Skip to content
Part 27 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Bashir Lema ya kasance tare da ni har tsawon sati guda duk kuma da son ya tafi harkokinsa da yake.

Ba wani ciwo da ke damu na illa kasala koyaushe ina nan kwance kamar ruwa sai da na yi sati a ɗaki Easter ya ba izni ko ya fita ta dinga ɗauko abinci ta kawo mini dama tuni na sallama mata gyaran wuri na su Dina ma ba su cika zama gidan ba musamman da yamma kullum sai sun fita da Khalil shi ma ban ƙara ganin shi ba tun ranar da ya shigo, na ɗan ji ƙarfi na yi wanka na fita zuwa kitchen

“Wow! Ɗin da na ji Khalil na faɗi ba ta sa ni waiwayowa ba har na shige kitchen ɗin na ɗauko kazar da na ce ma Easter ta faɗa ma Peter ya gasa mini.

Maimakon ɗaki kan dinning na nufa na zauna ina yankar kazar ina kai wa bakina ban koma ciki ba saboda lallashin da Bashir Lema ke mini na dinga fitowa ina shan iska fitar da su Dina ke yi wani lokaci har da shi suke fita ko ya yi mini tayin zuwa ba na zuwa.

Tsawo rabin kyau, doguwar mace duniya ce.

Furucin da Khalil ya furta cikin harshen nasara ya sa na ƙara kai na zomayena wurin, Amal ta ja wani mummunan tsaki “Wai me kake nufi da wannan yar ƙauyen? Ya ɗaga hannayensa alamar surrender “Ban nufin komai, kawai kin san ban iya ɓoye gaskiyata ita ɗin ta haɗu, Papi ya yi ma gayu shigar sauri.”

Suhaima ta naɗe hannaye “Me kake so ka ce?  Ya ɗage  kafaɗu “Doguwar mace duniya ce.”

Ina ji cikin su wata ta so yi masa tsaki don ji na yi ya ce  “Kul! A kula  ba a yi mini tsaki daughter duka nake.”

Ya tashi ya yo wajena yana tafiya irin ta isassun maza.

Ba shiri na miƙe na bar wurin da muka haɗe a hanya ya ce “Ya za ki tafi ba ki gama ba? Na ce ta ishe ni. Na wuce su sun baza kayayyaki da alama shopping suka yo kowacce na kwasar na ta.

Tun da na shiga ɗaki ban kuma fitowa ba sai washegari yana ɗaki na fito na wuce su Amal su dukkan su har Khalil ban kai ga shiga kitchen ba na ji muryar Amal

Hey! Ina shower gel ɗina na nema ban gani ba?  Kallon sama da ƙasa na juyo na yi mata na ja tsaki zan wuce ta fizgo rigata na waiwayo a fusace tare da yi mata kashedi ta kiyaye ni ba ta ji ba Khalil ma da yake mata magana ba ta fasa ba bi na ta yi tana faɗin “Mu je gaban papin sai na fito mata da shower gel ɗinta.

Raina idan ya yi dubu ya ɓaci na dai samu nasarar danne zuciyata da ke faɗa mini in shaƙo ta har muka shiga ɗakina barci na bar shi yana yi amma yanzu zaune yake bakin gado yana waya, ganin na shigo Amal ta take mini baya ya sa shi hanzarin sauke wayar ya tambayi me ya faru Amal ta yi tsagal ta faɗi mishi shower gel ɗinta da suka sawo ba ta ga nata ba kuma Easter ta ce ta gan shi a toilet ɗina.

A razane na dube ta shi kuma ya ce me za ta yi da shower gel ɗinki?

Ta gatsina fuska “Me take da shi Papi? Ko kayanta ba ka ga masu arha ba ne?

Kamar bai gane me ta ce ba ya ce ta shiga toilet ɗin ta duba ba wani shower gel nata a ciki ta wuce ina tsaye ina jin kamar na haɗiyi zuciya na mace ya miƙo mini hannu ban motsa ba ya tashi tsaye zuwa toilet ɗin sai ga ta ta fito riƙe da shower gel wanda ban san da shi ba ta nuna mishi  ya ce ya za a yi ta ɗaukar miki ita da ba fita take yi ba? Sunaye kala-kala ta shiga kira na da su da suka danganci ɓarayi

Ina nan tsaye kamar an dasa ni har ta fice ya iso inda nake tsaye zai riƙe ni na kauce na ce kar ya taɓa ni tambayarsa na yi shi kenan ba hukuncin da zai mata ta laƙa mini sata ta ci mutuncina?

Ya ce na yi haƙuri daga ta gani ta ɗauka

Na ce “Kenan ka yarda ni ɗin barauniya ce ɗaukar mata na yi? Girgiza kai ya yi ya ce da zan ɗauka kayansa da yake ajiyewa zan ɗauka bai yarda ba.

Na ce “Zan tafi Kaduna ka saukake mini aurenka.”

Ya girgiza kai ya iso gare ni duk yadda na kai da ture shi sai da ya riƙe ni kalaman rarrashi yake jera mini na bijire mishi ta hanyar faɗin ba zan iya ba na gaji daga bai iya tsawata ma ya’yansa ba zan iya ci gaba da zama da shi ba.

Duk kuma surutan da nake bai ce zai tsawata mata ba nuna mishi na yi na haƙura na zauna shiru abina.

Ƙarfe biyar saura na yammaci ya same ni kwance bisa sopa cikin shiri yake yana ƙamshi sosai ya yi kyau, tun da na mishi kallo ɗaya na lumshe idona in tashi mu fita na sha Ice cream da nake so ya ce mini na ce ba za ni ba.

Ya tsuguno gabana ya fara mini magana cikin rarrashi na ce ban jin ƙarfi ne ya ce to me zai kawo mini na ce Moon Cake.

Ya tashi ya fita window na miƙe na tsaya ina kallon harabar gidan a kan idona shi da yaransa uku suka fita, na ja ajiyar zuciya ganin ficewar motar na bar wurin na isa ga wardrobe dina na fara fitar da kaya, kala huɗu kawai na ɗauka saboda rashin ƙarfin jikina kafin ma na gama haɗa su na gaji liƙis, sai da na zauna na mayar da numfashi idona ya kai ga agogon da ke kafe a bango biyar ta kusa zuciyata ta fara mini saƙe-saƙen kar na fita yanzu, tafiyar dare akwai haɗari musamman yanzu da tsaro ya yi ƙarancin a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Na danne zuciyata na ɗauki jakar  da na shirya kayana na fita.

A Gate Sam na kawo gaisuwa na raɓa shi na fita sai raba ido nake da na kama hanya kamar shege a rabon gado ina wasi-wasin inda na nufa tafiya nake ina nazari har na fado babban titi anan na samu abin hawa zuwa lokacin gaɓɓaina sun gama jigatuwa ga ta rashin ƙarfi ga ɗaukar jaka inda zan samu motar da za ta Kaduna na nemi ya kai ni, tafiya muka yi ba kaɗan ba kafin muka isa.

Mutum daya da mota mai lodi ke jira ya hutar da ni fargabar jira

Bismillahi mujreha wa mursaha inna rabbi la gafurur rahim

Ita na furta yayin da Direban ya tayar da motar yana shirin barin tashar, na ciro wayata na duba lokaci biyar har da rabi na yi fatan Allah ya kai mu lafiya.

Direban na zabga gudu ina zabga addu’a a raina don a tsorace nake da yadda nake jin hanyar ba kyau ƙarfe bakwai daidai kiran Bashir Lema ya fara shigowa na san sun dawo kenan, silent na mayar da ita na zuba mata ido kiran na ta shigowa yana yankewa har na gaji na kashe ta gabaɗaya.

Ƙarfe takwas da rabi Allah ya yi ikonsa muka shiga Kaduna lafiya.

Ana zuwa unguwar Sunusi na sauka duk da kafin ni mutane da dama sun sauka, wuri na samu na zauna ina mayar da numfashi don bayan rashin ƙarfin jiki ga zaman mota da na sha na yi tiɓis.

Ina nan zaune wani mai keke napep ya zo wucewa na tare shi na shiga.

A ƙofar gidanmu na ba shi umarnin tsayawa na sauka na sallame shi na kinkimi jakata na tura Gate na shiga.

Wurin mu na yi ma tsinke maganar da na dinga ji ta ɗarsa mini tunanin ko su waye a ɗakin, takalma da na gani a kofar ya sa ni ƙara amincewa ba Mama kaɗai ba ce.

Sallama na yi a hankali na ɗaga labulai gabaɗaya suka yo mini caa! Hassana Mama Lubna, Baba Isah da Baba Ali.

Gabana ya buga sanin in ka ji gangami da labari tabbas akwai dalilin taruwar su mai daɗi ko akasin haka.

Hassana ta yi saurin isowa gabana ta kama hannuna tana duban jikina  “Me ya sa ki tahowa ba sanin mijinki?

Baba Ali ne ya jeho mini tambayar da ta sa ni gane maƙasudin taruwar su.

Ban yi magana ba wucewa na yi na zauna “Ba ki ji tambayar da ake miki ba ? Baba Isah ya ce cikin fushi ba tare da na tada kai ba na ce “Ni ba zan iya zama da shi ba “Saboda me? Baba da Mama suka haɗa baki wurin tambaya “Ba ya iya kwaɓar ya’yansa, ba zan iya zama  suna mini abin da suke mini ba.”

Wannan wane irin zancen banza ne? Ya’yansa za su hana ki zama ban son shashancin banza, wancan aure watanni uku kacal ya lalace wannan ma daga dawowar sa ƙasar za ki ɗebo ƙafa ki ce yayansa? To ba za mu ɗauka ba gobe zai zo ki koma ɗakinki.

Kowace mace da kika gani a ɗakinta da irin haƙurin da take.

Baba Isah ne da wannan dogon bayanin.

Na fashe da kuka na ce “Ni ba zan ƙara zama da su ba matuƙar sai na zauna da shi.”

Mama da ta taso mini ta sani tashi na shige ɗaki ina fashewa da wani sabon kukan.

Ban saurari maganganun da suke ba na dai ji bayan ɗan lokaci kaɗan duk sun watse.

Mama ta shigo ta same ni maimakon ita ma ta fahimce ni ta ji damuwa ta tabbatar mini ta yi ba zan kashe aurena ba Hassana ƙanwata da aka aurar tana tare da kishiya ba wanda ya ji sai ni zan kwaso ƙafafuwa in ce ya’yan miji.

Ta fita ta bar ni ina kwasar kuka da sai da na ji kaina ya ɗauki ciwo na na sarara ma kaina na yi lamo kan katifar yammatancina barcin da na yi ba mai yawa ba ne, tun da na yi sallah na koma kan katifar na tattake ina jin Hus’uwan  yana ba ni haƙuri in tashi na karya,k Hanan ma ta zo tana taɓa ni da kiran sunana tun da Usaini ya ce mata na zo.

Ban tashi ba ban kuma karyan ba ƙarfe goma na ji shigowar Baba Isah da Baba Ali da kuma Bashir Lema, shi na ji suna ta ba haƙuri kan rashin hankalina na tahowa ba da sanin shi ba.

Shi kuma ya ce ɗan saɓani muka samu da yarinyarsa ya dawo bai gan ni ba.

Haƙurin suka ci gaba da ba shi da na dinga ji kamar na haɗiyi zuciya na bar duniya karshe na ji yana godiya suna yi suma, ya fita Mama ta leƙo kira na, na miƙe cikin hijab na tsuguna daga kofar ɗaki Baba Ali ya fara magana “Ummu Radiyya ki koma ɗakinki ki dubi baiwar da Allah ya yi miki ya ba ki miji mai arziki da mutunci kina cikin wadata mu kan mu muna ci daga arzikin nasa duk a dalilin ki amma ki nemi shurewa, duk a yan’uwanki wa ya auri wanda ya kama ƙafarsa daga tahowar ki jiya ba tare da ya yi miki laifin komai ba duk da kasancewar shi babban mutum mai yawan sabgogi ya bar su ya biyo ki.

Nan yar’uwarki Fa’iza kishiya ta dake ta ta taho sai da ta yi watanni biyu a gida mijin bai zo ba sai mu muka neme shi.

Ki gode ma Allah yana son ki ki tashi ki bi shi ku tafi.”

Na share hawaye ban motsa ba Baba Isah ya ce “Tashi mana.”

Na tashi na fara takawa don barin ɗakin  Baba Isah na gaba ina biye da shi.

Bashir Lema na tsaye jikin motarsa Husaini da ya sanya jakata a Boot ya miƙa ma kuɗi, ya matso kusa da ni ya ce  “A sauka lafiya Aunty Ummu.”

Ya matsa jikin kofar ya buɗe mini na shiga.

Bashir Lema suka tafa da Baba Isah ya ce “Na gode ƙwarai.”

Baba Isah ya ce “Kai za a ba hakuri, da ta taso ka da iyashegenta.”

Ya shiga motar ya zauna gefena yana faɗin sai mun yi waya.

Baba Isah ya faɗi a sauka lafiya ya juya ciki.

Direban ya tashi motar jikina na ji ya jingina “Ummuna ki bar kukan nan haka.”

Na ƙara ƙudundunewa a hijab ɗina “Me zai sa ki taho ki bar ni? Kin ɗaga hankalina.”

Kamar na ja tsaki sai dai na fasa na fito da fuskata daga cikin hijab na ce “An sa ni na biyo ka ba tare da an saurari abin da ya’yanka ke mini ba, na ji zan koma.”

Na shaƙi hanci na kalle shi cikin ido “Amma wallahi duk wadda ta ƙara yi mini ba zan ƙyale ta ba duka zan ma duk wacce ta shiga cikin mutuncina.”

<< Ummu Radiyya 26Ummu Radiyya 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×