Skip to content
Part 7 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Turo kofar kawai ya yi ya shigo ba tare da ya nemi izinin yin hakan ba, abin da na yi ta rokon ya daina yin hakan, saboda yadda kullum sai yallabai ya gaya mini cewar shi bai taba ganin mai yi mishi irin wannan cin kashin ba a ofis din shi, sai shi.

Kullum na yi mishi maganar sai ya ce mini wai shi bai san hakan yake yi ba, amma bari gobe in ya zo zai kula ya gyara, amma kuma hakan ba zai hana shi goben in zo zai kula ya gyara, amma kuma hakan ba zaj hana shi goben in ya zo ya sake ba.

Na daga ido na kalle shi fuskar shi kadaran-kadahan yana tsaye cikin shigar suit farare sol, ya zuba hannayen shi duka biyu cikin aljihun wandon shi, ko kallon inda yallabai yake bai yi ba, balle ya sa ran zai gaishe shi.

Ya ya kin gåma ne ko da saura?”

Cikin nutsuwa na-ce mishi, “Da dan saura kadan.”

Ya dago ido ya kalli agogon da ke ofice din alamar lokaci yake son sani, a hankali ya bude baki ya ce mini, “Bari in jira ki.”

Ya juya ya fita.

Yana barin office din yallabai ya dube ni cikin takaici ya ce, ‘Shi kuma don fitinar tsiya ba ma zai rinka bari sai an tashi ba, ya rinka zuwa daukar na ki?

To duk tsiyar shi ma dai ai dolen shi ya bai wa wai auren ki ko kuma a bayar yana kallo tun da bai taba ganin inda wa ya auri kanwarshi a, balle ya ce shi haka zai yi.”

Ya rufe zancen na shi da jan wani mummunan tsaki.

“Tashi ki bishi ku tafi ke ashe ma ba wani nisa ya yi ba, gashi nan na hango shi koma ya ji maganata ne ya sa ya yi motsin? Oho,”

Na yi maza na karasa cike takardun na mika mishi na dauki jakata na fito.

Na samu ya dan fara tafiya na biyo bayan shi.

A hanya muna tafiya na shiga rokon Yaya Almu akan ya rinka gaida yallabai. Ya ce mini, “Ke kar fa ki kawo mini sakarci nine zan rinka bin samarin ki ina gaishe su? Ina ce a ka’ida ni ya kamata su rinka gayarwa tun da nine in ta dauro zan ba su.”

Na yi maza na ce, “Yallabai yana gaishe ka Yaya Almu ko yau din nan na ji shi ya gaishe ka sau biyu, sannan ma shi ba saurayina ba ne. “

Ya ce, “To ban ji gaisuwar ba, gobe in na zo daukan ki zan kasa kunne in ji, don in amsa.”

A gida da daddare ina hira a dakin su Yaya Almu shi da Junaidu ne a ciki suna cin danbun shinkafar da na yi wa Umma na debo musu suna ci muna hira sai kawai na ji bakina ya sako wani zancen na daban.

Na ce, “Kai ana teba a duniyar nan. Tebar yallabai din office din mu fa ta kai girman wancan filon sau biyu.”

Yaya Almu kam ko motsawa daga inda yake bai yi ba, bai bar cin abincin shi ba, hakan nan bai daga ido ya kalli fillon da nake magana akai din ba, balle ya nuna wata alama ta ya ji maganar da na yi.

Sai Yaya Junaidu ne ya ce mini, To ai burgewa kenan ita teba da kike ganinta ai ado ne wurin namiji da yawan mata kuma ita suka fi so da sha’awa a jikin mutum, kuma ga dukkan alamu ke ma kinan cikin su, don na lura son yallabai din kike yi, saboda kullum sai kin yi mana hirar shi, ai in kin ji mace tana yawan maganar namiji ko da kushe shi take yi, to son shi take yi, ita irin nata salon soyayyar kenan.”

Na ce, “Kai Yaya Junaidu.”

Ya yi maza ya ce,   “Eh mana ai in kin ga kare yana sunsunar kashi to daukan shi zai yi.”

Na juya ta wurin Yaya Almu don in ji shi kuma abin da zai fada. Yanayin da na gani a tare da shi ya sa na yi maza na mike na yiwo waje da gudu bayan na ce musu sai da safe.

A daki kuwa ina kwance ina tunanin ya kamata a ce ni da kaina na dauki matakin gasawa kaina baki.

Ranar Asabar din karshen wata ya zo ranar da yake zamowa ranar tsabtar muhalli ne a kasa gaba daya, ban da haka kuma mu a gidan mu ranar zuwan Baba ne, don haka ana fitowa daga masallaci muke kama aikace-aikacen tsabtar gida, wanda su Yaya Almu suke jagoranta, daga gidan mu bar zuwa fence house babu inda ba a gyarawa tsab.

A irin. wannan ranar suma su Umma ba a zaune suke ba, rana ce ta haduwar matan gidan a babban kicin din taraiya na kusa da sashin baba, don shirye-shiryen abincin da za a tanada don Baba da bakin da za su cika gidan don zuwan shi.

Kasancewar Umma Karama ce a can ita ce za ta dawo yau tare da shi, sai Umma amarya ta tafi ita da Umma Amaryar ne a gida sune za su jagoranci aikin da za a yin komai na su a tsare yake, tuni sun riga sun shirya duk wani abin da za su yi saboda akwai hadin kai da fahimtar juna a cikin lamarin su.

A duk lokacin da Umma za ta yi wani abu tare da Umma Amarya abin kan zo mata da sauki kwarai, saboda irin biyayyar da Umma Amarya ke yi mata, ita kuma tana matukar kokarinta wajen kame ginmanta ba ta yarda ta yi amfani da ra’ayinta kawai wajen zartar da hukunci, sai ta saurari na Umma Amarya ko da kuwa ba ta gida to za ta yi waya ta tambayeta.

A hakan nan duk wani abin da za ta saiwa kanta, to takan tabbatar ta sai biyu ne.

Wajen karfe goma. sha biyu na shiga kicin din don in kira baba Maigyada ta tayani nawa aikin, saboda nima yau ban shiga aikin tsabtar gida ba, a dalilin ni ce mai yin abincin gida, kuma mafi yawancin yaran yan matan da kan tayani aikin su na wasu aikace-aikacen da aka sanya su tun a lokacin na samu har an gama sinasir, masa,

funkaso, da miyoyin su, masu dandano daban-daban an kuma shiga yin wani abin daban. Sha biyu da rabi na yi na bar wa su Baba Maigyada sauran aikin na je na yi wanka, na yi sallah, na yi kwaliya mai ban sha’awa cikin wata atamfar Holland fara sol, zani da riga da dankwalinta.

Na sanya sarka da yankunne, awarwaro da zobuna sannan nan yi amfani da jaka da takalmi tare da gyalen da suka dace da kayan.

Wani kamshi mai nutsar da zuciya nake yi lokacin da na iso inda Yaya Almu yake zaman jirana a Cikin motar shi ya kuma yi jiran ne don ya san tuni tun ba yau ba tun ina ‘yar kankanuwata baba ya sanya dokar tafiya da ni wurin taro shi bai yarda a bar ni a gida in jira isowar shi ba.

Ina shiga na zauna na ce mishi;

Kar dai har su Yaya Junaidu sun tafi?”

Daidai yana kan titi ya ce mini, “Ai sun isa Aiport yanzu muma dai ina ganin daga kafa za mu yi, don kar ya iso ba ma nan.”

Ba mu fi minti goma da isa airport din ba jiriginsu Baba ya sauka. Yan mutanen da suka fito kadan ne sai ga Unmma Karama ta bayyana, Baba yana biye da ita.

Cikin zuciyata na ce kai Baba ya more kyawawan mata, to wace ce ba wacce ba a cikin su?

Umma Karama doguwar macece ta Samanta ba ta da girma sosai, kamar ta kuturinta.

Sannan fara ce sol tafi duk sauran matan farar fata.

Ita kuwa Umma Amarya madaidaicin tsawo ne da ita, wankan tarwada ce, tana da cikakkiyar fuska mai dauke da manyan idanuwa.

Sai Ummana wacce take doguwa a tsaye ingarmar mace mai surar jiki mai kyau da bayyanar da yawan shekarunta, kalar jikinta yana tsakanin na Umma Karama ne da Umma Amarya tati wanan ba ta kai wancan ba.

Gata da gashin kai mai yawan gaske, har a yanzu da furfura ta soma ratsa shi, tsawon shi da cikar shi yana nan a hakan kuma na san jin Yaya Almu yana gaya mini ke kam in da kin yi sa’a kin dauko gabadaya gashin Umma da ban san abin da za ki yi ba.

Ni da kaina na san ni din kama da Ummana nake yi a komai in ban da wuri biyu na darata manyan idanuwa sai kuma hasken fata da ban karasata ba, ta dan wadannan abubuwan guda biyu tanan ne nake ganin na dauko Baba, don shi kam Yaya Almu da Yaya Junaidu duk kalarmu kusan daya ne, dan hasken da na fishi bai wuce na ni din, don ina mace ba ne.

Motar da aka dauko Baba na shiga dama kuma haka yake yi in shigo gaba ni da Yaya Junaidu shi da matar da ya dawo da ita kuma suna baya.

“Ya ya dai uwata?” Ya yi mini tambayar bayan na gama gaishe su shi da Umma Karama.

“Tsakanin Junaidu da Zubairu da Kabiu da Lamido wanene mai takura miki? “

Na yi murmushi nace,  “Baba ai su Yaya Kabiru su ba sa fada su sai dai kawai a yi ta mutunci da su, babu ruwan su, Baba ya yi dariva ya ce. “Sun dai fi Junaidu da Lamido kirki kenan?”

Na yi murmushi na ce, ‘A’a Baba ba haka nake nufi ba, ba su dai kawai mu’amallar mai dadi ce ba ruwansu da ka ga sun sawa mutum ido in dai ba gani suka yi za a fita can waje ba, shi ne za su ce ina zuwa?”

Baba ya yi murmushi ya ce, ‘A’a lalle lamarin su mai dadin ne, to bari tun da ba kya son sa ido zan yi magana da su Junaidun su kawar da idanuwansu daga gare ki kar wanda ya takurawa uwata,”

Na yi murmushi kawai don na san raha kawai Baba ke mini a dalilin na sha kai karar Yaya Almu wurin shi kan takurawar da yake yi mini sai kawai ya ce mini in je wurn mu ta yi wannan shari’ar amma shi ba zai shiga tsakanin mu ba. don mun fi kusa.

Umma kuwa ko akan idonta Yaya Aimu ya yi mini ba ta magana don haka babu amfanin in kai mata karar shi.

Muna isa gida sashin Ummana baba ya zarce duk da ya samu mutane da yawa da suka san da zuwan shi, sun zo Suna jiran sh1 al’adar baba ne a duk lokacin da ya iso gida sashin matan shi yake Wucewa sai ya gama gaisuwa da sù, sannan ya taho wurin jama’ar da ya samu mati yawancin lokaci ya kan ci abincin shine tare da su, sannan ya gana da wadanda zai gana da daddare kuma ya kan yi zama tarc da su Yaya Junaidu gaba daya manyan samarin gidan su bata lokaci suna tattauna al’amura hakan nan bai tafiya sai ya samu lokaci ya zaga dakunan kwanan yara ya kuma gan su gaba daya, mun cika falon Baba mu yaran gidan bayan fitowa daga sallar Asuba kananan yara amsa gaisuwar su ya yi suka tafi.

Ni da su Anti Rashida da su Yaya Almu kuwa dukkan mu muna ciki har da Umma na ma don ita ce ta kasance tare da shi a zuwan nashi saboda in ya tashi tafiyar zai tafi ne da Um yama amarya.

Anti Aina’u ta sake gaisheshi ya amsa sannan ta soma zata yi mishi magana akan bukatarsu kan karatun su bai bari ta karasa ba ya katseta ta hanyar ce mata bana zaton hakan zai yiwu kuna nan gidan Aina’u in kun lura za ku ga ban taba tsare samari da yan mata sun kai matsayin dadewarku ba akwai wani kwadayi da buri da nake dashi ne yasa nayi haka na jira lokaci to yanzu kuwa ina ganin lokacin yayi don haka nan bada dadewa ba zan sallameku ku je dakunan mazajenku ku huta, maganar karatunku zai zammo tsakaninku da su ne duk da dukanku abin iko na ne hakan ba zai sa in shiga cikin hakkin aurenku ba saboda haka in kunje gidajenku sai ku yi kokarin sasantawa da su.

Ina jin haka na saki wani lallausan murmushi da ya kara baiyanar da tsananın farın ciki na na dan mike na duckusa kan kafafuwa na don ya ganni da kyau na ce.

“Uhum, Baba.” Ya juyo da natsuwarshi zuwa gare ni ya ce.

“Menene Uwata?”

Na sake sakin wani murmushin kafin nace mishi “Zan zama kenan nice babba a cikin gidan nan idan su anti Kubra suka tafi gidajensu da su yaya Almu dukansu.”

Baba yayi murmushi ya ce “Ai yan zuma ke ce babba a cikin gidan nan uwata ko da wani wanda ki ke ganin ya girmeki ne? Ke ce fa uwata ina wani girma daya wuce miki wannan? In kuwa Su Lamido da Junaidu nc suke saki ki ke shakkar hakan bari iny miki maganinsu ina Lamido?”

Ya ya Almu ya ce mishi “Gani baba.”

Baba ya kalleshi ya ce “Kai kafi kowa takurawa uwata na hana ku daga yau shekara daya da rabi daya wuce ta kawo min kararka kan kasata girkin da bazata iya ba, to daga yau na sauke mata wannan girkin da ka dora mata karta sake shiga kicin sai don ra’ayinta hakan nan sauran yan matan dukansu a nemt sabbin masu aiki in kuna ganin wadannan sun girma.”

Yaya Almu ya amsa ckin ladabi ya ce “To Baba.”

Baba ya sake kallona ya ce “Yaya da akwai wata mas’alar uwata?”

Na yi murmushi na ce “Babu.”

Ya ce “To daina tunanin wani girma da ya wuce ki na yanzu ke ce uwar mutanen gidan nan gaba daya don haka kina da girma mai yawa kin ji ko?”

Na ce mishi “To Baba.” Na koma na zauna cikin zuciyata kuwa ina tunanin baba bai gane irin girman da nake nufi ba.

Gabadayanmu Baba ya sallemmu bayan y yi mana addu’a ya sanya mana albarka kowa ya tashi ya fita ni kuwa nayi nufin ci gaba da zamana a wunin sai da yaya Almu ya sake lekowa ya kira ni na tashi naje inda yake tsaye sai kawai ya kalleni ya ce “Mun ke kam zan ga ranar da zakiyi hankali baki ji kalmar da yayi amfani da ita bane wajen sallamar mu? Ya ce mu dan bashi wuri ya ga matarshi kafin jama’a su zo.”

Na bata rai na ce “A’a, to ba Ummana ba ce a ciki kuma ma ai wasa yake yi daya fadi hakan ba shima dariya ya yi ba?”

Ya ce “Wasa? To daga yau na sake ganin shi da Umma suna ciki kin shigar musu ba tare da kin Jira sun kira ki ba, sai na bata miki.”

<< Wace Ce Ni? 6Wace Ce Ni? 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×