Skip to content
Part 26 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Na ce “Zai shigo, idan zai wuce.” Ta ce “Kul yi yanda na ce” jikina ba karfi na miƙa hannu na karɓi mayafin sai na fita. Tunda ya dawo ban taba bi ko hanyar dakin ba. Ina ƙwanƙwasa ƙofar ya ce a shigo, na murɗa na shiga da Sallama, zaune yake yana kurbar tea, wando ne kawai a jikinsa sai farar singlet.

Ganin kayan da ya ciro ya barbaza a ko’ina, yasa na shiga kintsa su, na haɗa mishi wadanda zai yi tafiyar da su dan ya ajiye su wuri guda, na gama na shiga kintsa dakin, ji nayi an janyo ni sai na fada kansa, ba ki iya gaisuwa ba ko? Ban magana ba sai tura baki da nayi “Kukan me kike jiya? Maimakon amsa kuka na kama mishi “Lallai yarinyar nan, wai yaushe kika zama shagwababbiya komai kuka?

Gane ba zan yi magana ba yasa ya shiga yamutsa ni ina mishi kuka “Tafiyar da zan yi take sa ki kuka? Ba ki ji me Aunty ta ce ba ko na zauna ba abin da zan miki. Ko abin kike so? Da sauri na shiga girgiza kaina sai ya ci serious “Ki yi hakuri to, kamar yau za ki ga na dawo, ki yi ta min addu’a kin ji?

Ni ma zan ta miki Allah ya ba ki lafiya.” Maganganu masu daɗi ya yi ta gaya min, sai na ji zuciyata tayi sanyi daga haushin sa da nake ji tun gano sherin da ke tsakanin su da Latifa. Mun dade tare har lokacin tafiyarsa ya kusa, dan jirgi zai bi, muka fito ya rufe dakin ya miƙo min key, har inda motarsa take nayi mishi rakiya bayan sun yi Sallama da Aunty Kulu. Wucewarsa komawa daki nayi na hau gado, lamo nayi, ina tunanin rayuwa.

Muryar da na ji suna gaisawa da Aunty Kulu ta sa ni bude ido ina duban ƙofar, “Wuce ciki ki same ta, ina jin ko tayi barci bai yi nisa ba” na tsinkayi muryar Auntyn, ta shigo da Sallama, wajen kafafuwana ta zauna yayin da nake tashi zaune, “Ka ga yar gatan, Aunty kina lunkume ta adana ki.”

Murmushi nayi “Kina dai yi min tsiya Aunty Laila” “Ba tsiya ba ce Allah, na ga ma kin sha kwalliya, an sa Atamfa ko yau za a maida mahaifa? “Kai Aunty Laila, kwanana goma fa kike min wannan maganar.” Ta ce “To ai ke ɗin ce, kullum kamar matar limamin Madina, ba ki da aiki sai saka dogayen riguna, kamar wacce aka yi wa gori.”

Rausayar da kaina nayi “To dan Allah ya zan yi, tun aure na, kayan auren suna nan, a Kaduna ban san ko’ina ba ballantana in ce zan kai ɗinki, shi kuma bai ce min in kawo akai ɗinkin ba. Amma yanzu da na dawo za ki raka ni in bayar da dinkunan, dan tun zuwa na garin nan, kin san komai, ciwo ne ya dabaibaye ni” Wani kallo take min baki sake “Kina so ki ce tun aurenki kayan auren suna nan ajiye? Na gyaɗa mata kai tayi shiru cikin tunani, wayarta da ke cikin jaka ta ɗauki ƙara ta ciro ta tana kokarin amsawa, Ahmad ne mijinta, ya ce yana waje.

Miƙewa tayi tana shaida min abin da kenan, har falon Aunty aka shigo da shi, ya ɗan jima kafin suka tafi tare, txt ta turo min bayan wucewar su, ta ce akwai zancen da take so muyi sai ta dawo.Muna waya da Tahir sosai bayan tafiyarsa.Ranar da ya yi sati guda da barin Lagos, tun wayar safe da muka yi ban ƙara jin sa ba, sai dare har na kwanta ya kira na ce “Yau shiru? Ya ce “Ƙanƙara ya tafi.” Muna yar hira ina zabga hamma, da yanayin yanda nake magana yasa ya ce “Mu kwana lafiya, yarinyar nan barci kike ji.”

Da safe nayi wanka ina saka kaya, kiran Haj mahaifiyar su, Tahir ta shigo wayata. Na ɗauka da murmushi a fuskata, bakin gado na zauna ina gaishe ta, yanayin yanda na ji tana amsawa yasa ni tunanin Lafiya, ta ce “Ina fata Ummulkhairi ba za ki daga hankalinki ba, ki yi hakuri ki danne, dan kishiya bata da dad’i, amma ki duba wasu kika tarar, ki yi hakuri dan girman Allah. In banda taruwar da aka yi kaina, da tun jiya da ya iso ya warware auren da ya je aka dauro mishi ba tare da sanin kowa na shi ba.”

Mamaki da faɗuwar gaba suka sa na kasa tambayarta makamar zantukan da take yi, wadanda nake ji suna min kama da almara. Har saida ta ce “Kina ji na Ummulkhairi? Da ƙyar na bude bakina da nake jin ya min nauyi na tambayeta “Ban gane maganganun ba Haj, Tahir din ne ya yi aure?

“Yanzu dama bai sanar miki ba? Mu ma jiya da ya zo yake faɗi, wai shekaranjiya.” Wani haƙurin ta shiga bani, wanda na gwammaci da ta ƙyale ni in ji da halin da na tsinci kaina. Ina ajiye wayar Haj, gado na fada, wani irin yanayi nake ji wanda na san sai wadda aka yi ma kishiya ta san shi.

A haka Aunty Kulu ta shigo ta same ni, zama tayi kusa da ni “Ki yi hakuri, Ummulkhairi.”

Kallon mamaki na bi ta da shi watau su sun sani, kamar ta san tunanina “Jiya da daddare Sodangi ya kira ni ya gaya min, ya kuma roke ni, in rarrashe ki, Kawun ku ma ya turo ni in ba ki haƙuri. Wani irin aure ya yi irin na bariki, ba wani na shi da ya sani, sai da aka ɗaura ya isa ƙanƙara yake faɗi. Ajiyar zuciya na fidda ban yi magana ba, ganin duk iya kokarinta ban ce kanzil ba yasa ta kira Aunty Laila a waya ta shaida mata ta ce ta kira ni ta bani baki, maimakon kiran sai ga ta ta zo da kanta suka haɗu ita da Auntyn, duk maganganun da suke gaya min sauraren su kawai nake ban ce uffan ba.

Aunty Laila ta ce “Dagewa kawai za ki yi ki gyara kanki, ki san ke wace ce, ba wata kishiyar da za ta tada miki hankali.” Aunty Kulu ta ce “Shiyasa nake so ta kwantar da hankalinta ta bani hadin kai.” Ta tashi ta fita Aunty Laila ta bi ta da kallo, sai da ta ja kofar, sai ta fuskanto ni “Maganar da na ce za mu yi, Ummulkhairi tun haduwata da ke Allah ya haɗa jinin mu, nayi imani tsakani da Allah kike tare da ni, kamar yanda nake tare da ke dan Allah.

Na ce “Haka ne” ta cigaba “Ina so mu yi magana ta gaskiya, ki ɗauka kamar za ki gaya wa Yaya Sani, dan kin san in zai cuce ki, to kenan zai cuci kansa.” Na ce “Ina fa jin ki, Aunty Laila, tsakanin mu ai amana ce da kauna ta gaskiya” ta ce “Yawwa so nake ki gaya min yawan miscarriage din da kike ba ki ganin komai, ko jin komai? Dan kin ga duk a sakamakon gwaje gwajen da ake miki koyaushe ana tabbatar da lafiya kike ba wata matsala da ke haddasa miki hakan.”

Ajiyar zuciya na fidda “Humm, Aunty Laila yanzu saboda wannan tambayar kike ta wannan zagayen zagayen da kwane kwanen? Na gaya mata duk sa’adda nayi mafarki jini na bi na, daga bayan nan na hakakke indai Tahir zai kwanciyar aure da ni to zan yi mafarki ina yin mafarkin kuma zan tashi cikin jini.” Kai ta girgiza Sai kuma tambaya ta biyu, dan Allah ɗan zaman da kuka yi da kishiyoyin ki ya mu’amalar ku ta kasance?

Maimakon in fara da mu’amalata da kishiyoyin nawa kamar yanda ta nema sai na faro mata tun fara neman aurena da Tahir ya yi, har zuwa auren mu, zamana a kankara, na gangaro komawata Kaduna, da irin zaman da nayi, har yanda ta kasance min a Lagos, yanda nake fama da matsanancin zafin jiki hakan yasa dole Tahir ya hakura da ni, idan kuma ya dage sai ya yi a hakan za ki ga rabo ya shiga ranar da ya ƙara kuma sai ki ga nayi bari.

Ga kuma matsalar kasala da ta sanya ni gaba, ban iya mora wa kaina komai.” Ta ce “Ban katse ki ba, Ummu to kin ga wadannan suna daga cikin abubuwan da na nakalta a zaman ku, na ce ba karamin so mijinki yake miki ba. Yanda ba ki iya hassala ma kanki komai daidai da sharar ɗakinki sai na shigo na taimaka miki, za ki iya wuni ba ki yi wanka ba, amma duk ya hakura da ke a haka, alhali ga matansa can har biyu a gida.”

Na ce “Haka ne” amma a raina na ce. Da ya kyale ni ai ba ki san tashin hankalin da ya haddasa min ba, yanzu kuma dan dan karan wulaƙanci kishiya ya min bai ko gaya min ba.” Ta ce “Ina jinki.” Na cigaba “Kuma matsalar zafin jiki ko da rana Tahir ya zo da bukatarsa jikina zai dau zafi, rashin gyara kuma wallahi da ba haka nake ba ina iya kokarina wurin tsafta, amma sai na wayi gari daidai da wanka kan dole nake yinsa.”

Na cire dankwalina “Sumata na manta rabon da in taɓa ta sai ranar da zan yi barin nan, ko cikin nan da ya kai yanzu, tun samun sa, Tahir bai ƙara zuwa da buƙatar sa ba, sai ranar da ya zube, na rufe fuskata da hannuwana “Kar fa ki ce ina ta miki rashin kunya Aunty Laila, abubuwan ne suna damuna gami da daure min kai, na rasa hanyar warware su.”

Wani kallo ta min sai ta tashi ta fice, ta jima suka dawo tare da Aunty Kulu, wadda na san yanzu cikin aiki take duk da tana da yara masu yi, ta kan yi wa mutane na musamman waɗanda suka ji suka gani za su biya ko nawa ta caje su. Zama tayi Laila ta warware mata matsalata kamar yanda na shaida mata. Ni kam boye fuskata nayi dan kunyar Auntyn, da gamawar Laila ta dora da cewa “Na saka ki cikin maganar nan, Aunty dan ki taimaka ki isar ma Kawu, a cikin sanin da Allah ya ba shi ya taimaki rayuwar Ummulkhairi domin duk me hankali zai gane inda matsalar take.”

“Kwarai kuwa Laila”. Auntyn ta faɗa tana jijjiga kai “Duk hada laifin, Ummulkhairi tun zuwanta ya kamata ta maida gidan nan gidan su, da tuni cikin hukuncin Allah an gano matsalarta, to bata zuwa in ba Sodangi ya dauko ta ya kawo ta ba, su kuma tafi tare.” Laila ta langabe kai “Ki yi mata uzuri Aunty wadda bata da kuzarin yi ma kanta wanka ko share tsakar ɗakinta ina ta ga tunanin zuwa wani wuri? makarantar da take zuwa ita kadai take lallabawa ta je kuma Allah yasa har take fahimta.

Aunty ta ce “Shi kenan, bari in je in samu, Malam da izinin Allah matsalarki ta zo ƙarshe, Allah dai ya raba mu da sharrin makiya da mahassada.”

Laila ta ce “Amin” Auntyn ta fita.Ta ɗan jima sai ga ta ta dawo, Taso mu je wurin Malam.” Na miƙe ina neman hijab, ta dubi Laila “Har ke ma taso mu je.” Dan haka mu ukun muka rankaya bisa jagorancin Aunty. Kishingide yake akan darduma ya ɗora hannunsa kan tintin, cikin nutsuwa muka shiga bayan ya amsa Sallamar mu, muka zube daga nesa muka gaishe shi ya tashi zaune ya fuskance mu, “Na ji matsalarki, Ummulkhairi wurin Maijidda, na ce kina yin azkar din safiya da maraice kuwa, da addu’o’in da muka samu daga fiyayyen halitta, da karatun Alkur’ani?

Dan da muka je neman aurenki ana ta fadin Tahir ya yi dace da mace ta kwarai, me tarin ilmin Addini, ko da dai ko kana yi ba za su hana idan Allah yaso ya jarabceka ba.”

Da ƙyar na bude baki dan nauyin sa da nake ji na ce “Duk yadda na so yi tun zuwa na garin nan ban iyawa, sai ma in manta” kai ya gyaɗa “Allah ya shige mana gaba, Maijidda samo min ruwa a dan kofi” ta mike ta fita cikin sauri, da ta dawo addu’a ya dauki tsawon lokaci yana yi, kafin ya ce in taso in karɓa na miƙe har ina harɗewa na karbo ya ce in sha da Bismillah na koma wurin zamana na shanye ya ce “Za mu yi ta yin addu’ar nan, har tsawon sati guda, Maijidda dubo mun ganyen magaryar nan ki kuma sa a nemo min Dan Bello (babban yaronsa ne).

Ta fita cikin sauri ya ce Mu ta shi mu tafi, mu ka yi mishi godiya, ni da Aunty Laila, Albarka ya yi ta sanya mana ya ce Mu riƙe abotar mu, wadda muka ƙullata domin Allah. Mun fita Aunty ta dawo ya dube ta “Tahir ya gagara shi ne za a sabauta baiwar Allah, addu’o’in da nake ba Tahir su zan bata In sha Allah, Allah zai warware al’amarin. Aunty Kulu ta ce Amin, Malam, Allah ya kara girma.”

Isowar ɗan Bellon Aunty Kulu ta bar falon umarni ya ba shi ya tattaro mahaddata da ke karatu a makarantar Malam ɗin, za su fara saukar karatun Alkur’ani har tsawon sati guda

<< Wa Gari Ya Waya 25Wa Gari Ya Waya 27 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.