Skip to content
Part 36 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Na kafe shi da ido ba ko shakka ya wuce wai Abakar ne duk da sauyi mai yawa da ya samu da ya bambanta shi da Abakar dina na farko Abakar da yake dogo baƙi siriri wannan ya murɗe da alamu yana motsa jiki ga wani glowing da fatarsa ke yi tabbacin yana cikin hutu, sanye cikin ƙananan kaya jar riga da baƙin wando masu daraja.

Duk da ƙamshi da jiddadin falon ke yi tunkaro mu da ya yi wani irin ƙamshi yake yi .

Kallona da na ga ya yi ya sa na yi gaba na nufi ɗakina har lokacin gabana na dokawa .

Kwanciya na yi a gado ina tunanin ta inda aka haihu a ragaya wace duniyar Abakar ya faɗa har ya duro gidan nan, abokin Khalil?

Na tambayi kaina gashin kaina da na ji an shafa ya sa ni ɗaga kai Bashir Lema ne lafiya ya tambaye ni na lumshe idona na ce “Ba komai.”

Kayansa ya tube ya canza da na shan iska ya dawo ya tashe ni na ci Moon Cake da nake ta ɗokin na dawo gida na ci, amma ganin Abakar ya hargitsa mini ƙwaƙwalwa kaɗan na ci na miƙe na ɗauro alwala har sai da na yi isha’i ina  zaune wurin da na yi sallar ya shigo ya ce in fito a ci abinci kai na girgiza mishi ya ce ko ba ni da lafiya na ce a’a ya ce to in zo mu je ko kaɗan in ci.

Na miƙe ya bi ni da kallo wata riga mara nauyi kalarta sky blue ke jikina ta toni asirin cikina after dress na ɗora na rufe kaina da gyalenta muka fita mun samu duk sun hallara har baƙon Khalil aka hau tebur ba don na so ba na hau na zauna Amina ta kawo mini abincin da ta yi mini don na samu na bar wurin na ce ta kai mini inda nake zama can na koma ina ta kallon Amal tana ta kauɗi ita ta yi saving ɗin baƙon.

Ban ci da yawa ba na tsame hannuna na tafi daki na zare after dress ɗin na kwanta a gado tunanin yadda Abakar ya zo gidan nan ke mini yawo cikin kai da kuma son sanin yadda rayuwarsa ta kasance bayan fitowar sa, Turai na tuna yadda Khalil ya ce wa Amal abokinsa zai dawo daga Turai to ta ya?

Nan ma shigowar oga Lema ta raba ni da tunanin ya yi shirin kwanciya ya kwanta ya rungume ni ta baya.

Da safe ban fito da wuri ba don ba na son haɗuwa da Abakar so nake sai ya tafi, sai dai fatan da nake bai ci ba da fitowa ta da su na fara arba shi da Khalil, zan raɓa su in wuce  Khalil ya ce “Morning Aunty.”

Na amsa na tafi kitchen Amina tana ciki haka Peter ta yo wuri na ta gaishe ni Peter ma ya gaishe ni daga inda yake.

Na ce ta kawo mini abinci ɗaki na juya.

Yanzu ma Amal na ta kauɗi Dina na zaune kawai, gani na ta taso ta bi ni muka tafi hoton wani gaye da gani tashin Turai ne ta nuna mini, sati guda kenan da haɗuwar su har ya fara maganar shigowa gida na ƙara kallon hoton ina kallon yadda ya rina gashin kansa “Ni kam na fi son irin Taj mai ruƙo da addini da idan ya ga na yi ba daidai ba zai gyara mini ba irin wannan ba shi ma tashin turan ne.”

Ta faɗi da sanyin murya.

Na ajiye wayar gefena “Ki yi ta addu’a Dina Allah ya yi miki zaɓi ma fi alheri.”

Ta ce ta gode ta mike ta ce bari ta bar ni in ci abincina.

Ban ƙara fitowa ba sai la’asar still Khalil na nan da Abakar duk na takura da zaman baƙon nan har kuma sai da ya kwana uku ina ɗaki kamar yadda na zaɓa ma kaina tun zuwan shi.

Amina ta zo kira na Khalil na son gani  na, na sauka gadon a hankali don daga barci na tashi jikina ya yi nauyi, ina taku irin namu na masu tsohon ciki na isa falon tsaye suke a tsakiyar falon shi da bakonsa sai Amal Khalil shigar ƙananan kaya ya yi Abakar yau kaɗai tun zuwan sa ya sa riga da wando na yadi ya ɗora hula ya yi kyau ƙwarai da har na ji wani abu na fara ɗarsuwa a raina da na fara neman tsarin Allah daga sheɗan jefaffe.

Baƙona zai tafi Aunty shi ne zai maki sallama.”

Na ce “Allah ya tsare a sauka lafiya.”

Na juya na koma ɗakina salatin annabi na yi ta irgawa da yan yatsuna don samun salama daga tunanin Abakar da yake neman zame mini barazana ga nutsuwa ta.

Hakika bayan tafiyarsa na samu nutsuwa sai dai jefi-jefi na kan tuna kwana uku da tafiyarsa na ji Amal na tambayar Khalil yaushe zai dawo ya ce anya zai dawo ɗan Kaduna ne karatu ya kai shi Turai ya fara business yana turo abin da ya saya ana sayar mishi in ba ki labari a shekaru huɗu da ya yi gayen ya tara ba laifi.” Ta girgiza kai kamar za ta fashe da kuka “Ni ba wannan ba ina son sake ganin sa ne yaushe zai dawo?  Ya ce na faɗa miki ba anan yake ba ta ce To ba ni contact ɗinsa.

Ya ciro wayarsa ya ba ta ta ruga da gudu ta nufi wurin su ya bi ta da ido cikin saƙawa da kwancewa sai dai ba zato washegari sai ga Abakar ya dawo sam ban ji daɗin dawowar tasa ba wurin Bashir Lema na ji rumfa ya buɗe a nan Abuja yana shigo da wayoyi daga ƙasar China.

Wani yammaci Lema ya fita da ya’yansa ni da na ce ba za ni ba daga ni sai su Easter hatta Khalil ina zaune a garden na hangi fitar shi, takun da na ji idona na kan wayata ya sa ni ɗaga kai gabana ya buga ras ganin Abakar na tunkaro ni wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta ƙwace mini da isowar shi, na miƙe zan yi tafiyata ya ce “Kar mu yi haka da ke Ummu, ki ba ni lokaci mi yi magana na san fushi kike da ni saboda tafiyar da na yi ban yi miki bayani ba.”

Na girgiza kai “Ba wannan maganar, idan ma a baya na yi wannan fushin igiyar auren da ke kaina yanzu ta goge wannan babu wani hurumi ko dama da za mu yi magana ni matar wani ce.”

Na fara ƙoƙarin tashi ya ce “Na sani, amma don girman Allah ki saurare ni saboda ke na dawo gidan nan.”

Saurin duban shi na yi ya zuba mini ido ba shiri na sunkuyar da kaina don jin da na yi idanuwansa za su yi mini tasiri.

Na ba ki labarin wani dan manya da aka kawo frison ɗin da nake aka haɗa mu ɗaki daya shi ya yi sanadin fitowa ta , ba kuma wani ba ne illa Khalil.

Na yi saurin ɗagowa na dube shi ya ɗaga mini gira “Yes na kawar da kaina “Abin da ya faru da shi wata girl friend ɗinsa ya zo Nigeria zai koma London ta sanya mishi haramtattun ƙwayoyi a jakarsa saboda sun samu saɓani, a airport aka yi ram da shi .

Haɗa mu ɗaki daya da aka yi muka saba shi ne yake tambaya ta abin da na yi aka kawo ni nan na yi mishi bayani  ya yi mini alƙawarin kafin ya fita zai yi magana za a fitar da mu tare.

Akwai jami’in tsaron da ke kula da shi tun zuwan shi komai na amfani ana kawo mana, jami’in tsaron ya ce ya kawo mishi waya zai yi magana da sister ɗinsa hakan kuma aka yi daga sama aka bayar da umarnin sakin mu ni da shi, mijin ƙawar sister ɗin shi ya fito da mu.

Da muka fito ya ja ni zuwa gidan ƙawar sister ɗinsa anan muka kwana biyu har mijinta da ba ya ƙasar ya dawo ya gana da mu, jin abin da ya faru da ni ya tambaye ni ina sha’awar ci gaba da karatu na ce E kuɗaɗe ya ba mu masu kauri ya ce zai sama mini gurbin karatu wace ƙasa nake so bakina ya ambaci China don ita ɗin Cibiyar kasuwanci ce ni kuma ba abin da nake so irin zama ɗan kasuwa.

Mun yi godiya a gare shi mun kuma gode ma matarsa saboda don ita  ya yi duk abin da ya yin.

Ita kuma ta ce mu je  in yi international passport Khalil kuma ya roƙe ta su shiga lamarin a buga mana visa da wuri yana so mu tafi tare da shi kafin a samu makarantar.

Da muka baro gidan shi ne na zo Kaduna, kwanana uku kaɗai ya kira ni tunanina ko visa ta fito ne na yi hanzarin komawa sai dai ɗaki ya kama mana a hotel cikin Abuja, karatun da aka kwaɗaita mini shi ya hana ni ƙyale shi na dawo Kaduna.

Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba aka buga mana visa tunani na wurin auntynsa da ya ba ni labarin wurin ta yake sai ga mu a jirgin China ashe wurin wata yarinya yar Nigeria da ke karatu a can za shi.

Fitar da muke zaga gari ya kai ni wani wuri da yan Nigeria suke, aikin su yi ma baƙi jagora idan sun shigo ƙasar sayayya kuma suna yin tafinta a biya su, cakuɗe suke da yan China masu yin wannan aikin.

Zuwa biyu uku na yi sabo da su na kuma maƙale a wurin su sai sannan na fito da dalolin da mijin ƙawar sister ɗinsa ya ba ni na sayi waya da kaɗan daga ciki.

Matar na fara nema ya ba ni lambarta ina gaishe ta lokaci -bayan-lokaci tare suka zo ƙasar ita da mijinta ya yi mini komai na makarantar tuni Khalil ya bar ƙasar.

Na fara karatu a ƙasar China ina tare da yan Nigeria nan idona ya buɗe na gane gari ni ma na fara irin aikinsu idan ba na  karatu sannu a hankali na fara sayen waya na turo ta Nigeria ta hannun wani ɗan kasuwa ya kai ma Amiru kamar wasa aka saye ya turo mini kuɗaɗena .

Akwai wata kasuwa kamar mu anan akwai inda ake sayen kayan hannu su ma haka komai kusan sabo ne da ya ɗan samu yar matsala ko an ƙera shi da niyyar gwaji nan ake kawo wa wasu abubuwan kuma saboda daɗewa a ajiye sai a yi gwanjon su.

Can na soma zuwa in sayi Kaya in sanya a jirgin ruwa a kawo ma Amiru shi kuma ya rabar ma yan kasuwa cikin rahusa ya turo mini kuɗina daga haka ina karatuna ina taɓa saye da sayarwa na tara har ta kai ni ga buɗe ma Amiru shago.

Lokacin da na ga na samu rufin asiri ya kamata in waiwaye ki Amiru ya tabbatar mini tuni kin yi aure na shiga wani hali na damuwa da na saita kaina da ƙyar na cigaba da harkokina, amma na kasa mancewa da ke ke ce mace ta farko da na fara so har gobe kuma ke nake so ban kuma tashi ganin ki ba sai da wannan abin.”

Ya ƙare faɗi yana nuna cikina takaici mai yawa ya bayyana a muryarsa. Wani kallo na maka mishi sannan na miƙe zan tafiyata “Haba Ummu ni ne fa me zai sa ki yi mini haka?

Me nake maka?

Na tambaya ba tare da na haɗa ido da shi ba  “Kamar ba ki san ni ba kamar ma kina ƙyamar zama a inda nake .”

Baki na riƙe don mamakin da ya baibaye ni “A sanin da na yi kai ɗin masanin addini ne ban sani ba ko kai ma zaman turan ya shiga kanka ya birkita maka sanin daidai.

Wannan zaman da muka yi ni da kai sai mun nemi yafiyar Ubangiji don ba mu da hujjar yin hakan.”

Na taka na bar shi tsaye na yi tafiyata.

Ban sake ganin shi ba sai washegari mun fita da Lema mun dawo yana gyara parking su na hango shi da Khalil a wasu kujeru a harabar gidan.

Muka jero yana riƙe da hannuna ban dubi inda suke ba sai da suka kawo gaisuwa ga maigida Lema.

<< Ummu Radiya 35Ummu Radiya 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×