Skip to content
Part 17 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Muka ci abinci tare da su Nabila, Aunty Fatahiyya ta zo ta ce ma su Aunty Larai idan za su tafi akwai motoci da za su mayar da su ni anan za su bar ni.

Ai kam shirin tafiya suka fara suna yin isha’i suka tafi suka bar ni da su Su’ada sai ja na suke da zance murmushi kawai nake musu, suma tafiyar suka yi ya zama part ɗin Hajiyar ba kowa sai wasu yan’uwanta.

Aikowa ta yi aka kira ni daga bedroom ɗinta na fita ita kaɗai na samu a falonta sai Bashir Lema da na lura da shi daga baya kaina ƙasa na zauna, nasiha ta yi mana ma fi ƙarfin nasihar kansa ne tana ta jaddada ya kula da haƙƙina da ke kansa.

Ta sallame mu ya miƙe bayansa na bi har harabar gidan kamar ba shi ne da magrib ba masaka tsinke ba yanzu sai iska da sanyi mai ratsa jiki.

Ya buɗe mini gaban motar na shiga na zauna sannan na gaishe shi da yi masa barka da dawowa tambayar yaransa na yi masa a ƙarshe wani ƙayataccen murmushi ya saki “Na bar su a Lagos gidan wani aminina one week za su yi.”

Murmushi ya suɓuce mini don har raina  na ji ina son yaran nasa.

Yana ja na da zance muka kai gidan, wani dattijo ya wangale Gate ya kutsa hancin motar ciki sai da ya fara fita na buɗe na fita ko da ya zagayo ya gan ni tsaye sai ya wuce ƙofar shiga ciki ganin ya sa key ya buɗe na tabbatar ba kowa a gidan sai mai gadi da muka bari bakin Gate hannuna ya kama muka shiga ciki saman muka haye bai shigar da ni ɗakin da aka kai ni ba wani daban ya buɗe “Wannan shi ne nawa, dukkan su kuma naki ne idan kin fi son nan ɗin za ki iya dawowa.”

Kai na ɗaga mishi bedroom din ya wuce riƙe da hannuna na zauna bakin gado ya soma tuɓe tufafin da ke jikinsa abin da ya sanya ni sunkuyar da kai ya dawo daga shi sai guntun wando ya hawo gadon ya kwanta ya jingina da pillow”Ki cire kayanki mu kwanta.”

Kamar ina jira na miƙe ganin zan bar dakin ya ce”Ina za ki?

Na haɗiyi yawu “Can zan koma kayana na can.”

Miƙewa ya yi ya bi bayana abin da ban so ba yana tsaye yana kallona na ciro kayan barci da su Lubna suka jera mini a wardrobe, toilet na shige can na tuɓe kayan jikina na yi brush na sanya turaruka riga da wando na sanya na yane jikina da mayafina har alwala na ɗaura kafin na canza kayan don ina tunanin za mu gabatar da sallah kafin kwanciya.

Na fita na mayar da kayan da na tube cikin wardrobe hannuna ya ƙara kamawa “Ko kin fi so mu kwanta anan?

Kai na girgiza ina rufe idanuwana don yadda ya kama dukkan hannayena ya kuma kafe ni da ido “Ko’ina ya yi mini.” Na faɗi a hankali “To mu koma can amarya.”

Can ɗin muka koma abin da ya tambaye ni ina buƙatar wani abu?

Na ce a’a, ya ce na ci abinci wurin Haj? Na ce E. Daga haka wasanni ya fara da ni ina ta jin mamaki ba mu yi sallah ba ta neman albarkar aure tuna kusan rabin rayuwarsa a Turai ya yi ta ya rage mini mamakin ni dai na karanta addu’ar da Manzon tsira ya koyar a yayin saduwa.

Wata irin kiɗima ya shiga da ta fi wadda Abakar ya shiga a darenmu na farko kuma ya zama na ƙarshe.

Ni kuma na sha azabar da na kasa banbance ta da ta farko, ya tsahirta mini ya kuma ta lallashina da taimakonsa na tsaftace jikina ya zaɓo mini wata rigar barcin na sanya muka kwanta yana riƙe da ni a jikinsa,barci na yi sosai da sai da na farka na ga haske ya shigo ɗakin shaidar gari ya jima da wayewa mamaki ya ishe ni ganin shi kanannaɗe da ni kenan shi ma bai tashi ya yi sallar ba ?

Na fara motsi da jikina sai ya buɗe ido saki na ya yi sai ya yi  miƙa ya sanya hannunsa yana shafa gashina yana mini sannu.

Hannuna ya kama na sauka muka shiga bathroom duk yadda na kai da jin kunyarsa sai da ya sa na yi wanka gabansa na ɗaura alwala ina ɗaure da tawul na fita mai na murza sai na ciro hijab da zane da na ɗauko tun daren jiya na kabbara sallah.

Na yi sallama ya fito, kusa da ni ya kabbara tashi sallar azkar na kama daga ba ni da Kur’ani anan ya kama hannuwana yana jifa ta da wani lallausan murmushi na lumshe idona da na fahimci ido yake so mu haɗa “Ina kwana? na ce cikin siririyar murya bai amsa ba sai kamo ni da ya yi muka koma gado, kalamai yake jera mini da suke sanya ni cikin wani yanayi da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba.

Muna cikin haka wayarsa ta ɗauki ƙara ya dauko ta ya sa a kunne “Ok kawai ya furta ya juyo gare ni ya ce yana zuwa kai na ɗaga masa ya fita ɗakin.

Allah ya rufa mini asiri lulluɓe nake cikin duvet don daga ni sai zanen da na idar da sallah ya zare mini hijabi,  jin turo ƙofa bai sa na ji komai ba sanin shi ne sai dai bayan shi wata mata ce ɗauke da kwando matar za ta girme mini ta gaishe ni har tana ranƙwafawa na amsa ina jin ba daɗi yadda ta shigo ta riske ni ta ajiye kwandon ta juya ya matso jikin gadon sai ya miƙo mini hannunsa “Sauko mu yi break past.” Zanen jikina na ƙara ɗaurewa sai na yaye abin rufar na sauko yana ta kallona, kwalliya na faɗa mishi zan yi sai da ya raka ni har ɗakina ya ce mini zai je ya yi wanka na zauna gaban mirrow na yi shafe-shafena na sanya turaruka sai na koma wurin kayana atamfa na ɗauko ɗinkin riga da skirt sanin in dai aka yi mini daidai jikina suna matuƙar karɓa ta, sun zauna jikina sun karɓe ni fiye da zato na yi ɗaurin ɗankwali, ina ƙara kallon kaina ya shigo bayana ya tsaya ya sanya hannuwansa ya zagaye cikina yana duba na ta cikin madubin na rufe idona yaba kyawun da na yi yake yi ba komai na gane cikin zantukan na sa ba don yunwa ke damu na a lokacin, duk yinin jiya ban ci wani abin kirki ba ga wuyar da na sha hannunsa ta kara taimakawa wurin wawakewar uwar hanjina.

“Ina jiran 10.am  ta yi na aika a yi mana order sai ga shi Haj ta aiko mai aikin da ta ɗaukar miki za a ƙaro miki wata don ta yi miki kaɗan.”

Ajiyar zuciya ta ƙwace mini jin zancensa wai mai aiki daya ta yi mini kaɗan ko a gidanmu wa ke mini aikin?

Ya ja ni muka fita maimakon bedroom falo muka tafi muka hau dinning, an shirya kayan abincin da na baro a bedroom dinsa  shi ya zuba mini komai ɗan Tea ɗin da ya haɗa mini na kalla ina tunanin inda zai maƙale mini sai na tuno kofina na gida da nake shan Tea ban gane bambancin da ke tsakanin su ba sai da na sha wannan ya ji wadataccen ingredients saɓanin na gidanmu da muke shan shi a yadda ya samu ga soyayyen ƙwai har da farfesu na naman kaza, duk komai na ci na sha bread dinma na masu da shi ne don narkewa yake a baki duk da komai kaɗan na ci saboda wanzuwar sa a wurin na ji cikina ya cika shi kuma na yi mamakin abin da ya ci Black tea sai naman nan da bai fi hudu ba.

Ya riƙe ni muka koma kujerun falon ya faɗa mini nan falona ne ni da shi ya ja ni muka sauka ƙasa wata ƙofa ya buɗe muka shiga  falo ne matsakaici sai ƙofofi huɗu, uku ya buɗe bed room ne da toilet ya shaida mini na yaransa ne su uku dayan ba kowa sai nake ta ƙiyasta shekarun yaran da har za a bar su ƙasa su kaɗai muka fito wata hanya ya bi da ni sai muka samu ƙofa ya tura ta buɗe kitchen ne irin na yan gayu sosai ya yi matuƙar burge ni don ban taɓa ganin irin sa a ido buɗe ba sai dai a akwatin talabijin.

Ganin na tsaya daga ƙofa ya dawo ya kama hannuna muka shiga ciki abubuwan amfani da aka zuba ya nuna mini daga nan muka shiga store ya kuma tambaye ni idan akwai abin da nake so ban gani a wurin ba kai na girgiza mishi na ce babu ya ce “Wannan da ta shigo kamar yadda na faɗa miki ita za ta dinga yi miki komai za a samo wata saboda su Dina.

Dina! Na maimaita sunan a raina muka fita, a falon ƙasan muka zauna matar nan ta fito ta ƙara gaishe mu ta tambaye ni abin da za ta yi, ko’ina fes yake yana tashin ƙamshi  na ce ba komai, ta ce “To za ta koma gidan Haj ta ce ta zo ta karɓar mana abinci.

Na ce sai ta dawo ta fita ya rufe ƙofar ya ja ni muka haura sama ɗakinsa ba mu sauko ba sai da ta dawo.

Tsawon wunin nan bai matsa ko nan da can ba yana tare da ni sai washegari su Nabila suka zo shi ne ya ce mini bari ya je wurin Haj.

Kitchen muka shiga muka dafa abin da suke so ni dai da duniya ba abin da nake so irin madara, ta gari na kwaɓa da ruwan ɗumi na sha na yi ƙat sai na ɗan ci naman da Nabila ta gasa, na kasance cikin nishadi na zuwan nasu ga waya na yi da Mama da su Lubna da Aunty Larai,  Lubna ta ce mini za su zo gobe ita da Aunty Ya gana suma wuni suka yi mini sai dai su ba su shiga kitchen ɗina ba Basira sunan mai aikin ita na sa ta yi duk abin da suka ce suna so .

Hassana ma mun yi waya da ita sauran ranakun duk yammaci fita yake da ni mu zaga wuraren shaƙatawa da ke cikin garin Kaduna mun yi hotuna a can wurin yawonmu,  ya koya mini son shi da kaunarsa a ɗan zaman namu.

Ranar da na cika sati guda ina sane ranar ya’yansa za su iso kamar yadda ya faɗa na shiga kitchen tare da basira duk da son da ya yi na zo mu kwanta,  muka shirya abin ci da na sha lafiyayyu.

Mun gama kenan Basira na shirya tebur ina goge hannuna ya shigo kitchen ɗin cikin shigar da har na gane ya fi mu’amala da ita shadda ce amma ɗinkin ƙarami ne sun zauna jikinsa ya yi kyau ƙwarai bai sa hula ba sai farin glass.

Hannu ya miƙo mini na noƙe kafaɗa ina ɗan murmushi “Why? Ya faɗi yana jifa ta da wani narkakken murmushi ya mayar da hannayensa ya naɗe “Ban yi wanka ba.”

Ya duba agogon hannunsa “To ki yi wankan idan na dawo zan gani. Abokaina da suka zo jiya mai baƙaƙen kayan ya kira ni Zaria za mu tafi idan kin yi wanka ki jira ni.” Na ce “Abinci fa?  Ya ce “Kar ki damu.” Na ƙara cewa  “Su Dina fa?  Ya saki murmushin da ke ƙara masa kyau ya ce  “Sun kusa isowa.” Ya tako zuwa inda nake ya shafi kumatuna “Sai na dawo.”

Duk yadda nake daga ni sai wata yar riga da ta zarce gwiwata kaɗan sai hula haka na bi shi har inda motarsa take ya shiga ya ɗaga mini hannu na yi masa kyakkyawar addu’a sai da ya ja motar na koma ciki.

Sama na hau na yi wanka tare da kwalliya wata doguwar riga ɗinkin free size na sanya sai sarka da yan kunne fashion har da abin hannu ban fita ɗakin ba gadona na hau na kunna wayata na shiga WhatsApp, saƙonnin da na taras an ajiye mini na duba na yi reply kafin na sauka na kira Mama da duk yau ban kira ta ba mun daɗe muna magana har ta tambaye ni na kira Baba Ali tun da na na tafi na ce mata a’a ta ce na kira shi sai na gaishe shi na ce mata to.

Kiran nashi na yi da muka ƙare waya da ita har da ma Baba Isah duk da shi na kira shi, ajiye wayar na yi saboda barci da na ji na fara ji na duba agogon da ke kafe a bangon dakin ƙarfe ɗaya da rabi na yi hamna sai na rufe idona.

Barci ya fara ɗauka ta na ji knocking da faɗuwar gaba na farka na miƙe ina alaƙanta hakan da rashin yin addu’a da zan kwanta, na sauka gadon na isa na buɗe kofar Basira ce sai da ta ɗan ranƙwafar da kanta ta ce “Barka da rana Haj.” Na amsa ta ce su Amal sun iso wata faɗuwar gaban na kuma ji na ce mata ina zuwa

<< Ummu Radiyya 16Ummu Radiyya 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.