Skip to content
Part 5 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Mun shiga Hospital ɗin, a ɗakin da Basma take sai yayyen Tahir na samu, Yaya lawal sai Baban Ummi, na gaishe su da girmamawa kafin na gaida me jikin da masu jinyar ta.

Su Yaya Lawal su ka ce mini matan ai har sun shiga mota, direba ya shigo da abincin da na kawo musu na ce “Ai kuma ga abinci na kawo maku” Yaya Lawal ya kira matarsa a waya ya ce su dawo na zo, sai ga su da murnar su.

Muka tari juna wurin da suka yi sallah muka koma suka zuzzuba abincin aka zubawa mazan matar Yaya Lawal sai fadin irin canzawar da nayi take yi da a hanya ta haɗu da ni me wuya ta yarda ni ce. Sun gama suka yi harama da Maman Ummi muka jero zuwa mota take ce mini,

“Ba ƙaramar lada kika samu ba Ummulkhairi dan da da bakar yunwar mu za mu koma, saboda yanayin hanya muke tsoron tafiyar dare.” Murmushi nayi na damka mata cooler na ce ta kai wa Hajiyar su Tahir na ƙara da cewa “Ya aka yi Tahir bai zo ba?” Ta ce, “Sai da suka zo aka kira shi ya ce baya kusa ya je kaciya in muka ce kuma a tsaya jiransa dare zai yi mana.”

Sai da duk suka zauna na ajiye musu 10 thausand na ce su sha mai sai godiya suke na juya, ban koma wurin Basma ba inda direba ke jirana na isa da shigata ya ja motar sai muka bar Asibitin.

Sai dare Tahir ya dawo ina ɗakina ko abincin daren Halima ban fito ci ba, waya nake tayi da ƴan’uwana da su Laila da ƙawata Hafsat. Latifa ta leƙo ta ce mini ana kirana a falo. Bin bayanta nayi da kallo bayan ta fice kafin na miƙe hoda na murza na fesa turare sai na fito, Halima ana zaune ana kaɗa ƙafa Latifa ma na zaune haka zalika Ogan.

Gaishe shi na yi ya amsa cikin dakewa dan haka a hannun kujera na ɗofana. Mazaunaina, kallona ya yi “Me yasa dan Halima ta yi miki maganar abinci sai kika ɗauke abincin gidan yau aka wuni da yunwa?” Faduwar gaba na ji jin zancensa. Sai nayi shiru ina kakkaɓin jin wani rainin hankali da za a yi mini, cikin ƴar hasala ya ce “Ba ki ji ina miki Magana.”

Kawai sai na ji hawaye sun cika mini ido tausayin kaina ya kama ni, kallonsa nayi sai muka haɗa ido hawayen suka gangaro mini ban damu da in share su ba na ce

“Ni dama ba abincin gida nake yi ba, ƴan ƙanƙara da za su zo nayi mawa. Kuma ina gamawa na kai musu Hospital.”

Lura na yi jikinsa ya yi sanyi su kansu matan sun yi laƙwas. Shiru falon ya dauka wayarsa ta dauki ƙara ya ɗauka cikin girmamawa ya soma Magana, “Haliyata”

a yanda na fahimci wayar ta su labari take ba shi na aiken naman da nayi mata, ko

ta nemi ya bani wayar ne sai ya miƙo mini godiya tayi ta mini da sa albarka bayan na gaisheta,

Muna gamawa na miƙe na ajiye mishi wayar kusa da shi na wuce ɗakina ina ta kakkaɓin wulaƙancin da aka so yi mini cikin kishiyoyi. A daren na daɗe barci

bai ɗauke ni ba ina ta tunanin irin wannan zama da kuma ƙalubalen da ke cikin auren nesa.

Yanzu da a garin mu nake inda iyayena da ƴan’uwana suke da gari na wayewa sai in tafi gidanmu ko gidan daya daga cikin ƴan’uwana na san dai ko ban faɗa masu damuwar da ke damuna ba a ƙalla za su sanya ni cikin farin cikin da zai mantar da ni damuwata.

Hausawa suka ce ya kamata auren na gida ko ba ka ci ba ka ga uwarka. Rashin samun barci da ban yi ba sosai yasa ni makara daga sallar da nike tashi a karshen dare ina yi inda nake raka’a biyu, a sujadar karshe ina karanta (LAILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN) sau 41 sai in faɗi bukata ta in dago in yi tahiya in sallama.

Gari na wayewa kuwa na kira Babana da mamani na gaishe su Tahir na shigowa na roke shi in shiga gidan Kawu Attahiru, Sha daya na yi na fito na tafi sai da na fara gaida kawun sannan na koma wurin Haj, na dai zauna ne kawai daga ita ba magana take ba, sai mai aikinta da ta shigo muka yi ta hira.

Wuni nayi zungur har aka yi sallar magrib, na idar da sallar isha’i Hajiyar ta leƙo ta ce in fito in ci abinci a kasa na zauna bisa carpet na kusa kammala cin abincin muryar Tahir da na ji ta sa ni daga kai fuskarsa haɗe take kamar hadari maida kaina ƙasa nayi

gaishe da Haj Hajara ya yi sannan ya dube ni “Zaman me kike yi har yanzu?”

Kara sunkuyar da kaina na yi ina shirin tashi Hajiyar ta yi magana “A’a Sodangi ka bar ta ta ci abincinta, nan ma ba gida bane?” Bai yi magana ba illa harɗe hannayensa da ya yi a kirjinsa, kallon da yake bi na da shi yasa jikina ɗaukar rawa na san ran ƴan mazan a ɓace yake.

Na kai kwanukan kitchen na dawo, sannan nayi mata sai da safe har na fice ban ga tahowarsa ba. Ga mamakina da shigata falon matan na samu duk kan su hada Basma wadda bani da labarin dawowar ta ina tunanin bayan fitata aka dawo da ita,

Gaishe ta na yi tare da yi mata ya jiki ta amsa da yanayinta na kodayaushe, na wuce zan shiga ɗaki naji muryar shi “Ina za ki zo kema ki zauna.” Dawowa nayi na nemi wuri na zauna shi ma zaman ya yi ya dafe kunci da hannu bi biyu, ya dauki mintoci kafin ya ɗago “Na tara ku ne domin na ja wa kowaccen ku kunne,in kuma jaddada muku zaman da kuke kuna zama ƙarkashina ne, dan haka dole in sa doka a bi, ba wadda ta fi ƙarfina duk kuma me son zama da ni dole ta bi umarnina.

Ba zan lamunci ci mini zarafi a cikin gidana ba, ba kuma zan dauki yawan faɗa ba,

dole kowacce ta zauna da ƴar’uwarta lafiya. Sannan wace hujja ce tasa ba a kai wa Basma abinci ba alhali kun san daga asibiti ta dawo bata da lafiya? Duk kan mu shiru muka yi.

Har Halima me nuna gadarar ita isashshiya ce yau shiru kake ji kamar ruwa ya ci ta.

Da na fahimci ya ƙare fadan sai na ba shi hakuri, miƙewa ya yi ya haye saman shi,

nima tashi na yi na shige nawa ɗakin.

Halima ke juyi bisa gadonta maganar barci ma ya ɗauke ta ma bata taso ba a yau,

wani tururi ke tasowa a kasan zuciyarta, wai ita Tahir zai tara wadannan kucakan da yake ganin mata ya tara ya wulaƙanta ta, Kullun cikin kashe kudade take amma har yau malaman sun kasa mata maganin matsalolinta.

Zaune ta tashi kirjinta na cigaba da suya, “Wallahi ba zai yiwu ba, ba ƴar iskar da ta isa.” Ta buga kanta jikin gado sai kuma ta dafe kan, sai gabanin hudowar alfijir barci ya yi awon gaba da ita abin da ya ja mata muguwar makara. Tana farkawa toilet ta wuce ta dauro alwala.

A gurguje tayi sallah ta fita zuwa kitchen zuciyarta na bugawa ka da Tahir ya ci zarafinta a gaban matansa. Indo ta samu a gefe ta gama gyara kitchen tana jiran me girki dan doka ce daga me gidan bai yarda me aiki ta girka abin da zai ci ba, gaishe ta tayi sai suka soma aikin.

A daidai nan Ogan ya fito fita yake son yi, ganin dinning wayam yasa shi

yin ƙwafa har yau Halima bata gama sanin shi ba, dakin basma ya fara shiga suna zaune ita da me kula da ita suna breakfast.

Ya gaida matar wadda take ƙanwar mahaifin Basma tana shirin fita Ya ce “Yi zamanki ba daɗewa zan yi ba” bata yarda ba, kwanonin da suka yi amfani da su ta shiga tattarawa ta ce “Ai na kammala zan miƙa su kitchen ne” sai da ta fita ta ja musu ƙofar,

ya dubi Basma “Ya jikin? a hankali ta ce “Da sauƙi” “Daddy na ya yi ta neman wayarka ta ƙi shiga shi ne ya kira ni yana tambayata lafiya” ya ce “Ok bari in kira shi” hannunsa yasa aljihu ya ciro wayar  “Wa ya kawo muku abinci” ya tambaya dan ya yi mamaki ko shi me gidan ba a ajiye nashi ba, amma su suna ci.

Kamar bata son maganar ta ce “Ummulkhairi ta kawo” Ummulkhairi? Ya ambaci sunan cikin mamaki. Lokacin kuma aka daga wayar da ya kira cikin girmamawa ya soma gaishe da surukin nasa. Sai da ya amsa ya ce “Jiya ba mu haɗu ba.” Tahir ya ce “E wallahi mun samu saɓani ne”

ya ce “To dama na so mu zauna kan Basma ina so in kafa sharadi kan zamanta,

wajibi ne zamanta da matanka a guji abin da zai bata mata rai kamar yadda ka sani ɓacin rai ke tada ciwon ta dan nayi nayi mu wuce Abuja ta ƙi kamar yadda ka ki raba mata gida da matanka.

Ga Hajjo nan yar’uwata ce za ta zauna da ita dan taimaka mata. Duk yanda Tahir yaso

ya yi magana kasawa ya yi dan wani ɓacin rai da ya taso ya tokare kirjinsa har surukin nasa ya kashe wayarsa. Bai bi takan Basma ba wadda tun daga ganin canzawar yanayinsa ta gane ba me daɗi Daddynta ta fada masa ba.

Fitowarsa da Latifa ya ci karo wadda ya nufi ɗakinta wucewa ya yi ta bi shi a baya tana fadin “Ni dai wallahi na gaji da horon yunwar da matar nan take mana a ranar girkinta. Ina dalili har 10 mutum bai yi breakfast ba” Shi dai bai ce komai ba har suka shiga ɗakin nata.

Bai jima ba ya fito ya bar ta da takaicin ɗakinta ne kawai ya shiga baya jimawa, kome yake yi dakin sauran? tayi ƙwafa bari ka ga ya shiga ɗakin waccan munafukar yarinyar da ta lura yana ba matsayi na musamman, dan Halima ko da take tsula tsiyar ta

ba ko wane lokaci yake ƙyale ta ba. Miƙewa tayi ta bi shi ta ga sa’adda zai fito.

Da ya shigo ɗakina zaune ya same ni ina karyawa, dan yanzu saboda cikin jikina bana juriyar yunwa. Na fito na ga ba alamun Halima sai na shiga kitchen din dan na taimaki kaina. Na soma aiki kenan matar ƙanwar mahaifin Basma ta shigo, cikin mutunci muka gaisa,

“Dan Allah ruwan zafi nake so in dafa wa mara lafiyar yunwa take ji, ko tea ne in hada mata. Murmushi nayi na ce “Ba damuwa bari in dafa mata” Godiya ta mini ta koma ta dawo ɗauke da flaks, Lifton na sa da kayan ƙamshi, sai da ya tafasa sosai sai na juye mata, ta amsa tana ta godiya.

Kunun gyaɗa na dama me kyau sai nayi farfesun kaza, na kai wanda zai ishe ni daki kafin na dawo na kwashe sauran zuwa dakin Basma, da na ƙwanƙwasa matar ce ta bude, sai da na gaishe da Basma sannan na miƙa musu, nan ma matar ce tayi godiya.

Sai da nayi wanka na gyara jikina, cikin wani material fari me zanen manyan fulawoyi, ɗinkin doguwar riga da tayi kyau a jikina, na zauna zaman karin ne ya shigo. Ya bi ni da kallo kafin ya sauke kan abin da nake ci, “Ya kike cin abinci a daki bayan za a ci gaba ɗaya?

Kai na langabe “Ba na juriyar yunwa yanzu shi yasa na shiga kitchen din” “Ya yi kyau”

abinda ya faɗa kenan sai ya zauna, “Ina kwana? Na soma gaishe shi. Sai da ya amsa na tambaye shi yaushe zan tafi gida?

“Nan ba da jimawa ba” Amsar da ya bani kenan ina cin abincina amma a takure nake dan mayun idanuwansa da ke cikin farin Glass ɗinsa na rai da rai da ke kaina suna tasiri a jikina, shigar kananun kaya ya yi duk hassadar ka dole ka yabi Tahir, dan wani kwarjini da Allah ya ba shi ga cikar zati da iya ado na mazan da suke ji da kansu a wannan zamani.

Na miƙe dan samun wurin zama,taku ɗaya nayi ana biyun ƙafata ta bigi tashi wadda na fahimci da biyu ya yi dan na tafi zan kifa ya taro ni na faɗa kan jikinsa, gaba ɗaya ƙamshin turarensa ya mamaye ni. Wata ajiyar zuciya yake fiddawa yayin da hannunsa ke yawo cikin jikina, wai har yanzu ban yi ajiya ba?

Ya fadi cikin lumshi hannunsa na kan cikin yana shafawa, ganin yana kokarin danne ni kan kujerar da muke yasa ni soma kwatar kaina, ina tuna mishi ba ni ke da wannan alhakin ba, hannayen nawa ya kama da hannu ɗaya  ya cigaba da sha’aninsa.

Sai dai kofar da aka buɗe gaba ɗaya ta sa ni kwace hannayena jikina na rawa. Latifa ce tsaye kanmu tana huci dan duk yanda taso daurewa kishi yasa ta gwammace koma me Tahir zai mata sai dai ya yi mata amma sai ta ga abin da ke sa shi daɗewa a dakin  wannan shegiyar yarinyar da tafi tsana a duk cikin kishiyoyin nata.

Kuma ga shi ta tabbatar da zargin ta. “Daga kin shigo kin ga abin da kike son gani sai ki fita ki bani wuri.” Tahir ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, duk kuma ture shin da nake ban samu nasarar ture shi a jikina ba.

Juyawa ta yi ta fita tana gunjin kuka, ni ma sai sannan na samu ture shi na gudu bedroom ɗi na na sa key. Shi ma miƙewa ya yi sai ya fice, dakin Latifa ya koma wadda ya samu kwance tayi rub da ciki tana sharbar kuka, tsawa ya daka mata ya ce ta tashi zaune tilas ta tashi ta zauna, mugun kallon da yake watsa mata yasa ta hadiye kukan.

“Wannan ya zame miki na ƙarshe da za ki yi mini laɓe, ko sai ina tare da wata ki fado sai ka ce rayuwar wasu arna ko marasa addini. Abin da nayi nayi ne dan in tabbatar ko kina laben da kika saba, kuma sai kika tabbatar mini da zargina kika shigo.

Na ƙara kama ki sai kin bar mini gidana wallahi” Ya juya ya bar mata ɗakin.

Rantsuwar da ya yi za ta bar mishi gida idan ta ƙara mishi laɓe, ya firgita ta, dan ta fi kowa sanin waye Tahir. Yana fita Halima ya gani suna shirya dinning ita da me aiki, kallo ɗaya ya yi musu ya haura sama. Wasu kayan ya sauya yana sa turare ta shigo.

“Abinci ya sauka” ta fadi tana duban sa, ganin yana neman rabe ta ya wuce yasa ta shan gaban sa, “Wai me yasa kake son yi min wulaƙanci? wani shegen kallo ya mata,

“Matsa ki bani hanya malama, kuma ban ce ki daina gama abinci lokacin da kika ga dama ba, ki yi tayin hakan sai dai har yau ba ki gama sani na ba, ba kuma ki san dalilin da yasa nake raga miki ba.

Ina ganin wannan karon sai na tura ki gida, kilan kya koyi hankali” Ya fice ya bar ta kamar an dasa ta, Ai kam ba babban tozarci irin ace Tahir ya kore ta, da wane idon za ta dubi yan gidansu? Ina jin kai da takamarta, idan ta dawo ya za ta dubi kishiyoyinta.

Zabura tayi ta sauko sai dai tana saukowa yana tashin motar ba kowa falon kamar ta aiki Indo ta mika wa su Basma abincin girman kai ya hana, ita ma takaici bai bar ta ci ba. Latifa ma ta dade kwance ba abin da ke mata yawo a ido sai halin da ta ga Tahir da wannan yarinyar, cikin wani shauƙi yake wanda ko yana me gaba ɗayan da ita bata taɓa ganin shi hakan ba.

Can sai ta tuna fushin da ta gani a idonsa bata san irin matakin da zai dauka kanta ba. Miƙewa tayi tuna dabarar da za ta fishshe ta.

<< Wa Gari Ya Waya? 4Wa Gari Ya Waya? 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.