Hannayena na sa na rufe fuskata “Ya kamata ki yi haƙuri da kukan nan haka Ummu Radiyya, ki zama musulma ta ƙwarai ta hanyar imani da ƙaddara idan musifa ta samu Musulmi Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un aka ce ya faɗi ba koke-koke ba.
Na sauke hannayena daga fuskata na ja ƙafafuna zuwa jikin bango daga ƙofar ɗaki ina maimaita Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Matar Baba Ali ta biyu da muke kira Maman su Samira da ke kwashe shanya sasanmu ta dubi inda nake tana kwashe kayan tana ninkewa sai ta ɗora saman kai ta ce “Sai haƙuri Ummu duka auren wata huɗu ki kwantar da hankalinki ga yan’uwanki nan ba ki gani su ko auren ma ba su yi ba?
Zura mata ido na ɗan yi nazarin maganganunta nake yi har ta gama kwashe kayanta ta tafi, yaransu uku yammata ƙaramar ita ce sa’a ta da maganar aurena ta tashi daga su har ya’yansu sai da suka nuna baƙin cikin su yammatan su Aliya duk da na sa su cikin hidimar yammatancin zamewa suka yi, har yau kuma da aka kwaso kayana ba su leƙa ɗakina ba.
Watsar da maganganunta na yi na koma faɗin Hasbunallahu wani’imal wakil. Sai da na ji zuciyata ta rage zafin da take yi na rarrafa na shiga ɗaki.
Jin yadda shari’ar Abakar ta kasance jama’ar arziƙi suna ta shigowa suna ƙara jajantawa.
Washegari baban Abakar ya zo tun da safe ya duba ni, da zai tafi ya kawo kuɗaɗe ya ba ni ya ce na yi haƙuri na yi ta addu’a.
Da hantsi sai ga Amiru ya zo ɗauka ta zuwa prison din da aka ajiye Abakar.
Wani benci aka ba mu saboda wani ma’aikacin gidan yarin da Amiru ya sani muna jiran a fito mana da shi wata doguwar hanya na zura ma ido da suka taho da jami’in.
Ƙarshen ramewa Abakar ya rame ya yi duhu, na sauke fuskata ƙasa har suka iso gare mu ina sauraren maganar da suke da Amiru kusa da ni ya zauna “Ummuna.” Ya faɗi yana leƙa fuskata na share siraran hawayen da suka taho mini amma ban yi magana ba, hannunsa ya sa ya ɗago fuskata hakan da Amiru ya gani ya sa shi tashi ya ba mu wuri.
“Ki yi haƙuri Ummu Radiyya imani da kaddara na cikin shika-shikan musulunci mu rungumi ƙaddara mu samu mu ci wannan jarabawar. Abu ɗaya nake tunawa in samu sassauci budurcinki da na karɓa a darenmu na ƙarshe, fatana kin ɗauki cikina a wannan haɗuwa ta mu ko da ban fito ba na bar baya na bar ma Baba abin da zai kalla a madadina.
Kuka sosai na fashe da shi ya ruɗe ya shiga lallashina, ina share hawaye ina faɗin “Wace irin magana ce wannan in zo wajen ka kana faɗa mini ba za ka fito ba. Hannayensa ya haɗe yana ba ni haƙuri zan yi magana jami’in ya ce lokacin ku ya cika.
Na ajiye ledar da na sanyo mishi abinci na tashi na tafi ba waiwaye Amiru ya biyo ni muka tafi.
Na koma gida na zauna ina yawan kai ma Abakar ziyara rashin samun sauƙin Haj Iyami na ƙara jefa ni fargaba game da makomar Abakar.
Har lokacin kuma ba a ƙara komawa kotu ba don sauraren ƙarar na rasa me zan sayar na saya ma Abakar kayan amfani da za su taimaka mishi zannuwana na akwati suka faɗo mini sai dai ina fargabar ko Mama za ta amince na dai yi karfin halin tunkarar ta ɗan jim ta yi kafin ta ce “Ba a son sayar da sutura Ummu Radiyya idan ka fara ba ka bari amma daga lalura ta gifta Allah ya san niyyarmu ni kuma ban da isassun kuɗi ballantana na ba ki ki ɗauki biyu a kai ma Ya gana (don sana’arta ce) Zan kira ta a waya.” Murmushi ya suɓuce mini na jin daɗin amincewar ta ita ma Maman na ga farin ciki a ta ta fuskar na ganin yau kaɗai tun daga faɗowar ibtila’in nan na yi murmushi.
Yammacin ranar ta aiki Hassana ta kai ma Aunty Ya gana atamfofin wadanda na fitar da kaina. Kudinsu ta ba ta ta juyo saboda jin me za a yi da kuɗin.
Sayayya sosai na yi masa ban kuma jira ranar da nake kai mishi ziyarar ta zo ba na shirya na tafi na gabatar mishi da su, tsayawa kawai ya yi yana kallo na wanda na san mamakin inda na samo kuɗin da na sawo mishi wadannan kaya yake yi.
Kafin ya yi magana jami’in da ke tsaye kanmu ya ce minti goma da ya ba mu sun cika.
Na tashi na tafi tun daga ranar kuma sai ganin sa ya zama abu mai wahala ko ka je ba a bari ka gan shi ga shaari’arsa an ƙi yi , Baba na zuwa duba ni lokaci lokaci Amiru ma ya kan zo .
Ganin ban san ranar ƙarewar zaman ba a wani zuwa da na yi na kuma samu sa’a na gan shi .albarkacin Baba Isa da muka je tare .
Kallon juna muka yi ta yi a maimakon magana saboda daɗewar da muka yi ba mu ga juna ba.
Na share fuskata na tambaye shi yadda yake ya ce “Kin rame Ummuna, ki sa haƙuri ki yi mini addu’a.”
Na gyada kai “Allah zai fitar da kai Abakar, sai wata alfarma da nake roƙo a gare ka.”
Da sauri ya ce “Mene ne? Kamar kuma ya kiɗime da jin maganata don akwai alamar zullumi cikin muryarsa.
“So nake ka yi mini izni a gidansu Nabila akwai matar yayanta tana ɗinkin zannuwan gado in dinga shiga ina koyo.”
Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya fitar “Ki je Ummu Radiyya, da har na cika da fargabar ko kin gaji ne.”
Murmushi na yi wanda ba nishaɗi a cikin sa na goge hawaye da ban iya tsayar da su matuƙar ina gaban shi a gida dai na soma dangana na kan zauna cikin mutane har idan suna hira na tsoma baki.
“Ki bar kukan nan haka Ummu Radiyya ki shiga cikin bayin Allah masu haƙuri.”
Ya rage murya yana duban jami’in da ke kusa da mu “Ba ki samu ciki ba ko Ummu Radiyya?
Na dube shi sai na rufe idanuwana
.na girgiza kai don ya bar maganar na ce “Idan na koma zan nemi Amirun na ji yadda ake ciki da shari’arka na rabu da ji daga Amirun
Ya hura iska”Amiru ba ya gari zuwan sa na ƙarshe ya shaida mini ya samu babbar mota zai fara kai kaya Lagos.”
Na girgiza kai cike da juyayi don na san babu mai kula da shi da ya kai Amirun.
Aka shaida mini lokacina ya cika na yi sallama da shi na koma gida.
Washegari na shirya na tafi Tudun wada gidansu Abakar, a kofar gida na samu Baba bai yarda mun gaisa a nan ba ya ja ni zuwa ciki, gani na Haj Nasara ta kama kame-kame don daga ita har yayanta ba wanda ya leƙa gidanmu, sai Aunty Habashiyya kaɗai na gaishe ta kafin na faɗi ma Baba dalilin zuwa na kan shari’ar Abakar shiru.
Ya ce wallahi suna ta ƙoƙari shi da amininsa Alh Musa, abin da ya kula kamar da wani ƙullin cikin lamarin .
Muka tattauna Haj Nasara na sanya mana baki ban wani daɗe ba na yi musu sallama na tafi kuɗi Baba ya ba ni amma ban karɓa ba .
Rashin samun abin hawa ya sa na yi ta takawa a ƙafa ganin gidan wata Hafsah da na yi sabo da ita a a ɗan zaman da na yi unguwar sai na ji ina sha’awar leƙa ta mu gaisa don har gida ta bi ni ta jajanta mini na kutsa gidan haɗe da sallama ta tare ni da faran-faran ɗinta ta kai ni daki muna gaisawa matar wan mijinta da suke zaune tare ta shigo muka gaisa sai jajanta mini abin da ya faru da Abakar take yi har tana faɗin in faɗa ma iyayena mu baza malamai a yi addu’a don magana na ta yawo an ce Haj Nasara ta ce muddin kuɗi na magani Abakar bai fitowa haka ma yaron Haj Iyami na biyun ya sha wannan alwashin Maganganun nata suka ɗaga hankalina musamman da tana cikin fadi wata makociryarsu ta shigo tana jin abin da take fadi ta ce ita ma ta ji .
Komai kasa furtawa na yi na yi musu sallama na bar gidan.
Ina isa gida ko zama ban yi ba na fara labarta ma Mama abin da na jiyo nasiha ta yi mini in fita hanyar surutan mutane in rungumi sallar daren da na fara sanadin barci da ban yi dogo, in ta faɗa ma Ubangiji in sha Allahu zai warware komai.
Na ɗan ji sanyi kaɗan amma maganar ta zauna mini a rai.
Na fara zuwa gidansu Nabila koyon ɗinkin zanen gado ba a kuma ɗauki lokaci mai tsawo ba na iya na ce ma Nabila mu dinga koyo tare ta ta ce ita ba ta iya wahala kuma fa idan na shiga gidan tana tare da ni abin da dai ta dage take faɗa mini mu jona HND ɗinmu da zarar shekarar nan ta ƙare don mun kammala diploma kenan aka yi aurena ni ma kam ina son cigaban amma kuma babbar damuwa ta Abakar ya fito a wurin nan.
Baba Isa ma sai da ya zo ya samu Mama kan karatun nawa ta ce sai ta tambayi mijin nata idan ta je da na koma ban samu ganin sa ba sai dai na koma gida cikin damuwa.
A wannan tsakanin Haj Iyami ta rasu wasa gaske kuma ba wanda ya kuma ganin Abakar ma’aikacin da Amiru ya sani shi ya ba Baba wasu takardu guda biyu ya ce da taimakonsa Abakar ya rubuta su don kuma ya sauƙaƙa ma Baban zarya ya ce magana ta gaskiya Abakar ba shi cikin gidan nan an ɗauke shi tun washegarin rasuwar Haj Iyami an bar gidan da shi a sirrance.
Da ya ga Baban ya shiga wani yanayi ya ce ya koma gida ya yi ta mishi addu’a amma Abuja aka wuce da shi.
Daga can gidanmu ya yi ma tsinke ya shigo amma iyakarsa Gate ya jingina da bango tahowa ta don amsa kiran da Mama ta yi mini ina gidansu Nabila wurin koyon zanen gado.
Baba na share hawaye da haɓar malum-malum ɗinsa gabana ya shiga tsalle na tsuguna kan ƙafafuna kalaman Mama da Alh Musa suka ƙara kiɗima ni, takarda Baba ya miƙo mini wani bi-biyu nake ganin ta na miƙa hannu na amsa na kuma kasa buɗe baki na yi magana Alh Musa ya ce “Ƙara haƙuri Ummu Radiyya, muna ta addu’a in sha Allahu zai kawo mana ƙarshen abin.” Kai na yi ta gyaɗawa uwa ƙadangaren gobara har suka yi ma Mama sallama ina nan tsugune kamar an sanya wa bakina gum, Mama ta kamo hannuna na miƙe da ƙyar don nauyi da na ji jikina ya yi muka shiga cikin gida.
A tsakar ɗakinmu ta zauna ta miƙe ƙafafunta hannayenta a sama tana yi ma Ubangiji kirari kafin ta roƙi ya kuɓutar da Abakar a duk inda yake “Me ya faru da Abakar ɗin wai Mama?
Na samu ikon tambayar ta ina zama daga ƙofar ɗakin. Ta yi tagumi da hannu biyu Hassana ma da ke karakainar ɗora abincin rana ta tsaya ta zura ma Mama ido Hanan ma da ba ta da wayo ganin halin da muke ciki sai ta dube ni ta dubi Mama.
Hassana ta ce “Me kuma ya faru da Abakar ɗin?
Mama ta dube ta sai kuma ta dube ni “Ki sa haƙuri Ummu, kowane bawa da irin ƙaddararsa ya zama dole in sanar da ke Abakar ba shi gidan yarin nan an ce an ɗauke shi an tafi da shi Abuja.”
Hannu na ɗora saman kaina ido a warwaje da nufin na kwarma ihu ko na samu sauƙin raɗaɗin da ke tasowa daga ƙasan zuciyata, sai dai na samu bakina da maƙalewa na miƙe tsam na wuce ɗaki na hau katifata duk abin nan takardar da Baba ya ba ni na runtse a hannuna kuka na yi ta yi mara sauti sai hawaye, idona kuma na kan takardar amma na kasa samun ƙarfin gwiwar da zan buɗe ta, da na yi nufin buɗewar sai wani rauni ya saɗaɗo ya lulluɓe ni, ina jin tulin fargaba na me zan taras.
Gumin hannuna har ya fara jiƙa takardar kamar wadda ta riƙe kunama haka na saki takardar da sauri.