Skip to content
Part 33 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Tun ina jin kamar wasa har na fara juyi ina faɗin wash! Ya tambaye ni na faɗa mishi bai tsaya wata-wata ba ya sa ni na ɗauki lulluɓina muka fita yana faɗi masu ba ni da lafiya hospital za mu Suhaima da Amal da ke jikin motar Amal za su fita Allah ya gwada mini wani murmushi da Amal ta yi.

Mun isa asibiti likita mace ta duba ni bayan bincike da gwaje-gwaje sun samu nasarar tsayar da jinin da ya soma zuba da murɗawar cikin, likitar ta ba da tabbacin na sha magani ne da zai zubar da cikin ya juyo yana tambayar abin da na ci

Na ce ‘Ni yau ban ci abinci ba sai ɗaya saura ya ce wa ya ba ni abincin? Na ce Vicky, ransa ya tsananta ɓaci muna asibitin har yamma ya ɗauke ni muka koma gida.

Mutanen gidan ya tara kafin ya titsiye Vicky sai ta fadi abin da ta sanya a abincin da ta ba ni har ya yi yunƙurin zubar da cikin jikina.

Vicky na gurfane tana ta razgar kuka da rantsuwar ba ta sanya komai ba tun tana magiya da turanci ta dawo da yarbanci ta shiga hausa, Amal ta ce  yarinyar nan munafuka ce dole a kore ta ashe har hausa ta iya ba wanda ya taɓa sani sai yau.

Aka tambayi Peter shi ma ya rantse bai ba ni komai ba na ci.

Kudi Lema ya ciro ya miƙa mata ya ce ya sallame ta ya bar falon na bi shi da ido har ya fice na ja ajiyar zuciya jin Vicky ta riƙe ƙafafuna da ɗaiɗai suka fara watsewa aka bar ni daga ni sai ita, ta share hawayenta ta tsayar da kukan ta ce Amal ce ta sanya ko ma me aka sa miki na kalle ta da sauri “Don an ce ke ce shi ne kika ga gara ki yi mata sharri?

Ta shiga girgiza kai  “Ban yi mata sharri ba na saurari zantukansu tun Mama na nan suna da ƙuduri na ganin bayan cikinki na taɓa kama ta tana sanya miki magani a drinks shi ya hana ni barin abincinki gudun a cutar da ke.

Abin da suke faɗi a kanki ya sa na ƙi nuna na iya hausa suke magana da hausa a gaba na.”

Ta haɗe hannaye  “Ki gafarce ni ko ƙadangaren da kika gani shiri ne kawo shi aka yi saboda tsoron shi da kika faɗi kina ji firgitar da za ki yi ta sa cikinki ya zube.

Amal ta sha alwashin sai ta ɓarar da shi mahaifiyarta na ƙara sanya ta a hanya kar ki haifi namiji ya ƙwace musu uba.”

Na zuba mata ido  “Amma mene ne tsakanin ki da Khalil?

Ta fyace hanci “Na kama shi ya shiga ɗakinki tun daga nan yake mini barazana idan na faɗa sai ya keta mutuncina ko jiya ya shiga kina garden.”

Ta haɗe hannaye “Ki rufa mini asiri kar ya sani, ya yi alkawarin keta ni ki taimaka mini kar a kore ni idan na tafi ban san inda za ni ba iyayena sun kore ni tunda suka gane na shiga musulunci.”

Wani kallo na yi mata ba shiri zancen da ta fadi kuma ya hana ni mamakin ganin Bashir Lema tsaye da ban san san da ya dawo ba.

Cigaba da ya ce ya ankarar da mu tsayuwar shi kukan ta yi ta yi har sai da ya ce “Ki faɗa mana ko ke wace ce? Ni ma kuma zan sa a yi mini bincike a kanki na samu karya kan abin da kika faɗi ranar za ki gane kala ta.

Ta goge fuska “Ni mutuniyar Kano ce, a can aka haife ni iyayena mutanen Okene ne Yoruba ne ba musulmai ba. Kai ni boarding a makarantar yammata ta Katsina na haɗu da Hauwa Bello ita kuma bakatsiniya suna zaune a Abuja yadda take gudanar da ibadarta yana burge ni har na ji son in shiga musulunci na kuma faɗa mata ta ji tsoro ta ce iyayena fa? Na ce kar ta damu.

Na musulunta a makaranta na koyi karatu da ibada wurin Hauwa da bincike a wayata, iyayena ba su taɓa sani ba har na kammala Secondary na shiga jami’a, ina shekara ta uku watarana suka gano ni kora ta suka yi don mahaifina ya sha alwashin sai ya kashe ni.

Hauwa na kira ita ta turo mini kuɗin mota na bar  Kano na tafi Abuja, Hauwa ta yi mini masauki a gidansu mahaifinta yana matuƙar jin tausayina mahaifiyarta ta ce ba ta yarda da zama na ba sai na bar gidan za mu ci amanarta.

Hauwa ta ba ni kayanta kala huɗu ta kai ni gidan wata yar’uwar babanta bayan Maman ta yi mini korar kare.

Auntyn Hauwa ita ta taimaka mini ta haɗa ni da wata mai ɗaukar masu aiki ta kawo ni nan.

Bashir Lema ya tako inda nake zaune ina zubar da hawayen tausayinta ya share mini hawaye ya kama hannuna na mike  mun fara tafiya ya ce mata ta koma ɗakinta “Za mu je gidan Friend ɗin taki zan ga mahaifinta.”

Muka tafi muka bar ta tana godiya.

Da shigar mu ɗakin kayana ya ce in ciro set uku na yi yadda ya ce ya ciro jaka ya sanya su, na rataya ta  ya ce mu je. 

Ina gaba yana biye da ni da muka zo hanyar da za ka yi ɗakin Vicky na  ce zan yi ma Vicky sallama ya ɓata rai ya girgiza kai na marairaice ya duba agogo sai ya ce in tafi, na wuce da sauri na nufi ɗakin

Ina tura ƙofar zaune na hango ta bisa sallaya ta haɗa kai da gwiwa ta ɗago muka haɗa ido na ce “Me ya sa da kika musulunta ba ki canza suna ba?

Ta ce “Na sanya ma kaina Amina sunan mahaifiyar fiyayyen halitta, sai dai makaranta Vicky  ake kira na haka ma gida da ba su san da canjin sunan nawa ba, shi ya hana sunan bi na.”

Na gyaɗa kai “Za mu fita tare da ogan ya ce na ɗauki kaya set uku ƙarshen ta ba yau zan dawo ba  ki kula da kanki da mutuncinki.”

Ta ce  “In sha Allah. Na gode.”

Na fita ta rufe ƙofar.

Shi ke tuƙin ina gefen sa ba wanda ya yi magana a cikin mu sai kuma da ya tsaya gaban Gate din Haj Fanna na gane gidan.

Ya shiga da motar ya yi parking muka fito ina tunanin text ya yi mata don tana tsaye tana jiran isowar mu, ta tare mu kamar ranar farko muka shiga ciki sai da na gaisa da ita ya yi mata bayanin akwai matsala a can gidan shi ne ya kawo ni na kwana biyu kafin ya samu gida da zai kama mini haya ko zan koma can sai na haihu.”

Da mamaki ta nemi jin wace irin matsala ce za ta sa ya kama haya? Sama-sama ya ba ta labari ta yi ta al’ajabi da kakkaɓin waye ke son ganin bayan cikina don bai faɗi mata Vicky ko in ce  Amina ta faɗi Amal ce.

Da kanta ta tashi ta kai ni wani ɗaki da ke haɗe da bayi na hau gado na zauna ina tunanin al’amuran da suka gudana yau, muhimmi labarin da Vicky ta ba ni idan har gaskiya ne zancenta zan taimake ta iyakar iyawata Amal ba ta ba ni mamaki ba a yadda take mu’amalanta ta za ta aikata fiye da haka sai Khalil ina yake samun key na ɗakina da har yake shiga ya ɗauki kuɗi?

Ina nan zaune na zuba tagumi ta shigo wasu kyawawan sleeping dress ta ba ni ta ce in yi amfani da su, kujerar dressing mirror ta janyo ta zauna ta ce na kwantar da hankalina daga Allah ya tseratar da ni daga sharrin su cikin bai zube ba don ta san ba kowa ba ne sai ya’yansa.

Godiya na yi mata ta tashi ta fita ta bar ni da kakkaɓin yadda aka yi ta san ya’yansa za su aikata haka?

Sallah na yi, na yi shirin kwanciya na rufe rabin jikina da lallausan duvet ta turo kofar ta shigo ta ce mini zai wuce na fito mu yi ban kwana na yi mamaki don na yi tunanin ya tafi tuni.

Na janyo wayata da na sanya silent sai na ga kiran sa har uku na yunƙura na sauka yana tsaye a tsakiyar falon rakiya na yi masa har jikin motarsa kwantar mini da hankali ya yi ya ce Fanna ba ta da matsala in yi zama na har ya samu gida

Na koma ciki zuciyata cike da tunanin alaƙar da ke tsakanin sa da Haj Fanna, ina mijinta? Ita ba ta da yara?  Sune tambayoyin da suke ta mintsina ta.

Tana tsaye na same ta na yi mata sai da safe na shige rage hasken ɗakin na yi na kwanta na daɗe barci bai kwashe ni ba har Bashir Lema ya kira bayan isar sa gida.

Da safe da na tashi tana ta ba ni kulawa na karya na yi wanka ina gefen ta tana ta amsa waya da ta fahahimtar da ni ita ɗin yar kasuwa ce har kantin da ya kai ni ya saya mini kaya nata ne.

Da rana sai da ta tambaye ni abin da nake so ta sa aka dafa mini muka ci abinci tare bai zo ba sai dare ya dai kira ni har sau uku ni kuma na kira Vicky don hankalina yana kanta ta tabbatar mini tana lafiya, shi kuma da na tambaye shi ya je wurin mahaifin ƙawar ta ta ya ce a’a ya tafi wani uzurin ne.

Washegari ma da daddare ya zo muka yi hira ya tafi rana ta uku ne ya zo da yamma ita ya faɗa ma fita za mu yi, ta ce ga part ɗin can can Yallaɓai Lema kai ya girgiza mata ya dube ni ya ce in tashi  mu tafi mayafi na ɗauko na kayan da ta ba ni don na gama sanya set biyun da na zo da su.

Muna tafe yana waya da kwatance muka isa wata unguwa Tudun Nura sai da muka sauka muka ɗan taka zuwa gidan Alh Bello da aka kwatanta mana magidancin shi ya fito ya tare mu da girmamawa aka buɗe ɗakin da yake tarar baƙinsa ya faɗi abin da ke tafe da mu

Magidancin ya tabbatar da zancen Vicky ya kira ɗiyarsa Hauwa ƙawar Vicky da matarsa har ma muka ji mahaifin Amina Vicky pastor ne kuma mai kuɗi sosai.

Bashir Lema ya yi musu kyauta ta kuɗi tare da tabbatar musu zai riƙe Amina Vicky suna ta godiya muka fita muka tafi, bai mayar da ni ba wata unguwar muka tafi sai dare na koma  amma Haj Fanna na jira na ba ta kwanta ba na yi mata sai da safe na shige.

Da safe bai kira ni ba kamar yadda ya saba sai wuraren sha ɗaya ya faɗa mini fita ya yi duba wani gida  da aka nuna mishi ta waya ya yi da ya je kuma ya gani bai yi mishi ba .

Ya ce amma ba zan wuce sati ba za a samu.

Ina cikin wayar Haj Fanna ta shigo cikin kwalliya tsayuwa ta yi har na sauke wayar sai na gaishe ta ta amsa cikin fara’a ta janyo kujerar madubi  ta zauna har lokacin fara’ar na nan a kan fuskarta ta ce “Momin twins na ga yau kamar kin yi kumburi ta fuska?

Na shafa kumatuna na ce  “Ga ni nan dai.”

Ta ce “In sha Allah ba damuwa. Fita zan yi na shigo mu yi magana.”

Na kara tattara nutsuwa ta ta ja ajiyar zuciya sai ta fara

Ina son taimakon ki ne a zaman ki da Lema, matuƙar kina son zama da shi sai kin tashi kin taimaki kanki,  zama da shi ba abu ba ne mai sauƙi akwai mata da yawa da na san sun so Lema amma Farida ta yi musu iyaka da shi ni nan ina cikin su!

Wani kallon da ba shiri na yi saurin watsa mata  idonta fes bisa kaina.

<< Ummu Radiya 32Ummu Radiya 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×