Hawaye ke cika idona na yi iya yi na na mayar da su ba tare da na dubi kowa a cikin su da suka zura mini ido suna jiran abin da zan ce na ce “A ba su.”
Miƙewa na yi na bar su suna murna ina gyara goyon Hanan na fice kamar ana tunkuɗa ni.
Gaban Mamanmu na zube da na samu zaune bakin gado, kuka mai cin rai da ke tasowa daga ƙasan zuciyata na rushe da shi, na yi mai isa ta ba ta ce mini komai ba har sai da na sanya dukkan hannayena na share hawayena
“Me zai sa Mama ki yarda a karɓe mini kayana ina marainiya wa zai saya mini wasu idan na tashi w…. Maganar maƙalewa ta yi na kasa ce mata idan na tashi wani auren.
Kaina na ji ta dafa “Ki yi haƙuri Ummu Radiyya na rasa yadda aka yi na kasa hanawa amma Allah da ya ba ki waɗannna zai ba ki wasu duk wanda ya rufa asirin wani Allah zai rufa nashi, in sha Allahu za ki samu waɗanda suka fi su.”
Ba don maganganun nata sun ratsa ni ko sun sanyaya mini zuciya ba na miƙe Hanan da ke mutsu-mutsu na sauke mata ita a ƙafa na tafi ɗaki na kwanta a katifa ina famar kuka mara sauti, karɓe mini kayan ɗaki da gasken gaske ya girgiza duniyata.
Kwana biyu kawai da yin maganar aka zo kwashe kayan Baba da ya zo ɗakinmu kwana yana ta lallamina da daɗin baki kar na damu wasu kayan zai saya mini idan na tashi wani auren.
Ni dai da ba sabawa na yi yana mini magana da ja a jiki irin haka ba kasa sakewa da shi na yi, shi ba mai sakin fuska ba ne ko can sasan shi ka shiga cikin tsare gida yake bai kuma yawan magana, wadda za ka ga murmushinsa da hirarsa Mama ce idan yana tare da ita.
Wai Aya uwar son banza kayan dakin nawa bai ishe su ba ta ƙara turo shi wai ba ta sayi tukwane ba a ba ta nawa aro idan taro ya tashi abin da ta samu za ta biya.
Ni ya samu da maganar kai tsaye na ce A’a, Mama da ke cikin ɗakinta ta fito ta ce mini in tashi in je na mike na tafi na bar su ban san me ta ce mishi ba na dai ga an bar ni da tukwanena.
Aliya ta sanya ni a harkar bikinta don haka na shiga aka yi da ni har Nabila na gayyata.
Bayan bikin na mayar da hankalina kan ɗinkin zanen gado, ni da ogata muke tafiya kasuwar barci mu amso zannuwan gadon idan muka kammala in kai musu.
Aiki tuƙuru nake yi ba gajiya ta kan ba ni ɗari uku har biyar tarawa nake ina fata in tara wani abu daga kudin da zan yi hidimar makaranta.
Masu ba ogar tawa aiki mutum hudu a cikin su suka yo kaina duk sona suke, tana da masu ba ta aiki sun yi su goma aikin ya kan yi yawa dole sai dai ta ba wasu haƙuri yan kasuwar kuma suna son aikinta saboda ba ta ha’inci
Masu so na sun yi mini tayin karɓar aikinsu , idan na dawo gida ba su bari na sakat da wayarsu a tsorace na fara karɓa na kuma ta sa Nabila muka je muka yi ma ogar tawa bayani, matsalar ba ni da keken ɗinki kusa da mu akwai wata budurwa da ta koyi aikin tuni an sai mata keken ɗinki sai dai ba ta da costomer har gida mahaifiyarta ta same ni ta ce mu dinga aikin tare da yarinyarta mai suna Abida idan na yanka gidansu nake zuwa mu yi aiki, idan muka kammala na kan raba kuɗaɗen da aka samu in ba ta kasonta nawa dai ya kan fi yawa.
Ina samun alheri sosai.
Ranar wata laraba da yammaci na karɓo aiki, a ƙofar gida mai keke ya sauke mu ni da Abida. Ganin Hassana tsaye da wani abin ya ba ni mamaki, da na ƙara kallon inda suke sai na gane mutumin Malaminmu ne na islamiyya Malam Mahir Assalafi, na kinkimi Faiba ta da na sawo muka gaishe shi ni da Abida muka shiga gidanmu.
A inda muka saba zama mu sha iska na hango Lubna tare da Mama tana taya ta haɗa turaren wuta, tun kafin na ƙarasa nake aika mata saƙon fara’a, muka sauke faibar Abida ta gaishe da su ta juya na zauna kusa da Lubna na karɓi yarinyarta da take goyo ina tambayar yaushe ta zo.
Ta ce tana shigowa aka ce yanzu na tafi.
Fuska na tsuke ina duban Mama “Ya aka bar Hassana ta fita zance?
Kafin ta yi magana Lubna ta riga ta “To ya kike so? Na ƙara tsuke fuska “Saboda Allah nawa Hassana take January ɗin nan ne fa ta cika 17ys a ce har ta fara zance? Karatu ya kamata Hassana ta yi kamar yadda burin babanmu yake mu yi ilmi mai zurfi da za mu dogara da kanmu. Kuma fa Malam Mahir na gani tare da ita.
Da wani sanyi da na ga Mama ta yi lokaci guda ta ce “Malam Mahir ya aiko a tambayi babanku izni ya fara zuwa wurin ta.”
Na ce “Amma gaskiya karatu ya dace da Hassana, ko fa Secondary ba ta ƙare ba.”
Rufe bakina Hassanar ce ta shigo tana isowa kuma na yi mata maganar karatu a maimakon fara zance tun yanzu.
Haɗa rai ta yi ta nufi ɗaki tana maganar da ban ji me ta ce ba.
Lubna ta janyo hannuna na dube ta “Halin da Mama take ciki za ki duba, idan an tarkaci karatu ina kuɗin da za a yi hidimar makarantar? Ta abinci ake yi Ummu Radiyya, ke ma na fi so ki bar wannan shigar gamin gambizar da kika koma kina kwalliya kina gyara jikinki ko kya samu wani mijin.
Na bi jikina da kallo ina fitowa wanka Abida ta shigo ta ce mai keke na waje ta kira mana da zai ɗauki zannuwan gadon da muka yi ya kai mu kasuwar barci na ce ta fara fitar da kayan ni kuma na yi sauri na murza mai na sanya farar riga sai zane wani ɗankwalin Mamanmu da aka ba ta tsarabar maka na ɗauka shi na ɗaura a kaina, na sanya gyale.
Ajiyar zuciya na sauke ban yi magana ba na miƙe “Mai na nan na kawo miki da hoda.” Lubna ta faɗi “Na gode.” Na ce na wuce ɗaki kayan abincin da ta saba kawo wa na fara cin karo da su tana iya kokarinta lokaci lokaci take kawo kayan abinci.
A ɗakinmu Hassana na samu tana shirya karanta da lokacin da zan fita tana guga kamar ba zan mata magana ba sai dai na ce “Amma Hassana saboda Allah a ƙananun shekarunki ya kamata a ce kin fara tsayawa da samari? Samarin ma Malam Mahir da kika san aure kai tsaye zai kawo shi, ke ma wankansa da kyansa da ke ɗibar yammatan Abdullahi bn Mas’ud ya ɗebe ki ba ki tunanin yana da mata?
Haɗe rai ta yi sosai ta yi maganar da ban ji ba na kaɗa kai ina ƙare mata kallo ita nan gani take ta kai yin aure duk da dai ita ɗin ta biyo jikin Mamanmu matsakaicin jiki da tsawo gare ta ga ta fara sol kamar dai Maman tamu, komai na cikar budurci ya bayyanar mata ta yi girman da aka ce ma wanda bai san shekarunta ba ta yi sha tara da gudu zai yarda.
Na fita daga ɗakin jin ana sallama, yaro na samu ya ce ana sallama da ni a waje.
Ciki na koma na ɗauko gyalen da na cire, Mama na ce ma zan leƙa waje ana kira na.
Lubna ta taso da sauri ce mini ta yi mu koma in ɗan yi kwalliya don Allah.
Murmushi na yi da ya tsaya iya laɓɓana na ce “Ni fa ko da ba na kwalliya akwai masu cewa suna sona fuska ce kawai ba na bayar wa,duka yaushe na rabu da Abakar a ce har na fara sauraren wasu mazan kamar ina jira.”
Ta girgiza kai ba ta ce komai ba har na wuce.
Ina zaton cikin masu so na ne na kasuwar barci don wani cikin su ya dage sai na ba shi address ɗina Abida ta faɗa mishi ya ce yana nan zuwa da daddare.
Ina ta ba za ido don gano inda mai neman nawa yake cak idanuwan nawa suka tsaya kan wani dogon matashi da na ƙura mishi ido da kyau sai na tabbatar Abakar ne, da sanyin jiki da na gwiyawu na ƙarasa inda yake yana murza hannuwa
“Abakar! Na kira sunan cikin wani irin yanayi, hannunsa ya miƙo zai kama nawa sai kuma ya yi saurin janyewa “Ka fito Abakar? Na tambaya ina ci gaba da kallon shi
“Allah ya nufa Ummuna.”
Dukkan mu mun kasa ɗauke daga kallon juna, ni tsananin ramar da ya yi ya koma siriri na gaske ga baƙi da ya yi duk da dama shi din ba mai haske ba ne.
Na share hawayen da suka kawo mini ziyara, wani ɗan dakali a gidan da ke jikin namu ya nuna mini muka tafi can muka zauna “Allah ya ƙaddare ni da fitowa Ummuna, ta sanadin wani aboki da na yi a can, ya yi mini alƙawarin fitar da ni bai fi wata guda a ciki ba aka fitar da mu tare.
“Alhamdulillahi.” Na faɗi cikin farin ciki da ke tasowa daga ƙasan zuciyata “Amma da ka fito yaran Haj Iyami fa idan suka gan ka kana yawo?
Ɗan murmushi ya yi “Ki bar Nigeria kawai Ummuna an kira su sun sanya hannu an kashe Case ɗin.
Cikin yar rikicewa na ce “Tun yaushe ka fito Abakar? “Satina biyu kenan, ina Abuja sai jiya na shigo Kaduna,akwai alamu na zan samu taimako daga fannin wanda ya yi sanadin fita ta.” Jikina na ji ya yi sanyi sati biyu da fitowa amma sai yau Abakar ya neme ni? Na dai share na nemi ya zo mu shiga gidanmu ya gaisa da su Mama.
Tun daga Gate ƙamshin abinci mai haddasa haɗiyar yawu ya daki hancinmu, muna yin part ɗinmu ƙamshin na ƙara shiga hancinmu na tabbatar namu ne
A falonmu na sauke shi Mama da Lubna suka zo suka gaisa tare da yi mishi barka da arziƙi, ruwa na kawo masa bayan tafiyarsu muka ƙara hira har sai da aka fara kiran sallar magrib ya yi mini sallama kan sai gobe zai dawo.
Na dawo rakiyarsa hannuna riƙe da kudaɗen da ya ba ni Mama na miƙa ma wa Lubna ta karɓa ta ƙirga ta ce dubu ashirin ne.
Kowa da tambayar da yake mini kan yadda aka yi Abakar ya fito, amsa na ba kowannen su kamar yadda Abakar ɗin ya faɗa mini.
“To yanzu sai mayar da aure kenan? Lubna ta tambaya
“Ƙwafa na yi a raina na ce Ho Lubna, ko a kanta aka ɗora ni iyakar ta kenan.
Amma a fili ce mata na yi “Ba mu yi zancen ba, duka fa jiya ya dawo.”
Ta ce “Ai gara ya yi ki koma ɗakinki.”
Lokacin na ji raina ya ɓaci kuma cikin ɓacin ran na yi magana “Idan ma an yi zancen komawar da wane kayan zan koma? Lubna ta yi kwataƙyas, domin ita da ta ji zancen bayar da kayan bayan faɗa da ta yi har kuka ta taya ni, bayan bikin kuma ta daɗe ba ta zo gidan ba har sai da Mama ta yi cigiyarta ta ce mini kuma baƙin cikin ba su kayana ya hana ta zuwa.
Kamar yadda Mama ta ce mini a wancan karon yau ma ce wa ta yi Allah da ya ba ni waɗancan shi zai ba ni wasu, dole muka rufe maganar.
Shinkafar da Lubna ta kawo Mama ta dafa har da kayan ciki ta kawo da kayan lambu, Mama da ranar girkinta ne kuma Baba kuɗi ya ba ta da ba su isa kashe ƙishi ba ballantana su ɗaura alwala ta shirya lafiyayyar Jallof,
can gindin bishiya ta yi masa shinfiɗa ta shirya masa abincin.