Skip to content
Part 8 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ta daɗe muna hira ina aikina har sai da aka kira sallar azahar ta tafi gida, na tashi don yin sallah.

Na idar Hassana ta kawo mini abinci da ta girka, Mama ta fita tun muna zaune da Nabila.

Tare da Hassanar muka ci daga nan na tattara kayan aikina na adana na kira Abida na shaida mata zan fita sai dai gobe mu kai musu.

Ruwa na samu da Hassana ta ɗora bayan ta sauke abinci na sirka na shiga wanka.

Na fito na zauna na gyara kaina a gaban madubi hoda na murza sai wet lips da na goga ma laɓɓan suka ɗauki sheƙi, na taje gashin kaina wanda bai cika yawa ba ina da dai gwargwado, taimakon da rabbi ya yi mini ya ba ni yalwar gashin gaban goshi da ya kwanta lamɓam shi ya ƙara ma fuskata kyau, wanda bai san yawan gashina ba zai ɗauka wani uban gashi ne da ni.

Na daure shi ina duban fuskata wankan tarwaɗa ce ni sai Allah ba ni fararen idanuwa su suka ƙara ƙayata fuskata, doguwa ce ni samɓal ban ranƙwafa ba siririya ƙwarai da cikar ƙirjin da mai sama ya ƙwace ni ya ba ni ya hana ni zama kamar an zana ɗaya mazaunaina ma ba shafe nake ba hakan ya sa na shiga taro ba maza kaɗai ba mata ma sai sun dube ni.

Na sanya rigar ta zauna mini cif na yi ɗaurin ɗankwali da ya yi matuƙar yi mini kyau.

Sai duban kaina nake da na sanya sarka da yan kunne da warwaro yan kunnayen dogaye ne don na fi son dogayen yan kunne ko masu kamar warwaro, turare na ɗauko da na yi ma ɓoyo na musamman mama ce ta haɗa ma wata amarya haɗuwar turaren ya sa na matsa mata  sai da ta san mini na adana shi ina cin burin sai na koma gidan Abakar zan yi amfani da shi,

to kana naka Allah na nashi. Ji na yi yau ina son shafa shi.

Nan take kuwa na ɗauki wani ƙamshi mai sanyaya zuciya, takalmi mara tudu na zura don ba na mu’amala da masu tsinin dunduniya saboda tsawona, kuma wani hukunci na Allah ni da Husaini mu kaɗai muka biyo babanmu da ya kasance dogon Mutum, baƙin babarbare mai dogon hanci Hassana da Lubna har Hanan Mama suka biyo farare marasa tsawo.

Wow! Aunty Ummu, kin tashi wasan.” Husaini ne da wannan zancen yana saka hannunsa a baki ya saki wani fito.

Hassana ma ta ɗauka “Kanka ya bi jiki Aunty Ummu.” Murmushi na yi ina warware laffayar da ke hannuna Nabila ta shigo ita ma ihun na yi kyau ta rufe ni da shi na ce “Ai kin fi ni yin kyau.”

Ta taɓe baki “Bakinki ne yammata.”

Kalmar yammatanci da ta jefe ni da ita ta sa na ji wani iri na ce masu Hassana sai mun dawo.

Keke napep muka tare da za ta kai mu har ƙofar gida, ga mu nan tafe-tafe har cikin unguwar sarki muka tsaya kafin mu ƙarasa kofar gidan Marigayi Alh Ahmad Lema, saboda tun daga farkon shigowa layin gidan yake ɗinke da motoci cikin gidan ma da muka cusa kanmu don an wangale Gate harabar gidan mai tsananin girma cike take da jama’a.

Waya Nabila ta kira cikin ƙawayensu wasu su biyu suka zo suka tafi da mu cikin gidan mai sasa daban-daban.

Wani sasa mai girma da tsari a yadda na ji na daya daga cikin yaran gidan ne aka kai mu nan ‘yammata suka baje kolin su, da yawan su  familyn  su amaryar ne, wayayyu da su ga Naira ta zauna, sai ƙawayenta yan poly waɗanda sune su Nabila.

An ci Cake an sha abin sha ana ta raye-raye, dayake mata ne zalla na warware laffayata na taka rawar don bikin ya mini daɗi don na manta rabon da na ji nishaɗi irin wanda na ji a ranar.

Sai ga shi har na shafa’a yamma ta yi liƙis sai da ana kiran sallar magrib muka nemi tafiya,amma yammatan  suka hana wai mu bari anguna za su zo za su mayar da mu, ni dai na ƙi sam, mutum biyar suka raka mu suka tare mana abin hawa.

 Muna tafe ina faɗa ma Nabila yadda na ji daɗin bikin nan.

Gajiyar da na yi ita ta hana ni ɗauko dinkin zannuwan gado da na ci burin idan na dawo zan cigaba, isha’i kawai na yi na kwanta.

Washegari Nabila ta shiryo sai ga ta ta same ni kace-kace cikin aiki, ai kam ta buga ta raya na ce ba za ni ba, zan sallami mutane sai kira suke ta ce ai na kusa na bar ma Abida ta ƙarasa ta kai na ce a’a da ta kasa shawo kaina sai ta ce to na tashi na raka ta ta samu abin hawa.

Hijab na yayibo na sanya muka fita muna fita Gate Baba Isa na tsayawa da motarsa, na karasa jikinta da fara’ata yayin da Nabila ta tsaya inda take ta rungume hannaye a ƙirji, ya fito yana mini murmushi

“Sannu da zuwa Baba.”

“Yawwa, Ummu ina zuwa haka?

Na ƙara matsawa kusa da shi “Nabila zan yi ma rakiya.” Ya dubi inda take tsaye sai ta yi saurin cewa “Ina wuni.” Ya amsa da sakin fuska sai ya juyo gare ni”Raka ta ki dawo ina jiran ki.”

Na ɗaga mishi kai sai na koma wurin ta muka tafi.

A tsaitsaye na jira ta samu mota sai na juyo jin Baba ya ce yana jira na, na san akwai maganar da yake son yi mini.

A tsaye na same shi ya ce “Har ya gama da part ɗin su Aya ni yake jira in zo mu tafi gidansa.

Ya fara mani faɗan rashin zuwa sai mu daɗe ba mu je ba.

Haƙuri na ba shi na ce gobe zan zo.

Ya ce “A’a shi yanzu zai wuce da ni.

Na rasa yadda zan yi ya kuma duba agogon da ke ɗaure a hannunsa ya ce minti biyar ya ba ni in shirya mu tafi.

Suna maganarsu da Mama na shige Abida na fara kira ta waya na ce ta zo ta kwashe zannuwan gadon ta kai, shirya su kawai ya rage sai ta ƙarasa ta kai.

Na ajiye wayar na canza kaya don na yi wanka da safe sunana da yake kira ya sa ni mayar da hodar da na ɗauko hijab na sanya na ɗauki wayata na fita, yana tsaye inda na bar shi ya ce oya na ce ma Mama sai na dawo, Abida za ta zo ta kwashi zannuwan gado.

A gaban motar na zauna ya tayar da ita sai da muka bar layin ya ɗan juyo ya dube ni kaɗan sai kuma ya mayar da duban nashi titi,  “Ya sunan ƙawar nan taki? Ɗan jim na yi jin tambayar tashi

kafin na amsa “Nabila.” “Ita ma za ta ci gaba da karatun?

Na ɗaga mishi kai “Ya yi kyau, ba ni lambarta.”

Na yi saurin duban shi sai na ce “Waccan fa da ka zo ka ce na ba ka Baba.”

Ya taɓa kai “An yi haka an yi haka tabbas.”

Daga nan bai ƙara magana ba har muka isa gidan nasa da ke Mondo, flat house ne gidan  shi ya fita ya buɗe Gate ya dawo ya shigar da motar , na fita na shiga falon Aunty Larai ta tsara falon da kyau don ita ɗin yar gaye ce mai son ƙyale-ƙyale ta turare shi da turaren wuta ƙamshi na ta tashi gefe guda kuma ƙamshin abinci na fitowa ta kitchen ɗinta.

Na ɗaga murya na yi sallama sai ga ta ta fito da sauri kakkaurar mace gajera wankan tarwaɗa cikin kwalliya take ta burgewa.

Ta tare ni da fara’a na gaishe ta ta tambayi su Mama kafin ta ce “Taso mu shiga kitchen.”

Abinci take yi, ni ta bari na ƙarasa mata ta tafi wurin mijinta sai da ya fita ta dawo muka kammala na shirya abincin a wani wuri da suka ware don cin abincin.

Mun idar da sallar isha’i ya shigo muka ci abincin tare yana kammalawa ya ɗauki key ɗin motarsa ya ce “Gama Ummu na mayar da ke gida, kar dare ya yi.”

Aunty Larai da ke cin abincinta ta ce “Ka bar ta ta mini kwana biyu.”

Saurin kallon ta ya yi “Ba ta zo da kaya ba ban ce mata za ta kwana ba.”

“Yau dai kaɗai a bar ta ta kwana mini.” Ta ce ba tare da ta daina cin abincinta ba.

Shi kenan kawai Baba ya ce ya kama hanyar fita “Ina za ka? Ta tambaya  bai juyo ba ya ce “Ba daɗewa zan yi ba.”

Cokalin na ga ta yi saurin saki sai ta miƙe da azama ta bi shi na bi ta da kallo  kafin na ci gaba da cin abincina.ya  7uuuuuu

“Ki sake ni, ai ba sai kin riƙe mini riga ba zan dawo.”

Na ɗaga idona “Aunty Larai ce riƙe da rigar Baba, na yi saurin kawar da kaina daga kallon su har suka zo suka shige ɗakin barcinsu.

Na kammala na kwashe komai na kai kitchen, ba na jin barci amma hakanan na shiga ɗakinta da take sauke baƙinta ina tunanin rigar da zan sanya in kwanta,  wayata na yi ta dannawa muna chart da Abida bayanin yadda suka yi da masu kayan take mini sun ba ta wani aikin har ta sawo mana Faiba ta bayar da ɗinki ga waɗanda muke ba suna taya mu, gyaran muryar Baba na ji da ta sani ɗaga kai shi ɗin ne riƙe da wayarsa ya canja kaya zuwa jallabiya “Nombar da kika ba ni ta ƙi tafiya Ummu, ba ni wata idan akwai.”

Ya faɗi cikin rage murya,  ba na son kowace irin alaƙa da Baba ke shirin ƙullawa da Nabila ina sane yana cikin maza masu biye-biyen mata, Aunty Larai kuma tsaye take kan hana shi kula kowace ‘ya mace, kishi ne da ita ba na wasa ba duk wani motsinsa akan idonta yake, ba su haihu ba duk iya shekarun da suka kwashe da aurensu.

Ba ma haka ba duk waɗanda yake nema na san da ƙyar idan nema ne na aure ba na shaƙatawa ba, ba zan so Nabila ta shiga cikin su ba.

Zai yi wahala kuma ya taya Nabilar ba ta faɗa tarkonsa ba don akwai shi da ƙwalliya ɗan ƙwalisa ne duk da shekarunsa da suka fara nisa don ya kusa hamsin ban da bai haihu ba ya isa haifar kamar Nabilar.

“Ba ni Ummu.” Ya faɗi yana dawo da ni daga tunanin da na lula  ganin yadda nake laƙaƙin ba shi ya tako ya karɓi wayar ban so ba don na yi niyyar birkita lambar kamar yadda na yi ma ta farko da na ba shi, yana miƙo mini Aunty Larai na shigowa ɗaure da zane a ƙirjinta sai tawul da ta ɗora saman kai, hakan ya ba ni tabbacin wanka ta shiga Baba ya sulalo.

Juyawa kawai ya yi ya raɓa ta ya bar ɗakin ta bi shi da kallo sai da ya fice ta ja ƙwafa ta tako ta zauna gefen gadon da nake zaune

“Ummu Radiyya.” Ta kira sunana na amsa ina rafka tagumi da hannuna ɗaya wayarta ta miƙo mini “Wace ce wannan Ummu Radiyya? Gabana na ji ya soma dokawa hannuna na rawa na miƙa shi na karɓi wayar gabana ya tsananta da bugu ganin abin da na gani a fuskar wayar ko da hoton bai fita sosai ba ni da na yi ma Nabila farin sani ba zai yiwu a ce na kasa shaida ta ba.

Na haɗiyi wani kakkauran yawu sai na miƙa mata wayar “Ban gane wace ce ba Aunty.” Ta ja numfashi “Ina tunanin kamar na san ta kuma tunanin nawa na ja na tare da ke na san ta.”

Kai na ƙara girgizawa “Ban san ta ba Aunty.” Ta kaɗa kai sai ta miƙe “Bari na kawo miki riga sai ki tuɓe kayanki kar ki kwanta da su.”

Sai ta fice.

Wani irin huci na saki ina sake tallafe kumatuna, a haka ta dawo ta same ni, rigar ta ba ni ta fita na tuɓe kayan jikina na ciro kayan da ta kawo mini daga cikin leda na sanya na kashe hasken na haye gadon na kwanta.

Sam na gaza barci gari kawai nake so ya waye in gan ni a gida gaban Nabila don lamarin nan ya sanyaya mini yatsu, ina ake wanga lamari mai gida da kwanan kasuwa?

<< Ummu Radiyya 7Ummu Radiyya 8 >>

1 thought on “Ummu Radiyya 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×