Wayata ta ɗauki ƙara,na miƙa hannu jiki a mace na ɗauko ta Baba Isa ne ƙanen babana ina son Baba Isa saboda ko bai ba mu komai ba a ƙalla yana jan mu a jiki idan kuma ya ji mu shiru zai tuntuɓe mu, karatuna a poly shi ya tsaya kai da fata na samu addmision, ya kuma taka rawar gani wurin kula da ni. Ko banza ya fiye mana Mamu don ko da ta kasance ita ɗin uba ɗaya suka haɗa da babanmu da yana raye ba wanda ya kai ta cin moriyarsa kodayaushe tana gidanmu amma yanzu sai mu daɗe ba mu ji motsinta ba.
Ajiyar zuciya na sauke jin muryarsa “Ummu Radiyya ashe haka ya faru? Jiya da daddare nake samun labarin wurin Larai.” Na share hawaye “E Baba.”
“To yanzu ya ake ciki? Na ce “¹Yana can dai Baba.” Jin muryata na makyarkyatar kuka ya ce “Yi shiru Ummu Radiyya, ki yi haƙuri ban gari, amma da na dawo zan nemi inda aka kai shi sai mu ji yadda ake ciki.”
Na ce “Na gode Baba.” “Ki daina kuka ki yi ta addu’a, Allah zai fito mana da shi.” Na share hawayen da suka ɓalle mini, Hassana da ke haramar fita da kayan da na tuɓe Mama ta sa baki ta kira ta ta dawo ta ce ta bar wankin, zugum Mama ta yi cikin tunani na san bai wuce saboda maganar da Haj Nasara ta yi.
Na kai hannu na taɓa Mamanmu ta cira kai ta dube ni “Ko Hassana za ta je ta yi girki a ɗakina sai ta kawo?
Kai ta girgiza ” A’a a dai yi haƙuri ai yau ne kawai .”
Aunty Ya gana ta da iso da Lubna Aunty Larai ma ta zo ta ce jiya ta samu labari wurin Bushra yarinyar Gwoggo Mamu dukkan mu mun ji mamaki ashe sun ji amma ko Mamun ba ta kira waya ba.
Sallamar Baba a ƙofar ɗaki aka amsa gabaɗaya sai da aka gaishe shi ya kira sunana na fita ƙofar ɗaki inda yake tsaye na durƙusa kuɗi masu kauri ya miƙo mini “Ku sayi wani abun ku ci da rana.
Wata siririyar ƙwalla ta ziraro mini ta tausayin uban da ɗansa, na miƙa hannu na karɓa ina mishi godiya “Ki koma ciki ki ƙara haƙuri Ummu Radiyya, Allah zai duba al’amarin.”
Na mike na koma ɗakin ina tunanin ni da shi ko wa za a ba haƙuri?
Da rana ba wanda ya ci abincin da Fauziya ta miƙo da bai fi flate biyu ba, ga dakin da mutane da yawa don ko matan Baba Ali sai ranar suka zo.
Hassana na ta ƙunƙuni ganin an ba su abincin sai da suka tafi Mama ta rufe ta da faɗa Aunty Larai ta ce “Me ta yi?
Nan ta ba ta labarin complain din da Haj Nasara ta yi, faɗa Aunty laran ta kama yi don mace ce mai zafi Aunty ya gana na taya ta mama ta ce su yi haƙuri a bar maganar ai yau ne kawai Lubna dai ba ta ce komai ba.
Ban gane me Mama take nufi da yau ne kawai ba sai da yamma ta tafi wurin Baban Abakar ta roƙe shi son ta tafi da ni can gidanmu har a ga abin da Allah zai yi.
Ya ba ta haƙuri ya ce in don maganar da Haj Nasara ta yi, ta ce ba don hakan ba ne dama tana da niyyar rokon.”
Ya ce ba komai, amma ya so na zauna gabansa har a ga abin da Allah zai yi.
Ya ƙara da cewa yaran Haj Iyami sun aiko a zo a kwashe kayana, ya roƙi Mama ko za ta bari har gobe idan sun zo a je a kwashe kayan a kawo nan ɗakin Fahima, inda muke zaune.
Nan ma roƙon shi ta yi ya bari a tafi da kayan kar a kawo su nan su zama wani sanadin fitinar.
Ya ce ba wata fitina.
Ta dai roƙe shi ba da son ransa ba ya ce shi kenan.
Muna yin sallar magrib muka fito, ɗakin Haj Nasara muka shiga yaranta sun tafi gida sai Fauziya kaɗai ta yi saura sai Fahima.
Sallama Mama ta yi mata, tana jin har da ni za a tafi sai ta fara faɗin Allah sarki to sai sun zo kenan.
Muka fita muka samu su Aunty Larai da Hassana don sun ƙi shiga wasu kuɗin Baba ya ƙara ba ni da muka tsaya ƙofar shagonsa muna yi masa sallama, da na ƙi karɓa sai ya fara mini faɗa dole na amsa suka taya ni yi mishi godiya.
Keke napep muka samu har unguwar Sunusi Aunty Larai sai da ta raka mu har gida ta yi mana sallama ta tafi tare da jaddada idan za a kwaso kayana a kira ta.
Ɗakinmu da na yi ‘yammayanci na shiga na hau kan katifata da har lokacin tana nan sai kallon dakin nake da bai mallaki komai ba daga katifu guda biyu tawa da ta Hassana sai ma’ajiyar kaya sai labulan ƙofa da na window.
Na miƙe bisa katifar idanuwana na kallon rufin ɗakin ina roƙon Allah ya fito da Abakar.
Daren ranar ba ƙaramin kuka na yi ba ganin daga yin aurena har na dawo gida ga kayana ga kayana za a kwaso.
Mama da ta leƙo ta ga ina kukan faɗa ta kama mini ta ce in tashi in yi sallah na roƙi Allah maganin damuwata ba koke-koke ba.
Sai da na yi alwalar na zo na kabbara sallah ta fita ta ja mini ƙofa.
Da gari ya waye sai ga Baba Isa, na yi wanka muka fita tare da shi zuwa inda Abakar ɗin ke tsare.
Yau ma ba su ba mu damar ganawa da shi ba kuka na yi ta yi da Baba ya ce na zo mu tafi ban ko motsa ba, shiga ya yi ya fita sai ga wani jami’i ya ce in taso. ni kaɗai na bi bayansa, wata siririyar hanya bayan ya sa kwaɗo ya cire da ke jikin ƙofar, mun yi yar tafiya muka sake samun wata ƙofar ya sa key ya buɗe ta muka wuce tsoro ya fara ziyarta ta don wurin ba wadataccen haske duk kuma inda ya buɗe muka shiga sai ya sa kwaɗo ya datse.
Ban aune ba muka ƙara isa wata kofar yana buɗe ta muka shiga muka tsinkayi wata kofa daga gefe ƙarafuna ne a maimakon ƙofa hakan ya ba ni damar hango mutane a ciki ya kira sunan Abakar, wani baƙin siririn dogon mutumi ya taso yana layi sai da na yi masa duban tsanaki na tantance Abakar ne ya koma haka.
Hannu na ɗora saman kaina da niyyar fasa ƙara ya motsa bakinsa “Haba Ummu kuka kuma? Na share hawayen da suka sulalo mini
“Nan suka kawo ka?
“Nan suka kawo ni.” Ya ba ni amsa
Na kai idanuwana ga sauran mutanen da suke ciki da ban ga alamar imani a tare da su ba waɗansu irin kamanni ne da su da sai da yan hanjin cikina suka kaɗa duk da halin da nake ciki.
Na haɗiyi wani kakkauran yawu sai na mayar da maganaina zuwa ga Abakar “Kana cin abinci kuwa? Ya ɗaga mini kai ina ci. Idan akwai kuɗi a wurin ki ba ni na ba su. Ya rage murya “Duka na suke yi duk wuni dubu daya idan ban bayar ba su wuni suna duka na.”
Hannu na rawa na ciro duka kuɗin da Allah ya taimake ni na fito da su na miƙa masa “Ka ba su su bar dukan ka.” Dubu daya ya sa hannu ya karɓa “Amiru ya tabbatar mini yau za a cire ni a nan.”
Na share hawaye “Me ya sa aka kawo ka nan ɗin?
“Babban yaron Haj Uwani.”
Na girgiza kai “Allah zai saka maka. Ga shi ban kawo maka abinci ba.”
Ya girgiza kai “Amiru ya ba su kuɗi suna saya mini.
Daga bayana aka yi mini magana lokacina ya cika
Abakar ya gyaɗa kai “Ki je Ummu Radiyya, ki yi haƙuri.” Na share fuskata na juya ina kama hanya, mun fita na samu Baba muka tafi a hanya yana ta ba ni haƙuri a bakin titi ya sauke ni na ƙarasa don ya ce mini poly zai shiga ya kawo 2k ya ba ni na gangara a ƙasa.
Na shiga gida cikin zafin ranar da ya ɗaga na samu Mama tana ta haɗa kuɗaɗen cinikinta wai mai motar da aka samo za ta ba a kwaso kayana.
Tun daga kuɗin da Abakar ya ba ni ranar da tsautsayi ya ritsa da shi har wanda babansa ya ba ni kashi biyu sai wanda Baba Isa ya ba ni yau na haɗa duka na ba ta amma dubu biyar ta ɗauka ta ce na adana sauran a wajena.
Ɗaki na shiga na kwanta saman katifata idanuwana na kallon sama ina tuna Abakar, zamantakewar mu tun daga ranar da aka kai ni, na shiga shafa cikina ina tuna daren mu na ƙarshe wanda shi Abakar ya tabbata ango ashe -ashe, ko sai yaushe zai fito?
Gobe dai za a fara shiga kotu.
Zumbur na yi na tashi daga katifar na fita waje da niyyar ɗaura alwala in gabatar da salatud duha ganin ƙarfe sha biyu ne har na samu na yi.
Mama da ke zaune ƙofar ɗaki har lokacin ta yafuto ni, na isa inda take “Ki kira Nabila a tafi har da ita kwaso kayan naki, sai su tafi da Hassana, Ya gana da larai da wannan yarinyar (Lubna) za su wuce ta can.”
Kai na gyada mata na koma ɗaki na ɗauki wayata na kira Nabila ta ce ga ta nan zuwa don tana gida ba ta yin komai, za ta shirya yanzu.
Na sauke wayar sai na kai idona kan agogon da ke kafe a ɗakin sha biyu da rabi ya kusa ba halin yin salatud duha don ƙarshen lokacinta kafin a yi sallar azahar da minti goma ko ashirin, kafin in kewaya na yi tsarki na yi alwala lokaci ya ƙure na koma kan katifata na kwanta ina ci-gaba da tunanina Nabila ta iso suka tafi da Hassana.
Kafin la’asar suka dawo har su Aunty Larai ganin kayan da ake ta shigowa da su ya haifar mini da zubar hawayen da duk haƙurin da ake ta ba ni ba su tsaya ba wani daki daya da ke kusa da wurin namu aka shirya kayan, kayan kitchen ɗina aka sa a ɗakin Mama.
Matan Baba Ali sun leƙo suna ƙara yin Allah ya kyauta, ina cikin zubar da hawayena Mama ta miƙo mini wayarta tana shaida mini Gwoggo Mamu ce, a sanyaye na gaishe ta ta yi mini jaje tare da cewa ta so zuwa to ciwon baya ya matsa mata.
Na faɗi Allah ya sawaƙe na kama bakina na miƙa ma Mama wayar.
Da mugun ciwon kai na kwana a wannan rana zuwa safiya zazzaɓi ya rufe ni, Amiru da muka yi waya zai zo ya ɗauke ni zuwa kotu saurarar ƙara sai dai ya ɗauki Mama da ta hau da ƙyar saboda kunya suka tafi suka bar ni ni kaɗai a gidan don su Hassana ma sun tafi makaranta.
Ina kwance cikin zullumi da faɗuwar gaba sai addu’a nake yi cikin zuciyata.
Sai azahar Mama ta dawo, ta samu na tashi don na ji sauƙi kallon fuskarta ya sa gabana ƙara tsananta bugawa don fuskar ba walwala ta tsuke ta ƙwarai da gaske.
Da rarrafe na isa gaban ta “Me ya faru a can ɗin Mama? Hawaye na ga sun gangaro mata ta sa hannu ta yi saurin ɗaukewa, na zauna kan ɗuwawuna so nake in fashe da kuka amma hawayen ma babu sai zafi idanuwan ke yi mini.
“Kar ki yi kuka Ummu Radiyya ki yi haƙuri.”
Ina Abakar Mama? Na ƙara tambayar ta Lubna da suka shigo tare ta ce “Ki yi haƙuri Ummu, Alƙali ya saurari ƙarar da ya’yanta suka shigar amma ya ɗage sake zama har zuwa talatin ga wannan watan zuwa lokacin a ga yadda Allah zai yi da Haj iyami da har yau ba ta san wanda ke kanta ba.”
Ina Abakar an bayar da belin sa ? Na tambaye ta ina ƙure ta da ido. Ajiyar zuciya ta sauke sai ta kawar da kanta daga kallon da nake mata “Alƙali ya tura shi gidan kaso kafin lokacin