Skip to content
Part 9 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Zaman da Yaya Almu ya sani na yi a sashin Umma ya sa baki ba su yanke ba a wurin, kowa ya zo nan din dai yake sauka tamkar tana nan.

Hakan sai ya sani a cikin kidima da ayuka masu yawan gaske, don sai na zamo ni ce mai karbar su, sai na sauke su anan sannan na ke kai su wajen su wato masaukın su ni ke tsayawa in ga an kai musu wadataccen abincin da zai ishe su, kuma akan lokaci in kuwa gari ya waye ina idar da sallah zan je in ga na ba su ruwan wankan su su da ‘ya’yan su, in je in kawo musu abin karyawa, in sun gama in je in sakc kawo wani in ajiye musu, saboda ya’yan su kar su ji yunwa kafin a gama abincin rana.

Nan da nan na wastsake na shiga hidimar da da ba na kulawa da ita, sai dai in ga Umma tana ta faman zirga-zirga tana dawainiyar jama’a ban san wahalar abin ba, sai da na samu kai na a cikin shi lokacin ne na gane ashe ba karamar hidima Umma take wuni a cikinta ba, gashi ko na je na samu Umma Amarya na ce mata Umma ga bakin nan sun ce za su tafi sai ta ce ai ba sai kin zo kin gaya mini ba, kina ganin yadda Hajiya Babba take yi ba in na ce ch sai ta ce to je ki ki yi hakan don haka komai zan yi a kan su Yaya Almu nake kira in gaya mishi kamar yanda na ga Umman tana yi.

Rannan na sallami wasu baki na yi musu rakiya suka yi wa Umma Karama da Umma Amarya sallama sai da suka tafi na dawo na sami Yaya Almu a falon shi kadai yana zaune na zo na wuce da doguwar riga a jikina na shiga kicin na dauko filas din kunun gyada na zo na zauna zan sha ya kalleni ya ce, “Kar dai tuntuni ba ki sha kunun nan ba?”

Na. ce, “Na jira ne in sallame su su tafi takunna.”

Ya dago idanuwan shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, “Amma ba ki ga kamar za ki iya gadon Ummana a kan komai ba? Ai na ga kamar za ki iya uwargidanci ki iya sa hannu biyu, ki rungumi mijinki, shi da jama’ar shi.”

Na yi maza na tsuke fuska na ce, “Ni fa ba na Son irin wannan maganar,. na ce ba na son maganar uwargidancin, ni ba na so, ba na so na kara.” Na kara fuska ya ce,

“To yi hakuri Rabi ba maganar bacin rai ba ne, ni dai ina yi miki sha’awar girman ne tun da kema na ga kina yi wa kan ki.”

Na yi maza na ce, ‘A’a ni ba na yi wa kaina wani sha’awa in dai irin wannan ne.”

Sati biyu bayan nan na wayi gari cikin murnar cikana shekaru goma sha tara, sai dai abin takaicin shi ne Ummana ba ta nan duk da haka Umma Amarya ta sa an yi ta tuyan masa da funkaso tun cikin dare ana idar da sallar Asuba tasa aka yi ta fita da shi a mota ana kaiwa makarantun allo na cikin gari a gida ma an yi saukar Alkur’ani mai girma abin da na sani kuma shi ne ko Umma da baba suna nan iyakacin abin da za su yi kenan.

Na fito daga sashin Umma amarya bayan na yi kwalliyar kara wata shekarar, na je gaisheta.

Addu’o’i da nasihohi masu yawa ta yi mini, na shiga falon zuciyata cike da jimamin al’amuran da Umma ta yi mini nasiha a kan su.

Ina shiga ko gama zama ban yi sai ga yaya Junaidu ya shigo yana rungume da wani kwali yana ganina ya saki wani irin lallausan murmushi ya ce;

“Kai mun ji dadi yau Adawiyya ta kara wata shekarar. Na tayaki murma Babyna.”

Na taya shi murmushin na ce mishi, “Na gode maka Yaya Junaidu.”

Ya durkusa a gabana ya ce, dan lumshe mini idanuwan na ki sai na kirya goma kafin ki sake bude su.”

Na sake yin wani murmushin, sannan na yi mishi yanda ya ce din, na kuma shiga taya shi kirgen cikin nutsuwa, sai na ji ya kai karshe ya ce in bude idona.

Na sake yin wani murmushin don dadi wani kayataccen cake ne da aka kayata shi da kalmomi na fatan alheri ya sa yar kankanuwar wukar da ke soke jikin cake din ya yanke dan kankanin loma ya ce, “Bude dan bakin na ki in jefa miki shi a ciki.”

Ban yi mishi musu ba don haka sai na lumshe idona na bude mishi bakin nawa kamar yanda ya nema sai da na ji gardin shi ya sauka kan harshena sannan ne na maida bakin nawa na rufe na kuma bude idanuwana ina tauna cikin murmushi na ce, “Wace ce ta yi cake din gwana ce kwarai.”

Ya ce, Uhm Adawiyyah ba ta kai ki iyawa ba, ke dai na sa ta ta yi ne kawai don ina son burge ki.”

Na sake yin wani murmushin cikin lumshewar idanuwa, saboda tsananin dadin da nake ciki na ce mishi, “Na gode Yaya Junaidu.”

Ya mike tsaye alamar fita zai yi ya ce mini, “Bari in je in dawo Adawiyya zan zo in yi miki hira.” Na ce to sai ka dawo.

Yana fita na kira Hauwa na ba ta cake.din na ce ta je ta yanyanka ta raba musu. Ta ce to, ta dauka ta tafi.

Wajen karfe biyu da rabi na barwa Baba Talatu lura da sashin Umma na tafi ferce house don amsa kiran da Yaya Almu ya yi mini.

A bakin  get din shiga wurin na same shi yana sanye da farar kufta ya yi matukar yin kyau yana harde da hannayen shi akan kirjin shi, hanyar da zan fito yake kallo yana ganina ya dan saki ranshi kadan ya dan yi mini kallon sama da kasa, kafin ya ce mini.

“Wasa-wasa dai kin iya wani abu.”

Ya dan mintsina zuciyata na ce, “Ni ma fa ka ce kenan da wacce ta fini?” Na yamutsa fuka na ce, “To ai ko budurwar da za ka aura sai dai ta koya a wurina.” Ya zuba mini ido yana kallona a hankali ya ce mini, “To hadiye fushin naki ki maida wukar, in ma abin da na gaya mikin bai yi miki dadi ba ki ranki na yi don in faranta miki rai in taya ki murna ba wai dan ki fushi ba.

Yanzu ina kike so in kai ki?”

Na dan yi shiru kadan cikin tunanin dadin da nake ji ba mai yawa ba ne, a dalilin rashin Umma kusa da ni na ce mishi, “Mu shiga nan kawai.”

Bai yi musu ba ya wuce gaba na bi bayan shi yana fadin, “Duk yadda kika ce ai hakan za a yi.”

Mun keta cikin fence house din dawakin suna ganin Yaya Almu suka shiga haniniya, suna zarya, wai su ma nan sun ga wanda suka sani. Na ce, “Oh ka ji mini dawakin nan wai suma sun gane ka.”

Ya dan kalle su ya ce, “Eh yau da gobe ai ta ki karfin wasa, suma kuma suna irin tasu fahimtar.” Na ce haka ne.

Cikin gidan katakon yaya Almu ya bude mana komai na ciki a tsare yake gwanin sha’awa ga kamshi ga iskar da ke kadawa ta ko’ina, tana kara nutsar da zukatan dan adam. Ina zama yaya Almu ya miko mini kofin ruwan sanyi na ce,

“A’a.” Ya ce dan karbi ki sha ko kadan ne ai ruwa rayuwa ne.

Ban yi mishi musu ba na karba na sha, shi kuma ya nemi wuri ya zauna yana fadin, “Shekaru goma sha tara ne yau tun da Rabi ta shigo cikin duniyar nan mai cike da al’amura masu ban mamaki da al’ajabi a wancan shekarar kamar yau na gaya miki muhimmancin shekaru goma shatakwas na kira miki su shekarun girmna da hankali da nutsuwa, haka ne ko ba haka ba ne?”

A hankali cikin nutsuwa sosai na ba shi amsa da cewar, “Haka ne.” Ya sake kallona ya ce,”.

To tun da kin shekara kina da hankali ya kamata a ce mafi yawancin abubuwa na rashin hankali kin rage su, in ma ba ki daina gaba daya ba. Sai na ce to bari yau in yi amfani da muhimmancin ranar wajen baki shawara ina fata ba zan takura miki ba, ko ki dauka ina yawan shiga cikin harkokin ki, tun da baba ya ce bai yarda a yanzu a yi miki  hakan ba.”

Na dan yi murmushi na ce, “A’a babu takura” Ya ce, “To me zai hana ki canza yanayin shigar da kike yi? Ina nufin ta yawan mu’amala da kananan kaya, ba ina nufin ba sa karbarki ba ne, amma ado ne da na ke ganin ya dace ki yi a gidan mijin ki, yanzu ba da ba ne kin riga kin girma, in kowa bai lura da hakan ba, ya kamata ke ki lura da kan ki misali dubi siket din da ke jikin ki, ko gwiwar ki bai rufe ba, sharabarki tana waje ji ‘yar rigar da ke jikin ki kin yi kyau har kyau tun da kina da shi, amma bai dace kowa ya rinka ganinki a haka ba. Rabi ai kina da daraja ya kamata a ce kinan rowar kyan jikinki ga mutane da bai dace su rinka gani ba.”

Na kalleshi cikin sakin fuska na ce mishi,

“To. zan gyara.

“Kin yarda za ki gyara da gaske?”

Na ce. mishi,, “Eh ai in nka ba ni shawara ina amfani da ita.” Ya yi maza ya ce, “Haka ne aike mai ganin girman na gaba da ke ne. Rabi to tun da kin yarda za ki gyara bari mu fara gyaran daga yau sai ya zama tun ranar da kika tun daga ranar da kika cika shekaru goma sha tara ba ki sake sanya suturar rashin hankali ba, ko ya ya kika gani?

Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin abin da hakan ke nufi, kenan ba zan sake Sanya kananan kaya ba? Na tuna irin kyan da nake yi a cikin su da nishadin da suke sanyani kan in cemmishi komai sai ya dan matso kusa da ni ya rada mini.

“Mafi darajar tuban da ake so bawa ya yi shi ne na barin abu a lokacin da yin abin yake matukar yi mishi dadi, sannan in ba ki sani ba daina sanya su ba yana nufin daina yin kwalliyar ba ne, a’a sai dai fita daga yin wacce ba ta dace ba, zuwa komawa wacce dace da ke.”

Na gyada kai nuna alamar yarda tare da cewar hakan ne.

Yana jin na fadi hakan ya yi maza ya mike ya yi dakin hutawar Baba ya fito rungume da wani dan madaidaicin kwali da aka kawata shi ya sha ado tanfar dai kar a kwance shi a bar shi haka in ya so ma a yafe abin da ke cikin shi, Zuwa ya yi ya ajiye shi a gabana yana kallon cikin sakin fuska.

“Zan bude miki kwalin ne ko za ki yi da kan ki?”

Na yi murmushi na ce, “Bari in yi da kaina.”

Na matso na durkusa a gaban kwalin ina ta faman ailkin daye adon nan da aka kawata shi da shi, har na kai ga jikin kwalin, wani kyakkyawan kati na fara gani a jikin shi an yi rubutu kamar haka:

Happy Birthday to my lovely sister. “

Sannan wasu kalmomi suka biyo baya. Na bude kwalin sosai gaba daya cikin shi dogayen rigunane, hijab, after dress da wani dan akwati a can Kasan kwalin na sa hannu na dauko shi, madaidaitan warwaraye ne masu matukar kyau na gold guda hudu na kalle shi cikin farin ciki kan in yi mishi wata maganar y ace mini;

“Ban sai miki zobe ba saboda ga al’ada Saurayi ke bada kyautar zobe.”

Na yi murmushi na ce, “Na gode Yaya Almu.” Ya kalle ni cikin nutsuwa ya ce, “To yanzu da ba ki da saurayi ya ya kenan ko kuwa zan yi wa Umma magana ne ta sai miki zobunan da za su dace da su?”

Na ce mishi, “Aa ba ma sai an saya ba, na gode.”

Hira sosai muka yi da yaya Almu har muka gangaro kan zancen aure na ce mishi, ai in aka yi bikin ku kuka tafi zan yi kewar ku.

Ya dan kalleni cikin nutsuwa kafin ya ce anya kuwa Rabi? Ai nafi zaton murna za ki yi maimakon kewa musamman ni da na kc takura ki da yawa na ke yawan shiga al’amuran ki wadanda suka dace in shiga da wadanda ba su dace ba duka.

Na dan yi murmushi na ce, ‘Ai Umma ta ce mini in daina dauka ‘yan ubanci kake yi mini, kana yi mini hakan ne don ganin kai ne ka cancanci ka rinka kwabata kan abubuwan da nake aikatawa.

Sai da ya dan gyara zama kadan kafin ya ce mini gaskiya ne Rabi ban iya kawar da ido kan kuskuren ki don so nake in ji ana cewa kin fi kowa hankali, kin fi kowa nutsuwa da sanin ya kamata shi ya sa kike ganin ina yi miki abin da nake yi mikin, amma ba don ina kin ki ba.

Na ce, ‘Ai na yarda.”

Ya tashi ya je ya yi alwala ya dawo nima na je na yi na dauki riga guda daya a cikin rigunan nan na saka na yane kaina da gyalanta na yi sallah ta.

Sai da muka yi sallar Isha’i, sannan muka fito daga wurin maimakon mu shiga gida motar shi ya ce mu shiga na bi umarnin shi yana tashinta yana gaya mini, “Bari mu je mu ci abinci tun da ba mu je gida da wuri ba, balle ki yi mana girki.”

Na ce mishi to. Muna tafiya cikin tafiyar ya danna mana faifan da ke cikin rediyan motar tashin muryar Maria kelly ce ta soma tashi cikin wakarta mai taken Always be mine baby! Chines Restaurant ya kai mu sai da muka ci muka sha, sannan muka yi wa su Umma take away din abin da muka cin muka kawo musu.

Tun daga rannan yaya Almu ya shiga saya mini dogayen riguna masu matukar kyau, kan ka ce me ye wannan sai suka zamo sune suturar da nake amfani da ita na maida kwalliyar hijab ita ce kwalliya mafi daraja a wurina.

<< Wace Ce Ni? 8Wace Ce Ni? 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×