Cikin yan mintuna muka sauka birnin na ikko. Da motar gidan Kawu Attahiru aka zo ɗaukar mu. Mun samu kyakkyawar tarba wurin Aunty Kulu, sai da Tahir ya taso daga aiki sai ga shi shi ɗin kuma ya kwashe mu zuwa gidan su Laila, inda muka samu biki ya kankama kasaitaccen biki ake yi wanda aka ce tun saura sati guda aka fara, mun samu Aunty Laila tayi mana duk ankon da aka yi na bikin, ni dai dadin bikin rabi da rabi nake jinsa saboda cikin jikina. Sai da aka wuce da Amarya muka yi wa Momin Laila sallama, muka koma gidan Kawu Attahiru, da niyyar washegari za mu koma Kaduna.
Dan Laila sun tafi Katsina raka Amarya ɗakinta. Sai dai me washegari muna cikin kintsawa sai ga text din Tahir ba fa yau za mu koma ba na ajiye wayar ina fadawa Hadiza abin da kenan, ita kuma ta fita gayawa Aunty Kulu. Lokacin tashin Tahir daga aiki sai ga shi bai shigo ba ta waya ya kira ni ina fita ya nuna min gefensa na shiga umarnin rufe motar ya bani sai ya yi mata key ribas ya yi ya bar layin, sai da muka dan yi nisa ya ce “Ke yanzu saboda Allah idan aka bar ki sai ki koma ba ki gana da mijinki ba?
Shiru nayi ban yi magana ba daidai yana shiga wani wurin shakatawa da zaman mu tambaya ta ya yi me za ki ci na ce ban jin yunwa. Mun jima sosai a wurin sai dare ya mayar da ni wanda sanɗa nayi tayi kar Aunty Kulu ta gan ni har na samu shigewa dakin da aka yi mana masauki.
Latifa ke kai kawo a dakinta, rashin dawowar Ummu ya tsaya mata, bata kuma san wanda za ta tuntuba dan jin yanda ake ciki, haɗa su ya yi su biyu da Halima ko ya abin yake? da tayi yunkurin kiran Halima sai ta rasa kwarin gwiwa, dan rashin mutuncin da ta ragargaza mata da aka sake ta, har kuma ta tafi ba wani shiri tsakanin su.
Wani tunanin tayi yasa ta suro wayarta ta kira ya yi biyar bata daga ba, kamar ta hakura sai dai ta kuma kira cikin sa’a ta daga, “Ya aka yi? Halima ta ce daga dagawarta, gaba ɗaya sai ta so daburcewa ta rasa ta ina za ta fara. Cikin karfin hali ta ce “Ina ta kira ba ki daga ba? Wata yatsina Halima tayi kafin ta ce “Ina tare da mijina time ɗin yaushe zan ji wani kiran waya? Wani malolon kishi Latifa ta haɗiya kafin ta sa dauriya me yawa wurin cewa.
“Ashe kuna tare ita wannan bakar dagar ta bar ki da shi? Ni na sha zuwan ta za ta dauke mishi hankali.” Wa kenan? Halima tayi saurin tambaya. Mutuniyarki Ummulkhairi, sai anjima fita zan yi” Latifa tayi saurin kare maganar kuma ta kashe wayarta. Wata zufa Halima ta ji tana tsatstsafo mata Ummulkhairi na garin nan?
To har yaushe ko da Tahir bai shiga sabgarta akalla da ya tashi aiki zai yo gida amma yan kwanakin nan baya shigowa har sai tayi barci dole ta dauki wayarta ta kira Latifa dan san jin karin bayani sai da ta ja mata aji sannan ta gaya mata. Halima ta ce, “Bai kawo ta nan ba” sun dade suna magana kafin suka ajiye waya Halima ta nemi yar nutsuwar da take ciki ta rasa, da da ne tarar sa za tayi a yi ta ta kare dan ba za ta yarda yana barin ta yana fita wurin waccan shegiyar yarinyar da ta tsana.
Haka ta ci gaba da kasancewa kullun Tahir ya tashi wurin aiki zai zo ya fita da ni, mu zaga gari, har shagon mu na ɗinki mun je na ga ci gaban da wurin ya samu duk da cewa na Kadunan ma da Tahir ya nema mana tuni an fara aiki. Har sai ana gobe zai koma Kaduna ya samu a jirgi muka koma.
Washegari kuma suka zo shi da Halima. Kowa ya san tafiyar nan tawa ce duk da a raina ba san tafiyar nake ba, dalilin cikin jikina da ya yi matukar yi min nauyi, amma sai ya ce Latifa ta shirya, ban nuna komai a fuskata ba na hadiye na bar ma raina. Sai shiri su Latifa ake yi cikin wani farin ciki na ta gaza boyewa. kwanan sa daya aka shigo da wasu galla gallan motoci na zamani guda biyu, ya damka makullansu ga Halima da Basma, nan ma kallo nayi da idona nayi musu murna.
Latifa sai murna ta koma ciki yi tayi kamar za ta kama da wuta kan masu aiki ta sauke ɓacin ran ta, daga ba hali ta ce wa Ogan dan me? Ranar da ya zo Basma ce ta karbi bakuncinsa sai ni da zan karba yau, sai la’asar na shiga dakinsa na gyara, sai na fada kitchen muna tare da Hadiza ba ƙaramin taimako take min ba. Cake nayi a lokacin, sai na dama kunun gyada na shirya su a madaidaicin tray na ɗauka Tahir zan kai wa dan bai wani ci abincin kirki ba da rana, kamar ma dai yana da damuwa dan walwala tayi karanci a fuskarsa, shiyasa nayi tunanin sa ma mishi dan abin taɓawa kafin dare.
Wata doguwar rigar material na sa, daga kirji ta kama ni sai daga kasa a ka buɗe ta, wani karamin bakin gyale na yane kaina da shi, na fito ina taku irin namu na masu ciki. Na shige Latifa da Basma da na samu zaune ta kofar baya, na bi wurin motsa jikin Tahir na nufa wani karfe yake ɗagawa ya yi gumi kashirban, na dan tsaya ina ƙare mishi kallo har ya fuskanci da mutum a wurin.
Waiwaye na ga ya shiga yi har ya gan ni daga inda nake tsaye, sai da ya kare min kallo ya yafito ni, karasawa nayi inda yake wasu fararen kujeru da ke wurin ya isa ya zauna kan wata ta zaman mutum biyu kusa da shi ya buga da hannunsa, sai na zauna gefensa. Ruwa ya fara dauka ya sha ya ajiye gorar, sai na miƙa masa Cake, ci ya yi sosai sai na ba shi kunun gaba ɗaya ya shanye murmushi nayi sai na tattara kayan sai na miƙe, na soma tafiya na ji shi bayana, har ya zo ya wuce ni wurin motar da ya zo cikin ta ya isa ya bude Boot kayan da ke ciki ya shiga cirowa maigadi ya ƙwala wa kira, ya iso cikin sauri, zan shige su in shiga ciki ya kira ni, na karasa wurin su. “Kayan haihuwa na saya Ummulkhairi” ya fadi yana kallona murmushi nayi sai nayi mishi godiya.
“Maigadi zai kwashe sai ki kira Hadiza ta kwashe.” Na daga mishi kai. Cikin na wuce na shaida wa Hadiza ta fita cikin sauri, da na shiga daki ta sa kayan nayi ina ta kallo suna da matukar yawa, kyau, da tsada, a dayan ɗakina muka adana su. Sai da Tahir suka wuce da Latifa Kawu Attahiru wanda shi ma ya shigo garin ya aiko aka kira ni.
Ina tsugunne gaban sa magana yake min, “Ni na hana Tahir tafiya da ke a wannan karon, Ummulkhairi. Duk da mamakin kalamansa da na ji ban ko motsa ba. “Duk da shi ma bai so hukuncin nawa ba, ki zauna anan, ki ci gaba da rainon abin da Allah ya ba ki har Allah ya sauke ki lafiya. Kina amfani da sakon da ake kawo miki ko? Na ce “E”. “To ki ci gaba, Allah ya raba ku lafiya, ya bamu masu albarka.”
A zuciyata na fadi Amin a baki kuma na ce “Na gode”. Cikin matsananciyar kunyarsa da nake ji. Na cicciɓa na miƙe sai shi min Albarka yake, sai da nayi wa haj Hajara sallama sai na baro gidan. Wannan karon Tahir bai samu shigowa ba Latifa ita kadai ta dawo, tana dawowa kuma Basma ta tafi. Tafiye tafiye yake tayi, ya dai je kankara duba Haj da ta yi fama da zazzabi, ko Hadiza ta so tafiya duba mahaifiyar tasu, amma Tahir din ya hana ya ce sai ya zo su tafi gaba ɗaya, dan akwai biki a gidan su na yaran yayyensa su uku mata biyu Namiji ɗaya, da Latifa wadda bata taɓa zuwa garin ba ya ce za a yi tafiyar, sai Basma, wadda ta gwada mishi bata son zuwa ya yi fushi duk da dawowar da tayi ta ce za ta je ganin yana fushi da ita, ya ce A’a. Ni dai har yanzu haihuwa shiru tuni watan haihuwar ya wuce Dr Muhammad ke karfafa ni da ba wata damuwa lafiya ƙalau ba wata matsala.
To ya zan yi na zuba ma sarautar Allah ido ina dai ta addu’a in samu mu rabu lafiya. Saura sati guda ya rage tafiyar su, da rana na ji duk na rasa me ke min daɗi, sai kawai na hau gado ba dan in yi barci ba, shiru kawai nayi idona rufe. Kukan wayata yasa ni miƙa hannu na dauko ta, sunan Yayata Habiba na gani na ɗauka ina gaishe ta, sai na ji tana fadin “Ummulkhairi idan kin samu hali ki taho gida Babanmu ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ne ya buge shi yana Asibiti bai san wanda ke kansa ba.
Kuka kawai na saka na kashe wayar, na lalubo lambar Tahir, ina kuka nake gaya mishi halin da Babana yake ciki. Kwantar min da hankali ya shiga yi ya ce zai shigo gobe mu tafi. Na ajiye wayar na ci gaba da kuka na, Hadiza ta shigo tana tambayar abin da ya same ni, sama sama na fada mata, zama tayi tana ta bani baki.
Haka muka ƙarasa wunin ranar, Hadiza dai tana ta aikin rarrashina, Tahir ma motsi kaɗan zai kira ni, ni dai na kasa kwantar da hankalin da suke so in yi, dan gani nake kamar mutuwa ya yi aka boye min musamman da na kira Ummata bata daga ba, tsoron kiran wani na ji sai kawai nayi ta addu’a.
Gari na wayewa ya fara min waya mu kasance cikin shiri dan da ya zo ba zai tsaya ba za mu wuce. Har kayan haihuwa na diba dan bamu san abin da Allah zai yi ba. Falo na dawo na zauna Abaya ce sanye jikina sai gyalenta na rufe kaina, “Ina masu tafiyar ku fito” Muryarsa da na ji a kaina ta sa ni daga kai na soma gaishe shi, sauran matan ma da ɗaiɗai suka riƙa fitowa suka yi mishi barka da zuwa.
“Ku zo mu je ina Hadiza? Ya fadi yana duba na, Hadiza ta fito tana janye da trolly ta soma gaishe shi ya juya ni dai mikewa kawai nayi na fito ina yamutsa fuska dan marata da na ji tana tsungula min. Direban da zai ja motar ya taimaka wa Hadiza saka kayan mu cikin Boot, ganin yanda nake yi Tahir ya ce yaya dai na ce ba komai. Ni da Hadiza ne a baya, sai shi da direba a gaba, wata irin tafiya nayi me matuƙar wahala muna isa kuma Asibitin muka zarce inda na samu duk yan gidan mu a can Ummata dai faɗa ta rufe ni da shi da ban yi hakuri ba na taho da wannan tsohon cikin.
Kuka na kama mata mutanen cikin dakin suna cewa tayi hakuri ta daina min faɗa ta bar ni in ji da halin da nake ciki, Tahir dai na tsaye bai ko yi tari ba ya ɗan jima kafin ya yi musu sallama kuɗaɗe masu kauri ya ajiye ya juya ya bar dakin, sai da aka yi min magana na tashi na bi bayan sa dan har Hadiza ma ta fita, ina fita na gan shi tsaye hararata ya yi “Wai wa ya shagwaba ki ne yarinyar nan komai ki buɗe baki ki kama wa mutane kuka?
Baki na tura ban yi magana ba, “Ki zauna mu ga abin da Allah zai yi, idan na shigo daurin aure sai mu koma tare, zan tafi da Hadiza in kai ta wurin Haj yau zan koma Kaduna”
Ajiyar zuciya nayi na ce “Allah ya tsare” “Zo ki raka ni, ko ba za ki iya ba? Na girgiza kai sai na fara tafiya, biyewa tafiyata ya yi muka jera har inda motar take nayi ma Hadiza sallama na ce ta gaida min Haj. Sai da motar tasu ta bar wurin na kama hanyar komawa ina takawa a hankali.
Kwana na hudu aka sallamo Babanmu wanda Alhamdulillahi ya samu sauƙi, har yana ce min me yasa na zo sai ga yan kankara mota guda sun zo duba Babana, hada Hajiyar su Tahir Hadiza dai da muka yi waya ta ce rashin wuri ya hana ta biyo su, na ji dadi sosai da karar da suka yi min, nayi ta godiya.
Washegari da hantsi na lallaɓa nayi wanka da ruwan da Ummana ta kai min, nayi kwalliya sama sama na sa doguwar riga ta Atamfa ɗinkin Babba ne, ban daura dankwali ba, kaina calaba ce tun da na zo daurewa kawai nake dan fama nake da ciwon baya musamman cikin dare, sai gari ya waye in tashi garau. Bakin gado na koma na zauna gwoggo ta leƙo “Ummu har an yi wankan? Ina murmushi na ce “E Gwoggo” ita ma murmushin tayi “Daki ya dauki ƙamshin turaren wuta kamar har an soma Jegon, Allah dai ya raba lafiya.” A zuciyata na ce Amin.”
Sannunku da zuwa da ake ta fadi a tsakar gida yasa Gwoggo lekawa. “Ke Ummu ga mijinki nan hada wata kila cikin kishiyoyin ki ne.” Na ce “To” ina gwalo ido gwoggo ta kauce ita ma ta shiga fadin Maraban ku. Tahir ne gaba sai Latifa na biye da shi, ni ma sannu da zuwan na shiga yi musu da shigowar su, na ce wa Latifa “Zauna” ta zauna sai Tahir da ya tako inda nake kamar zai zauna, ko tuna gadon Ummana ne ya yi sai na ga ya fasa, kaina ya tsaya “Ya jikin? Na ce “Alhamdulillahi.
Magana muka yi tayi yana gaya min lokacin komawata asibiti ya yi Dr Muhammad ya kira shi ga shi bana nan. jin motsin za a shigo yasa shi kaucewa ya zauna kujera yana kallona “Cikin nan ya miki girma da yawa muna komawa ba zan koma Lagos ba zan kai ki wurin Dr ya duba min ko akwai abin da zai miki. Murmushi nayi “Lokaci ne, yana yi zan haihu.”
Ummata ta ƙwala min kira na tashi na fita yana bi na da kallo abincin da ta shirya dan shi, ta bani in kawo mishi da kaina na zuba mishi zan zuba wa Latifa da ke ta wani yamutsa ta ce ta koshi na ce to ta zo mu je ta gaida Babanmu, muka dawo muka samu Tahir ya yi nisa da cin abincin.”
Ba na iya wuce tayin abincin Umma, Ummulkhairi, dan ita ɗin gwana ce wurin yinsa yasa mutum har ya ji kunnensa na motsi” murmushin zancen sa nayi Latifa kuma ta ƙara tamke fuska sai da ya gama ya ce “Tare da ke za mu wuce ƙanƙara Ummulkhairi.”
Na dan jinjina abin sai na ce mishi “To” dan wallahi zuwa na gida ba ƙaramin daɗi nake ji ba kowa kaunarsa yake gwada min da tausayi. Mun yi sallama da yan gidan mu muka dauko hanya sai tunani nake a raina ita kuma ko ya zaman mu zai kasance da ita? Daga ita ba ɗaki ni ba ɗaki a Ƙanƙara.