cin abinci mai nauyi alale nake son ci amma ba ni da tabbacin ko zai ci na bar ta sai gobe, tuwo na yi shawarar yi kuma sai ya ci in ga ƙarshen tsiyar ya’yansa masu ɗaukar kansu turawa.

Miya na haɗa da ta ji kayan haɗi an sawo mini ɗanyar kuɓewa da na rubuta, ina aikina Peter ya shigo ya gaishe ni ya kama aikinsa na gama haɗa miyar na ɗora tuwon semo, sai da na gama ƙulla tuwon kulli uku kawai na yi na rage wutar miyar na fita yin sallar magrib na shiga ya gama alwala zai yi Sallah kamar in ce ya je masallaci an fara sai kuma wata dabara ta faɗo mini na yi shiru muka yi sallar ya riga ni idarwa ya fita wurin yaransa.

Da na idar a dakin na zauna sai da na yi isha’i na fita ba kowa a Main parlor sai Easter tana goge wuri na wuce  a raina ina yaba rigimarta gyaran duk wannan gidan ita kaɗai duk da dai kusan komai da na’urori take yi kuma inda ni zan raba aikin shi Peter da yake namiji sai ya yi gyaran gidan duk da shi ɗin ma ba aikin maza ba ne ita kuma sai a bar ta da girkin.

Na damu miyata ta yi na zuba kuɓewar na ba ta lokaci da ta yi na zuba na haɗa komai na fita nan Main parlor din na zauna ina jiran fitowar sa, Amal ta fara fitowa sai Dina da Suhaima suka fito karshe suka nufi dinning shi ya nuho wuri na na ce na gama ya yi murmushinsa ya ce  “Mu je to in ci. Yau zan ci girkin baby.”

Na tashi muka tafi sai da ya zauna  na tafi na ɗauko tray da na shirya abincin na dawo bai fara cin komai ba yana jirana duk da an zuba mishi ina ciro tuwo na saci kallon fuskokinsu taɓe fuska dukka suka yi na zuba miya shi kansa akwai alamar mamaki a fuskarsa amma bai yi magana ba ya fara ci na sanya daya ni ma na ci, na sha lemo da na haɗa shi ma na zuba mishi.

Ina miƙewa kuma shi ma ya miƙe ya biyo ni muka tafi.

Muna shiga wayata na ɗauka ya ce “Kin ga fitar da na yi ta mantar da ni mu fita a canza wayar, amma ki yi mini haƙuri za a canza.”

Na ce “Na gode.

Wa’azin marigayi sheik Jafar Mahmud Adam ya yi kan rayuwar musulmi muryar malamni na kwararowa cikin fasaha da balaga da tsananin fikra da Allah ta’ala ya yi ma malamin baiwa da shi.

A kujera daya muka zauna yana ba ni labarin fitar da ya yi wurin wani tsohon abokinsa da suke tare tun farkon zuwan sa London yanzu ɗan majalisa ne na gwamnatin tarayya tun kafin ya dawo yake so shi ma ya shiga siyasa ya fito takara amma shi bai da ra’ayi ya dai ba da gudunmawa ta kuɗi har abokin nasa ya haye  yanzu ya kira shi kan wata kwangila da yake so ya yi masa hanya mai girma Gwamnan Kaduna ya ba shi  ta kai wuta a wani yanki na ƙauyukan jihar.

Na yi masa murna da fatan alheri.

Tun muna magana a hankali sai na ji ya yi shiru yana sauraren wa’azin raina ya tumbatsa da farin ciki da kuma wannan wa’azin ya ƙare wani ya shiga shi ɗin ma na sheck Daurawa da yake yi kan haƙƙokin iyaye akan ya’yansu da tarbiyyar yaya, nan kam har na tashi na fara shirin barci ya taso da wayar a hannu ya ajiye ta bisa gado har muka gama shirin kwanciya muka kwanta kaina na kan ƙirjinsa yana shafa gashin kaina na rufe idanuna na ce barci nake ji ya ranƙwafo da kansa daidai fuskata yana tambayar me na ce na ce barci. Kafin ya yi  magana wayarsa ta yi ƙara ya kai hannu ya ɗauko ta sai da ya cire maganar tawa wayar sai ya amsa jin da mace yake wayar sai na yi fakare ina son gane wace ce.

“Mota kike so don na saya ma su Dina sai na saya ma Khalil?

Ya yi shiru cikin saurare kafin ya ce  “Khalil namiji ne yana da kuɗaɗen da zai sayi mota ko ban saya mishi ba.”

Ya ƙara yin shiru kafin ya ce  “Mota ce dai matsalar? Sai ya dawo zan saya mishi shi ma.”  Ya kashe wayar ya ajiye ina tunanin matarsa ce mahaifiyar su Amal saboda sunan Khalil da ya ambata wanda na san sunan ƙanenta ne da take ruƙo. Amma ina zai dawo na tambayi kaina, na daɗe ina saƙe-saƙe kan matar tasa da na samu kaina da son ganin ta in ga yadda take, barci da ya yi awon gaba da ni ya katse mini tunanin.

<< Ummu Radiyya 23Ummu Radiyya 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×