Sai da ƙarfe ɗaya muka shiga Kaduna, kayan kwalliyata na ciro na kuma gyara fuskata. Na goggoga turaruka a jikina. Ina nuna ma direba hanya muka isa har gidan, horn direba ya yi, ina niyyar sanar ma shi ba maigadi ya saurara, aka wangale get ɗin, wani wanda ban taɓa gani ba sai a yau, shi ya buɗe, ya kuma iso wurin yana tambayar wurin wa muka zo. Ni na yi mishi bayani, haƙuri ya shiga bani kafin ya soma gaishe ni.
Motar ta kunna kai cikin gidan, Maigadin ya biyo mu da sauri, na fito ina. . .
Masha Allah Allah yakara basira ameen.Daga jin novel din nan zai ilmantar sosai musamman zaman takewar kishiyoyi
Nice piece Allah ya kara basira Amin
Masha Allah. Sannu da ƙoƙari Qanwata Maryam. Ubangiji Allah ya ƙara basira tare da ɗaukaka amin summa amin ya Allah.
Masha Allah nvl yyi dadi sosai akwai ilimin zamantakewar aure sosai acikin shi,Allah yasa mu amfana da ilimin cikinshi