Skip to content
Part 23 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Muna haɗa ido da Amal ta ce “Ke yar ƙauye ki saurara da kyau ki ji gidan nan da kike gani Dina ta yi art dinsa, nan inda aka sanya ki Mommynmu ta faɗa ma Dina yadda za ta yi mata, amma an sanya ki ciki, wallahi ba naki ba ne ba za ki zauna ciki ba.

Suhaima ta amshe “Ki zo ki fita! Na dube su na dubi inda kayana suke wayam! Kamar sun san tunanina Amal ta ce  “Mun fitar miki da kayanki fita ki bi su.” Daga nan suka fara bala’i su yi da hausa su yi da turanci, ni ma ramawa nake na ce ba zan fita ba takaicina daya rashin sutura a tare da ni da sun ga ɗanyen kai duk yadda na yinƙura sai towel din jikina ya fara barazanar ɓallewa na yanke fita in nemi kayana sai dai a yi ko ni ko su na wuce su na fita ba kayan nawa a falon suka rufo ƙofar bedroom din Suhaima ta ce hakan ya fiye mini sauƙi raina ya gama ɓaci don haka Amal na cewa kayana na main parlor na fita ba su bar ni ba datse kofar suka yi suka take mini baya.

Dina idona ya fara tozali da ita zaune a falon tana kaɗa ƙafa kafin na hango akwatunana da kayan kwalliyata na nufi inda suka watsar da su Bashir lema ya fito su yake tambaya me ya faru suka kuma mayar mishi da yadda suka faɗa mini, a wannan gaɓar na yi tunanin zai kalli tsantsar rashin dacewar abin da suka yi ya tsawatar musu sai dai saɓanin haka lallashin su ya yi ya ce su je wajen su su ci abinci ba zan koma wurin mahaifiyarsu ba.

Gaban akwatunana na duƙa hawaye na ta gudu bisa kuncina, ina tunanin inda zan raɓa in sanya kaya don ga masu aikin nan na ta karakaina, ga ni daga ni sai towel.

Ya tattara su har Dina suka shige wata ƙofa, ya dawo ina buɗe akwati rigar da ke sama na zaro ban kula da ƙaton arnen ba na miƙe zan sanya ya kare ni ban dube shi ba don yadda raina ke ƙuna, ina gama sanya rigar na duƙa na ƙara yamutsa akwatin na samu hijab na zura, wayata da na hango a yashe na isa na ɗauka sai na kama hanya

 “Ina za ki?

 Ya biyo ni yana tambaya ban tsaya ba ban kuma yi magana ba ya sha gabana”Me kike yi haka? Ina za ki na ce?

Zan koma inda na fito.”

“Me zai sa ki tafi? Ya yi mini tambayar da na ji kamar ya watsa mini ruwan zafi! “Kana tambaya ta me ya sa zan tafi ba ka ga abin da suka yi mini ba, su kaɗai ne ya’ya da za su yi ta cin zarafina? Zan tafi gidanmu aure na haƙura.”

Ina kai ƙarshe na fashe da kuka! Ya isko ni ya kama ni gam-gam na kasa kubcewa kalaman ban haƙuri yake jera mini da haɗa ni da girman Allah in koma kan dole na bi shi ban fasa kukana ba kofar da muka shiga farko ita ya kara nufa da ni sai dai kofar farko yanzu ya buɗe muka shiga wannan ɗaki ne guda sai dai katon gaske ne komai na rayuwa akwai daga kujeru har gado da wardrobe da mirror sai wata kofa da na tabbatar bathroom ne ya zaunar da ni bakin gado  “Ki zauna nan zan kawo miki kayanki, nan wurina ne babu mai korar ki na bar miki shi.”

Ya fita ya dawo da akwatunana idona na kan wayata ina shafa screen dinta da ya fashe, ya duƙo “Me ya samu wayar? Na nuna mishi “Za mu fita sai ki zaɓi wata dama ai ta tsufa.”

Na mayar da hawayen da suka taho mini ya wuce bathroom bai jima ba ya fito  “Zo ki yi wanka.” Sai sannan na dube shi da kyau ya sha wanka cikin wata fatar riga da gajeren wando masu taushi ƙafarsa ma farin silifas ne, fararen idanuwansa ya kafe ni da su na sunkuyar da kai ya matso “Tashi ki yi haƙuri.”

Na girgiza kaina don mayar da hawayen da ke ta barazanar sulalowa ya kai hannu ya shafo su “Ba na so, na ce ba na son kukan nan.” Ya ɗago ni na ce “Ni na yi wanka “Ki ƙara.”

Muka shiga bathroom din tare ya fito ya bar ni na ƙara wankan don ban son yawan magana da shi, na fito ban gan shi ba kan mirror na ga ya kwaso mini kayan kwalliyata da suka watsar.

Na janyo kujerar madubi na zauna na zuba ma fuskata ido duk ta yi wani iri kamar ta kumbura, na buɗe mai na fara shafawa wayata ta yi ƙara na tashi na taka zuwa bakin gado na ɗauko ta na dawo Nabila ce ina ɗagawa ihu ta fara yi mini murmushin da ba nishaɗi a ciki na saki jin tana ta murnar ta ban ce komai ba ta ce “Lafiya kike kuwa?  Na ce “Lafiya lau nake Nabila gajiyar hanya ce.” Murmushi mai sauti ta yi da har na ji shi cikin kunnena”Ba zan yi mamaki ba daga ke ɗin matar manya ce, motar mijinki ina ganin ko jirgin sama ba zai fi ta daɗi ba. Ka shiga  ka yi zancen gajiya.”

Na ce “Kin taɓa shiga ne? Ta ce “Ko da ban taɓa ba ai aiki da hankali.” Na ce “Na ji yanzu dai yaushe za ki zo? Dayake tana garin mijinta da ya je Weekend Kaduna  ya taho  da ita ta ɗan kwana biyu.

Ta ce “Gobe na so zuwa amma ya dage sai Weekend ya kawo ni saboda tsadar bolt.”

Na ce “Shi kenan, amma na so ganin ki, kila kuma ni ki gan ni kafin Weekend ɗin.”

Ta yi dariyar jin daɗi “Allah ya sa don na san Ogan naki ba shi da matsala.” Na ce “Ba shi da ita, matsalar sa ya’yansa.”

Ta ce “Suna nan da halin su ko?  Na ce “Suna nan, mai hali na fasa halinsa ne? Ta ce “Allah ya kyauta, ki yi ta haƙuri da su su ma mata ne dole duk zaman su watarana sai sun tafi gidan wasu.”

Na ce “Haka ne.”  Muka yi sallama na ajiye wayar kan mirror na ci gaba da shafa man.

Na ƙi faɗa mata abin da suka yi mini ne yanzu sanin halin ɓacin ran da za ta shiga.

Na murza hoda na goga lip glow a laɓɓana na goga humrorina sai na miƙe ya turo ƙofar, wurina ya yo  “Sanya kayan mu je ki ci abinci.”

Na wuce na ɗauko wata rigar material na sanya na daura ƙaramin gyale a kaina

Mai aikin da na ji ya kira  Peter  ya yi knocking ya ba shi iznin shigowa ya shigo ya fara  jere kayan abinci a kan tebur ya ja ni muka zauna, shi ya buɗe komai ya zuba mini ganin abin da aka kira abinci ya tayar da hankalina ganyaye ne dankali kawai na gane a ciki sai cream da yake ta malalawa, ya sa cokula ya ce in ci na kama na rasa ta inda zan fara na muskuta na kara juyawa wayarsa aka kira ya ce mini yana zuwa ya bar wurin na tattara na rufe komai ina nan zaune Peter ya shigo raina ya ɓaci da wannan yahudancin ni kam ba da ni ba kafin ya gama kwashe kayan abincin na miƙe na hau kan gado na jingina da kan gadon Mama nake son kira amma ban son ta ji ni a yanayin da nake ciki, bai dawo ba sai waya da ya kira ni ya yi mini bayanin sai dare zai dawo ko me nake so in kira Peter ko Easter a waya.

Ban yi ko ɗaya cikin abin da ya ce ba na dai tashi na yi Sallah har magrib ban sa  komai a cikina ba tun karin safe yunwa ta addabe ni kafin takwas ya shigo ko da ya nemi in fito can babban falo a yi Dinner ce mishi na yi na ci abinci takaici ne ya hana ni yi mishi bayanin ba zan iya cin wannan cimar ba.

Na kwanta cikina na ƙugi dan ƙaramin fridge din da ke bedroom ɗin na buɗe na samu ruwa na sha cikina ya ƙulle na koma na kwanta ina ta juyi kamar wadda ciwon cikin ajali ya kama a haka ya shigo ya same ni shirin kwanciya ya yi ya hawo gadon, ni dai ranar ban san da barci ya sace ni ba.

Da asuba da yunwar na tashi haushin da nake ji ya hana ni yi mishi magana ina idar da sallah ko azkar da karatun Alqur’ani ban iya yi ba na buɗe ƙofa na fita yawo na yi ta yi a kantamemen falon ina laluben kitchen Allah ya ba ni sa’a na gano shi ta hanyar wata window ta glass da na hango abin da ke ciki sai dai ƙofar a rufe take, juyawa na yi kamar na ɗora hannu aka na yi ta zunduma ihu.

A hanya muka haɗu da shi hankalinsa tashe ya farka bai gan ni ba ya tambaye ni inda na je wuya aka ce ko da magani ba daɗi ita ta sa dole na bar fushin da nake da shi na faɗa mishi yunwa nake ji kamo ni ya yi ya ce in zo mu je ya yi sallah sai ya kira Peter ya haɗa mini abin karyawa na bi shi sai da ya yi sallar ina ta juye-juye ya ce in zo mu je kafin mu fita na shaida mishi ni fa ba na son abincin namiji kuma ya bar shigo mini wuri ni matar aure ce.

Ya ce to mu je kitchen ɗin, shi ya ɗauko key ya buɗe na bi kitchen ɗin irin na turawa da kallo to an ce ba a ƙwace wa yaro garma na duba komai amma na rasa abin da zai taimake ni ba cima ta na juya inda yake tsaye na ce  Tea zan sha ban samu madara ba, ya matso ya fito mini da ganyayyakin shayi kala-kala na rasa yadda zan zuba su na ce mishi ban iya amfani da su ba a raina ina faɗin tirƙashi baƙin Tea zan sha ta ina zai tare mini wagga tsohuwar yunwa?

Ya ce “Ki yi haƙuri in kira miki Peter ya haɗa miki in ya so sai na yi ma wani abokina magana ya samo miki mace da za ta taimaka miki.”

Na ce “Macen da na gani jiya fa? Ya ce “Easter ba ta yin girki gyaran gida ne aikinta.”

Na yi tagumi ba ni da mafita tilas in yarda wayarsa ya latsa kira Peter ya kama hannuna muka koma main parlor muka zauna har ya zo ya yi masa bayanin ya haɗa mini abin break da na san ko ya yi ba lallai in iya ci ba na yi saurin cewa ni ya dafa mini Black tea  sai ya haɗa mini da soyayyen ƙwai idan akwai bread sai a ba ni ya maida mishi abin da na ce da turanci, nan muka zauna acikin kujera 2 sitter ba ɓata lokaci sai ga shi da madaidaicin tray ya ajiye gabana bayan ya janyo wani dan tebur zai zuba mini na ce is ok ya ranƙwafa mini ya wuce ya tafi ina ganin baƙin ruwan nan sai raina ya yi baƙi ba zan sha madara na more ba.

Amma ina daidaita zafinsa na kai baki sai lissafi ya canza ido na fara lumshewa hakika ba ƙaramin daɗi ya yi mini ba ba bread sai wani abu da ban san sunansa ba amma la shakka da fulawa aka sarrafa shi na haɗa da ƙwai ai sai ɗan gari, ban ankara ba sai wuri don na cinye komai ina zufa takaici na ɗaya baƙin Tean ɗan kaɗan ne bai ishe ni ba na jinjina flack’s din ba komai, na share zufar da ta tsattsafo mini muka haɗa ido da Bashir Lema murmushi ya yi mini ya ce “Mu je to ki yi wanka. Na ce barci zan yi muka tafi ɗaki bai bari mun yi barcin ba sai da ya karɓi hakkinsa da bai samu haɗin kaina da daddare ba daga nan barci muka yi har goma da rabi sha daya yake break past muka yi wanka na shirya cikin wata bubu ta less na koma kan gado na zauna na miƙe ƙafafuna.

<< Ummu Radiyya 22Ummu Radiya 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.