Skip to content
Part 40 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Kallona ya yi ta yi bai yi magana ba har na tsargu kafin ya ce “Zan yi magana da mahaifin ƙawarta sai a yi komai a wurin sa na yi masa godiya na tashi na tafi duk da shi na so ya yi ma Amina komai amma hakan ma na san ya yi ƙoƙari yadda yake son ya’yansa an ce ba a son ɗiyar tasa mai aikin gidansa ake so Abakar kuma ya ce ba zai auri Amal ba don yana son nema wa ya’yansa uwa ta gari.

Ranar da Amal ta samu labari Abakar zai yi aure hauka ta yi ta yi a gidan iyayen na fama da ita Haj da ta zo garin ta yi ta zubar da hawaye tana faɗa mishi illar gatan da ya nuna ma ya’yansa, ni kuma na yawaita sa wa’azuzzuka a wayata sai ya zauna ya yi shiru.

A hankali nake ta shirin bikin Amina mahaifiyarta ta turo mini kuɗaɗe masu yawa ta ce in ƙara na adana da niyyar bar wa Aminar bayan bikinta ta nemi sana’a.

Komai gidansu ƙawarta Hauwa’u aka yi shi har ɗaurin aure mun nufi Kaduna kai amarya Abakar ya gina gidansa tsararre kusa da na mahaifinsa da aka ɗaga za a sayar ya saya ya gyara ɗakunanta sun shiryu  matuƙa, na ga su Haj Nasara da ya’yanta da suka yi ta mamakin yadda na zama na gaishe da mahaifin Abakar tare da yi mishi alheri.

Gidanmu nake kwana in wuni gidan Haj bayan tashi bikin kafin na koma Abuja.

Na samu Amal da mahaifiyarta kamar su cinna mini wuta ga yanzu ba Amina dole na fito na nemi abin da zan ci Aman ma da ya yi ƙafa bai son mu zauna a ɗaki haka zai ta kuka yana dukan ƙofa sai na buɗe mishi ya fita tun daga ranar da ya fita Amal ko uwarta ne suka maƙala mishi hannu a ƙofa ya datse kukan da yake mai gigitarwa Easter ta zo ta kira ni samun shi hannu a jikin ƙofa na cire mishi da dabara jikina ko’ina na rawa tsananin kukan da yake ni ma na fara kuka asibiti muka kai shi ni da Iliya babansa kuma da ya dawo ya yi ta balbala mini faɗan da bai taɓa mini  ba .

Da ya shekara na kai ƙololuwa wurin takurar zaman har na fara tunanin komawa karatu da ba ni da ra’ayi a da, ga yawan tsokana daga Amal ba hali na fito a haka har Suhaima ta haihu ban shiga lamarin ba iyaka ta ido idan ta tsokane ni tun ina ƙyale ta na koma ramawa hakan ya sa muke yawan samun saɓani na gaji na tasa shi da son komawa Kaduna ya ƙi sam har sai da na je biki a familyn su na ƙi dawowa na share gidana na yi zama na fahimtar da na yi ina da shigar ciki ya sa ni yaye Aman Bashir Lema bai zo ba muna dai waya tun ban damu da rashin zuwan nashi ba har na damun na kuma ƙi bin shawarar Nabila da ke ce mini in koma tun matarsa ba ta raba ni da shi ba maimakon komawar sana’a na fara ta sayar da turarukan jiki da na ɗaki kamar mahaifiyata ɗaki na ware na shirya kayana ina ciniki sosai saboda talla da nake yi a kafafen sada zumunta.

Bayan tawa matsalar sai ta Amina kuma da ta kunno watarana da hantsi ina ɗaki barci nake na huce gajiya don mun je Kano yi ma Maman Vicky gaisuwa na rasuwar mahaifinta wayata da ke ɓurari ta sa ni buɗe ido sai na ɗauko ta muryar Aminar na ji tana shaida mini zuwan ta na ce ta shigo ina bedroom ɗina,  zaune na tashi ina kallon ƙofa har ta shigo ɗauke da Aman tana mishi wasa yana dariya don tana cikin mutanen da yake so tana son tafiya da shi gidanta ta ce ya yi mata kwana biyu sai na ce a’a har yanzu ita ɗin amarya ce, yarinya aka samo mini da ke taya ni ayyukan gida da renon shi.

Gefen gado na nuna mata ta iso ta zauna , ba ta zauna anan ɗin ba kujerar madubi ta ja ta zauna ta ce mini ina kwana na dubi fuskarta da ɓari ɗaya ya kumbura sai na ji hankalina ya tashi na ce “Me ya same ki a fuska? Ta yi murmushi da za ka san na ƙarfin hali ne  “Ba ki bari mun gaisa ba Aunty.”

Na girgiza kai “A’a fara faɗa mini abin da ya same ki.”

Nan take idonta ya tara ruwa ta girgiza kai “Ba zan ɓoye miki ba Aunty, don daga momma na sai ke Dear ne ya mare ni!

Gabana ya doka na ƙura mata ido kafin na ce “Shi Abakar ɗin ne ya mare ki? Ta ɗaga kai “Me kika yi masa?

Hawaye suka zubo mata ta sa bayan hannu ta share “A makwancinmu Aunty yana kira na da suna Ummu, abin yana baƙanta mini  na nemi ya bari ba na so bai barin ba kullum muka zo kwanciya haka muke hakan kuma yake kawo saɓani tsakanin mu sai yau ya faɗa mini idan bai kawo Ummun ba a ransa ba ya gamsuwa da ni! Na yi kuka sosai na faɗa masa maganganu masu zafi da ya sa ya mare ni saboda na zagi ita Ummun da yake kira mini.”

Ta daɗe da yin shiru amma ban samu abin cewa ba wani irin tashin hankali na shiga me sunan abin da Abakar yake yi?

Na haɗiyi yawu da ƙyar na fuskance ta don wani nauyin ta na ji don sai in ga kamar ta san ni ce Ummun da yake kira mata a shimfiɗa, hakika na ji ba daɗi ba cin fuska sama da abin da aka yi mata.

Ki yi haƙuri Amina, haka auren yake dama sai haƙuri.”

Wani kallo ta yi mini na rashin fahimta “Haka fa kika ce yake Aunty? Namiji ya dinga kira maka sunan wata macen a shimfiɗa?

Na miƙe tsam na isa inda take na kama hannunta ba ta ƙi ba ta miƙe ta biyo ni ɗakin muka bari muka sauka ƙasa inda ɗakin turarukana yake kafin mu shiga na ƙwala ma mai aikina Ma’u kira ta iso da hanzari na ce ta karbi Aman don da mun shiga sai ya samu ya yi mini ɓarna, ta karɓe shi hannun Amina yana tirjewa suka tafi muka shiga dakin tana ta dubar ko’ina ta ce “Ma sha Allah kin ƙara ƙayatar da ɗakin nan Aunty Allah ya ƙaro kasuwa mai albarka.”

Na ce “Amin. Kin ƙi Amina na faɗa miki ki gyara jikinki ko ba ki tsira da ɓacin ran maza gabaɗaya ba za ki samu sauƙi kin ƙi to yanzu sai ki gyara.

Wani kallo ta yi mini kamar za ta fashe da kuka “Kamar ba ki ji me na ce miki yana yi mini ba ko ba ki fahimci girman zafin da zan ji a raina.”

Na dafa kafaɗarta “Na sani Amina, mazan kenan ni ma ɗin ba ki ga a ciki nake ba? Ta dube ni kawai ba ta yi magana ba na cigaba “Wata na biyu nake ciki tun da na baro Abuja Daddyn Aman bai tako ƙafarsa ba sai dai ya faɗa mini sun tafi kaza sun je wuri kaza da matarsa.

Na ja ajiyar zuciya “Tare da ke muka zauna tunda muke da ke kin taɓa ganin ya tasa ni ya tafi da ni wurin harkokinsa?

Ta girgiza kai “To da ƙuruciyata ma an watsar da ni ita kuma ya tasa ta zuwa duk inda za shi ga yaro ga cikin jikina kuɗi kawai yake turo mini don haka ina so ki yi haƙuri duk macen da kika gani a gidan aure tana da ta ta irin matsalar duk wadda ta ce miki ba ta da matsala ƙarya take.

Don haka haƙuri zan ba ki shi zan ce ki yi shi muka gada ke dalibar ilmi ce kin san aljannar mace na ƙarƙashin kafar mijinta, ki yi gyara in sha Allah za ki samu sauƙin tsiyarsa.

Kai ta jinjina mini na  fara ciro kala-kalan turaruka na jiki da na tsugunno da na sanyawa a ɗaki wadanda na sa wa a ɗaki shi kaɗai ta karɓa na zuba mata a leda mai ɗauke da tambarin abubuwan da nake sayarwa na miƙa mata ta karɓa da godiya  muka fito kitchen na shiga ta bi ni muka haɗa abin karyawa tare muka fito muna karyawa ina ƙara ba ta dabarun da za ta kama mijinta su zauna lafiya.

Wuni ta yi mini na ƙara ba ta haƙuri ni na ɗauke ta muka tafi zuwa gidan nata daga waje na tsayar da motar ta dage sai na shiga ba don na so ba na fito ta ce in shiga da motar mana, na ce ai ba zan daɗe ba.

Tana gaba ina biye da ita muka shiga har falonta daidai Abakar ya fito daga kitchen ɗauke da flate wani kallo ya yi mana da ta sa hanjin cikina yamutsawa na daure na ce mishi “Barka da gida.” Ya ɗaga mini hannu kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ” Yawwa.”

Ban zauna ba na ce “Zan koma Amina.” Ta dube ni da nuna rashin jin daɗi a fuskarta “Ba ki fa zauna ba Aunty.”

Na yi murmushin yaƙe “Yamma ta yi kuma zan biya unguwar Sunusi.”

Na juya ta biyo bayana sai da na shiga mota na zauna tana riƙe da murfin ta ce “Ki yi haƙuri Aunty.”

Na ce “Haƙurin me? Hawaye shar suka zubo daga idonta  “Abin da Dear ya yi miki da shigar mu  kuma ya san ba ni da kamar ki.”

 “Me ya yi mini ni bai mini komai ba.” Na faɗa da murmushi a fuskata don na kauda mata ɓacin da ranta ya yi 

Ta girgiza kai ban bari ta yi magana ba na ce “Ki lallaɓa shi ku daidaita.” Ta shafa kumatunta  “Marina fa ya yi.” Tausayinta ya yi matuƙar kama ni “Zan mishi magana amma ki yi haƙuri.”

Ta gyaɗa kai “Shi kenan zan yi komai saboda ke.”

Na ce “Na gode.”

Ta ce a sauka lafiya.

Na ja motar na bar wurin cike da tunani.

Gidanmu na wuce a can na ci abincin dare sai takwas da rabi na fito na koma gida.

Kwana uku da faruwar haka Bashir Lema ya zo na yi masa kyakkyawar tarba shi ma kuma na samu soyayya da tarairaya daga gare shi ya yi ta shafa cikina yana mamakin ina da ciki amma ban shaida mishi ba maganar da yake ta yi kan kyan da na yi da idan ba ya nan yamutsewa nake amma yanzu ya yi fushi bai zo ba daga na ƙi komawa Abuja shi ne na yi wannan kyan na gaji da nacinsa na faɗa mishi muka je asibiti aka ƙara tabbatar da ciki wata uku a jikina ya kai ni gaban Haj ta yi mini faɗa mu koma tare ta goyi bayana ta ce zama da Farida sai shi tun da na kafe ban komawa ga ciki jikina ya bar ni kawai.

Sati guda ya yi mini ya koma Abuja saboda bala’in kira daga Mamansu Amal da daddare idan ka ga ta bar mu sakat sai idan ya kashe wayarsa.

Da safe ya tafi na dawo rakiyarsa na kwanta a ɗaki don in rintsa barci na fara ɗauka ta na tsinkayi kiran waya ganin sunan Amina na ji idona ya buɗe hakanan kuma na ji gabana ya buga na tashi zaune, da sa wayar a kunnena kukanta ya yi mini sallama na dafe kunci da hannuna ɗaya na tambaye ta me ya faru ta ce ya ci mutuncinta wai ita haka ta ga mata na zama ta zauna fuska duk ƙuraje ba ƙyalli ba gyara ba ta koyi da ni ba ta ga yadda nake sheƙi ba ?

Haƙuri na ba ta na ce gani nan zuwa gidan.

Barcin na nema na rasa na dira daga gadon na yi wanka don haka kaya na canza na gyara fuskata na ɗauki wasu set na kayan gyaran fata na Sunaf skin care products da duk wanda ya san ni ya san sune sirrina na mallakar fatar jiki mai sheƙi da burgewa na dubi fuskata a madubi yadda take walwali madalla da Nafisa da ta samar ma mata kayan gyaranta (Don tuntuba 07039131269)  jiya-jiya na karɓi sakonsu daga Zaria faduwa ta zo mini daidai da zama zan bai wa Amina sai in sake sanyawa a kawo mini wasu na sanya takalma na fita dakin sako na tura ma Lema zan fita na jefa wayar a jaka na sauka ƙasa Ma’u na iske a kitchen tana wanke-wanke, na faɗa mata zan fita amma ba zan daɗe ba.

Ta ce idan an ɗauko Aman daga makaranta ta dafa mishi indomie? Don zuwan nan da babansa ya yi ya kai shi wata private school ya sa kanensa yana zuwa ya kai shi ya dawo da shi   duk da ban so haka ba wata makaranta ta haddar Alkur’ani na so fara sanya shi  idan Alkur’ani ya fara shiga kansa sai a sa shi bokon to da na faɗa mishi bai yarda ba.

Na ce mata ba zan daɗe ba amma idan an kawo shi ban dawo ba ta dafa mishi.

Ta yi mini fatan dawowa lafiya na fita.

Ina ta saƙe-saƙe a raina har na isa gidan a bedroom ɗinta na same ta ta yi kuka har ta gaji ta dube ni da idanuwa da suka sauya kala saboda kuka wulaƙancin da Abakar yake mata take faɗa mini cikin zubar hawaye ni ma nawa idanuwan suka tara hawaye ta nuna mini kan mirronta da dan manuninta “Ki dubi tarin kayan kwalliyar da na tara amma yake mini wannan wulaƙancin na buɗe jaka na fitar da kayan gyaran Nafisa na ba ta na ce in sha Allah indai don gyaran fata ne da wannan ƙurajen in sha Allah an wuce wurin.

Ta ce ta gode na ce ta je ta yi wanka ta gyara fuskarta da ta yi ƙozai-ƙozai ta miƙe ta shiga bathroom na ciro wayata ina latsawa har ta fito ina zaune ta yi amfani da kayan Sunaf skin care ta sanya doguwar riga muka fita falo na ce hala kin banzatar da kayan da na ba ki ba ki amfani da su?

Ta ce “Huum! Ko da fa ba ni amfani da su kullum yana maƙale da ni ba ya bari na na huta amma yana mini wannan wulaƙancin yanzu kuma da nake amfani da su sai abin ya ƙaru kuma bai bari ba.”

Na ji kunyar maƙale matan da ta faɗa mini na kuma ji tausayinta kan kiran sunan wata da yake mata a shimfiɗa.

Na miƙe na ce “Ki ƙara haƙuri duk wanda kika ji ya ce ya yi haƙuri bai ci ribar sa ba kaɗan ya yi .”

Ta ce “Ina za ki? Na ce “Gida zan koma.”

Ta girgiza kai “Don Allah ki zauna Aunty zuciyata zafi take ganin ki na ji sanyi idan kika tafi zan koma cikin damuwar.

Na koma na zauna jikina ya yi sanyi hirar Aman ta kawo mini mai makaranta nan na zauna har ta yi girki sai dai ban ji daɗin dawowar Abakar ya same ni ba yau ko ɗaga hannun ban samu ba wuce mu ya yi ta tashi ta bi shi sai hayaniya na ji lokacin ina gyara mayafina zan fita.

<< Ummu Radiya 40Ummu Radiya 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×