Skip to content
Part 28 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ya kawo hannunsa zai riƙe hannuna na matsa da sauri sai da na dangana da jikin ƙofar motar murmushi mai sauti na ji ya yi bai yi magana ba.

Mun yi tafiya mai tsawo ba tare da ya ƙara magana ba kafin ya tambaye ni ko zan ci wani abu ban tanka ba duk da yunwar da ke kartar yan hanjina, kiran wayarsa aka yi ta yi wanda ya sa ya yi ta faɗin ya kusa shigowa a Abuja, duk kuma da saurin da yake da muka isa shi ya fara fita motar ni kam ban motsa ba ina share hawaye ya leƙo ya ce fito mana y miƙo hannu ban kama ba na sanyo ƙafa waje kafin na fito.

Wuce shi na yi na yi tafiyata duk da har wani jiri nake ji saboda yunwa yana biye da ni har falo muka same su dukkan su suna zaune Khalil kaɗai ya taso don tarar sa shi ɗin ma bai nufi wurin su ba kamar yadda ya kan yi ko su ɗin ba su taso ba shi ya isa wurin su,

hannu kawai ya ɗaga masu ya bi ni ina shiga ɗaki gado na hau na kwanta ya tsaya kaina yana faɗin in tashi in yi wanka a kawo mini abin karyawa ban kula shi ba har ya juya ya fita.

Ta’azzarar kartawar yan hanjina ya tilasta mini tashi na shiga bathroom wanka na yi na ɗauro alwala na fito mai na murza na shafa hoda, ina taje gashin kaina da na ji duk ya ishe ni,  tun da na tsefe kitson da na zo da shi shi kenan ban kuma wani ba lokaci-lokaci ina wanke shi in shafa mayuka in kama shi da ribbom.

Jin ji

Ya shigo ɗakin ina kama gashina da ribbom ban dube shi ba ya ce “Ki sanya kayan ki fito ki ci abinci.”

Ban yi musu ba wurin kayan na isa na fara lalubar waɗanda zan sa.

Riga da wando ne na material tsawon rigar iya ƙugu tana da dogon hannu yana zaune a kujera yana jiran na gama, na wuce shi na zauna gaban kayan abincin da aka jera duk da matsananciyar yunwar da ke addaba ta a tsanake na fara karyawa.

Sai da ya ga na yi nisa da karin ya yi mini sallama kan zai je neman da ake masa ban yi magana ba har ya fita sai dai ina ta  jinjina ma sha’anin so to in ba so ba wa zai yi wannan aikin mutum kamar wannan haɗaɗɗe a halitta mai tarin ilmi da wayewa ga masu gida a ranar ma Allah ya hore mishi ya zauna ya lalace a kaina ina sha mishi ƙamshi.

Sai da na yi dam na tashi na haye gado na bar kayan abincin.

Sai dare ya shigo ina naɗe a gadon ban da kuma wannan abincin ban kuma cin komai ba sallah kaɗai ke sauko da ni a gado.

Wani abincin ya sa aka kawo mini aka fitar da waɗancan sannan ya sa ni na sauko muka ci abincin tare ya kira Easter ta gyara gadon  na ce ba za ta shigo mini daki ba daga da ita a ka haɗa aka yi mini sharri ni na lallaɓa na gyara na gama kuma na gaji liƙis kamar wadda ta yi wani uban aiki.

Haka muka kwana bakwai ba na fitowa idan ya fita har sai san da ya dawo ya sa a shigo mini da abinci, ɗakina ba wani datti yake ba na kan ɗan gyara daga na samu sauƙin kasalar.

Kwaɗayi da nake ji a ranar ya sanya ni fitowa, ina gifta su Dina na ji Amal tana faɗin sunan atamfar da na sanya, na kawo iya wuya dukkan su ba su ankara ba na isa gabanta na dunƙule hannuna na tafka mata naushi a fuska wata irin ƙara ta fasa ban saurara ba na ƙara kirɓa mata wani zan kai na uku na ji an riƙe mini hannu na waiwaya Khalil ne, na yi saurin ƙwace hannuna ya tambayi me ya faru ban amsa shi ba sai ita Amal ɗin da nake ma kashedin ƙara shiga harkata.

Suhaima da ta ruga kiran papinsu suka dawo tare, ganin yadda nake zuba huci ya kamo ni yana faɗin me ya kai ni faɗa da Amal na san ina ɗauke da ciki, idan wani abu ya same shi fa?

Ba su Dina ba hatta Amal da ke zabga kuka sai da ta dube shi Suhaima ta maimaita ciki?

Ya ja hannuna muka wuce faɗa ya yi mini sosai kan rashin hankalin da na yi na faɗa da Amal.

Idona sharkaf da hawaye tuna na tafi gida iyayena ba su tsaya sun saurare ni ba domin su ƙwato mini yancina.

Na sa bayan hannu na share hawayen cikin sanyin murya na zayyane mishi wulaƙancin da suke mini na suturuna tun zuwa na garin.

Atamfar jikina ya ƙura ma ido kamar a jikinta zai gano gaskiyar abin da nake  faɗa mishi, takowa ya yi inda nake ya kama ni zuwa gado muka kwanta hawayen da ke tsere kan fuskata yake share mini sai zantukan kar na ƙara faɗa da kowaccen su idan sun yi mini abu na faɗa mishi kawai.

A raina na ce sai ka ce wani abu zai musu idan na faɗa mishi.

Ya ce yanzu da mun yi kokawa ta daki cikina wani abu ya samu cikin fa? Ba ya so kar na ƙara.

Ya sake ni ya miƙe ya ce in tashi in shirya fita za mu yi ina share hawaye na tashi na isa gaban madubi na gyara fuskata na canza kayan jikina shi sai da ya yi wanka ya shirya na bi bayansa muka fita.

Ba kowa a falon ya ce na jira shi a mota, ya tafi wurin ya’yansa.

Na shiga gaban motar ina jiran shi, bayan shuɗewar mintoci ina jiran sa ya isko ni shi ya ja motar muka bar gidan.

Babu mai magana har ya tsaya cikin wani Mall cikin wani katafaren kanti muka shiga duk da na ga sunan wurin sai da muka shigan na ga ainihin abin da ake sayarwa kayan ƙawa ne na mata babu abin da babu, ma’aikatan wurin sun kawo gaisuwa cikin girmamawa wata ma’aikaciya ta tsaya da son taimaka mana shi ya ce ta zagaya da ni na zaɓi duk abin da nake buƙata, bayan ta yi gaba ya raɗa mini “Ki zaɓi duk wasu kaya masu kyau da tsada duk laifina ne da aka ce kar in yi miki kayan aure bayan auren ban yi miki ba.”

Na wuce shi na bi ta ita ta taya ni ɗibar kayan daga manyan zannuwa zuwa less materials Abaya English wears kayan barci takalma da jakunkuna su sarka da yan kunne tamkar dai masu haɗa kayan aurewa koma na zaɓa a ciki aka shirya komai na koma wurin shi na ce ina so a wanke mini gashi ya ce yana mota idan an kammala, ATM ya bayar suka zare kuɗaɗensu.

Na ji daɗin gyaran gashin da aka yi mini ya yi kyau sosai fuskata ta yi fayau, na rufe kaina matashiyar da ya sa ta taya ni zaɓen kaya ta raka ni har gindin mota na shiga muka tafi a maimakon gidan mu wata hamshakiyar unguwa ya shiga na yi ta kallon tamfatsa-tsamfatsan gine-ginen da ke cikinta har ya tsaya gaban wani Gate,  horn ya matsa aka buɗe Gate ya shigar da motar.

Wata babbar mace doguwa mai jiki baƙa ta tare mu da fara’a, ina fitowa ta kama hannuna tana yi mini oyoyo shi kuma ta yi mishi barka da zuwa muka nufi ciki.

Kan lausasan kujerun da ke tamfatsetsen falonta ta yi mana masauki, bayan shan ruwa da lemon da ta sanya aka kawo mana na ji tana tambayar ina kayan, ya ce suna Boot.

Mai aikinta ta aika ta zo da su ta buɗe ta cire duk abin da ke ciki wanda ke buƙatar ɗinki ta ajiye su gefe ɗaya hannuna ta kama muka shiga ciki bedroom ta kai ni muka zauna bakin gado hannunta na cikin nawa yadda ake tattalin miji da kula da shi take faɗa mini tare da nasihar kar in kuma kula su Amal in mayar da hankali kan yadda zan ɗauke hankalin mijina don mahaifiyar su Amal ba ƙaramar hatsabibiya ba ce ta yi bala’in kanainaye rayuwar Bashir Lema, yin aurensa ma wani iko ne na Allah da ya sa sai ya yi ta ce in saki jiki da ita ita ma kanuri ce kamar ni, duk wani abu da ya shige mini duhu in neme ta.

Ta faɗa mini sunanta Haj Fanna ta tashi ta ɗauko mini turaruka da ta ce irin namu ne na yan Borno in riƙe su da kyau.

Wata da tun zuwan mu ta kira a waya ta zo ta sa ta auna ni muka fita suna maganar ɗinkunan da za a yi mini ita da Bashir Lema, anan na ci abincin dare  har wanka ta sanya ni na yi na yi amfani da turarukan da ta ba ni ai kam na ga amfanin su sama da nawa da nake amfani da su.

Tun kafin mu kai gida ya canza yanayi, hirar da yake zama su yi da yaransa bai zauna falon ba biyo ni ya yi muka kwanta da wuri.

Tantancewar da na yi a hannunsa a wannan dare ta ƙara mini rashin ƙarfin jiki tun da ya fita ina gado sai sai da ya dawo ya sa ni na yi wanka muka ci abinci, ganin ko gadon ban gyara ba ya yi ma Haj Fanna magana kan yar aikin da suka yi magana ta ce ya ɗan ƙara mata haƙuri an kusa kawowa.

Da safe asibiti ya kwashe ni muka tafi ya yi ma Dr complain kan rashin ƙarfin jikina haƙuri ya ba shi ya ce lokaci ne in sha Allah na kusa jin sauƙi da cikin ya ƙara ƙwari ya rubuta magunguna ya saya muka dawo.

Da yamma ya fita shi da ya’yansa da ban sake sa su a ido ba tun faɗana da Amal, sun dawo kafin magrib abin da ya sawo mini kawai ya ba ni ya fita, na bararraje ina kwaɗayi na tsinkayi kiran sa na ɗaga wayar da ke kusa da ni, ya ce na fito main parlor na same shi, ban so tashi ba na miƙe, cikin kayan da ya saya mini ne na sanya wasu  riga da skirt masu kyau ƙwarai kaina rolling na yi na fita.

Suna zaune har Khalil wanda nake ji yana yawan yi masa faɗa kan yawan dare.

Dukkan su sun zuba mini ido na kai duba na ga wata budurwa da na gani a tsugune ɗan nesa da su, ya buga hannu na isa na zauna budurwar ya nuna mini ta yi saurin ɗagowa ta gaishe ni da harshen nasara, ko ba a faɗa ba da ganin ta za ka tabbatar da ba bahaushiya ba ce ya gabatar mini da ita a matsayin mai aikina da za ta dinga yi mini komai.

Na dube shi shi ma ya dube ni da kyawawan idanuwansa da ke cikin farin glass na narke fuska yadda nake mishi idan zan yi mishi shagwaɓa basarwa ya yi don duk sun zubo mana ido “Ko ba ta yi miki ba? Ya tambaye ni  kai na girgiza ya faɗa mini dakin da zan kai ta na miƙe ta tashi ta bi ni na kai ta ta yi mini godiya.

Da na dawo falon ban zauna ba wucewa na yi ya taso ya biyo ni tun a hanya ya haɗa ni da jikinsa.

A kan kujera muka zauna ya ce ya ce  “Ya aka yi faɗa mini idan ba ta yi miki ba.”

Na ƙara kwantar da kaina a kafaɗarsa na ce ina jin tsoro ya ce na me na ce sharrin masu aiki duba Easter ta yi mini sharri.

Bai yi magana ba sai wayarsa da ya ciro ya kira Haj Fanna magana kaɗan suka yi ya miƙo mini wayar ta ce na kwantar da hankalina sai da ta ja kunnen yarinyar mai suna Victoria kafin a kawo ta ta ce ba za su lamunci kowane rashin mutunci irin na masu aiki ba, idan wani abu ya ɓullo za a yi mata hukunci daidai da laifinta.

Na yi mata godiya muka yi sallama

<< Ummu Radiyya 27Ummu Radiya 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×