Skip to content
Part 11 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Dare ya yi nisa sosai sannan na samu barci ya ɗauke ni  mai cike da mafarkai kala-kala, makara ce ta ziyarce ni har sai da Aunty Larai ta shigo ta tashe ni bayan an idar da sallah.

Shaida mata na yi ina fashin sallah, ta fita ta bar ni na juya don gyara kwanciya amma sai na nemi barcin na rasa ya ƙaurace ma idanuna, tunanin da na kwanta da shi ya maye gurbin shi.

Miƙewa na yi na faɗa bathroom da ke cikin ɗakin, wanka na yi na yi brush da sabon maclens da brush ɗin da na samu Aunty Larai ta ajiye mini.

Na fito na shiga ɗayan ɗakin nata don na san matuƙar na zo kwana nan ɗin gabaɗaya take bar mini ta koma na Baba.

Mai na shafa da hoda da turare na koma  na mayar da kayana sai na fita falon, jin motsinta a kitchen na nufi can sai da na gaishe ta ba kama mata aikin muka kammala tare.

Ta yi mini tayin na yi zama na a wurin ta, na yi mata maganar sana’ata ta ce idan na dawo nan na koyi snacks don shi ne sana’arta in bar wannan zanen gadon da take ganin akwai wahala sosai .

Shiru na mata don ban gamsu ba.

Baba ya fito cikin kwalliya yana ƙamshi muka karya yana miƙewa don fita, na ce zan bi shi ya sauke ni, Aunty Larai ta ce tun da safe? Sai take faɗa mishi son da take na dawo nan.

Ni ya duba ya ce. “Idan ta yarda sai ta dawo.”

Saurin miƙewa na yi na ɗauko lulluɓina, Aunty Larai da ta ga lallai tafiyar zan yi ta miƙe ta ce tana zuwa .

Baba na ta duban agogo da ɗan tsakin zai makara sauri yake .

A motar na same shi bayan ta kawo mini leda mai ɗauke da kayan kwalliya sai dubu biyu godiya sosai na yi mata na shiga motar ya ja muka tafi.

A hanya na yi tunanin zai yi mini zancen Nabila sai bai yi ba har ya sauke ni ya kawo dubu biyu shi ma ya ba ni, na hau wata motar sai na isa gida.

Cikin halin rashin walwala na tarad da Mama Hassana na kwance wai kanta ke ciwo, na duba wurin girki komai ba su ɗora ba, na matsa kusa da Mama na tambaye ta ta ce ba kuɗi a hannunta amma tana sa ran za a yi mata biyan bashi, ajiyar zuciya na sauke na fita na tafi ɗakin Hussaini yana kwance na tashe shi na aike shi, kafin ya dawo na kunna gawayi yana kawo mini gyaɗa na soya sama-sama na fece ta na haɗa da danyar shinkafa na sanya kayan ƙamshi na ba shi ya miƙa mini niƙa yana faɗin shi ta ina zai kai niƙa?

Na ce ya samu yaro ya ba shi ya miƙa.

Na duba muna da lemon tsami, yana kawo mini ba a jima ba na dama kunu ba lokacin ƙosai buredi da na ba shi ya sawo na haɗa na kai gaban Mama.

Hassana ta taso ta zuba ta sha haka ma Husaini, na ba Hanan sai na yi mata wanka, Hassana da ke da jarabawa ita Husaini suka shirya suka tafi.

Na shiga ɗaki na kwantar da hanan barci nake so ta yi na tafi wurin Nabila.

Ƙarfe biyar na yammaci a falon Bashir Ahmad Lema babban ɗa ga marigayi Alhaji Ahmad Lema tsohon attajiri mai tarin ya’ya da mata uku. Falon a cikin family house nasu yake yaransa yammata su uku ke zaune sun zuba ma TV ido suna kallon Bridal shower da aka yi na ƙanwar mahaifinsu Su’ada.

Mahaifinsu ya fito cikin shirin fita ganin abin da suke kallo shi ma ya kai dubansa ga TV yammata ne ke rausayawa cikin nishaɗi, aka haska Ummu Radiyya Bukar da ke rausayawa suna dariya ita da waɗanda ke tare da ita, wani abu Alh Bashir ya ji ya soke shi da ko tantama ba ya yi ya san ƙaunar yarinyar ce farat ɗaya ta kama shi da rabon da ya ji abin da ya jin tun yana saurayi.

Maimakon tafiya zama ya yi kusa da ƙaramar yarsa mai shekaru ashirin da biyu ta matso daf da shi “Papi ba fita za ka yi ba?  Ya shafa sumar kansa “Zan fita Suhaima, me kuke kallo ne?

Sai da ta ɗora kanta a kafaɗarsa cikin sangarta ta ce  “Event din bikin Aunty Su’ada.”

Ya jinjina kai yana ci gaba da kallon, abin da yake jin na ƙara dabaibaye zuciyarsa da gangar jikinsa.

Yarsa ta biyu da ke riƙe da remote ta taso ta zauna daidai ƙafarsa tana ɗora kanta  a gwiwarsa “Zan bi ka Papi.”

Ya shafa kanta “Ni ma na fasa fitar nan my daughter Amal.”

Ta ɗaga kai ta dube shi cikin mamaki kamar za ta yi magana sai ta fasa.

 bai ƙara katarin ganin an nuno ta ba shi ba abin ya ce su mayar mishi baya ya kuma ganin ta ba ya dai daure har ya ƙare yana fata su tashi a falon ya zare faifan.

Miƙewa ya yi ya taka inda babbar yarsa mai shekaru ashirin da bakwai ke kwance fara ce tas kamar shi komai nata nashi ne in ka ɗauke ita ba ta da jiki gajera ce dai kamar shi sai dai duk ta fi yan’uwanta kyau don ita kamar ya yi kaki ya ajiye, saɓanin Amal da Suhaima, Amal tana da ɗan tsayi kaɗan siririya ba ta cika hasken fata ba kamar su daya da Suhaima sai dai ita Suhaima ba ta kai tsayin Amal ba.

Duk kwaramniyar da ake Dina na riƙe da wayarta ba ta ko gwada ta san me ake a falon ba.

“Daughter.” Ya kira ta yana kallon ta ta ɗago ido idanuwansu suka shiga na juna sai ta mayar da nata kan wayarta “Yes Papi.” Ta faɗi a ƙasan maƙoshi rashin maganarta na damun shi  “Zan fita ba wata damuwa? Ya faɗi cikin harshen turanci ta ɗago wannan karon murmushinta mai kyau ta yi masa har fararen haƙoranta suka bayyana ta girgiza mishi kai da ke alamta ba ta da matsalar shi ma murmushi ya yi zuciyarsa na mishi daɗi ganin murmushin yar tasa don bai haɗa komai da son da yake ma yayansa ba.

Wayarsa ta shiga ƙara ya zaro ta a aljihun wandonsa, ganin mahaifiyarsa ce ya rage muryarsa ta ce ya same ta a falonta.

Hannu ya miƙa ma Dina amma sai ta girgiza kai ya san ba za ta ba ya juya ga su Amal da Suhaima ba Amal ta fita falon sai Suhaima ita ma da ya miƙa mata hannu ya ce wurin Haj za su noƙewa ta yi sai dai ita ta faɗi dalilinta Haj faɗa, su kuma sun saba iyayensu suna bin ra’ayinsu ne.

Ya sa kai zai fice Amal ta dawo ita ba musu ta bi shi suka fice.

Daga fitar su wani dogon corridor suka miƙe da ya kai su wata babbar ƙofa suka shiga  wani tafkeken falo mai kamanceceniya da nasu, wata dattijuwa ce zaune tare da wasu mata su biyu, da ka ga dattijuwar za ka san jininsu ɗaya da Bashir Lema don ba za ka ɗauka ta haife shi ba saboda hutun da ya baibaye ta nan kuwa shi ne ɗanta na fari.

Wuri ya samu ya zauna Amal ta lafe a bayansa matan da ke zaune suka gaishe shi hajiyarsa ta gabatar masa da su tana nuna su kai kawai ya ɗaga suka miƙe suna yi ma Hajiyar sallama tana yi musu godiya suka fice .

Da fitar su ta juyo gare shi idonta na kan Amal, “To ka ga irin abin, ƙatuwar budurwa tana maƙale jikinka da ya dace tana ɗakin mijinta.”

Amal ta ɓata rai  “Dubi shigar ‘y’ayanka

wai ɗiyan musulmi me ake da yahudu da nasara?

Tsam Amal ta miƙe ta taka ta bar falon, uban ya bi ta da kallo yana jin ransa na matsewa ganin ran yar ta sa ya ɓaci.

Wallahi ka dawo da tunaninka ga rayuwarmu ta Malam Bahaushe ta addini da al’ada, ba rayuwar mai jan kunne ba wannan da suka fita mai baƙin mayafin Badariyya ce ɗiyar Haj Hinde da muke ya’ya maza, mijinta soja ne an kashe shi a faɗan boko haram, daga yarinyar da aka nuna maka ka ce ta yi maka yarinta ba za ka iya auren tsarar Dina ba ga Badariyya ita kam za ta yi daidai da ra’ayinka.”

Gabansa ya ji ya buga tuna yarinyar da ya gani kwata-kwatanta da ƙyar idan za ta yi shekarun Suhaima, ga shi yana jin yadda ƙaunarta ke mishi yawo ba zai iya haƙura da ita ba.

“Ka yi shiru? Ta ce ganin kamar hankalinsa ba ya kanta “Ki ba ni lokaci Haj ki bari na koma London zan lallashi Farida za ta yarda mu dawo Nigeria gabaɗaya, zan yi auren Haj.”

Wani farin ciki ya kama Hajiyar jin yau ya amsa da kansa zai ƙara aure, gefe ɗaya takaicin zai koma London na lulluɓe ta.

“Ba za ka koma ba Bashir!  Saurin kallon ta ya yi sanin duk rintsi ba ta faɗin sunansa ta ɗaure fuska sosai “A sauran rayuwar da ta rage mini sai na tsamo rayuwarka daga halaka, za ka dawo Nigeria za ka yi aure irin namu wanda addini da al’ada ta tanadar mana yaranka mata guda uku da Allah ya ba ka ka aurar da su ka koya musu rayuwa irin ta addinin Islama.”

Kansa ya dafe sanin abu ne mai wahala matarsa Farida ta yarda ta dawo Nigeria “To amma Haj aikina fa? Bai ko rufe baki ba ta ce “Ka nemi wani anan.”

Kafin ya yi tozali da yarinyar yana jin zancen mahaifiyarsa ne kawai jira yake a ƙare bikin ƙanwar tasa da shi ma ita ta matsa sai ya zo, yaransa kawai ya yi niyya su zo wanda dama duk wata hidima ta gidan na su sai Haj ta sa ya turo su sai dai idan suna karatu lokacin idan kuma suka samu hutu Nigeria take cewa ya turo su ba a san ran uwarsu ba wadda tun komawar su London sau ɗaya ta tako Nigeria rasuwar mahaifiyarta ta kuma tafi da ƙaramin ƙanenta da ya ba Dina shekaru biyu.

Ba wani aure da yake da sha’awar ƙarawa Farida ta ishe shi da suka yi aure tun ƙare Secondary Sch ɗinsu, ajinsu ɗaya sun liƙe ma juna tun suna js 3 zamanin mahaifinsa na raye ya yi masa kashedi ya fi sau shurin masaƙi ya rabu da Farida yana da ƙananan shekaru karatu zai yi, ya yi kunnen uwar shegu.

Mahaifin nasa ya aika gidansu Faridar kan shi ɗansa karatu zai yi su faɗa ma yarsu amma kamar ana daɗa zuga su.

Ya shirya ma Bashir tafiya karatu waje sai da ranar tafiyar ta zo aka neme shi  aka rasa, duk wani faɗa da barazana an yi kan Bashir ya ce shi a aura mishi Farida iyayenta talakawa ne liƙis da ke zaune a Badarawa su kan su sun ja sun tsaya tun da ‘yarsu ta ce sai Bashir to aure sai an yi.

Hajiyar Bashir Farida ba ta yi mata ba haka ma mahaifinsa da ƙyar aka rarrashi Ahmad Lema ya yarda da batun auren kar wani abu mara daɗi ya ɓullo don duk inda Bashir yake tana tare da shi.

An kai kuɗi gidan su Farida ana kai wa kuma tsohon kakanta ya ce su bayar da sadaki a ɗaura aure, iyayen Bashir sai dai aka dawo masu da labarin an ɗaura aure kafin a yi maganar tarewa nan take biyo shi ta wuni ɗakinsa.

Babansa ya taso da zancen tafiyarsa karatu da kanta ta iske baban a falonsa ta durƙusa ta roƙi kar Bashir ya tafi ya bar ta, ta tafi ta bar shi sake da baki ya ma rasa wane irin tunani zai yi.

Dole ita ma aka nema mata makarantar, watan su uku kacal a can ta haifi Dina, kafin su kammala karatunsu ta haifi ya’yansu uku Dina Amal sai Suhaima ta kuma kalallame Bashir suka ƙi dawowa suka kama neman aiki ba su dawo ba sai da mahaifin Bashir ya kwanta ciwon ajali mahaifiyarsa ta yi ta masa waya tana roƙonsa ya dawo ya ga mahaifinsa su gana kwanan su biyu da isowa ya amsa kiran mahaliccinsa.

Mahaifiyarsa ta tsaya tsayin daka da addu’a kan ba zai koma ba da kanta ta jagoranci yi masa gini a jikin nata aka gyara mishi  ba su ƙara komawa waje ba duk nacin Farida sai da suka shekara goma shi da ita sun samu aiki da suka yi ta nema ta yanar gizo ba a son Haj ba suka tattara suka koma.

Hajiyar ta dage da addu’a har ta sa ana taya ta Bashir ya baro ƙasar waje ya dawo Nigeria yaransa su yi aure ko Suhaima da take ƙarama saura shekaru biyu ta kammala karatunta. Ɗabiunsu da shigar su duk sun juye na turawa, kullum da wannan take kwana take tashi Bashir shi kaɗai ne ɗanta namiji sai mata uku,  Haj karime ke bi mishi sai Fatahiyya Su’ada ce ƙarama da ta haifa har ta fara shiga shekarun girma tare da cire tunanin sake haihuwa.

<< Ummu Radiyya 9Ummu Radiyya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.