Skip to content
Part 19 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Su uku na samu a cikin falon zaune kan ledar cin abinci. Na zauna na gaida Uwargidan, wadda yanayin ta ke gwada a sama take, ban wani saki jiki ba, sama sama na dan taba abincin kadan dan ban saba da su ba. Da aka kammala tsakiyar falon aka koma, me aikin ta zo ta kwashe komai. Sai mamakin shigar da Basma tayi nake a raina, riga da wando ne jikinta rigar me bayyana surar jiki ce, kuma bata sa komai a ƙasa ba, ga na shanunta nan zahiri waɗanda suke a tsaitsaye kuma manya.

A kasan raina kuma wani kishi ke cin raina, na ganin yanda take ta gilmawa gaban Tahir. A fakaice na dubi Uwargida Halima gogaggiyar mace ce, ga hutu da ya ratsa ta, fara ce sosai gajera, ƙatuwar gaske. Yan biyu suna barci akan kujera. Gyaran murya megidan ya yi kafin ya yi godiya ga Allah, sai ya gabatar da ni a wurin matan nasa tare da nasihar mu zauna lafiya ni ma ya gabatar min da su. Da ya gama bayanan sa ya ce in akwai me magana tayi, kowacce ta girgiza kai, ya ce “To ya batun rabon kwana daga ga amarya ta zo.” Uwargida Halima ta kara ɓata rai, Ai Amarya ba yau ne za ta tare da kai ba, dan haka za ta jira har sai girki ya zagayo kanta.” Basma ta ce “Haka ne.”

A ranar Uwargidan ce da girki. Basma ya umurta ta nuna min general kitchen na gidan, ta nuna min wanda yake me girma ne kwarai, akwai Electrics kala daban daban da tukwane, kayan girki nau’i iri iri, ta kuma nuna min store.Da muka fito ya ce in kwashe ƴan biyu su taya ni kwana, Husainar na fara dauka na kusa shigewa na tsinkayi muryar daya daga cikin su tana cewa “Ba ka ce gida za ka mayar da su ba? ban ji me ya ce ba na shige, na dawo ɗaukar Hassana na gan shi tsaye da alama fita zai dan har da key a hannunsa, na dauke ta na wuce, a gado na kwantar da su na cire hijab din jikina na matsa gaban dressing mirror ina ƙare wa kaina kallo, ina kuma tuna matan nasa da na gani, ina da kyauna daidai gwargwado dan ban da muni musamman idan nayi kwalliya ina matukar yin kyau, ba abin da na rasa na surar ya’ya mata, diri me kyau Ubangiji ya yi min, fatata tana da haske ba dai sosai ba.

Ban san iya lokacin da na ɗauka cikin tunani ba sai shigowar Tahir na ji, na ta da kai muka haɗa ido, “Har yanzu ba ki kwanta ba? ya tambaye ni, na daga mishi kai, ledoji biyu ya miƙo min na karba tare da godiya. Ki yi kokari ki kwanta, dare ya soma yi” Ya faɗa yana juyawa na bi bayansa da kallo har ya kai ƙofa sai ya rufo min. Ajiyar zuciya na fidda sai na buɗe ledojin, ta farko gasassar kaza ce, ta biyun kuma da ta fi girma tarkacen kayan shayi ne, da abubuwan amfanin yau da kullum. na ajiye komai inda ya dace sai na dan ci kazar sama sama na adana sauran, sai nayi shirin barci, wasu riga da wando na ɗauko na saka, rigar kamar vest take, ta kama ni tsam ko cibi bata kawo ba, wandon ma me kama jiki ne, tsawonsa iya gwiwa, rigar fara ce wandon blue.Na hau gado tsakiyar ƴan biyu na kwanta, na yi addu’o’ina na shafa musu ni ma na shafa. Na dade cikin tunani kafin gwanin iya sata ya yi nasarar sace ni. Asubar farko na farka. Bathroom na wuce na dauro alwala, na fito na tada sallah, na idar ina Azkar wayata ta shiga ƙara, na miƙa hannu na ɗauko ta, sunan Haj ke yawo saman screen ɗin, nayi sallama murmushi kwance saman fuskata, tare da gaishe ta, ta amsa tana tambayata ba dai matsala ko, na ce lafiya lau, bayan tambayarta mutanen gidan sai muka yi sallama.

Ummata na kira sai dai ita faɗa ta rufe ni da shi wane irin kira ne da sassafe? na faɗar mata da gaba. Na ce “Kai Umma amma ita Hajiyar su Tahir yanzu ta kira ni.” Muka taɓa yar fira sai muka yi sallama. Ganin yaran sun tashi zaune kan gado, yasa ni miƙa musu hannu suka sauko na wuce bathroom da su na wanko musu baki nayi musu wanka, sai da na gama yi musu kwalliya sai na rasa kayan da zan canza musu. Kettle na ciro na jona ruwa ya yi zafi na haɗa musu tea, suka sha suka haɗa da kazata ta daren jiya, ba su kammala ba aka kwankwasa kofa, daga ni sai kayan barcin daren jiya, zane na daura sai na buɗe, me aikin jiya ce, cikin mutuntawa ta gaishe ni ta ce “Me kai yan biyu makaranta ne, ya kawo kayansu, na karba na koma ciki na sanya musu uniform din, ta kama hannunsu sai suka fice.Kamar in yi wanka sai na ga bari dai in gyara kumbata, zanen da na ɗora saman kayan na cire na zauna ina gyaran kumban, murɗa ƙofar da aka yi yasa ni daga kai Tahir ne cikin shiri yake na wani lallausan yadi, kamshinsa tuni ya karaɗe wurin, kallo yake ƙare min, ya ce “Kin karya? na ce “A’a” ya ce “Why? na ce “Wanka nake so in fara yi” “Ki tabbatar kin fita kin nemi abin da za ki ci, saboda fita wurin aiki, ba sa samun damar tsayawa yin abin karyawa, sai dai wadda ke da aiki tana bani abincin rana ni da ita. Da daddare ne ake yi gaba ɗaya. Kai na daga mishi, “Ni zan fita wurin aiki” nayi masa addu’a.Ta window na koma ina lekensa, har sai da motarsa ta fice gidan.

Wanka nayi, nayi kwalliya da wata doguwar riga fara, sai gaban da aka yi ma ado da yarfin baƙi da brown, gyale me laushi kalar brown na ɗaura a kaina.Tea na haɗa na sha ban fita ba kamar yanda ya ce, na gyara gadona zuwa yan goge goge da shara, da na gama barci nayi har zuwa azahar, yunwa ce ta tashe ni har jikina na ji yana rawa.

A daddafe nayi sallar azahar. Ban da zabi dole na fita zuwa kitchen, ban hadu da kowa ba sai da na shiga kitchen din, Halima ce tsaye da alama bata daɗe da shigowa daga wurin aiki ba, gabana na ji ya fadi da ganin ta sai na rasa me zan yi, sannu nayi mata ban ji ta amsa ba sai fuskarta da ta ƙara daurewa, juyawa nayi na koma ɗaki yunwa na ci gaba da nukurkusa ta, awa daya na bata kila ta kammala da na koma sai na samu kitchen din a datse an sa key. Cikin sanyin jiki na koma tea na ƙara haɗawa na sha.Sai kusan la’asar Tahir ya shigo, ya ce na ci abinci na ce “E” ranar dai ban samu na ci abinci ba sai da daddare da aka haɗu gaba ɗaya, shi ma rashin sabo yasa na tsakura kadan na koma ɗakina. Hakan yasa washegari suna fita wurin aiki ni ma na fita shinkafa jallof na dafa ban yi amfani da nama ba kifi nasa na zuba kayan lambu, har kunun aya na hada. Na koma daki na adana abi na sai azahar in ci lokacin da na zuba sai ga Tahir ya shigo ya ce “Na shigo a sa’a, dama fita zan yi neman abin da zan ci dan Halima yanzu za ta ɗora mana.” ban tanka maganar shi ba sai sannu da zuwa da na shiga yi masa, kunun ayar da na tsiyaya ya ɗauka ya sha ya lumshe ido “Da daɗi Ummuna”

Murmushi nayi muka ci abincin tare sannan ya fita”.Gadona na hau nayi ɗaiɗai ina jin dadin iskar da ke kada ni, tare da murnar ban yi amai ba, dan a yan kwanakin nan sai in yi ta fama da tashin zuciya, wani lokaci har sai na yi amai. Hafsa na kira muka sha fira, muna kammalawa kiran maman Ummi ya shigo muka gaisa da tambayar bayan rabuwa ta ce “Kina da labarin dawowar su Amma?

Na ce “Ko kaɗan”.Ta ce “Sun dawo, iyayen Usaina ma sai da suka neme ki dan su ba ki haƙuri, aka ce kin koma Kaduna, amma sun kira Sodangi” Na ce Kin ga kuma bai gaya min ba”. Mun ta fira har na soma hamma, sai da aka fara mata warning sai muka yi sallama. Abin da ya yi ta gudana kenan sai sun fita wurin aikin su sannan in lallabo in yi abin da zan ci. Kuma matukar zan ci Tahir zai shigo tare za mu ci da shi, har a na gobe aiki zai zo kaina, duk sun fita wurin aiki cake nayi cikin sauri da niyyar zan adana abina ina ci a hankali, na kai shi ɗaki me aiki Ade ta iske ni ta ce min an yi baƙuwa. Na fito falon, wata mata na samu ƴar gaye, na zauna ina gaishe ta ta amsa cikin fara’a “Ni matar abokin mijinki ce, Engineer Rabi’u Bello. Sunana Haj Shema’u na kara mata sannu da zuwa, dan na ji sunan mijin nata a bakin Tahir, na miƙe “Zo mu shiga ciki Haj” Bata musa ba ta bi bayana, Ade dai tana ta goge gogenta a falon. Muka shiga ta zauna tana ta kallon ko’ina a falon, na debo mata Cake din da nayi da lemo, tana ci tana kurbar lemon a hankali, ta dube ni “Ɗaki ya yi kyau Amarya, ya ma sunanki?na ce “Ummulkhairi” murmushi tayi “Suna me daɗi, ina sauran matan gidan? ko da yake suna wurin aiki ko?na ce mata “E” “Sai ke kaɗai suka bari” ta buɗe jakar da ta ratayo, wasu kwalabe da robobi ta ciro tana nuna min, “Kin ga kina amfani da wadannan, mijinki babu wacce zai kuma kallo da gashi sai ke, dan za ki zama tauraruwa, idan ma bai hankada su ba”.Bayaninsu ta shiga yi min ɗaya bayan ɗaya ina kallon ta da saurare, sai da ta gama ta ce “To wanne, da wanne za a ba ki? dan kasaƙe nayi kafin na fadi “Bani da kuɗi” wani kallo ta min “Kina Amarya kike faɗin ba ki da kudi? to gara ki san wacce kike ciki, kishiyoyinki duk aiki suke suna diban albashi ga abin da suke samu wurin megidan, ke kadai ce yarinya a cikin su, kuma an ce iyakar karatunki Sakandire, to wallahi ina mai ba ki shawara ki hura wa maigidan wuta ya maida ki makaranta.

Ta haka ne kaɗai za ki iya gogayya da wadannan matan. “Ungo”. ta miƙo min wata yar roba “Tsarki ake da shi, mijinki sai ya kusa suma in ya kusance ki, kina ganin ya susuce sai ki bijiro mishi da zancen ya samo miki makaranta”. ban amsa na ce “Ni fa ba ni da kudi” ta ce E na ba ki ne, taimakon ki zan yi Ummulkhairi, ina kallon ki kamar ƙanwata, idan ma maganin matan bai yi ba akwai inda zan amso miki taimako. Bani lambar wayarki. Na faɗa mata ta sa ta kira sai ta shigo. Na karbi maganin da ta bani ina godiya, da sauri na ga ta dubi agogo “Bari in tafi Ummulkhairi” na ce “Tun yanzu? ba ki tsayawa in yi girki” kai ta girgiza “Ke ke da girki kenan?na ce A’a” ta ce “Ba dai ke ke musu girkin ba? na ce “A’a nawa ne ni kaɗai, megidan dai kan ci idan nayi”. Ta ce “A kul kika kuma ba shi, su suna wurin neman kudin su, ke kina nan, bayan gadin gidan da kike musu ki yi ya ci, nan gaba ma cewa zai ki yi har su, kar ki yarda ki zama ƴar tsaron gida”.Ta soma tafiya na bi ta a baya har wurin motar da ta zo cikinta. Sai da ta shiga sai ta leƙo “Ko fa mijinki kar ki ba labarin zuwana.”

Kai na daga mata sai na koma ciki jikina a sanyaye ina tunanin al’amarin wannan mata, dan abubuwan ta da yawa sun ɗaure mini kai. Dirowar na bude na saka abin da ta bani, na dubi agogo, lokaci ya tafi zai yi wahala har in gama girki wata cikin su bata shigo ba, tunanin kuma halin da zan kasance idan ban ci ba na tuna, dan yanzu ban jimirin yunwa. Haka nan na shiga na soma aikin ina jin faɗuwar gaba ina kuma auna wannan mata da inda ya dace in sa maganganun da ta zo min da su. Ina juye abincin Basma ta shigo, kamar yanda da na ga daya daga cikin su zan ji faɗuwar gaba yanzun ma hakan ce ta faru da ni, gane ba za ta kula ni ba yasa na gaishe ta, ta amsa ta cigaba da abin da take, na jera komai kan wani babban tire ban ko tsaya ɗauraye kayan da nayi amfani da su ba na fito kitchen din.Har muna zaune muna cin abinci da Tahir tunanin matar bai bar ni ba, musamman da ta ce kar in kuskura in ƙara ba shi abinci na.

Da muna waya da Hafsa da yammacin ranar kamar in bata labari, sai dai na fasa.Na dai yi kokarin yakice tunanin ta da ya hana ni sakat ya min tsaye a rai tsawon wunin yau.

Washegari da zai fita ya miƙo min key na wurinsa, na ce me zan dafa? sai da ya lumshe ido ya ce “Indai girkinki ne komai kika dafa zan ci.” Da rana bai dawo ba, daga office taaziyya suka wuce shi da wani abokinsa zuwa Zaria. Sau biyu ina fita da niyyar gyara sashen megidan sai in dawo.

<< Wa Gari Ya Waya 18Wa Gari Ya Waya 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.