Mun yi wanka muka yi sallah, sai aka ci abinci, kwanciya kowa ya yi muka huta gajiya.Gari na wayewa na ce zan wuce, Laila na min tsiya na kosa in ga Habibina, ni kuma bata san tsoron ƙara wani laifin nake, dan na samu da daddare ya kira ni, ya ce da yaushe za mu taho, na ce da safe in sha Allah. Kwalliya nayi cikin wata kyakykyawar Abaya, nayi rolling da gyalenta, takalmina high hill ne, hannuwana sun sha zabban zinari sai agogo baƙi na fata, da na daura a tsintsiyar hannuna.
Na rabu da su Aunty Laila muka kama hanya, na cire sim din da na saya a can na mayar da ainahin sim ɗina. Ai kam kamar jira sai ga kira ya soma shigowa, dama kiran nayi gudu shi yasa tun saukar mu jiya ban canza sim din ba, na bari in dan huta, ko Tahir da ya kira a ta Daddy ya kira.
Duk kiran daga ƴan’uwana ne sai Hafsa, ni kuma na kira su Ummata da Babana da Gwoggo sai na kira Hajiyar su Tahir, Maman Ummi ta kira ni. Ajiyar zuciya me karfi na fidda da na zo nan. Agogo na kalla ganin lokaci ya yi nisa yasa ni gyara kwanciya tare da kokarin cire kowane tunani dan samun nasarar barci ya kwashe ni. Asiya ta biyo min mun je sunan friend ɗinta kamar yanda ta ce. Sa’adda ta zo Halima da Latifa sun fita sai Basma da ke ɗakinta.
Da muka dawo na bukaci ta kai ni in sayi kayan tsaraba, sai da na sayi duk abubuwan da nake buƙata sai ta sauke ni gida, bata ko shiga ba ta juya kan motarta. Lokacin tafiyar mu na ta karatowa ina ta shiri na a hankali, kafin bikin gidan su Tahir za a fara na wani abokinsa dan haka za mu tafi kafin bikin gidan nasu da sati daya. Ana gobe tafiyar na ziyarci Sallon, duk wani gyara an min, mun yi waya da Aunty Kulu ita ma za ta bikin, amma sai ana saura kwana biyu bikin za su isa.
Na riga na gama kintsa komai, hada tarin tsarabar da nayi, safiyar da za muyi tafiyar har hawaye sai da nayi dan murnar yau za ni gida, in ga iyayena da ƴan’uwana da Hafsa Aminiya ta hakika. Me kula mishi da shukoki ya aiko ya daukar min kayana, sai da na gama fidda mishi kayan sai na fito cikin kwalliya, dakin Basma da Latifa na shiga nayi musu sallama, muka kuma yi sallama da Indo me aiki.
A harabar gidan jikin motar da za mu yi tafiyar Tahir ne tsaye cikin shirin tafiya, Halima na kame cikin motar, Tahir ya dube ni “Waɗanne irin kaya ne haka kamar in kin tafi kin tafi kenan? Dan murmushi nayi “Tsarabar su ce ta Saudiyya.” Ya gyada kai, na shiga na zauna gefen Halima, ina gaishe ta tana amsawa da ƙyar, da na lura cikin fushi take sai na kama kaina, littafin du’aul mustajaba na na ciro na fara dubawa.
Tahir na sallama da maigadi da me ban ruwan fulawa Direba ya shigo, Tahir din ya shigo ƙarshe. Bismillahi mujreha wa mursaha inna rabbi lagafurun rahim. Ita bakina ya rika furtawa ya yin da motar ke sulalawa a hankali dan ficewa daga gidan.
Gudu direban ya yi cikin ikon Allah da amincewar sa muka isa lafiya. Gindin wata bishiya ya parker motar, duk da rana da tayi zafi bai hana mutanen gidan su Tahir fitowa domin tarar mu ba, nan muka bar shi da jama’a muka wuce zuwa ciki, sai sannu da zuwa ake mana yaran gidan da iyayen su, yaran na ta tsalle suna fadin oyoyo Aunty Ummulkhairi. Muna zuwa sashen Tahir Halima ta ci burki, wata daga cikin yaran gidan ta ce “Key na wurin Haj” ce ma wadda ta fada matan tayi ta je ta karbo mata. Ni dai na karasa zuwa ciki, Hajiyar na zaune kujerar da ke kusa da kofa tana fadin “lale lale, ku shigo maraba.”
Kan ka ce me dakin Haj ya cika, yaran sun zagaye ni, Faisal da ya shigo ya gaishe ni na mikawa wata jakar leda da na ruko biscuit ne da chocolate na ce ya je da su ya raba musu, waje ya yi suka bi shi nan muka samu aka shiga gaisawa da tambayar bayan rabuwa, sun dan jima cikin dakin kafin suka fice suka bar ni da Haj, tana cin farfesun kazar da nayi na taho mata da shi, Tahir ya shigo kusa da Haj ya zauna ya shiga gaishe ta ta ce “Sai yanzu ka samu kanka? Murmushi ya yi ta mika mishi ruwa, ya ce “A’a Hajiyata, abin da ke gabanki dai zan ci.”
Ta ce “Za ka fara ko? a kawo min abu daga gidanka kuma mu cinye tare.” dubana ya yi shaidar ya gane daga gare ni ya fito. Sunkuyar da kaina nayi ina ƙara hakikance wurin Haj Tahir ya gado son cin nama. Yasa hannu ya dauki naman.
“Halima fa? Ya tambaya. “Ban gan ta ba, dama hada ita? Haj ta ba shi amsa fuskarsa ce ta canza sai ya mike.” Ina kuma za ka? Bayan Umma ta shirya muku abinci” (Maman Ummi) Ya ce “Ina zuwa Haj” sai ya fice, ta bi shi da kallo. Ni ma miƙewa nayi na ce zan yi alwala, na kabbara Sallah na ji shigowar Halima, sai da ta gaida Haj sai Hajiyar ta ce mata “Ga abinci can ki jawo ki zuba” cewa tayi ta koshi sai ga Tahir ya dawo har ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya “Wa ya yi gyaran wurin mu Haj? “Ƴaƴanka ne, Rabi’ah da Sadiƙa, wani abu ne? Kai ya girgiza “A’a gyaran ya yi, sun gyara ko’ina yanda ya dace.
“To ma sha Allah” ta fada fuskarta na washewa da dariya, ganin na idar da sallah Haj ta ce “Matso ki ci abinci, kun sha hanya.” Na matsa inda Tahir yake cin abincin na zuba Halima ta dube mu sai ta mike “Haj bari in je in huta? “To, ai kun sha hanya.” Haj ta bata amsa. Suna hirar su ina sauraren su, har sai da aka aiko kiran shi a waje sai ya fice. Duk da gajiyar da nake ciki sai da nayi wa Tahir girkin dare, har kuma zuwa lokacin ban shiga bangaren namu ba, ina wurin Haj. Har sai da nayi mishi text ya zo ya ci abinci, ya min raply ina ina? Na ce “Wurin Hajiya” ya ce “A’a in ɗauki abincin in koma wurin mu.”
Magiya na tura mishi ya bar ni wurin Haj” Jin shiru ba amsa yasa na gane na fusata ƴan mazan, dan haka sai nayi wa Haj sallama na dau abincin, shigata jin muryar Halima da ke cikin kitchen tana waya ya sa ni saurarawa “To wai ta ma isa? Wallahi nake gaya miki tun isowar mu Part din ma bata leƙo ba, tana dakin uwarsa, ni yarinya ta isa ne, ita ma ta san ba wasa, wanda ya dauko ta ma a hannuna yake ballantana ita karan kada miya.”
Shiru ta ɗan yi kafin ta ɗora “Ai ta ma zo, da kafarta za ta bar part din, ai har mu bar garin, nan ɗin ya fi karfinta.” Dan tsaki na ja na wuce dakin Tahir inda na fara zama farkon kawo ni, dan in ba nan ɗin ba in dai ba na Basma zan shiga ba to ina zan zauna Halima ta shiga nata dakin dole dai a na shi zan yi masauki. Na yaba da gyaran da wurin ya samu, wanka na wuce na yi, na gyara jikina sosai ina fitar da daddaɗan ƙamshi, wasu riga da wando na ɗauko baƙaƙe, masu taushi, rigar me hannun vest, sun lafe a fatar jikina ban sa hula ba kitson da aka yi min two step sun sauko kan kafaɗata, ina kallon kaina a madubi Ina sakin tsaki, Halima za ta gane shiru shiru ba fa tsoro bane gudun magana ne, ni ko ita za a ga wanda zai kori wani anan ɗin.
Jin motsi yasa ni juyawa, Tahir ne Sannu da shigowa nayi mishi ya ce “Ki fito ki bani abinci.” na bi bayansa zuwa falon, Halima na zaune gani na na ga tayi wani shock, nayi dariya a raina. Mu zuba mu gani. Inda na ajiye abincin can bayan kujera inda na san ba lallai Halima ta gani ba na isa na janyo trey na kawo gabansa, na zuba mishi yana fara ci na saka hannu.
Ya dubi Halima.”Ki zo ki ci mana”. Kai ta girgiza dan kadan take jira ta fashe na miƙe zuwa kitchen na wuce ina kaɗa abin zama.
Haka na tsiri zirga zirga har ya kammala cin abincin, ina kwashe kwanonin zuwa kitchen na shige dakinsa na hau gado.Kallonsa tayi da fuskarta ba annuri, “Ita wannan ya za a yi ta shiga dakinka? Ba tare da ya dube ta ba ya ce “To ya kike so? tana da ɗaki anan ne idan bata shiga nawa ba.”
Shiru tayi zuciyarta na harbawa, ganin ya mike ya shiga dakin na shi yasa ta cikin ruɗani, bata samu ba sai da ta ga ya fito ya shiga dakinta. Barci na nayi cikin kwanciyar hankali, ƙarfe huɗu na tashi na fuskanci Ubangijina, sai da na yi Sallar asuba na koma na kwanta Tahir ya leƙo ya ga na tashi ya samu ina karatun Alkur’ani.
Barci nayi zuwa bakwai da rabi na tashi na shiga kitchen, ina aikina ina sauraren Radio da na kunna, hango Maman Ummi da na yi za ta gifta na sauke Glass din window na kirata ta dawo muka gaisa, ta ce “Ke ba ki ji gajiyar tafiya ba har kin tashi? Na ce “Haba gajiya ai tabi lafiya” Haɓa ta riƙe “Da wannan dressing din kike zama sai ka ce daga ke sai mijinki? Kallon jikina nayi ina wata yar dariya.
“Kin ji ki, me ya dame ni da wata? Ita ma tayi mana.” Wata muguwar dariya ta saki “Ai kam da an sha kallo, sunan wani abu kindirmo.” ta wuce tana cigaba da dariya. Na cigaba da aikina har na kammala Halima bata fito ba, Maman Ummi na kira a waya na ce ta turo min Faisal shi na ba abin karyawa ya kai inda yayyun Tahir ke zama su karya kowa ya kawo na wurin sa. Na ɗora dogon hijab zuwa sashen Haj, ni na gyara mata ɗakinta na sa mata ƙamshi, tana karyawa da abin karin da na kawo mata na fita na koma wurin mu, ɗan turus nayi da shigata, ganin Tahir suna karyawa da matarsa, na ji abun amma sai na kanne, yaye hijab din nayi na ajiye saman kujera riga da wandona tun na daren jiya ne jikina, na karasa wurin su na gaida Halima zan wuce ciki ya ce,
“Ya za ki wuce ba ki karya ba? Ni ma na fito ban gan ki ba sai abincinki na kasa jiran ki zo ki bamu abincin, dan fita zan yi”. Na ce “Wanka zan yi” ya ce “A’a zo ki karya.” na zauna muka karya, sai na shige, ban yi wankan ba kayan tsaraba na fitar ina warewa, mazan gidan yadi ne da darduma, matan Atamfa da darduma da doguwar riga, sai yaran kowane daki na ba mutum biyu, sannan na ciro sabulai da omo na hada musu da shi.
Na haɗa gumi Tahir ya shigo ya yi wanka zai dauki kayan da zai sa, ya dube ni “Sannu da aiki” nayi murmushi ya ce Katsina za su wuce daurin auren abokin nasa, anjima in shiga wurin mahaifiyar abokin nasa in yi mata Allah yasa alheri” na ce
“To” tare da yi mishi addu’ar Allah ya tsare hanya. Sai da na gama ware na kowa har na Haj sai na kira Rabi’ah da Sadiƙa suka yi ta mikawa jama’ar gidan. Girkin rana na daura ƴanmatan gidan na taya ni sai na shiga wanka, kwalliya nayi cikin wasu riga da Skirt na Atamfa da suka kama ni dam, yaran na ba umarni suka raba bayan na ɗibi na Ogan,
Suka bi sashe sashe suka miƙa wa kowa, wadataccen mayafi na rufe jikina na fito zuwa dakin Maman Ummi dan kai mata hira, matan gidan da basu shigo yi min godiya ba sai godiyar suke. Da shigata na faɗa kan kujerar ta, na yaye mayafin daga inda take zaune take kallona, “Amma dai matar nan ba karamar muguwa ba ce.”
Duban ta nayi “Me nayi? Irin wannan matsu ai sai ki sa matar can hawan jini.” ido na kaɗa “Wai ke shi kenan sai in ƙi kwalliya, dan wata? Ita ma sai in bata so ba.” “A’a ki bari dan Allah, kina ga mata kamar a kife ta da kwando, ga wata irin kiba da ta ƙara narkawa, ko fa wuya bata da shi.” Wani kallo nayi mata “Allah dai na jin ki, haka kuma yaso ganinta.”
Saurin kama bakinta tayi “Astagfirullah, Allah haushi take bani, baƙin hali ne da matar nan, ai jiya ta ga ranar baƙin hali, takaici ya kusa kashe ta da ta ga ba wanda ya bi ta kanta, kowa Ummulkhairi.” Dan mu kauda hirar Halima na ce. “Ina danbuna? Dan na gaya maki ki yi min” Umminta ta kira ta ce ta ɗauko min ina ci muna hira, anan muka yi Sallar Azahar sai muka nufi dakin Haj, nan ma hirar muka yi kafin muka fito zuwa gidan bikin, shi ma makota suke da gidan su Tahir muka shiga dakin mahaifiyar Angon muka zauna aka fadi mata matar Tahir ce, ta ce
“Kai wadda ta zauna nan ban gane ta ba”. Hayaniya gidan ya kara ɗauka ana fadin yan daurin aure sun dawo. Mun dan ƙara zama muka yi mata sallama muka fito Tahir na hango tsaye jikin motarsa yaro ya aiko in zo sai na nufi wurin sa kallona yake har na kai inda yake hannuna na sa na rufe fuskata malum malum ya ciro cikin mota “Wuce min da ita” na karba ina faɗin “Hada malum malum sai ka ce shi ne Angon”. Iyee me kika ce?
Ya fadi da sauri noƙe kai nayi ina murmushi “Abokina ne ummulkhairi, ina me tabbatar miki tare aka goya mu, an sanya mu makaranta tare halin rayuwa ya raba mu kowa ya yi inda ya yi” na ce “Allah Sarki, Allah ya sanya Alheri, shi sai yanzu ya yi aure” Mun ɗan jima sai da wasu suka zo wurin sa sai na wuce, wurin mu na wuce ajiye rigar, ban ga Halima ba kila ta tafi gidan su. Maman Ummi ce suka shigo da matar babban yaya maman Saddiƙa, ta ce “, Ummulkhairi har kun dawo daga gidan bikin ? Na ce “E” ta ce “Ai Sodangi ba ƙaramin burgeni ya yi ba abin da ya yi ya bani sha’awa” na ce “Me kenan?
Ta ce wannan abokin na shi me aure yau, tare aka ce an goya su, har suka girma sai Allah ya jarabci shi abokin da shaye shaye, bai ma cika zama nan ba idan ya ɓalle ya shiga duniya sai a daɗe ba a ji duriyarsa ba, to yanzu ya ɗan nutsu shi ne ya dauko Aure, Tahir duk yanda ya zama bai kyama ce shi ba ya zo takanas dan halartar ɗaurin auren sa, shi aka ce ma ya dauko Amaryar” nayi murmushi ina faɗin “Ni ma gaskiya ya burgeni.
Ku fa masu karatu ya burge ku?