Na ɗaga kai na ce “Ki ci kar ya huce.” Ta ce “To. Mu ci tare. Hannu na sa muka ci sai muka koma hira sai da ta dafa ni ta ce
Maganar ƙanwar mijinki akwai ƙamshin gaskiya Ummu.”
Na yi saurin duban ta “Sai dai ta yi miki maganar ne ta yadda bai dace ba ba ma huruminta ba ne yi miki.
Na san komai game da yadda kike gudanar da rayuwarki kina ba ni labari, amma tarar shi za ki yi ki buƙaci ya kaiki ki canza suturu daga yana da hali, amma kin fi karfin zannuwan dubu ashirin da din nan wannan gida aljannar duniya.”
Muka yi dariya na ce “Zan gwada, Allah ya sa na iya, kin san ni ban iya cewa wani ya yi mini abu wata irin zuciya Allah ya ba ni mai haƙuri da abin da ta samu, ban iya roƙon wani.”
Ta dafa ni “Na san ki, amma shi ɗin mijinki ne da kika fi kusanci da shi kan kowa ana soyayya ana mishi shagwaɓa za ki tambaya.”
Na ɗaɗa mata duka a cinya ta dafa cinyar da sauri tana ɓata fuska “Wannan wace irin mugunta ce za ki fasa mini cinya?
Na ce “Maganarki ta ja miki.” Ta harare ni “Haka ma za ki ce? Ya yi kyau.”
Na ce “Zo mu je kitchen mu yi girki.” Ina miƙewa tsaye wani kallo ta yi mini “Ba ku da me girki ne?
Na ce “Akwai sai dai irin nau’in girke-girkensa na turawa ba ni ciki.” Ta ce “Namiji ne kenan?
Na ɗaga kai ta miƙe muka fita su Amal sun tashi don haka ba mu samu kowa a falon ba sai TV da ke ta aiki, muka wuce kitchen Peter na ciki yana aikinsa muka fara namu muna ciki har muka gama ganin na zuba wani daban Nabila ta tambaye ni na waye na yi mata bayanin na Mama Zulai ne baki ta taɓe “Amma ko darajar girkin ba ki ci ba, sai ta zauna tana jagoranci ana cin fuskarki sai ka ce ba ta da ya’ya mata.”
Na ce “Ni ma mamakin da nake yi kenan da ba ta tuna ita ma ta haifa.”
Nabila ta ɗauki namu abincin na ɗauki na mama Zulai kan dinning na ajiye mata don Easter ta shaida mini sun fita da su Amal.
Wuni sosai Nabila ta yi mini Suraj ya zo ya ɗauke ta.
Ina ta juya yadda zan yi ma Bashir Lema maganar sayen suturu da na dai kasa sai na hakura.
Satin Mama Zulai uku ta tafi gida,
a ranar da ta tafi kuma ya yi daidai da isowar ƙanen Mamansu Amal, Khalil, ban da masaniyar isowar shi ina ɗaki na fito za ni kitchen na ga Suhaima da Amal na tsaye gaban wani matashi suna murna Dina kuma na zaune kusa da shi na wuce abi na duk da na ji muryarsa yana faɗin ” Wace fine Baby ce wannan wow!
Na shiga kitchen ɗin na rasa me zan dafa don wata irin kasala na tashi da ita tun safe, abincin Peter da yake juyawa sai na ji yawuna ya tsinke ba kuma abin da nake so irin in ci.
Abarba na markaɗa na tace na sanya a jug na ɗauki madara na zuba na tafi ɗaki ina gifta su suka fara kiran kuɗin material din jikina kamar yadda suka saba ban yi mamakin yadda aka yi suka sani ba daga na sanya shi Mama Zulai na nan.
Ban ko dubi inda suke ba na shige.
Da na koma ɗaki duk yadda na so na gyara gadona kasala rufe ni ta yi na kasa komai sai kallon ɗakin nake ga toilet ɗina shi ma na gaza wankewa, na kai awa ɗaya kwance na tashi da ƙyar na shiga na yi wanka na fito na shafa mai na murza hoda na sanya turarukana ina buɗe wardrobe kayan da ke sama na ɗauko riga ce da skirt ta wata blue atamfa da ratsin fari kaina da na samu na tsefe na kama shi da ribbom sai na sanya kayan, yadda na saba ɗinkina daga rigar har skirt din sun kama ni, na yi dauriya ina kallon kaina gabaɗaya na sauya jikina ko’ina ya ciko fuskata ma haka na yi kyau ga wani irin haske na shafa cikina da ke shafe kamar ba yan hanji ina tuna irin yunwar da nake ji kasala ta hana ni fita neman abin kari, na dai daure na sanya hijab na yi sallar azahar, anan bisa sallayar na dubi agogo wannan wace irin kasala ce da ta uzzura mini har na kasa ba da farali a farkon lokaci.
Na yunƙura na tashi na zare hijab ɗin na ɗaura ɗankwali na fita in ci abinci don na san dai yanzu sun gama dinning din na nufa kai tsaye ban kalli inda suke ba na zuba abincin na zauna a wurin na fara ci ina jin yana mini wani daɗi da ya ba ni mamaki takun tafiya da na ji ya sa ni ɗaga kai matashin nan ne gabjaje dogo baƙi sanye da farar t shirt mai rubutu a ƙirji sai Blue wando kansa ya tara suma da aka yi ma askin zamani “Hey Baby! Ya fadi murmushi a kan bakinsa sai kuma ya yi saurin rufe bakin ya dafa tebur ɗin da duka hannayensa yana fuskanta ta “Oh sorry Babyn Papi I mean.”
Na dube shi har lokacin murmushin bai bar kan fuskarsa ba “An ce yau Papi zai dawo ko? Na daga mishi kai “So beautiful babyn Papi!
Saurin ƙaran duban sa na yi ina mai tabbatar ma kaina in har yana da cikakken hankali to tarbiya ba ta gama wadatar shi ba.
Kujera ya ja ya zauna ganin abin da ya yi ya sa ni miƙewa ya ce “Ya za ki tafi kuma? Yana nuna flate din abincina na ce “Ya ishe ni.”
Wayata ta yi ƙara a tare ni da shi muka kai duban mu gare ta na ɗauka ina wucewa murmushi na ƙwace mini don sosai na yi kewar sa kwanaki uku kenan itowaba ya gari yana can kan aikin sanya wutar lantarki a ƙauyuka biyu na yankin Kaduna ta kudu da ya samu kwangila.
Shagwaɓa na fara mishi ya tabbatar mini na ba shi mintuna ashirin zai iso gida, wani daɗi ya ƙara mamaye ni cikin kwanaki ukun nan na shiga damuwa shi ne abokin mu’amala ta a gidan idan ba ya nan sai dai wayata kallace-kallace a tv bai dame ni ba.
Maimakon ciki da na yi niyyar tafiya waje na yi na nemi wuri na zauna zaman jiran sa, ban aune ba sai Khalil na gani bisa kaina “Me kike yi anan?
Ba tare da na dube shi ba na ce “Papi zai dawo yanzu.”
Ya tafa hannaye “Ba ki tambayi ko waye ni ba? Na ce “Ai na san ka Khalil ko? “Yea yea. Ya fadi da mamaki, yana ja na da hira wata in amsa shi wata in mishi banza aka wangale Gate motar Bashir Lema ta sulalo harabar gidan, da sauri na miƙe na nufe ta ina isa yana fitowa hannu ya buɗe mini da niyyar in shiga ya rungume ni sanin mutanen da ke kewaye da mu ya sa na ƙi, Khalil ya iso suka tarbi juna cikin murna sannan su Dina.
Ciki muka wuce sun kewaye shi suna ba shi labari Amal ta faɗi Dishes din da ta sanya Peter ya yi masa ya shafa kanta yana gode mata duk yadda suka so ya zauna da su a falon ya ce zai shiga ya watsa ruwa, ya dubi Khalil ya ce sai ya fito za su yi magana ya ce a fito lafiya.
Hannu ya miƙo mini na taso daga inda nake zaune nesa da su na kama muka nufi ciki, tun da muka shige su ya rungume ni yana raɗa mini kewa ta da ya yi, a gado muka dire sai da muka cire kewar juna da muka yi ina kwance jikinsa ya ce in ba shi labarin abin da na yi a kwanakin da ba ya nan, na faɗa mishi har kasalar da na tashi da ita yau na kasa yin girki.
Tayar da ni jikinsa ya yi ya ce mu je mu yi wanka ya kai ni likita ya duba ni duk da cewar da na yi ni ban ciwon komai bai yarda ba muka yi wankan jakar da ya dawo da ita ya buɗe fararen dalolin American ne ya buɗe Safe ɗinsa ya shirya su muka fita.
Su Amal na zaune suna jiran sa ya ce zai kai ni hospital ne ba zai daɗe ba.
Muka fita da kansa yake driving wata asibiti mai zaman kanta ya kai ni ba ɓata lokaci muka ga likita bayan tambayoyi da na sha gwaje-gwaje suka biyo baya likitan ya ba shi tabbacin yarsa ko ɗansa kwance a mahaifata har na tsawon sati tara, farin cikin da na gani a tare da shi irin wanda na gani ne a ranar da aka kai ni gidansa.
Maimakon gida yawo ya yi da ni ya kai ni wurin shaƙatawa na yi ciye-ciye da tanɗe-tanɗe wanda na tabbatar a yanzu su na fi so.
Ya sayi wanda zai kai ma ya’yansa har da Khalil sai takwas na dare muka shiga gidan, Khalil kawai ya zo tarar shi hatta Dina ta yi fushi can ya bi su yana rarrashi ni dai na shige na yi sallah har na yi shirin kwanciya sannan ya shigo.
Da safe da muka tashi barci har falona ya sa Peter ya kawo mini abinci da na ce ban so yana shigo mini ya ce don ba ni da lafiya ne.
Ni dai murmushi na yi don na san ba inda ke mini ciwo kasala ce dai kawai.
Muka karya bai fita ba mun kusa kammalawa aka yi knocking shi ya ba da iznin shigowa tunanina Easter ce shi ya sa ban damu da yadda nake ba cikin rigar barci mara hannu tsawonta kuma ko cinyoyi ba ta gama rufe mini ba, amma Khalil ne ya shigo idanuwansa kuma fes a kaina da hanzari na yunƙura na tafi inda na ajiye hijab din da na yi sallah na sanya komai da zan buƙata idan na yi wanka na ɗauka na shige bathroom na yi wankana na shirya sai da na ji yana kiran sunana na fita kusa da shi ya buga mini na zauna sun ci gaba da hirarsu ganin bai ce mini komai ba ya sa na fahimci so kawai yake na zauna kusa da shi ba don zan mishi wani abu ba ya kira ni.
Easter ta yi knocking ta shigo ta fara aikinta na tsaftace wuri, kusa da kunnena ya faɗa mini in yi haƙuri ta gyara mini ko’ina daga ban iyawa, kan ba yadda zan yi na yarda ta yi aikinta ta gama sai da ta fita ya ce in duba rigar da ya dawo da ita in ciro kuɗi in kawo mishi, na tashi na je na kawo mishi sunƙi ne na dalar Amurka ya zari masu yawa ya ba Khalil bayan ya tabbatar masa anjima ya fita ya fita ya zaɓo motar da yake so .
Ya yi mini sallama ya fita da fitar sa cinyarsa ya ɗora ni yana yaba kyan da na yi wai tun da ya dawo kullum ƙara kyau nake ya faɗa mini ko a mafarki bai taɓa zaton zai ƙara aure ba amma gani na a cassette na bikin Su’ada na dagula masa tunani haihuwa ma duk da yake son yaro namiji daga Suhaima ya cire rai da samun wasu ya’ya su ɗin sun ishe shi amma daga jiya da aka tabbatar masa ina ɗauke da ciki wani irin farin ciki yake ji da rabon da ya ji shi tun da aka tabbatar masa an ba shi ni.
Cikin yake shafawa yana tambayar ya nake ji na ce kasalar dai, ya ce yau ba zai fita ba zai kasance tare da ni su Amal da ke kiran sa a waya ya sa ya bar ni ya tafi na miƙe a kan sopa don ba abin da nake so irin in ta kwanciya.