Skip to content
Part 30 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Zuwa na falo na samu masu wankin gida ashe Amal ta ba Suhaima shawarar a kira su da gyaran Easter.

Na wuce su zuwa ɗakin Vicky sallah na samu tana yi da wani ƙaramin mayafi ina tsaye har ta idar, sai da ta idar ta yi addu’a a nutse ta juyo ta dube ni tana mai rusunar da kai ta gaishe ni jakar na tura mata na ce kaya ne ta yi amfani da su, godiya ta yi mini sosai na ce wannan guntun mayafin da take amfani da shi bai yi kaɗan ba? Ta ƙara sunkuyar da kai ta ce “Shi kenan gare ni.”

Na ji mamakin jin shi kaɗai ta mallaka tare da tausayinta na fita na ce mata ina zuwa ɗakina na koma na nemo mata hijabaina da mayafai don na tura kuɗi Nabila za ta ɗinko mini sababbin hijabai idan za ta zo wurin mijinta ta taho mini da su.

Na koma na ba ta nan kuwa murnar da ta yi har ta fi ta farkon.

Da na koma daki na samu ya tashi ya yi alwala ya fita masallaci don yawan wa’azin da nake sanyawa ya sa ko jam’in sallar asuba ba ya wuce shi yanzu.

Na yi tawa sallar kamar na zauna a ɗakin saboda sabo da fita kwana biyu sai na ji duk na takura, ya shigo ya yi shirin fita muka fita tare sai da muka tsaya a falo ya ƙara ma Suhaima kuɗi don ta ce waɗancan sun ƙare yanzu odar abinci za a yo mata.

Suka gama maganarsu ina tsaye ina kallon tv program din da ake a tashar da suka sa ya tafi da ni, na bi shi na raka shi ya shiga mota da na koma ban shige ciki ba falo biyu ne da wani haɗaɗɗen labulai mai ban sha’awa ya raba wanda ba su zama na zauna na ci gaba da kallona har baƙon Suhaima ya iso matashi ne su biyu suka zo shi da abokinsa suka gaisa da Khalil da Amal Easter ta yi musu jagora zuwa falon da za a sauke su wucewar mintoci goma Suhaima ta fito cikin ƙamshi riga ta sanya mai matuƙar kyau da ba ta gama kai mata har ƙasa ba sai siririn mayafi da ta rufe iya kanta ta wuce Amal na ta dariya da har sai da Khalil ya tambaye ta dariyar me take ta ce kan wannan gayen Suhaima ke ta ɓarin jiki ya tambaye ta da mamakin da ya bayyana a muryarsa ya ce “Mene ne aibun wannan gayen?

Ta kashe ido ta ce “Ba shi da tsawo.”

 Ya gyara zama  ya ce “Ke wane iri kike so?

Ta ce “Dogo  kyakkyawa haɗaɗɗe. Shi ya sa har yau ban ga namijin da ya yi mini ba.”

Dariya ya yi ya ce “Da kyau, babbar yarinya.”

Suna ta hirarsu ina sauraren su har Vicky ta fito sanye cikin daya daga cikin kayan da na ba ta atamfa ce ɗinkin doguwar riga da ya suturta surarta.

Kusa da ni ta ɗan duƙa ta tambayi abin da za ta girka kai na girgiza na ce ban jin cin komai ta je ta huta na tashi na tafi ɗaki ɓatan kuɗin Bashir Lema ya yi ta yawo cikin kaina.

Nawa kuɗin na ɗiba na zuba a drawer da niyyar gwada Vicky da nake jin ina zargi.

Da daddare muka kwance kafin mu shiga barci wayar Bashir Lema ta ɗauki ƙara ya ɗauka, a maganar da suke da mai kiran na fahimci Maman su Amal ce ƙarar Khalil ya kai mata kan yawon dare har suka gangaro kan samarin Dina da Suhaima ya ce saurayin Dina zai zo nan da kwana biyu. Ina jin muryata ta ce ta yi magana da Mama Zulai za ta zo ta duba mata yara…

Ya ce shi ba zai iya kula da yaransa ba har sai Zulai ta zo ?  Ta ce ita dai ta yi magana da ita za ta zo ya ce ba shi da bukata ya kashe wayarsa.

Ilai kuwa washegari muna fitowa sai ga Mama Zulai ta iso ni dai daga sannu da na yi mata na sa Vicky ta je ta gyara mini wuri don ba ta damar da za ta ɗauki kuɗin idan har ita ta ɗauki waɗancan sai dai da na koma dakin na duba suna nan inda na  ajiye.

Mai son Dina ya zo daga Kaduna mai suna Tajuddin ɗan manyan mutane ne Mutum mai kamala da Amal ta kira ustaz ƙwarai akwai alamar riƙo da addini a tare da shi, sosai Dina ta kamu da son shi ga yadda ta sauya yan’uwan na zolayar ta sai na kula Vicky ba ta son idan ta kammala abincina ta bar shi falo kamar yadda na fi so yanzu idan ta kai mini ciki na yi magana gobe ma ƙara kai mini za ta yi idan na ƙara magana sai ta ba ni haƙuri ta ce mantawa ta yi, idan na ce ta fita da shi sai ta ajiye ta zauna ta tasa shi har sai na fito kuɗi kuma na gwada ta ya fi a kirga ba ta ɗauka ba sai ranar da aka kai ni kitso na tafi tare da Vicky sai ga shi an kwashe mishi kuɗi da ya tambaye ni kuka na yi ta yi mishi sai ya dawo yana lallashina na shiga damuwa mai yawa kan wannan al’amari.

Wata ranar Laraba da na tashi ina marmarin cin ɗan wake na fita na tambayi Vicky ta iya ba don na sa ran za ta ce ta iyan ba ta ce ta iya na bar ta na fita can cikin shuke-shuke na sha iska wayata na kare a kunnena na kira Mama da Lubna Aunty Ya gana da Hassana har da Aunty Larai da su Baba.

Ina ta wayata na ga wucewar Vicky zuwa Gate tashi na yi na wuce ciki ina  tunanin abin da za ta yo a can, a inda na fi zama na hango kayan abincin da ta shirya mini yawuna ya tsinke da na buɗe flate din na ga yadda aka shirya ɗan waken da su ƙwai da cocomber ga yaji da mai gwanin ban sha’awa na ɗauki maggi me star na barbaɗa na motsa na debo zan kai baki na ji an riƙe hannuna cikin tsantsar mamaki na bi inda hannun yake da kallo wani sabon mamakin ne yakuma lulluɓe ni Vicky ce!

Kasa ce mata komai na yi sai ta saki hannuna ta haɗa hannayenta ta ba ni haƙuri na ce “Me ya sa za ki kama hannuna ki hana ni ci?

Ta ƙara sauke kai  “Ki yi haƙuri Madam.”  Ta ƙara ba ni haƙuri tagumi na yi na zuba mata ido har gumi ke tsattsafowa a goshinta “Kar ki ci Madam.”

Na ce “Saboda me?

 a ɗauki flate ta rufe ta gurfana ta ƙara ba ni hakuri ta ce yanzu za ta yi mini wani ta tafi ta bar ni kai a ƙulle na miƙe na tafi ɗaki da shiga ta wanka na yi ina wankan ina tunanin abin da ya sa Vicky ta hana ni cin ɗan wake na fita na tsane jikina na ji knocking sai da na murza mai na sanya riga na je na buɗe Vicky ce ɗauke da tray na ba ta hanya ta shige inda ta saba ajiye mini ta ajiye za ta juya na ce zauna Vicky ta koma ta zauna ni na sa ma dakin key na zauna sai na fuskance ta  “Mene ne dalilin ki na hana ni cin abincin nan?

Ta duƙar da kai na ce “Ba fa wasa nake ba kina son zama da ni sai kin faɗa mini.”

Ta ƙara sunkuyar da kai “Ki gafarce ni amma ban yarda da abincin ba an aike ni ne don a sanya miki abu.”

Faɗuwar gaba na ji na dube ta  “Ban son haɗin faɗa waye zai sanya mini wani abu?

Canza harshe ta yi daga turanci da tun da ta zo gidan da shi take ta koma hausa hausar ma raɗam kamar jakin Kano “Ba su yi tunanin ina jin hausa ba suka yi magana da hausa a sanya miki magani a abinci don cikinki  ya zube!

Wata faɗuwar gaba na ji wadda ta fi ta farko gabana na tsananta harbawa “Su waye kika ji suna zancen?

Ta ɗan yi shiru sai da na ƙara maimaitawa ta ce  “Madam ki yi hankali da Amal da Mama Zulai.”

Ta miƙe ta ɗan ranƙwafar da kafaɗa ta yi mini bankwana ban samu abin cewa ba har ta buɗe kofar ta fice ga tambayoyi danƙare a raina amma na kasa ko motsa laɓɓana sai ido da na bi kofar da shi .

Ɗan waken na ji ya fita raina na zauna na yi tagumi ban ci ɗan waken ba ban kuma fita ba har ya dawo shi ya sa ni fita tare da shi amma sam na kasa cin abincin wani irin tsoro ke ɗawainiya da ni da aka kammala ya hana ni komawa daki nan na  zauna tare da su shi da Mama Zulai suke hira ana ta nuna namun daji a tanƙamemiyar plasman falon an zo kan ƙadangaru na yi saurin rufe idanuna ina jan wata ajiyar zuciya da har ta sa ya waiwayo ya ga na rufe ido ya tambaye ni wata ajiyar zuciyar ta ƙara ƙwace mini na ce “Ƙadangaru aka nuna.” Mene ne da shi ? Ya kuma tambaya na ce “Ina matuƙar jin tsoron shi .”

Amal da remote ke hannunta ya ba umarnin ta canza tasha ta ce saboda me ya ce ina jin tsoron ƙadangaru.

Mama Zulai ta yi saurin ƙibta ma Amal ido ta tashi sai ta yi mishi sai da safe , Vicky da ke tsaye tana tsiyaya ma Suhaima ruwa za ta sha magani wai kanta ke ciwo ta dubi abin da Mama Zulai ta yi sai ta bar wurin zuwa kitchen tana saƙa yadda za ta saurari abin da za su kitsa don tana tafiya Amal ɗin ta tashi ta bi ta ta san kuma ko me za su ƙulla kan Madam ɗinta ne  ta san manufar zuwan Mama Zulai don ta zubar da cikin Madam ɗinta ne kamar yadda suke yin magana da hausa ba tare da sanin ita ɗin tana jin hausar ba .

Ta fita kitchen ɗin ta zagaya waje can bayan dakuna ko za ta samu sa’ar jin abin da za su tattauna ta samu nasarar jin su a dakin Dina sai dai ba ta ji sosai komai kasa kunnenta, Mama Zulai ta saki murmushin mugunta “Kin ji shashashar tsoron ƙadangare take. Akwai wani yaro da muka haɗu da shi ranar da muka fita gidan Haj Asma’u layinmu ɗaya a Kaduna, zan kira ya kawo ƙadangaru ba za a sanya a ɗakinta ba a kitchen zai sanya.”

Amal ta yi ɗan tsalle da ihu “Mu ma tsoron shi muke ji.”

Ta dafa kafaɗarta “Kar ki damu allura za a yi musu da ba za su iya gudu ba, ana sakin su idan ta gani sai ya kwashe su  in sha Allah yadda take tsoron su sai ta yi razanar da cikin zai ɓare.”

Amal ta ce ya yi, sai dai Mama Zulai ba ta yarda da Amal za ta karɓo kuɗi wurin papinsu ba dagewa ta yi  mominsu za ta kira ta turo kuɗin.

Ta tashi ta tafi nata dakin cike da farin cikin irin kuɗaɗen da za ta samu.

Da safe na tashi da farincikin wayar da muka yi da Nabila ta ce mini ta shigo Abuja tana nan zuwa yau.

Ban yi dogon barcin da nake ba wanka na yi na zauna zaman jiran ta.

Karfe sha ɗaya na safe na ji knocking na tashi na buɗe Vicky ce ke shaida mini zuwan baƙuwa na ce ta je ta kawo ta.

Ina nan ina kallon ƙofa Nabila ta iso na kama hannunta cikin tsantsar farin ciki muka zauna saman Carpet cikinta ya tsufa sosai duk da ba wani uban girma ya yi ba tana ta kallona tana faɗin kyan da na yi da yadda na murje fatata ta koma kamar ba ni ba .

Murmushi kawai nake ina sauraren ta na buɗe hijaban da ta kawo mini duka sun burge ni ina ta ɗaga su na ce za ƙaro wo mini wasu, ta kama baki wai ke duk me za ki yi da uban hijaban nan ?

Na yi murmushi “Ba su isa ta. Sune adon ya mace.”

Ta ce  “Shi ne ba ki yi ma yaran gidanku wa’azi su dinga sa wa?

Na buɗe ido “Ina ruwan kallo da gajiya?

In kin gan ni lahira kai ni aka yi, ko Suhaima da za mu yi sa’anni ban ishe ta saurare ba balle ta karɓi shawara daga gare ni.

Mai sauƙin cikin su Dina, ita kam karena ba ni ba ka ba ni korar ka.”

Ta numfasa ta ce “Allah ya kyauta.” Na ce Amin.

Muna ta hirarmu har azahar ta yi muka yi sallah Vicky ta sanar da ni ta kammala girki na kama hannun Nabila muka fita.

<< Ummu Radiya 29Ummu Radiyya 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×