Skip to content
Part 46 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ban tashi ba sai Azahar. A daddafe nayi sallah tea na ce Hadiza ta hada min dan sai na ji ina sha’awar shan shi. Ikon Allah kuma da na sha ban yi aman ba. Zuwan Asiya da yamma take tsokalata me juna biyu, nan na fahimci ciwona ciki ne, hawaye na kama yi har na ruda Asiyar, tana fadin “To meye abin kuka? kyauta ta Allah, yaranki lafiyayyu, dabo fa suke yi. A haka Tahir ya zo ya same mu, gane dalilin kukana sai ya sha mur, bai ce komai ba.

Ko da Asiya ta tafi kwanciya kawai nayi kan fillow ina ci gaba da zubar da hawaye. “Tashi zaune.” na ji muryarsa ba tare da na san sanda ya shigo ba, kallon sa nayi ganin ba wasa sai na tashin ina goge hawayen da dankwalina. Ya tokare hannuwansa a kirji kamar yanda na fahimci ya fi yi idan ransa na bace “Cikin ne ba ki so? Na ji ya tambaye ni ban tanka ba sai ya kara maimaitawa nan ma ko motsi ban ba “Good” ya fadi sai ya juya ya bar min dakin.

Tun daga ranar fushi yake da ni, baya min magana zai dai shigo ya tabbatar na ci abinci na sha magani dan tun waccan ranar ban kara amai ba, Dr Muhammad ya fadi yanda za a kula da lafiyar twince da abinda za a rika ba su, zan kuma ci gaba da shayar da su. Ni ma din bana mishi magana, dan haushin shi ma nake ji ina ganin shi ya ja min. Ko da girkina ya zo ban leko ko kofa ba ballantana in yi wani girki ko gyara mishi wuri.

Da daddare nayi wanka na bule jikina da kamshi, wasu riga da skirt na sa yan uban su, cikin kayan da muka sawo a Saudiyya ni da Laila, na kama gashina da ribbon na dubi kaina a madubi ni kaina na gane nayi kyau kayan sun yi min cif a jiki komai ya fito.

Flask na dauka zuwa kitchen ruwan zafi zan dafa, dan yanzu ba abin da nake so irin tea, in hada da cake. Tun da na hango su a dinning Tahir da matansa, sai na tabe baki wuce su nayi kamar ban gan su ba, ruwan na dora na sa kayan kamshi sai da ya tafasa sai na tace na juye a flask dina sai na fito yanzu ma ban ko gwada na san suna wurin ba.

Su Hadiza na samu su na kallo da Daada da Hussaina. sai nima na zauna, kiran Kamal da ya shigo wayar Hadiza yasa ta mikewa zuwa ciki, mun jima kafin Daada ta suri Areef, ta tada Hussaina da ta soma barci suka shige, ni ma mikewar nayi na kashe kayan kallon na wuce daki Mimi na ta barcinta, bathroom na soma shiga kafin na fito na sauya kayan jikina na haye gadon ina karanto addu’o’in kwanciya.

Hadiza da ke waya har lokacin ta dube ni kamar tayi magana sai kuma na ga ta ci gaba da wayarta, sama sama na ji ta kare wayar, sai ta rage hasken firilar dakin, tawa wayar aka soma kira ina dubawa ogan ne zan sanya ta a silent sakon sa ya shigo “Ki zo dakina za mu yi magana.”

Ajiiye ta kawai nayi a fatan da nake barci ya dauke ni na ji shigowar wani sakon, saurin bude idona nayi na dubi sashin da Hadiza take kwance duk da hasken da ke dakin ba me yawa bane ba zan iya gane halin da take ciki ba, ba ni da zabi sai na mike ina kara jinjina rashin kunyar namiji yana sane tare muke da Hadiza baya jin kunyar ta gane abin da kenan. Ban tsaya daukar Mimi ba na bar dakin da shiga ta zaune na same shi gefen gado rike da wayarsa can kuryar gadon na haye na juya baya.

*****

Washegari ina zaune a daki ni kadai ce, Hadiza ta je makaranta Daada sun shiga gidan Kawu Attahiru ita da yan biyu. Wayata na ji tana ruri na kai hannu na dauka Aunty Kulu ce kan layi murmushi na soma yi mun gaisa cikin raha tana tambayar me gidanta da kishiyarta, na ce suna gidan Kawu sai na ji ta soma ce min, “Me kenan ko meye sunan abin da kike yi wa mijinki? Hauka kike Allah ya yi miki kyauta irin wannan ki butulce? Mu ba ki ga neman ta muke ido rufe Allah bai bamu ba, sai ke Allah ya ba ki ya zabe ki cikin abokan zaman ki, yanzu kina ga murna za su yi da wannan rabon da Allah ya kuma ba ki, sai kuma ki ki wa mijinki dadin kai har ya kai ga kai kararki kina fushi da shi, to wallahi yana dawowa ki ba shi hakuri, kuma ku koma muamalarku kamar da. Ki gode wa Allah wannan cikin wata baiwa ce Ubangiji ya yi miki da bai yi wa bayinsa da yawa ba.

Jin tayi shiru na ce “Zan ba shi hakuri Aunty, kuma na bari ki yi hakuri ke ma Aunty dan Allah.” Ta ce. “Na gode, Ummulkhairi ki gaida yaran.” Da Tahir ya dawo na ba shi hakuri na sa ma raina dangana da cikin.

Halima da ke dakinta zaune, waya suke da Haj Shema’u kan inda za su hadu. Ta wayar ta kira Latifa, a motar Halima suka tafi wani dan kauye ne can idan an fita cikin Kaduna.

Sun karanta wa mutumin wanda ba musulmi ba ne bukatar su, ya ce bukatar su ta biya sun kawo kukan su inda za a share musu hawaye. Ya basu abinda zai basu kan cewa su zuba ida kishiyoyin nasu za su taka tare da bukatar su ga abin da suke so ya faru da su, sai kuma ka tabbatar wadda ka karba da sunanta ita ta taka idan aka samu akasin haka to kaikayi fa zai koma kan mashekiya.

Kowacce guda daya ya bata tare da cajin su makudan kudade. Sun taho cike da murna Halima ta amshi na Ummulkhairi Latifa da bata so Halima ta riga ta ba cikin rashin jin dadi ta amshi na Basma. Sun taho bisa hanya suka ba Haj Shema’u abin da suka yi za ta ba su idan ta raka su, a hanya ta sauka ta ce musu da inda za ta suna bace ma ganinta ta ciro wayarta mutumin ta kira ta ce acc no za ta turo ko ko dawowa za tayi ta karbi kash kamar yanda suka shirya?

Wata dariya ya kece da ita ya ce shi magani na gaske ya basu bai basu fake ba kamar yanda suka shirya. Hannu ta dora a ka ta ce “Me zai sa ka min haka? Cikin kishiyoyin nasu akwai wadda ban so a zalunta, yanzu ya kake so in yi? Ya ce “Wannan kuma ruwanki, abin da dai na sani ba zan kashe wa kaina kasuwa ba, ina so gobe su dawo har ma su kawo min wasu. Wayar ta sauke cikin matukar da na sani drop ta dauka zuwa gidan nasu za ta je ta fada wa Ummulkhairi, dan ba za ta bari a cutar da wannan yarinya da Allah yasa mata kaunarta take jin ta kamar yar’uwar ta ta jini.

Sai dai tana isa daga bakin gate take tambayar gate man ya ce “Maman yan biyu? dan turus tayi “Da ma ta haihu? Ya ce “Kwarai kuwa, yan biyu ta haifa mace da namiji, amma yau din nan suka tashi ita da jama’ar wurinta zuwa Katsina” Dafe kai tayi tashin hankalinta ya karu “Ba zan samu lambar wayarta ba dan Allah ? Girgiza kai ya yi “A’a fa ni dai babu, sai dai in tambaya miki masu gidan.”

Ta ce “A’a” ya ce “To bari in bambaya miki su Indo da laraba masu aiki” Laraba da ya gani tana shanya ya fara tambaya ta ce “Ni kam ina da ita amma wayata na wurin gyara, Laraba ma kuwa bata da wayar.” ya juyo wurin Haj Shema’u ya kora mata yanda suka yi, ta kara tambayar sa ko ya san sanda za ta dawo? Ya ce “A’a ” juyawa tayi cikin wani da na sani da ya kara rufe ta.

Mun sauka Katsina lafiya. Daada kuma muka kai ta har gida. Yayana Sani na je ma bakunta, zuwana kuma na farko kenan gidan sa tun da nayi aure. Matsa ma Tahir lamba nayi rokon safe daban magiyar dare daban, har Allah ya taimake ni ya bar ni. Kwanaki biyar nayi na isa Dutsinma nayi biyu, muka sha sunan kanwata Hauwau da ta haihu, sannan muka biya muka dauki Daada muka koma.

Latifa da ke tsaye gindin windon ta ganin motar da ta tsaya da mutanen da ke fitowa ciki dadi ya kamata, yau za ta cika aikinta, dan ita ko da ta amsa da sunan Basma a niyyarta kamar yadda ya ce da niyyar Halima ta amsa kuma ita take nufin sanya mawa, ta ce wa Halima ba za ta sanya wa Basman ba sai Ummulkhairi ta dawo. Dan guntun tsaki ta ja.

“In sa wa waccan shashashar a dauri kashi ko a bata igiya, ita da ma da ita da babu ai kusan daya ne. Za ta fara ta kan Halima kafin idan maganin ya yi ta koma ta amso wanda za ta sa wa Ummulkhairi, Fitowa tayi ta tare mu da fara’arta tayi mana Sannu, abin da ya yi matukar bani mamaki, ba ma ni ba har su Hadiza na san sun ji mamaki. Muna shigewa ta fada dakin Halima albishir tayi mata da dawowar su Ummulkhairi tare da fada mata ita fa yau za ta sanya na ta dan haka ita ma sai tayi kokarin sanya nata.

Dan shiru Halima tayi ni wallahi sai da na dauki sanya wa yarinyar nan na gane na ta ya fi wuya, sashen ta da mutane da yawa” yar dariya Latifa tayi “Ba wata wuya in kin sa kanki, tana karbar girki da ta shiga yi mishi gyara yi kokari ki sa, dan kin ga sannan ma baya nan sai ki ga ta fito ta taka.

Halima ta gyada kai cike da gamsuwa Latifa ta mike ta koma dakinta kafin ta wuce kuma sai da ta tsaya ta barbada abin a kofar Halima wanda yake fari tas kamar madara sai ka sa ido za ka fahimci da wani abu. Tana zama ta kira Halima “To ki yi kokari ki fito dan na aiki su Indo kasuwa Mutanen wurinta kuma na ga sun fita, ita kuma ta shiga kitchen in kin samu sa’a sai ki zuba mata kawai a wuce wurin.”

Ciccibawa tayi ta dauko abin inda ta ajiye sai ta fito sai dai tana taka kafarta a kofar dakinta kanta ta ji ya sara ta maza tayi sai dai ta kasa daurewa ta tafi dakinta ta koma ta hau gado ta rasa abin da ke mata dadi. Bata kara samun damar fitowa ba. Tahir ma da bai ga ta fito ba dakin ya bi ta sai dai ce mishi tayi bata jin fitowar ne kawai. Abinci ma har daki su Laraba suka kawo mata, duk yadda ta so ta ci kasawa tayi, barci ranar tayi shi ne amma ba mai dadi ba, farkawar da za tayi da asuba gabanta ya yanke ya fadi dan sabon al’amari a gaban ta, zanenta ta kai hannu ta yaye abin da ta gani ya sa ta kurma ihu!

Gaba daya gabanta ya zazzago birgima ta shiga yi tana kuka har falo, nan take gidan ya hadu kanta dan duk wanda ke ciki ya ji ihunta, temako Tahir ya nema wurin sa ta a mota zuwa Asibiti shi da mutumin da gidansa ke jikin na mu, sai ni da Daada muka zauna a baya tare da ita, an karbe ta a Asibitin an bata gado ko awa bata yi ba ta soma jijjiga likitoci suka rufu kanta, sun nemi sa hannun Tahir dan shiga da ita dakin tiyata an ciro yaro namiji wanda aka sa a kwalba dan bai isa haihuwa ba. Yan’uwan ta da na Tahir suna ta sintirin zuwa duba ta, mutum uku ke jinyarta mahaifiyarta sai kanwar ta da ke zaune gidan su saboda rasuwar mijinta, sai kuma karamar kanwar ta budurwa.

Ranar da ta fara tashi zaune kai ta hada da gwiwa tana ta kuka, yan dubiya kowa sai bata hakuri ake amma yin shirun ta ya gagara. Latifa dai ganin magani ya ci Halima yasa ta shiri ta koma dan karbo wanda za ta sa wa Ummulkhairi, sai dai bata yarda ta karbo wanda wani ciwo zai samu Ummulkhairin ba dan yanda ta ga ta kasance da Halima duk da abinda ya same ta Tahir bai tura ta gida ba, sai ma dawainiya da yake tayi da ita.

Dan haka wanda za ayi wa Ummulkhairi saki uku ta karbo yanda za ta kara gaba kowa ma ya huta. Ya kuma ba ta tare da kara jaddada mata sharadin maganin sa, ta amsa ta koma gida tana ta farin ciki ta boye abin ta sai ta koma shige wa Ummulkhairi ni dai ban saki jiki da ita ba, duk yadda tayi ta fakon ta sanya mugun abin dan Ummulkhairi ta taka abin ya zame mata jan aiki, amma dai bata hakura ba tana ta bi ta hanyar kisisinarta da duniyancin ta.

<< Wa Gari Ya Waya 45Wa Gari Ya Waya 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×