Skip to content
Part 12 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Wayarsa ta shiga ƙara ya ɗaga ana shaida mishi tafiyar da za su yi duba wani gida a Malali da yake so ya saya, ya gina gida amma a Abuja Dina ƙwararriyar mai zane ta zana gidan, ita da yan’uwanta suka zaɓi komai da za a sanya a gidan.

Bai fi wata guda da kammala ginin ba Farida ta hana shi saye a Kaduna wai sa dai su dinga sauka a Abuja da ya zo kuma Hajiyarsa ta matsa lamba ya mallaki muhalli a garinsa na haihuwa shi ne aka baza dillalai suna cigita mishi.

Cikin wata kasala da yake ji saboda tunanin yarinyar ya ce “Mu bari sai gobe yanzu ina da wani uzuri.”

Wancan ya yi mishi sallama suka kashe waya, Hajiya da ta tsare shi da ido ta ce “Amma me ya sa ba za ka duba gidan ba?

Ya dubi agogo “Akwai abin.”da zan yi Haj.”

Ta gyaɗa kai ya miƙe wurin sa ya koma ba ko ɗaya cikin yaran a falo hakan ya sanyaya ransa ya taka ya cire faifan ya juya ya fita Direban da ke tuƙa shi ya nema ya same shi a harabar gidan inda motarsa take faifan ya fidda yana tambayar inda za su kalla Direban ya yi ɗan jim “Falonka fa ranka ya daɗe? Tunani ya shiga kar su fito su gani amma sai ya ce “Mu je falon Haj.”

Cikin sa’a sun samu ta tashi ya danna faifan yana yi yana wucewa sai ya lura akwai yarinyar sosai a farko ya tsaya yana nuna masa “Wannan yarinyar nake so ka kalla da kyau.”

Iliya Direba ya ƙura ma yarinyar ido sai ya zare faifan ya riƙe a hannu “Mu je.”  Suka fice jikin motarsa suka koma ya ce “Wannan yarinyar nake so a yi mini binciken wace ita da inda za a same ta?

Iliya ya miƙa hannu ya karɓi faifan “Amma zuwa yaushe ranka ya daɗe?

Hannu ya sanya aljihu ya zaro bundle na yan dari biyar ya ajiye mishi saman motar, ya bi su da kallo yana haɗiye yawu ba shiri

Ƙarfe goma na daren yau nake son sanin komai, da safe ina so mu yi sammakon zuwa gidansu.”

Iliya ya share fuska ga ƙoshi ga kwanan yunwa “Yallabai a yi mini afuwa zuwa gobe.”

Kai Bashir Lema ya girgiza sai Iliya ya ga kamar yana nufin karɓe kuɗinsa hannu ya miƙa ya ɗauko su ya damƙe a hannunsa.

“In sha Allah za a samo ta kamar yadda ka buƙata.”

Key ɗin mota ya miƙa masa Iliya ya cafe ya faɗa motar ƙwaƙwalwarsa na harara masa inda zai nufa ya samo yarinyar, dama ya so jan lokaci zuwa gobe ko wasu kuɗin kamar waɗannan za su ƙara shigowa.

Gidan Amarya Su’ada da aka kai Gwamna road ya yi ma tsinke Allah ya taimake shi suna matuƙar shiri da ita, matarsa ƙwararra a kitso ita ke  masu kitso angon nata kuma shi ne ɗan aike a tsakanin su.

Yana ta zancen zuci ya isa gidan ko jiya Hajiya Babba mahaifiyar Su’ada ta aiko shi gidan ya kawo baƙi, ta waya ya kira Su’adar tunaninta Hajiyarta ta aiko shi ta leƙo da kanta ya fito motar suka haɗu bayan gaisuwa ya shaida mata cikin yammatan da suka halarci shagalin bikinta wani babban mutum ya ga ɗaya daga cikin su yana so, ya zo neman taimakon ta ta gano mishi ita.

Bismillah kawai ta ce mishi ta yi gaba ya bi ta a baya har falonta sai da ta gabatar masa da sansanyan lemo ta shiga ciki ta dawo da kundin hotuna a hannu ta mika mashi ta ce ya duba ko zai gano ta a ciki ya karɓa har hannunsa na rawa yana ta sheƙa mata godiya  ya fara dubawa har ya sare zai ga Ummu Allah ya nuna mishi ita ya zare hoton ya miƙa mata ta kalla da kyau ƙwarai ta san ta a fuska a poly amma ba ta san sunanta ba tunani ta shiga tana kallon hoton ta tuna tare suka zo da Nabila Kabir, wayarta ta janyo ta doka ma Nabila kira wayar ta ƙi shiga wata ƙawar ta ta da ke da kusanci sosai da Nabila ta kira zai yi wahala ba ta san yarinyar ba, ce mata ta yi ga wani pic nan za ta turo mata ta shiga WhatsApp ko za ta gano mata sunan yarinyar.

Kallo ɗaya ta yi ma hoton ta ba ta duk wani bayani da take so kan Ummu Radiyya, ta juya ga Iliya ta zayyane masa komai, lambar wayarta ya nema take ƙawar ta turo mata ta ba shi

Addu’a da fatan alheri ya yi ta zuba mata tun tana amsawa da murmushi a kan fuskarta har ta ce “Wallahi Iliya na gaji.”

Ya miƙe da sauri yana faɗin “Allah ya tsone idon oga daga ganin kowace mace sai ke kaɗai.” Ya bar falon tana faɗin “Amin amin.”

A hanya ya tsaya ya yi isha’i sai ya ƙarasa. A falonsa ya same shi ya zayyane masa komai har da hotonta da ya taho da shi ya miƙa mishi.

Jin sunanta Ummu Radiyya Bukar ɗan Borno ya tuna mashi da abokinsa da suka yi Secondary tare Isah ɗan Borno.

Wasu kuɗin ya ƙara ma Iliya tare da jinjina masa ba tare da la’akari da ya ba shi wasu ɗazu ba ya fita yana ta godiya.

Tashi ya yi ya shiga ɗakinsa sabon wanka ya yi ya shirya cikin wani yadi fari mara nauyi rigar ƙarama ce mai guntun hannu bai sa hula ba sai glass da ya manna ya fesa turare yana duban kansa a madubi hakika ba ƙaramin kyau ya yi ba bai faye tsawo ba yana da dirarren jiki ya ajiye dan tumbi na zallar hutu maganar ma a jingina su Suhaima a matsayin ya’yansa ba ta ma taso ba don ya haifi Dina yana da shekaru ashirin kacal.

A yanayin jikinsa da hutun da yake ciki ba za ka sha ya wuce arba’in ba takalmin Cover ya sanya ya fita ɗakin suka yi kaciɓis da Amal “Wow! Papi, ka yi kyau sosai.”

Ta faɗi cikin harshen nasara ya yi murmushi ta kama hannunsa tana tambayar inda za shi ya ce ba zai daɗe ba ta faɗa ma su Dina su kula da kansu idan bai dawo ba su kwanta.

Ya wuce yana barin ta da mugun mamaki to ina papinsu zai tafi ya bar su? Ta kaɗa kafaɗarta tana wucewa ɗakinta.

Iliya Direba ya samu ya ce su je gidansu Ummun.

Don tunda ya faɗa mishi sunanta ya riƙe  yana jin son sunan kamar yadda ya kamu da son mai shi.

*******

Barcin Hanan ya yi nisa na zare jikina hijab na sanya na fita na samu Mama na ce zan je wurin Nabila da Abida.

A tsakar gida na samu mahaifiyar Nabila da abokiyar zaman ta, na gaishe su na wuce daki kwance take tana danna wayarta na zauna gefen ta ta tashi tana duba na “Na aika aka ce kin tafi Mondo can kika kwana. Kuma ga shi na gan ki.”

Na ce Na dawo ne.”

“Shi ne kamar an koro ki.”

Fuska na yamutsa “Ina da aikin zannuwan gado Nabila, Baba ya kira ki?

Ta yi mini wani irin kallo”Wane baban?

“Babana mana, Baba Isah “Oho ya kira.” Ta ba ni amsa kai tsaye na ja ajiyar zuciya”Me ya ce miki? Ta juya ido”Ka ji ‘ya, to abin sirri ne.” Na kafe ta da ido “Iye  lallai, to wallahi ki shiga hankalinki Aunty Larai ba ta ɗaukar nonsense daga ni har ke ci mana za ta yi, in ban da ke da abin ki a shekaru irin naki ki kula Baba Isah da ya kusa hamsin?

Ta juya ido “To sai me? Wallahi sosai ya kwanta mini sai dai ina ganin mutuncin matar tasa, ya kuma tabbatar mini da gaske aurena zai yi don ni ƙawarki ce ba zai zo da wasa wuri na ba. Ke yanzu mai shekarunsa ya zo yana son ki sai ki ƙi aurensa?

Na kaɗa ɗanyatsa”Allah ya rufa mini asiri da auren tsoho.”

Ta harare ni “Dalla can wa ya ce miki tsoho ne? Shekaru arba’in da bakwan?

Sun fi matasan iya tarairayar mace a ririta ki a shagwaɓa ki.”

Na miƙe tsaye “Wallahi shekarun sun yi yawa ina ma laifin talatin da biyar. Ni dai na tafi wallahi kar ki haɗa ni da Aunty Larai.”

Ita ma ta miƙe ta janyo mayafi muka fita tare gidansu Abida muka je daga nan muka dawo gidanmu na kama yanka kayan da Abida ta sawo mana, har na fara ɗinki Nabila muna hira tana kallo na yi na yi ta koya ta ce ita sam wahala.

Wunin ranar aikin na wuni yi sallah kawai ke tashi na Abida kuma na gidansu tana mana ɗinkin keke ko abincin kirki ban ci ba,tara saura na yi matuƙar gajiya na miƙe na fara tattara komai na share ɗakin na sauya kayan jikina Mama ta shigo ɗakin ta ce ba za ki ci abinci ba kike shirin kwanciya?

Kai na girgiza mata “Na gaji sosai Mama, kwanciya kawai nake son yi.”

Na kwanta bisa katifata ta fita tana faɗin “Yau dai gajiyar ta zo, ke da ke kai har sha ɗaya.”

Na fara lumshe idanu na ji dawowar ta a hankali ta fara kiran sunana na amsa ba tare da na buɗe ido ba “Husaini ya ce ana sallama da ke a waje.”

Ɓigit na buɗe ido “Don Allah fa Mama ƙarfe tara  ni wallahi barci nake ji.”

“Ai kuwa daurewa za ki yi ƙi tashi ki leƙa.”

Kamar zan fashe da kuka na ce “Don Allah ki yi haƙuri Mama.”

Ta fusata ta balbale ni da faɗan idan ma Abakar nake ƙulafuci in sake lale, ta zura mini ido ne don ta ga iya gudun ruwana, to daga ta gane ni ɗin shashasha ce za ta sa ƙafar wando ɗaya da ni.

Ta fice tana ta faɗan zaune na tashi na haɗa kaina da gwiwa yaushe aka yi daren da har gari zai waye, duka wata nawa da mutuwar aurena da za a fara sako ni gaba da zancen wani auren.

Na miƙe tsaye na dauko hijab ɗi ta da na yi sallah doguwa ce har ƙasa na ɗora saman doguwar rigar da nake sanyawa don barci.

Na fita falo Hassana da Mama da Husaini suna zaune suna kallon shirin Daɗin kowa Mama ta ɗago ta dube ni “Haka za ki fita fuska ƙozai-ƙozai?

Na tura baki “Ni dai Mama haka zan tafi.”

Kallonta ta mayar ga allon talabijin ya ba ni damar wucewa ina fita Gate ban ga kowa ba hakan ya sanya ni fara waige-waige wani Mutum ya nufo ni da sauri ya tsaya a gefe na “Ranki ya daɗe ga mai kiran ki can.”

Na dubi inda yake nuna mini wata dalleliyar mota ce ta zamani kalarta ruwan madara na ƙara buɗe na kukana don in gan ta da kyau, wani haɗaɗɗen mutumi ne ya fito cikin ta sai na samu kaina da takawa zuwa inda yake gabana na dokawa da na rasa dalili na shaƙi haɗaɗɗen ƙamshin da yake sai na yi masa sallama.

Ya amsa yana kafe ni da ido ta cikin farin glass ɗin da na tabbata ya ƙara ma fuskarsa kyau.

Na gaishe shi ya amsa sai ya jeho mini tambayar na san Isah Ɗan Borno? Kai na ɗaga mishi na ce ƙanen mahaifina ne. Ajiyar zuciya ya fitar sai ya ce “Na gode sosai Ummu Radiyya ko?

Na ɗaga mishi kai hannu ya sa a aljihu ya ciro kuɗi sai ya miko mini “Ba ni lambar Isan.”

Wayata da ke hannuna na kunna na lalubo lambar na karanta mishi sai da ya gama kwashewa ya ƙara miƙo mini kuɗin na ce ya bar su na juya na shiga gida.

Inda na bar su Mama nan na same su na zauna kusa da Husaini ina harararsa “Ashe ma Baba Isah yake nema ka sa aka katse mini barcina.”

Ya ɗaga hannuwansa”Ni dai wallahi Direban motar ne ya tambaye ni Ummu Radiyya da kuma na ce kina ciki ya ce don Allah na kira ki.”

Fuskar Mama na duba sai na ga ta sauya jin zancen da muke tattaunawa, na miƙe na shiga ɗaki na kwanta ban daɗe ina tunanin dalilin da ya sa sai da aka kira ni ya tambaye ni lambar Baba ba da ko Husainin ya tambaya zai ba shi na shiga barcin da har lokacin ke cin idona.

<< Ummu Radiyya 11Ummu Radiyya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×