Gaba na ne yayi wata irin faɗuwa cikin kaɗuwa nace" Anty zan wuce?.."
Sheƙeƙe ta dube ni, cikin isa tace" yau a'i ba ranar makaranta bace, ki wuce kije abinda kika saba hutun ya isa haka.."
Cikin rashin fahimta nace" Anty me kenan? ai babu wani hutu da nayi.."
Cikin sanyi nayi maganar..
" ehh lallai, abunda kika saba shi zakiyi, yau bazaki je makaranta ba maza shige ki cire kayan nan..." ta ƙarke maganar da turani ɗaki da ƙarfi, har sai da na faɗi cikin hawaye na ƙwaɓe kayan zuciya na tafasa, a. . .