Skip to content
Part 38 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

A ranar ma a ɗakina ya kwana, da safe muna kwance aka kira wayarsa ƙarar wayar ya farkar da ni  ɗaukar ta ya yi ya duba sai ya kwantar da Aman da ke bisa ƙirjinsa ita ma wayar ya ajiye ta ya sauka gadon, ya zura takalmansa da ke jikin gadon ya fita na bi shi da kallo kafin na ɗauki wayar don duba wanda ya kira shi ganin sunan Maman su Amal ya sa na ajiye wayar na rufe idona da niyyar ci gaba da barcina sai dai hargowar da nake jiyowa ta hana hakan yiwuwa sam!

Na tashi zaune jin abin na daɗa kusanto ni na miƙe tsaye na buɗe ƙofa na fita, Maman su Amal ce ke zazzaga bala’i cikin turanci gangariya wani abin na gane me ta ce wani kuma oho!

Sam barka dai na fahimci tushen fitinar sai ya bar gidan da ni domin nan ɗin nata ne ita da ya’yanta.

Girman tashin hankalin ya sa na koma ɗakina har kuma gama gyaran ɗakina na yi wanka na yi ma Aman abin bai lafa ba cikin jego na kasa jurewa na fita gifta su na yi a Main parlor yana zaune tana tsaye kansa ko ya gaji da bala’in ne ita kaɗai ke yi ta waiwayo gare ni tana zagina girman shekarunta ya sa ban tanka ta ba sai da na koma ɗaki ya shigo ya yi shiri ya fita ko karyawa bai yi ba ni ma ban ƙara fita ba Amina da ta yi girki da rana ta biyo ni da shi.

Sai dare ya dawo nan ma ba su kwana lafiya ba abu fa ya ƙi ƙarewa har sai da Haj da wani babban Malami suka zo daga Kaduna, shakkar Haj da take yi ta sa dole ta karɓi sulhun aka kashe rigimar.

Ranar ni zan karɓi girki da kaina na yi na sha kwalliya cikin riga da skirt English wear don ma na so zuwa sallon har na sanar ma Iliya ta hana shi zuwa ta aike shi ga tawa motar ina kallo rashin ƙwarewa a tuƙin ya sa ni zuba ido na fasa fitar.

Da kaina na shirya tebur na bar Aman hannun Amina, da aka zauna cin abinci na yi serving ɗinsa da kaina sai dai ana gama cin abincin ban zauna kallon labarun da yake ba ya sa dai na kwantar mishi da Aman na tafi ɗaki.

Charting muka yi da Nabila har sai da na ji na fara hamma na miƙe na yi shirin kwanciya, barci ya fara cin ƙarfin idona na ji shigowar shi dole maganar da nake son yi masa sai da safe na ce ina so ya ci gaba da koya mini mota don ga motar jiya ina kallo ina son zuwa sallon rashin Iliya sai dai na haƙura.

Ya ce zai sanya ni wata driving school sai in ƙarasa koyon a can, na ji mamakin dalilin kai ni  can a maimakon ci gaba da koya mini da kansa.

Da daddare ta karɓi girki ban fito ba ya kira wayata muka yi sai da safe, da safen ma bai shigo wurina ba kira na ya yi ya ce  fita ta kama shi in yi ma Aman video na tura mishi yau bai gan shi ba, da na yi masa wanka na ɗauke shi na tura masa.

Da na fito ban ji motsin kowa ba har na gane sun fita, Amina ta kawo mini abin karyawa ta ɗauki Aman ta goya a abin goyo ta tafi ina cikin karyawa sai ga shi ya shigo na yi mamaki don baya dawowa daga ya fita.

Ya zauna har na kammala na tafi ɗaki ina gyara kayan saman mirror ya shigo, bakin gado ya zauna ya kira sunana tare da buga kusa da shi na bar abin da nake yi na isa na zauna kusa da shi ya sa hannu ya rungumo ni ta cikina a hankali ya raɗa mini “Ina missing ɗinki, yau zan dawo amma ban son ki wahalar mini da kanki da wannan girkin.”

Na ɓata fuska na ce “Amma girki shi ke ƙara danƙon ƙauna tsakanin ma’aurata.”

Ya ce shi ya yafe mini har raina na ɗauka abin da ya faɗa haka ne sai da dare ya yi mun kwana mun tashi da safe a gajiye nake ƙwarai saboda yawan buƙatarsa da ta ƙaru abin da ke ba ni mamaki sai da muka zama mu biyu ya ƙara yawan buƙata.

Barci ne ya ɗauke ni kaina bisa ƙirjinsa Aman na gefen sa don ba ya yarda mu kai shi gadonsa shi ke kwanciya da shi sai idan zai sha nono ya miƙo mini shi.

Buɗe kofa tare da maganarta ta sa ni ɗaga kai Mamansu Dina ce, na yayibi Duvet na rufe jikina gabaɗaya wani ɓacin rai na lulluɓe ni.

Bashir Lema da ke kwance daga shi sai guntun wando ya tashi zaune yana tambayar me ya shigo da ita? Ta tsaya ta shaƙi ƙamshin da ɗakin ke fitarwa ta ce wannan ƙamshin da ke fita daga ɗakina a cikinsa aka  sanya kulumboton da ya sa shi tarewa a gindina idan ya kwana ɗakina bai fitowa da wuri idan ni ke da girki kuma ya fi dawowa da wuri,shi ya sa ta ce ba ta yarda da wani kilibibin girki da na fara mishi ba, na yi karya in zo in same ta da mijinta in ce zan karɓe mata shi Bashir Lema nata ne.

Duk maganar da ya yi mata kan ta fita ba ta ji ba sai ta ƙarfin tsiya ya fitar da ita nan ma dai an jijjiga tebur faɗa suka yi ba na wasa ba dare kuma na yi ya kwana ɗakinta da safe ya yi mini sallama sun wuce Bauchi shi da ita.

Da yamma kuma sai ga Khalil ya dawo gidan daga tafiyar da ban san inda ya je ba, ni dai tun dawowa ta ban gan shi ba tare da Abakar suka zo Amal kamar an mata rahma ganin Abakar duk ajinta idan ta ga Abakar zubar da shi take tana manne da shi har na tattara na yi ɗakina don na gaji da kallon da yake mini.

Kullun yamma kuma sai ya zo har aka kwana uku masu gidan suka dawo bai bar zuwa ba zuwan nashi ya takura ni ainun ba ganin su da Amal ke mintsinata ba kallon da yake damu na da shi kamar ya manta shari’a  ga shi koyaushe ina cikin kwalliyar  English wear da na fi mu’amala da su da material sai Abaya, hakan ya sa na yi ta ma Bashir Lema tunin zuwa koyon mota don kauce ma zaman gidan da ya sanya ni tare da Amina muke fita da na mayar yar’uwata ba mai aiki ba, ita ce abokiyar hira ta tare muke renon Aman girki ne dai da matarsa ta hana in yi ba na yi sai ranar da na yi sha’awa in yi ma kaina Amina ke yi mana.

Hirarmu da Amina ta ilmi ce da take ƙara nema wurina sai yawan maganar Mamanta da take yi mini na ba ta shawarar ta gwada kiran mahaifiyar ta ta, ta ce mini tsoro take ji na ƙarfafa ta ta kira ta, ta zo ta same ni tana ta murna ta ce ta amsa mata.

Tun daga nan suke waya har ta ba ni muka gaisa tana ta mini godiyar riƙe mata Vickynta ni ma daga nan muna gaisawa ta WhatsApp har ta kira ni duk da take babbar mace a bar girmamawa ga mutanenta.

Ana ta mirginawa a haka har Aman ya yi watanni huɗu lokacin ya iya zama ya yi wayo sosai kamanninsa da mahaifinsa na ƙara fitowa zamana da Amal da mamanta gamu nan dai ta ɓarawo hannun mata idan ba ta jin tsiyar sai mu kwana biyu ba a hau sama ba  kuma abin ya juyo kowa hana mishi zaman lafiya take.

Na yi sabo da Mufida wata matashiya da ke da wurin gyaran kai da jiki da kuma sayar da kayan ado na mata daga zuwa gyaran kai muka yi sabo shaƙuwar mu ra sa ta ba ni labarin rashin mijin aure bayan kammala karatunta ya sa ta nemi kuɗi wurin mahaifiyarta ta fara business kamar wasa Allah ya daukaki harkar.

Saboda gudun me zai je ya zo daga matarsa ya sa na rage samun kulawar Bashir Lema kamar farko duk inda za ni zai sa Iliya ya kai ni idan kuma inda zan iya zuwa ne da kaina mu tafi da Amina. Cikakkiyar kulawarsa sai mun keɓe a ɗakina ga shi yanzu sai ya fi yi mini kyautuka yana yawan sanya mini kuɗi ta account ɗina ga kyautar da ta fi yi mini daɗi ta wasu banguls murtuka-murtuka da suka yi tafiya zuwa Dubai shi da uwar Amal har da Amal ɗin, ni kuma ya tura ni Kaduna bikin ɗiyar sister ɗinsa da suke uba ɗaya, duk da na ji haushin tafiyar da ya yi da ita ni ya tura ni ni kaɗai na ba kaina haƙuri na shiga shirin tafiyar.

A wurin Mufida na yi sayayyar kayan tafiyar don kuɗaɗe masu nauyi ya turo mini da suka ba ni damar sayen suturu masu daraja aka yi mini gyaran jiki da gashi na fito ina ta sheƙi.

Na dawo goye da Aman a abin goyonsa riga da skirt ne na wani pink din yadi da ya yi matuƙar yi mini kyau Khalil da Abakar da ke zaune falon na rasa wanda ya fi zuba mini ido saboda su na kasa zaman falon na leƙa Amina na fito na wuce ɗaki na riga su tafiya da kwana ɗaya sannan suka wuce na samu tarba mai kyau daga Haj da sauran yan’uwan Bashir Lema.

Da su Dina muka sha biki da Suhaima duk da ita Suhaima an sa ma mata aiki a Abuja tana zuwa Abuja a ranakun aiki ta dawo Kaduna ta yi Weekend.

Dina Tajonta ba ya ra’ayin aiki ita ɗin ma bai dame ta ba.

Sai da aka ƙare bikin na tattara na yi gidanmu, wannan karon ma ƙin komawa na yi har sai da suka dawo sai dai da na koma na samu shi da Amal kaɗai suka dawo wai ita ta tsaya Lagos wurin wata ƙawarta.

Kwana biyu da dawowa ta na fito da Aman a hannu Amal na zaune tana shan juice na ɗora shi saman sofa na koma ɗauko masa abin wasa na ɗauko na dawo na hango shi ya kusa fadowa ga Amal zaune ta yi kamar ba ta wurin na kwasa a guje abin da ya janyo yin tafiyar ruwa da jug din gaban ta abin da ke ciki ya malale, ina tare Aman Bashir Lema na shigowa wata ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta ƙwace mini na rungume shi a ƙirjina ba sanannen ciki na ji an zabga mini mari gigicewar da na yi ta sa na kusa sakin Aman, na buɗe idona don ganin wanda ya yi mini wannan aikin, Amal ce ke tsaye tana huci tabbacin aikinta ne na kwantar da yaron na miƙa hannu zan damƙo ta na ji an riƙe ni ƙamshin turarensa ya sa na fahimci waye ina ihu ina ƙwacewa da rantsuwar Amal ba ta marina ta kwashe ƙalau sai na rama.

Kujera ya danna ni ya bi ni ya sa mini nauyi yana faɗa mini na yi haƙuri.

Lub na yi ina ajiyar zuciyar bacin rai sai da ya sakankance ya sassauta riƙon da ya yi mini na tashi a guje na yi ɗakin Mamanta da ta shiga gabaɗaya na faɗa mata na shaƙe ta na fara kai mata naushi, a haukace ya iso ya fincike ni ya yi jifa da ni na faɗi kan hannuna cikin tsantsar fushi yake cewa ba ya ce na yi hakuri ba? Da jajayen ido na dube shi na ce “Haƙuri ko? Yarka ce za ta mare ni ni kuma don ba ni da galihu ka yi mini wannan jefarwar na miƙe ina riƙe hannuna da nake ji yana raɗaɗi na nufi ɗakina ina buɗe wardrobe yana  faɗowa ɗakin, ya danna key ya jefa aljihu ganin yana tunkaro ni da ihu nake faɗin “Kar ka zo aure yau ya ƙare.” Ya yi juyin duniya in saurare shi na ƙi fir ga hannuna ya matsa mini idan na ɗauko kaya ya mayar duk muka hargitsa su, wayarsa ake ta kira ya ƙi ɗagawa da na gaji na koma bakin gado riƙe da hannuna ina famar kuka ba a fasa kiran sa ba daga bisani aka koma dukan ƙofar bai buɗe ba wayar dai ya amsa na ji maman su Amal ce ta ce ta dawo ta samu Amal ba lafiya ta ce yarinyar nan ce ta shaƙe ta.

Ya ce E ita ta fara marinta.

Katse kiran ta yi sai ga ta, shi ya buɗe.

<< Ummu Radiya 37Ummu Radiya 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×