A ranar aka yi wunin Hassana ma sha Allah an fita kunya an yi mata komai da ake yi ma ‘ya.
Dakinta ya yi kyau shi kowa ke faɗi daga mahalarta bikin.
San da muka dawo gidan amarya kowa ya tafi gidansa sai yan Maiduguri hatta Lubna da Aunty Ya gana da suka so su ƙara kwana sai gobe Mama ta ce su tafi gidajensu, Mutum biyu suka bi Aunty Ya gana tunanin zuwan Bashir Lema ya hana ni tuɓe kwalliyata, ba a jima ba da idar da sallar isha’i na ji kiran waya ganin shi ɗin ne na fita daga ɗakinmu na shiga na Mama da take zaune tare da yayarta Maman Aunty Ya gana kusa da ita na ɗan duƙa, a hankali na ce mata ya zo yana waje.
Ta gyaɗa mini kai na miƙe na tafi tana faɗa ma yayarta angon ne ya zo da yaren kanuri.
Mayafina kawai na lulluɓa na zare ɗankwalina na rufa mayafin har kaina na fita.
Waige-waige na hau yi rashin ganin motar a inda na saba ganin ta, “Ga shi can ranki ya daɗe.”
Na waiwaya inda na tsinkayi muryar, Direban da ya saba kawo shi ne ya gaishe ni cikin rusunawa sai ya nuna mini wurin da motar ke ajiye da hannunsa, na isa wurin, ƙofar da na gani a buɗe na zagaya ƙafarsa ɗaya na waje na yi masa barka da zuwa bai amsa ba sai kallona da yake ya miƙa hannunsa ya buɗe dayar kofar ya yi mini alama da in zagaya na zagaya karo 0@na farko da na shiga motarsa kamar yadda ya yi ni ma ban rufe kofar ba bai ce na rufe ba hannunsa ya miƙo har jikinmu na haɗuwa ya rufe ƙofar ta wutsiyar ido na saci kallonsa ya yi kyau kamar kullum dama kuma shi ɗin m0ai kyau ne ga ƙamshinsa ya haɗu da nawa ya ba da wani irin ƙamshi mai tsayawa a rai.
Wayarsa ya kunna haskenta na ɗan rufe idona musamman da ya soma haska ni “Shi ya sa matar can ke mini ƙwalelen ganin ki ? Na yaba da aikinta.”
Ya sa ɗayan hannunsa da bai riƙe da wayar ya kamo hannuna wani yar na ji ƙunshina da aka tsara mini yake kallo ya kai baki ya sumbata murza hannun ya shiga yi kafin ya kashe hasken ya yaye mayafin da na rufe jikina har kaina ya haska yana kallon kitsona ya daɗe yana yamutsa shi, cikin wata irin murya yake tambaya ta wane irin turare na yi amfani da shi yana son shi zai sanya mini kuɗi na ƙara saye.
Ban yi magana ba saboda matsugunin da ya sama mini a ƙirjinsa wasu al’amura ya shiga gudanarwa da ƙiris ya rage ya aikata mai gabaɗaya na samu ya bar ni”Ban da rashin biza da ba zan bar ki ba.” Ya faɗi da muryarsa da har lokacin ba ta dawo daidai ba.
Ban ce komai ba sai kayana da ya raba ni da su nake ƙoƙarin mayarwa kaina ya mayar bisa ƙirjinsa yana faɗa mini irin sona da ya kama shi da halin da zai shiga a kwanakin da zai yi ba ni.
Ya yi ƙarshe da cewa in duba wayata ya sanya mini kuɗi in yi duk buƙatuna don yanzu komai nawa ya dawo wuyansa Hajiyarsa ta so a kai ni ɗakinta na fara zama kafin ya dawo shi ya ce a’a ya fi so a fara kai ni ɗakina, an kusa kammala gyaran gidan.
Hango lokaci a agogon motar ya sa na ce zan shiga gida ya ce “
Mu tafi na dawo da ke da safe.
Na ce “A’a. Ya ƙara matse ni a jikinsa da kyar na samu ya bar ni na ya fito ya yi mini rakiya har ƙofar gida ya faɗi mini ban da dare da ya yi da ya shiga sun gaisa da yayar mahaifiyata da Baba Isah ya ce mishi ta zo.
Na ce Tana nan har Allah ya dawo da kai.”
Yana tsaye na buɗe Gate din na shige.
Na yi tunanin zan samu su Mama sun kwanta sai dai saɓanin tunanina har lokacin suna zaune a inda na bar su motsina suka ji duk da ɗauke sawun da na yi na shiga na kwanta ina jiyo muryar Ya kaka na faɗin ita fa ba ta so a ɗaura aure a bar yaro gida Mama na mata bayani.
Ina kwance kan katifata idanuwana na kallon sama cike da tunanin abin da ya wakana tsakanina da Bashir Lema kulawar da yake ba ni ta fara sauko da zuciyata daga tsinin da ta hau na ƙara yakice Abakar daga cikinta sai dai ya kan faɗo mini ina tunanin dalilinsa na yin watsi da ni bayan ya fito.
Na gyara kwanciyata ina jin wani irin tsoro da ke baibaye ni game da wannan aure da na rasa na meye.
Da safe da ni da baƙi biyu da suka rage muka yi abin karyawa muka gyara gida hantsi na yi Nabila ta zo muka zauna a ɗakinmu ni da Hassana da ya zama nawa a yanzu Nabilar ta dame ni na kira Bashir Lema na faɗa mata tun safe ya kira ni mun yi bankwana amma ta ƙi yarda muna cikin taƙaddama kiran Aunty Larai ya shigo wayata na dubi Nabila na ce “Aunty Larai ce.”
Ta harare ni “Ai tuni na gane gwarza ni kawai kike ba wani sanin da ta yi.”
Na yi yar dariya na ɗaga kiran ba ta saurari gaisuwar da nake mata ba ta fara faɗin “Ummu kin kuwa san kuɗaɗen da Yallaɓai ya cika mini asusun bankina da su wai tukwicin gyara mishi ke da na yi? Sosai yake son ki Ummu don haka kika je biyayya sosai za ki yi masa. Gyara kuwa ya haɗu da shi na dinga gyara ki.”
Dariya na dinga yi don da jin kuɗaɗen sun kiɗima Aunty Larai
Ta ce “Dariya na ba ki ko? Na ce “A’a.” Ta ce “To mayar da hankali mu yi zance na gaskiya.”
Na kuma dariyar kaɗan sai na nutsu kamar tana gani na yadda ake kula da miji ta fara gaya mini sai kuma ta ce bari dai ina nan zuwa ta katse kiran na ajiye wayata na fuskanci Nabila da ta zuba mini ido labari na ba ta yadda muka yi ta zabga mini harara”Wanda ake cewa ba a so tun ba a je ko’ina ba an yi lub!
Na yi narai-narai “To ya kike so na yi Nabila? Ni ɗin kin san ba mai tsananta al’amari ba ce Baba Isah ya dage ba shi ba ni idan ban amince ba ga Mama na fushi da ni ba zan iya jayayya da su ba, daga su ɗin mutane ne masu muhimmanci a rayuwata.
Na haƙura da komai zan yi musu biyayya iyakar iyawa ta.”
Ta gyaɗa kai “Ƙwarai kuma kika yi farar dabara.”
Na ba ta labarin tsoron da na kan ji da na rasa na mene ne.
Ta ce “Mu yi ta addu’a in sha Allahu alheri ne.”
Na ce “Uhmm! Nabila kamar ba ke ke damu na da zancen karatu ba.” Ta yarfe hannuwa “Auren ai yana gaba da karatun, idan da rabo kin ci gaba a ɗakinki. Ko ni na samu wanda ya yi mini da gudu duk so na da karatun zan jingine shi na yi wuf da shi.”
Na ce “Allah? Ta ce “Wallahi.”
Sallama da ake yi ta sa mu yin shiru, sai maraba ake yi ma baƙuwa.
Ya kaka ce ta leƙo ta ce in fito na gaida surukata, mamaki ya rufe ni na dai miƙe na rufe jikina da laffaya na fita farar dattijuwa ce mai matuƙar kamala ta amsa gaisuwar da nake mata ni da Nabila cikin fara’a .
Ko ya aka yi ta san ni ce matar ɗanta kira na ta yi wurin ta na zauna kusa da ƙafarta bayani take ma su Mama na tafiyar ta sa, yana dawowa zan tare.
Su Mama suka yi ta addu’a, kwalaye aka shigo da su da ta damƙa mini na amsa da godiya hira suke ta yi da su Mama kamar da ma sun san juna.
Ni dai muka fita da Nabila muka shirya abincin rana sai da ta gabatar da sallar azahar ta ci abincin ta yi shirin tafiya Mama ta cika ledoji da alkaki da cincin da dubulan na Hassana da za a kai mata anjima muka raka ta ni da Nabila don na hana Nabilar tafiya gida saboda kunyar bakuwar da ta zamanto suruka a gare ni duk da ta ce ni ɗiyarta ce in bar jin kunyarta.
Direba na ƙofar gidan yana jiran ta ni na buɗe mata ta shiga Nabila ta ajiye ledojin ya ja suka bar wurin Nabila ta tafi gida ni ma na shige namu gidan na samu su Mama na maganar kirkin ta.
Muna chart da Bashir Lema muna voice note don yana faɗin yana son jin muryata har dai lokacin ban gama sakewa da shi gabaɗaya ba, Mama ba ta bari na fita duk da shi ya ce in fita abu na na so ci gaba da saƙar zanen gadona sai Abida ta dinga karɓowa tana kai wa Mama ta hana rashin abin yi ya sa nan da nan zaman ya ishe ni sai dai Nabila da nake samu tana shigowa.
Ana saura sati guda in tare Aunty ta zo ta ɗauke ni gyaran da ake yi mini sai ya zama wasa kan na yanzu na yi kyau har na gaji ana gobe tarewa ta ya dawo amma ya shaida mini Legos zai kwana sai gobe zai iso Kaduna.
A ranar ta mayar da ni gida ba komai za a yi ba kai ni kawai za a yi sai su cincin da alkaki da Aunty Larai ta yi mini na musamman.
Kai ni ya kasance da rana maimakon dare da aka tsara saboda sanarwa daga gidansu a kawo ni sun shirya walimar taryata kwalliya ta musamman aka yi mini sai sannan Aunty Larai ke ta fada kan rashin saya mini suturu masu tsada da kuɗaɗen da ya bayar don. gidansu gidan manya ne na dai yi kyau an naɗe ni da laffaya ga ƙamshi na musamman wanda da ka shaƙa za ka san ga masu abin nan sun zo wai yar garuwa ta ga hadari ta ce ga masu abin nan bari mu zubar da namu.
Lafiyayyun motoci aka kawo na ɗauka ta su Aya suna cikin masu tafiya Gwoggo Mamu ma ta dawo kai ni.
A karo na biyu na zubar da hawayen rabuwa da gida yayar Mama da ba ta tafi ba ita ta riƙe ni aka fitar da ni fuskata na rufe ƙawayena har da su Nabila suna tare da ni, a ƙofar gidan sauran motocin suka Parker wadda ta ɗauko ni ce kaɗai ta shiga ciki muka fito ya kaka na faɗin “Ma sha Allah Ummu irin wannan gida Allah ya zaunar da ke lafiya da yaren kanuri take maganar wanda ina ji sai dai ban iya mayarwa.
Nabila ta zo ta ta ɗan buɗe mini fuska”Ki dubi inda kika kawo mu amarya.”
Harara na balla mata muka fara takawa ginin shi ya mamaye filin gidan don haka ba wani fili amma fa gidan ya ƙeru wani isasshen falo aka fara shigar da ni bisa jagorancin matan da suka je biko step muka taka zuwa sama inda aka ce wuri na yake ma sha Allah kowa ke faɗi da aka shigar da ni falon da aka ce shi ne nawa aka wuce da ni dakin barcina da shi ma ya gaji da ƙeruwa turaren wuta aka kunna ko’ina ana guɗa, masu maraba suka gabatar da abincin saukar amarya suka ce za su tafi su kintsa da an idar da sallar la’asar za a tafi da ni can family house nasu.
An ci an sha da aka yi sallah kuma aka sake sabon shiri kowa ya gyara aka sake kwasar mu sai gidan nasu.
Kamar ranar bikin Su’ada yau ma cike yake, wasu mata suka tare mu suka kama hannuna suka tafi da ni har gaban Hajiyarsa da ke tare da jama’a albarka ta yi ta sanya ma aurenmu ta ce su kai ni part ɗin Haj Rabi abokiyar zaman ta ita ce mai bi mata, ita ma albarkar ta sanya aka wuce da ni wurin ƙaramar su Haj Balaraba.
Yan gidan sun ta gabatar mini da duk wanda na gani ina jinjina yawan zuri’arsu.
An fara gabatar da walima wurin da aka tanada domi na aka ajiye ni su yan gidan ke ta karakaina suna zuwa suna ɗaukar hoto da ni tare da gabatar mini da alaƙar su da angon, an ci an sha an yi nasihohi zuwa magrib taron ya tashi wurin Haj aka mayar da ni.