Skip to content
Part 19 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Part ɗin abokan zaman Hajiyar muka fara shiga muka gaishe su sai muka yi ƙarshe da na Hajiyarsu.

Tana ta ina ta saka ina ta aje da ni hakan ya sa ni farin ciki, an kawo mana abinci shi ya ci ni ban ci ba, sai da ya kammala ta dube shi “Su Amal sun iso ko?

Ya ce E.  Ta ce ” Umar ya ce ya gan ta ɗazu, ban ji daɗin shigar da aka gan ta da ita ba, nan fa Arewa ce cikin hausawa musulmai ba ƙasar waje ba garin arna. Ya’yanka mata ne ka koyi tsawatar musu kan tarbiyyarsu, kowa yana son ɗansa amma kaza tana taka ya’yanta ba don ba ta son su ba wa zai zo neman aurensu idan ba mai irin ɗabiunsu ba ?

Kai ya shafa “Kar ki damu Haj, ba fa wani abu suke yi ba ke kina hange irin na mutanen da ne,  amma yanzu ko anan ɗin normal ne.”

Hawaye Haj ta fara sharewa da suka tayar da hankalinsa har ni ma da nake zaune ina sauraren su.

Haƙuri ya shiga ba ta tana kuka tana roƙon shi kan ya gyara tarbiyyar ya’yansa.

Mun tashi za mu tafi ya yi gaba ta tsayar da ni haƙuri ta ba ni kan ɗabi’un jikokin nata da zan ci karo da su, ta tambaye ni lafiya dai muke na ce E.

Har ƙofarta ta rako ni sannan ta juya.

Muna hanyar komawa yana maganar mahaifiyarsa da yadda take kallon rayuwa dole sai an yi irin ta zamaninsu, ta kasa gane sauyin zamani ni dai daga uhmm sai uuhm nake amsa mishi don na fi ganin gaskiyarta, ganin da yake hakan ba komai ba ne saboda ruƙo da aƙidun yahudu da nasara wanda suke rayuwa cikin su .

Muna isa wurin yaransa ya zarce na hau sama na shiga ɗakina na fara tuɓe kayan jikina in samu na kwanta farar riga mara nauyi tsawonta iya gwiwa na sanya ina cire yan kunnayena ya shigo “Yau nan za mu kwanta? Ya tambaya yana duba na kai na ɗaga mishi ya isa gadon don har ya yi shirin kwanciya, ni ma na kammala na iske shi hannuwansa ya buɗe mini na shige wata leda ya lalubo hannuna ya sanya mini, a cikin kunnena ya raɗa mini in buɗe na tashi zaune daga jikinsa na ciro kwali da ke cikin ledar na buɗe kwalin dalleliyar waya na yi arba da ita mai matuƙar tsada na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina mishi godiya.

Ya zagaye bayana da hannunsa ɗaya ɗayan kuma yana sarrafa wayar sai da muka gama ganin ta ya sanya ta a caji ya kashe hasken ɗakin muka kwanta.

Ana tayar da Sallah a masallaci ina farkawa saboda sabo, na dubi gefen Abban Dina kamar yadda na fi kiran sa tun da ya ba ni labarin ya’yansa, barcinsa yake hankali kwance na nemi zare jikina ya ƙara rungume ni a hankali na ce Toilet za ni ya sassauta riƙon na sauka gadon, ruwa na tara mai zafi saboda sanyi na yi wanka kala biyu na ɗauro alwala, mai kawai na shafa sai turare gudun kar rana ta fito ban yi sallah ba na ciro wata doguwar riga na sanya da hijab na hau pray mat, a nutse na gabatar da ibadata, ina karatun Alkur’ani ƙasa-ƙasa na jiyo motsinsa na waiwaya ƙoƙarin saukowa yake muka haɗa ido murmushi muka yi ma juna ya wuce na bi shi da kallo tunani na ɗarsuwa a ma’adanar sirrina, cikina da ya fara kiran ciroma ya tuna mini rabo na da abinci tun jiya da la’asar.

Ba zan iya jurewa ba har a jima zan miƙe ya fito na koma na zauna har ya  zura jallabiyarsa ya tada sallah.

Yana idarwa janyo ni ya yi na kwanta a cinyarsa ina faɗin ina kwana da siririyar murya ya amsa sai na nemi miƙewa ya tambayi inda za ni na langaɓar da wuya yunwa nake ji ya shafa cikina sai ya yi murmushi na miƙe hijab ɗina na ninke na fita.

Basira na samu a kitchen daga abin da take sarrafawa na san ba namu ba ne, tana gaishe ni na fara neman abin da zan taimaki kaina bread na soya da ƙwai na haɗa Tea mai kauri anan na karya na koma sama jira na yake muka kwanta sai goma muka tashi shi ya yi wanka na raka shi ɗakinsa ya shirya muka dawo na shirya muka sauka ƙasa kan dinning su duka ukun shi ya isa wurin su suna gaishe shi yana ba su feck, Amal ta tura mishi kujera ya zauna shi kuma ya tura ta kusa da shi ya kira ni kai na girgiza na ce na ƙoshi.

Daya daga cikin kujerun falon na zauna suna karyawar su ina latsa sabuwar wayata da ya kammala fita ya ce zai yi, ina son masa rakiya amma duk sun kewaye shi daga inda nake zaune na ce sai ya dawo.

Suka fita yana jaddada musu su je gidan Haj su gaishe ta .

Ina nan zaune suka dawo, falon suka zauna sai na miƙe na koma sama na ƙara kallon hotunan jiya a falon ƙasa na ci burin kafe su idan an kawo, amma dai yanzu ban jin ƙarfin gwiwar kai su.

Da na gaji da zaman tunane-tunane Nabila na kwada ma kira na ce don Allah ta zo mini wuni ta ce ba ta da kuɗi na ce ta dauko mai motan idan suka zo zan biya.

Ta ce ga ta nan zuwa wanka za ta yi. Na zauna zaman jiran ta ina jin duk na takura, tun da aka kawo ni tare da shi nake wuni idan yamma ta yi ko dare mu fita tare, in shiga kitchen in yi duk ɓannar da nake so da madara idan na yi baƙi ne kawai yake bari na da su ko ya fita idan yana da wurin zuwa ko ya shige ɗakinsa.

Wayata ta yi ƙara Nabila ce ta ce na ba mai gadi kuɗin ya kawo mata sun iso, cike da mamakin saurin da ta yi na miƙe drawer na buɗe kuɗaɗen da abokansa suka zo ina da kwanaki uku suka yi mini kyautar su na zaro dubu biyu na sauka ƙasa suna nan a falon na ratsa su na fita tsaki na ji an ja ban waiwaya ba, ban ba mai gadin ba da kaina na leƙa tana tsaye jikin keke napep ɗin ta iso wuri na dubu daya ta amsa ta koma ta ba shi ta dawo wuri na muka riƙe hannu zuwa ciki.

Shigowar mu sai na ga ta dube su ta ce Sannunku rashin amsawar su ya sa ta dube ni mamaki ƙarara a fuskarta na ƙara riƙe hannunta muka haura sama wani tsakin na kuma ji an saki “Su waye waɗannan?  Ta tambaye ni tun ba mu gama hayewa ba ban ba ta amsa ba sai da na buɗe ƙofa muka shiga muka zauna”Yanzu ba ki gane su ba? Ta girgiza kai “Su waye? Na yi yar dariya “To ai da kin dube su da kyau, mutanenki ne da kika nuna mini pics ɗinsu a wayarki tare da maigidan nan.”

Ta gwalo ido “Ki ce Allah sune? Mene ne alaƙar shi da su?

Na yi ɗan murmushi “Yayansa ne.”  Zumbur ta miƙe tsaye na janyo ta na zaunar “Ta ina zai haifi kamar waɗannan? Na yarfe hannuwa “Ban sani ba. Amma dai ga shi ya suntulo abin sa.”

Ta yi yar dariya “Wallahi har kin ba ni dariya, wai ya suntulo abin sa amma dai wallahi da mamaki ango ya kwana da ƙunzugu.”

Dariyar muka ƙara yi ta ciro wayarta a jaka ta danna kira, sai da na ji sunan da ta ambata na gane wadda ta kira Su’ada na maimaita sunan, fakare na yi har ta gama jera tambayoyinta ta kuma yi fakare cikin sauraro sakanni masu yawa ta ɗauka sai ta ajiye wayar ta fuskance ni ta kama hannuna “Kin ji shekaru ashirin kacal yake da su aka yi aurensa da mahaifiyarsu.” Na jinjina kai cike da wani sabon mamakin.

Mun yi ta hira har aka kira Sallah muka tashi muka bayar da farali na ce ma Nabila “Ki taso mu je mu yi girki.”  Ta kishingiɗa “Wallahi liƙis nake ji na ina mai aikinki ki amso mana kawai.” Ban ƙi ta ta ta ba na tashi na fita sai dai a, flate huɗu kacal Amal ta bai wa Basira umarnin yi, don haka ba rabona ballantana wata baƙuwata.

Na dubi Basirar da ɓacin rai ga

nin yadda na kumbura kamar an sa mini yeast sai ta duƙa gabaɗaya jikinta ya shiga rawa “Allah ya huci zuciyarki ranki ya daɗe ki yi mini afuwa.”

Na ɗaga mata hannu “Me ya sa kike ɗora buƙatar su sama da tawa? Don wa aka kawo ki aiki gidan nan?

Cikin roƙo ta ce “Saboda ke.”  “To amma me…..

“Don Allah na ce ki yi mini rai, yanzu zan ɗora miki.”

Kai na girgiza “Ba na so.”

Na fita kitchen ɗin raina na zafi.

Gani na rai ɓace Nabila ta ce  “Ya dai? Na ba ta labari tare da ɗorawa da labarin farkon dawowar su.

Ta zabga tagumi bakinta ya furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!

Na dafa kafaɗarta sai ga hawaye shar sun wanke fuskarta “Addu’a Ummu, ita za ki dage da ita sai kuma haƙuri, haƙuri mai yawa za ki sa kafin ki ga ƙarshen abin nan.

Tsakani da Allah kin faɗa wata jarabawa ta ya’yan miji.” Ta share hawayen na yi murmushi na ce “Kina kuka ta ina zan samu ƙarfin zuciya? Ke da za ki ƙarfafa ni za ki sa na gaza? Na dauko wayar da ya ba ni daren jiya na nuna mata na nuna mata hotunan da muka yi sai da ta natsa na ce ta zo mu je mu yi girkin ta yarda muka sauka ƙasa suna cin abinci muka wuce kitchen Jallof din taliya ta ɗora mana don mu yi sauri ni na taimaka mata da yanke-yanke da kifi ta yi amfani cikakkun mintina talatin muka kammala na ɗaukar mana lemo muka shirya abinci a wani madaidaicin tray muka fita.

Muna ci muna hirar karatun da ta fara, sai da ta yi la’asar ta tafi cikin kuɗin na ba ta dubu biyar.

Har yamma Abban Dina bai dawo ba mun dai yi waya da shi su kuma ban ga sun tafi gidan Hajiyar da ya ce musu ba .

Da ya dawo ya gaji sosai don ina jin horn ɗinsa na sauka cikin kwalliya da na yi ina ƙamshi ganin na gifta su Suhaima da Amal da suka fito dan taron sa suka fasa yana tsayar da motar na buɗe masa jikinsa ya jawo ni yana yaba kyan da na yi, ina jikinsa muka kama hanyar ciki sai da za mu shiga na zame jikina suka taho suka yi masa oyoyo bai zauna ba ya ce musu ya gaji sama zai hau ɓacin rai ne ya bayyana a fuskarsu musamman Amal muka haura saman wanka ya ce na taya shi wanda ya jiƙa ni ya sa ni wani wankan, ƙafafu kawai na matsa mishi ya ce mu kwanta da na yi zancen abinci ya ce na bar shi ya ƙoshi.

Da safe ma yana yin sallah ya fita ya duba su ya dawo wurina soyayya da tarairaya da ke cika zuciyata yake gwada mini.

Ƙarfe goma da rabi muka ji knocking ba sutura jikina duvet ɗin da na rufe rabin jikina na yi saurin kai shi har ƙirjina shi kuma da ke sanye da guntun wando ya ɗauki singlet ya sanya,  sai da ya zura ƙafafuwansa ƙasa ya amsa don ba a daina ƙwanƙwasawa ba,  Amal ce raina na ji ya yi wani irin ɓaci daga inda take tsaye ta ce “Morning Papi.” Ya amsa mata ta ce sun fito ba su gan shi ba.

Miƙewa ya yi suka fita wani abu na dinga haɗiyewa na takaici wannan wace irin rayuwa na faɗo? Tagumi na zuba da hannayena bi-biyu idan fa abin ya yi yawa ni kam ba zan iya ba.

Zan gan shi yanzu zan gan shi anjima shiru kamar an aiki loma zagayen maƙoshi gadon na sauka na ɗauko zane na ɗaura zuwa ƙirjina na fara gyara gado sai ga shi ya shigo ko tayar da kai na dube shi ban yi ba  “Baby.” Ya kira ni na tada kai wardrobe ya buɗe ya ciro kaya dayake mun raba kayanmu a ɗakinsa da nawa “Za mu fita da su Dina, zan kai su gidan Haj, akwai gidajen da Haj ta ce su je zan kai su kin san yara sai da lallaɓawa.”

Kalamansa na ƙarshe suka ba ni mamaki na haɗiyi yawu “Ya yi, sai kun dawo.”

<< Ummu Radiyya 18Ummu Radiyya 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×