Skip to content
Part 1 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Gabatarwa

Wannan littafin shine littafina na farko dana fara rubutawa,labarin Yadda Kaddara Ta So, labarine wanda ya kunshi kirkira (fiction), ina kira ga duk wanda zai karanta wannan littafi, da ya yi hakuri idan har ya ci karo da wata hallaya ko ɗabi’a wadda ta yi kama da tasa. Na rubuta labarin ne akan rayuwar mutane hudu, Tafida, Maryam,  Henna da kuma Hanan, ban ce na kware akan rubutu ba, wannan ne karo na farko dana fara, amma ina fatan zai kayatar ya kuma nishadantar, haɗibda ilmantarwa. A wasu lokutan kaddara na faruwa a yadda ta so ba ayyada ɗan adam yaso ba, a waɗansu lokutan kuma takan farune a yadda muka so, kuma mukan sowa kanmu abbu ya kasance ba alkairi bane a garemu, sannan mukan ƙi abu ya kasance shine mafi alkari garemu, kamar de kullum Allah na nasa bawama na nasa, amma na Allah shine gaskiya, kuma Yadda Kaddara Ta So, hakane zai kasance, ku biyo ni cikin wannan littafin, domin jin YADDA ƘADDARA TA SO da TAFIDA, MARYAM, UCHENNA DA HANAM. Ina mika ginjina zuwa ga ba.

ST NICHOLAS HOSPITAL, LAGOS NIGERIA

“Wai ina dr. ESHAAN din ?” Wani likita da ake kira da Dr. Ola ya tambayi nurses din dake bakin aiki, yayin da ya fito daga dakin da aka kwantar da wani mara lafiya da aka kawo musu asibitin, nurse chinaza ce ta ce. “ Sir Saturday, Dr. baya zuwa ranar weekend”  “Ai nasan da hakan, amma dole ne ya zo, aikine na ceton rai, dan haka ku kirashi yazo da gaggawa”  “Ok Dr Joke ta faɗi tana juyawa, hanyar office dinsu ta nufa dan wayarta tana can  “ah-ah joke to where ?” Joke ta tsaya tana kallon Dr. Khabir babban Abokin Dr. Eshaan  “offce namu zanje na ɗauko wayana, zan kira TAFIDA ne”  “Wani abun ne ya faru ?”

Ta gyada kai “ eh an kawo wani pertinent ne kuma ana bukatarsa”  “ok jeki kawai bari na kira shi”  “ok” Ta juya zuwa inda ta fito, shi kuma khabir ya fito da wayarsa daga cikin aljihun lap coat din dake jikinsa ya nemo lambar TAFIDA a jerin contact din dake wayarsa ya aika masa da kira.

ALARO CITY LEKKI, LAGOS, NIGERIA

Alaro city wani haddaden estate ne wanda za’a iya kira da gari, rukunin gidajene masu kyau, tsarin ginin gidajen kamar a kasar turai, kuma a kowani block tsarin gudajensu iri daya ne, sunada masallaci da church, super market, filin wassani,bpolytechnic, asibiti, makaranta duka a ciki.

*****

Sanye yake da Jersey irinta cricket, green color a bayan rigar an rubuta ‘TAFEEDAH’, wandon Jersey din ne a jikinsa wanda ya sauka har kasa shima kuma green ne, anyi layin fari a gefen wandon, guwar kafarsa sanye cikin abun kariya da ƴan cricket ke sakawa a kafarsu ( batting pad), hannunsa sanye da safar hannu irin ta yan cricket, kansa sanye da helmet na cricket, hannunsa rik’e da cricket bat (sandar cricket).

Ya ɗau matsayarsa, yana jiran lokacin da zai cillo masa ƙwallon, aiko yana cillowa ya takarkara ya daki kwallon da duka karfin da allah ya hallita masa shi, ƙwallon ta tashi sama, kowa ya daga kai yana jiran yaga inda zata sauka, bata tashi sauka ba sai a ketaran layin da aka shata, aiko ƴan team dinsu suka saka ihu sukayi kansa suna kiran sunan sa, dama sun sani idan har wasa da TAFIDAH ne basu da haufi, yana murmushi ya cire helmet din dake kansa, ai nahin surar fuskarsa ta bayyana.

Dogo ne sosai, kuma fari, fari ba irin na Africans ba, fari irin na asalin Indians, ga sumar kansa irin ta asalinsa wato india, ta kwanta a kansa lif, cikin askin high fade, ga kuma razor part a gefe, ga wani bakin kwataccen gashi daya sauko tun daga sajensa ya had’e da wanda yake habarsa ya kuma zagaye bakinsa, kammanin fuskarsa sune suke tabbatar da asalinsa na ba’indiye. Kwatanta irin kyan da yake dashima b’ata lokacine, irinsa ake kira da end of discussion, wani irin kyau gareshi me ban mamaki, me kuma daukar hankalin me kallonsa, kwayar idonsa tafi komai jan hankali a fuskartasa, wadda ta kasan ce light blue color ce.

*****

Tsaye yake a inda ya aje cricket kit bag dinsa, yana saka kayan cricket din nasa a ciki, helmet itace a bu na karshe da yasaka a cikin jakar, sannan yayi zipping jakar.

Hannu ya kai ya bide karamin aljihun jakar inda ya aje wayarsa da kuma p-cap ɗin daya yazo da ita, p-cap ɗin wadda aka rubuta TAFIDAH a samanta ya saka a kansa sannan ya buɗe wayar tasa, missed calls ya gani daga Khabir, hakan ke nuna masa cewa akwai wani abun dake faruwa a asibiti, wayar ya saka a aljihun wandon dake jikinsa, sannan ya sab’a jakar a bayansa.

Sannan ya kama hanyar fita daga wajen wassanin, cikin da takunsa na kasaita da izza da kuma aji, wanda yake nuna cewa shid’in jinin sarauta ne, duk da bayasan hakan, amma sarautar a jininsa take, ko ina yabi idan da mutane sai sun ɗaga masa hannu shima kuma ya ɗaga, dan ba wani sosai ya cika magana ba, amma kuma yanada kirki, kuma kowa ya sanshi a wajen.

Kasan cewar filin wassanin da gidansa babu nisa hakan yasa yake zuwa a kafa, ko ina a estate din shimfide yake da kwalta, dan haka ya bi titin da zai sada shi da gidansa, ko ina ya wuce idan da ƴan mata sai sun ƙyasa, dan Tafida irin mutanannane wanda ba kowace budurwa bace zata ganshi ta kauda kai ba, Allah ya masa farin jinin ƴan mata, tafiyarsa ma kawai abar kallo ce.

Da haka ya karaso kofar gidan nasa wanda yake sak iri daya da sauran gidajen dake block ɗinsu, daga jikin gate din kuma akwai wani siririn allo da aka rubuta ‘DR. ESHAAN AUWAL TAFIDA, B3 NO 122’.

Hannunsa na dama ya ɗago wanda yake sanye da digital watch, daga saman agogon kuma a kwai wani stamped bracelet, me dauke da rubutun ‘TAFIDAH’.

Aagogon ya dan daddana nan take gate din ya zuge zuwa gefe, kai ya saka cikin kyakyawan gidan nasa, yana shiga gate ɗin ya kulle, ginin benine mai hawa daya, daga gefen ginin kuma glass ne tun daga sama har kasa, tun daga waje idan ka kalli saman gidan zakaga kujerun dake laye a saman rufin gidan, a parking lot din gidan kuma motoci uku ne, Audi RSQ 8-R, Honda elevate da kuma marsidis Benz.

Ƙofar entrance din ya bude ya shiga ciki, babban falone a farkon kofar, wanda yake dauke da set din ɗima-ɗiman kujeru, wata kofar glass ce ke facing din kofar shigowar, wadda zata sada mutum da garden din gidan, wanda kuma yake a backyard din gidan, stairs din da zai kai mutum sama kuma yana cikin falon, daga kasa idan ka daga kanka zaka iya hango ƙofofin dakunan gidan, domin corridor din dake kunshe da dakunan a ba katanga bace, glass ne aka saka kuma shima gajere, ƙofofu hudune a parlon, wadda suka kunshi kitchen, dakin guga, gym, sai store amma ba na kayan abinci ba, na aje kayan amfanin gida.

Stairs ya fara takawa wanda zai kaishi zuwa dakinsa, wanda yafi kowani ɗaki cikin dakuna uku dake gidan girma, komai na cikin dakin dark an light blue ne, sai kuma fari tun daga kan bad sheet, blanket, pillows, curtains, carpet harda set din kujerun dake dakin da dai sauransu.

Cricket kit bag din bayansa ya sauke ya ajeta a inda ya saba ajewa, ya cire wayarsa daga aljihu ya dora akan gado, ya karasa inda dayar wayar tasa take chargy ya zare chargyn ganin ta cika ya ajeta itama a inda ya aje dayar.

Ya dawo gaban dressing mirror ya cire agogon dake ɗaure a haannunsa ya aje a kan table din, ya cire p-cap din dake kansa ya ratayeta a jikin hat stand din dake kusa da dressing mirror din,Sannan ya shiga wanka.

Bayan wani lokaci ya fito daure da towel, yana goge jikinsa da wani towel din, a gaban dressing mirror din ya tsaya ya jona hand dryer ya shiga busar da sumar kansa, saida ruwan dake jikin sumar ya tsane sannan ya dauko hair straightener dinsa ya shiga taje gashin nasa, sannan ya dauko man daya saba shafawa sumar tasa ya shafa nan take ta soma kyalli, ya gyaggyara zaman gashin dake takiyar kan nasa, dan a gefe da gefen kan nasa da kuma baya babu sumar sosai, an asketa sbd askin high fade din da yayi.

Jikin faffaɗar lokarsa ya koma, wadda ta kusa cinye fadin katangar da take jiki, ya bude kofa daya, saida yayi taku daya biyu kafin ya isa shiga cikin wardrobe di, dan lokar ƴar bangoce, kuma kamar closet, manyan kaya ya zabo wani plane yadi golden color, ya saka a jikinsa ya fito daga wajen hannunsa rike da hula tangaran, yana gyara karin hular.

Saida yazo gaban mirror ya saka hular a kansa sannan ya feshi jikinsa da turare, ya dawo wajen shelve din dayake aje takalmansa ya dauko wani bakin moccasin ya saka a kafarsa, sannan ya juyo ya dauki wayoyin nasa a inda ya ajesu, ya dauki keyn daya daga cikin motocinsa ya fito, benz ɗinsa ya shiga ya wuce ST NICHOLAS HOSPITAL.

A babbar rumfar da a samanta aka rubuta Dr. ESHAAN AUWAL TAFIDA yayi parking, ya fito yana ta gaisawa da ma’aikatan dayake haduwa da su, har ya kai office ɗinsa, kuma tun kafin ya shiga cikin office ɗin nasa yaci karo da khabir, hannu ya bashi sukayi musabihi suna gaisawa sannan ya ce,

“Ai na kira ka ba ka d’auka ba, kuma dama nasan kana filin cricket”

“Sai da muka gama wasan naga kiran naka ai, shine na shirya na taho” Yayi maganar cikin yaran hausa, wadda ba zaka taba tunanin yasan hausarbama ballantana ya iyata, ga kuma suturar dake jikinsa, wadda take kara dangantashi da hausawan “me ke faruwa ?” Ya faɗi cikin muryarsa ma abociyar kamewa da nutsuwa me taushi da kuma zurfi “wai wani mara lafiya ne aka kawo shi, kuma ana bukatarka, shine Dr. Ola yace a kira ka” “Ok to muje na ganshi”.

Daga haka suka wuce inda aka kwantar da mara lafiyar, dubashi yayi yaga kuma matsalar tasa tana bukatar tiyata, dan haka ba b’ata lokaci suka shiga dakin tiyatar dashi.

Cikin nasara akayi aikin aka gama, ya fito yana bawa nurse bayanan magungunan da ya kamata a bawa mara lafiyar, office dinsa ya shiga, daga nan ya zarce banɗaki.

Hannunsa ya shiga wankewa a gaban sink, bayan ya gama kamar da akace kalli mirror idansa yakai wajen, gabansa ne yayi mummunar faɗuwa, sbd abinda ya gani, hankalinsa yakai kololuwa wajen tashi, a dugun zume yayi gaban mirrorn yana dudduba fuskar tasa, ƙwayar idansa wadda take light blue itace ta rikiɗe ta koma ja, wannan abun ba baƙo bane a wajensa, amma kuma a kwanakin nan abun ya fara yawa, a da sai yayi wata nawa abun bai tashi ba, amma yanzu kusan kullum sai ya tashi, yanzu har takaima idan nasa na sauya kala ba tareda yaji a jikinsa ba, hannu yakai ya riƙe kansa tareda lumshe idanunsa, addu’a yake san yayi amma bakinsa yayi masa nauyi kamar kullum, yasani dole abun nasa ne zai tashi, haka ya bude idonsa ya ƙarasa ya fita waje, da hannunsa yayi nuni ga inda wayoyinsa suke nan take suka tashi suna yawo a iska har suka karaso kan hannun nasa, da kyar ya samu ya fice daga asibitin, kuma yanata jugewa hada ido da kowa, dan kada wani ya samu yaga kalar idon nasa.

Cikin motarsa ya shiga, ya sakata a lock, ya dafe kansa a jikin sitiyari, yanajin abinda ya saba ji a duk lokacin da abun zai tashi, bayan wani lokaci ya dago da kan nasa, ya fita hayyacinsa gaba daya, kwayar idanun nasa ta ƙara komawa ja, bakinsa ya buɗe nan take wasu dogayen fiƙoƙi suka sauko daga haƙwaransa na sama, ya rikiɗa ya koma dodo, me ban tsoro, gaba daya jikinsa rawa yake, sai ya fara fisge-fisge, yana barazanar kifar da motar, wannan shine halin dayake tsintar kansa a ciki a wasu lokutan.

BINYAMINU USMAN POLYTECHNIC, HA’DEJIA, JIGAWA STATE NIGERIA

Wasu ƴan matane guda biyu tafe akan titin fita daga makarantar, yanayin tafiyar sune kadai zai nuna maka cewa a gajiye suke gaba ɗaya.

Ɗaya bakace sanye da atamafa da kuma mayafi, yayin da ɗayar ta kasance fara amma ba sosai ba, sanye take da hijabi har kasa, wanda ya ‘boye atamfar dake jikinta. Wadda ke sanye da mayafin ta buga tsaki tana faɗin “aikin banza, wallahi buzuwa bai sanni bane, shiyasa yakemin abinda ransa ke so, amma bari yazo sai na masa wankin babban bargo, yanzu haka shashanci ya tafi da motar, ni ya barni nan ina fama da rana”

Wadda ke sanye da hijjabin ta kalleta, yayin da suke ci gaba da tafiyar, dan har suna hango gate din fita daga makarantar “ke kuma wallahi Badar baki da hakuri, dan allah ki dinga shan ragowar ruwan alwalar yamma” Badar ta kuma yin ƙwafa.

“Ai ni Maryam ba zan iya da wannna halin naki ba, ke baki san mutanen yanzu idan baka ci uban su ba bazaka zauna lafiya ba” “Ki de dinga haƙuri”

Maryam ta faɗi tana dubanta, basu kai da ƙarasawa gate din ba sai ga motar da ake zuwa daukan Badar din ta shawo kwana, Badar na ganinsa tayi ƙwafa.

Tun kan ya karaso yasan cewa dama yau ya shiga tara, dan Badar ba zata kyale shi ba, wata ƙila yau yayi ta aikinsa dan yaya abokinsa ya biyewa har suka ɗauki wasu ƴan mata a motar, sa’arsa ɗaya akwai Maryam, yasan zata tausheta, a gabansu yayi parking, Badar ce ta fara bude kofar motar a fusace ta shiga, sannan Maryam ta zagaya ta ɗayan bangaren ta shiga itama, aiko bai shaba saida Badar tai masa tass, kuma wai duk da hakan ma Maryam ɗin na bata haƙuri.

Da haka har suka ƙaraso unguwarsu wato unguwar garko, a bakin wani lungu suka tsaya Maryam ta sauka

“Zaki zo an jima ne ?”

Badar ta tambaya “ wata ƙila ki ganni, amma bande sani ba ko wani aikin zai riƙeni”

“Dan Allah ki zo fulanys kitchen fa ta saki wasu sabbabin recipes ɗin”

“Gaskiya Badar kinci amana, wannan ai cin amana ne, taya zakiyi tiktok baki faɗamin ba?”

“Ke wallahi jiya da daddarene nayi, amma ai nayi saving vedios ɗin, idan kinzo sai na nuna miki”

“Amma ai ɗazu baki faɗamin ba”

“Ke mantawa nayi amma idan kin zo zan nuna miki”

“To sai na zo ɗin”

Ta faɗi tana rufe musu kofar, buzuwa yaja motar sukayi gaba, dan ita gidan kakar Badar ɗin a gaba yake, dan a gidan kakarta take da zama, iyayenta kuma suna kano, itace kaɗai ta dawo hadejia tun tana karama, kuma tun suna yara suke kawance da Maryam, duk da ita mahaifin Maryam ba wani kuɗi gareshi ba sa’banin mahaifin Badarriya wanda ya kasance me dukiya.

Maryam tayi ta shiga cikin layin nasu wanda yake dauke da kwatanni, har ta kawo kofar gidansu sannan ta sa kai, da sallama a bakinta ta shiga mahaifiyarta ce ta amsa mata “ah-ah har kin dawo ?”

“Kai Maamu, yanzun ne har ? Na jima fa”

Haka suke kiran mahaifiyar tasu, da mamanmu suke ce mata, bayan haihuwar ƙannentane suke cemata maanmu, dan basu iya kiran sunan ba, shiyasa suma suka koma cewa maanmun, gaba ɗaya yaran gidan biyar ne, babbar yayarsu fati wadda aka mata aure shekara huɗu baya, tanada yaronta guda ɗaya, sai ita Maryam ɗin, bayanta kuma sai kannenta ƴan biyu hassan da hussain, sai kuma auta Muhsin.

Maryam ta cire hijjabin dake jikinta ta rataye a jikin igiyar shanyarsu a lokacin maanmu ke cewa “ai ni gani nayi kunyi sauri wallahi”

Ta faɗi tana gyara wake a cikin wani farantin silver, Maryam ta shiga ɗakin dake a mazaunin nata a gidan, bayan auren yayarta fati, dan da su biyu suke kwana a ɗakin, jakar data saba zuwa makaranta da ita ta aje akan yar karamar katifarta, wadda take ɗame da bed sheet, ko ina a ɗakin tsaf, duk da ba wasu kayan tarkace a ciki, domin jakarta ta kayace kawai sai dan abinda ba a rasa ba, da wasu littatafan ta na makaranta da dai sauransu, wayarta kirar huawei 6A irin london use din nance,wadda screen gard dinta ya faffashe ta saka a chargy, Badarce ta bata ita lolacin da babanta zai saiya mata wata wayar.

Ƙaramin hijjabin data saba sakawa idan tana gida ta dauko ta saka sannan ta fito waje, kujera ƴar tsugunno ta janyo ta zauna a rumfa tana karbar tray ɗin dake hannun maanmu tareda faɗin “ina auta ne ?”

Ta tambaya ganin bataji ko motsinsa ba a gidan “baki ganshi a waje ba ?, wai yashi aka kawo a gidan malam isa za’ayi gyara shine su khalil suka zo suka ja shi ya fita” Maryam tayi dariya tana watsar da dattin data tsinto a cikin waken “auta kenan”

“Kin yi sallah ne ?”

“Eh mun je hostel mun yi”.

Tun daga bakin kofa suke jiyowa hayaniyar hassan da hussain, sai gasu sun shigo gidan da sallama, maanmu da Maryam suka kallesu a tare, a fuska kammaninsu daya, amma a hallaye kam sun Bambanta sosai “masha allahu, ka ce yau dai ba zamu yi asarar cefane ba, tunda ke za ki yi girki yau” Hussain ya faɗi cikin zolaya, dan shi dama akwaishi da zolaya da kuma sakin fuska, ba kamar hassan ba “wato ni idan ni nayi kenan asara kuke ?” Hussain ya nemi kujera ya zauna shima, Hassan kam dakinsu ya shige “ni fa bance ba Maanmu, kawaide nasan idan dai ya ya ce zata yi girki a gidan nan to ba mu da haufi”

Maryam tayi musu dariya, dan idan da sabo sun saba wannan faɗan nasu “Ince dai ko kunyi sallah?”

“Haba Maanmu sai ka ce wasu su Muhsin, tun tuni ai muka yi sallah”

“Aa hussain ba haka ba ne, ya kamata na riƙa tambaya sbd halin zamani” “Hakane kam, ina wannan abun?”

“Ka ji walaƙanci irin na hussain, yanzu autan ne wannan abun ? Sai kace wani kayan wanki ?”

Maryam ta faɗi tana dubansa “ah wannan abun mana, wannan yaron himmm”

“Yana waje akan yashin gidan malam isah, ni je ka kaɗo min shi ma, nasan ana jimawa zaka fara jin ana doke-doke, wasa ya koma faɗa, daga haka kuma sai iyayen ƴaƴa su fara fitowa har faɗan ya koma na iyaye”

“Yalo ne dama na siyo masa, bari naje na kaɗo keyarsa” cewar hussain yana miƙewa tsaye “saura kuma ka dokar min shi” “ai wannan shine dole maanmu, sai na moreshi” hussain ya faɗi yayinda ya kai bakin kofa “kai allah shirya mana”. Maryam na dariya ta mike da trayn a hannunta.

Wata yarinya ce ta yi sallama hakan yasa su kallon kofa a tare “Anti Maryam wai inji lawusa zata kawo kayan haɗinta kayi mata miti fayif” Maryam tayi murmushi, bata san sanda ƴan area ɗinsu zasu waye ba, wai miti fayif “ki je ki ce mata yaushe zan mata ?”

“To”

Yarinyar ta faɗi tana ficewa da ɗan tsallenta, Maryam ta karasa zuwa rumfar da sukeyin girki, ta aje tray din waken a gefe ta shiga kiciniyar hura wuta, kukan muhsin taji yana dosowa kofar gidan, ya shigo hannunsa a akan idonsa, gaba daya kayan jikinsa a turbuɗe da yashi, hatta da kansa ya baci da yashin, takalminsa a hannu ya shigo ya faɗa kan maanmu, hussain na biye dashi a baya, shi kuma yana shigowa yayi wuf ya faɗa ɗakinsu, dan kar maanmu tai masa faɗa akan dukar mata auta da yayi “yi hakuri me sunan Baba, Ya Hussain bai kyauta ba, ga yalon daya kawo maka”. Da kyar maanmu ta samu ta lallashi autan nata, dan dama ko ba’a taba shi ba ya iya kukan rigima, ina kuma ga an tabo shi.

Maryam ta girgiza kai tana ci gaba da aikinta, rayuwar gidansu na mata daɗi, duk da basu dashi amma suna cikin farin ciki, kuma haka halin mahaifinsu bai hanasu jin daɗin rayuwa ba.

Yadda Kaddara Ta So 2 >>

2 thoughts on “Yadda Kaddara Ta So 1”

    1. Idan kin shigo app/website din a sama ta dama akwai icon na mutum, ki taba icon din zai kai ki wajen login. A wurin login din, za ki saka email na ki ne ko username sannan sukuma da password sai ki latsa inda aka ce, ‘Log In’.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×