Skip to content
Part 18 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Maryam Pov.

Da misalin 04:30pm.

Maryam ta fito daga ɗakinta, kamar kullum sanye cikin hijabi har ƙasa, ƙasa ta sauƙo hannunta riƙe da wayarta, yau ta samu ta siyi credit ta saka, kuma ba credit kaɗai ta siya ba ta siyo abubuwa da dama da kuɗin da Tafida ya bata.

Yanzu haka zuwa za ta yi ta jere kayan da ta siyo ɗin, dan bata jima da dawo daga makarantar ba, dan a ƙafa ta taho sbd babu nisa, kuma a yau ɗinma har ta yi ƙawaye biyu, wanda suka kasance hausawa kamarta, Dan yawancin yan makarantar yarabawa da igbo ne, sai fararen fata, kuma ƙawayen nata sun faɗa mata su suna block 4 ne.

Yanzun ma sallah ta yi shine ta fito, so take ta je ta gama gyara kayan sai tayi girki dan yau girkin ma na musamman za ta yi, sai kuma ta zo ta zauna ta siyi data ta ɗan hau tiktok ta duba sabbabin recipes.

Ta kuma kira Anti Fati da Badar, dan tun ranar da tazo garin da suka yi waya da Anti Fati basu ƙara ba, kuma tayi mamaki da har yanzu Badar ba ta kirata ba.

Amma dai koma miye yau zata kirata, Dan tana soma ta kaiwa Maanmu su gaisa, ta ji ya suke.

Hannu takai ta kama handle ɗin ƙofar kitchen ɗin, ta murɗa sannan ta tura ƙofar, ledojin data aje akan kitchen islan ɗin suna nan, ledojin da suka gajiyar da ita, dan suna da nauyi ga yawa amma haka ta riƙo su niƙi-niƙi ta taho, dan ta shiga super market ɗin da ya faɗa mata.

Switch ta kukkuna ta ƙara hasken fitilun kitchen ɗin, daga wajen glass ɗin dake wajen stove ta kalli yanda neon strip light ɗin nan suka fara haske, wajen na matukar burgeta musamman ma da daddare ta yanda take hangosu ta saman balcony ɗin ɗakinta, kyanta ace ta zauna a wajen tana shan iska da daddare, amma tsoranta ba zai bari ta zauna a wajen ita ɗaya ba.

Ledojin ta shiga bubbuɗewa, sai da ta cire komai gabaɗaya, wani kitchen trolly na ƙarfe data siyo ta fara haɗawa wanda take so ta fara jera kayan miya a kai.

A kusa da ƙofar baya ta aje shi ta, ɗebo sauran kayan miyanta dake cikin fridge ta jere akan trolly ɗin, hakama sauran su doya dankalin da suka rage.

Sannan sauran abubuwan da ta siyo irin su jan nama, naman kaza, nutella, fruits, yoghurt, butter duka ta saka a fridge.

Su chocolate, cookies, choco pie, oreo da sauran kayan kwaɗayi da ta siyo kuma ta ciresu a ledojinsu ta saka a wasu containers na glass, tana saka biscuits ɗin oreo tayi murmushi data tuna da Auta.

Ta ɗebi kayan da ta siyo na bukatar kanta ta kai ɗaki, sannan ta dawo ta kwashe sauran kayan da suka rage.

Ta yanke cewar zata gwada dafa masa abincin al’adarsa yau, saboda ta nuna masa jin daɗinta akan abunda ya mata tunda baya san godiyar.

Dan haka ta yi niyyar dafa masa chicken biryani, bata tab’a girkawa ba, amma saboda shi zata gwada kuma tana fatan yayi daɗi.

Bata gama girkin ba sai kusan shida, ita ba iya cin abincinsu za ta yi ba dan haka ta zubawa taliyar rice stick ɗiinta ruwan zafi.

Ta yanka jan nama ta dora a wuta, sannan ta yanka albasa, sosage, red paper, green bell pepper sannan ta soya ƙwai ta haɗasu gu ɗaya ta saka seasoning.

Kafin ta kawo naman data tafasa ta haɗa sannan Kuma ta ɗauko taliyar data zubawa ruwan zafi ta zuba, ta saka soy sauce, ta jujjuya, sannan ta juyeta a warmer dan ba zata ci yanzu ba.

Sai tayo sallar magariba dan an kusa ƙira, dan haka ta ɗebi kayan data girka masa ta aje a kan island dan yau da kanta take san ta zuba masa abincin.

Ta ɗauki wayarta ta nufi dakinta. Tana sallah taji sanda ya dawo, bai nemeta ba dan haka bayan ta idar ta ɗauki wayarta ta siyi data, sannan ta kira Anti Fati, suka gaisa ta tambayeta ya gida ta amsa mata da kowa yana lafiya.

“Badar fa ta koma kano”

“Wai da gaske ?”

“Wallahi ta koma gida, cewa tayi babu Maryam a Haɗejia me zata zauna tayi”

“Allah sarki kaunata, zan ƙira ta ai”

“Ke yanzu bata da waya, a bikinki aka sace mata”

“Me? Tab ”

Ta tuna yadda Badar take ji da wayarta, kai mutane basu da kirki, yanzu a ɗan wannan taron da a kayi har aka samu zarafin zacewa mutum abunsa.

Daga nan suka ɗan tab’a hira kaɗan, daga bisani Maryam ɗin ta mata sallama, Anti Fati ta rufe da cewa.

“Dama Maanmu tace idan kin kira na faɗa miki ki ta ya ta da godiya kan abinda Tafida ya yi wa su Hussain”

Girar Maryam ta haɗe waje guda alamun mamaki.

“Su Hussaini kuma? Me ya musu ?”

Tana iya jiyo sautin murmushin Anti Fati daga wayar ga kuma hayaniyar lulu ƙasa-ƙasa.

“Bawan Allah kenan, ashe ma bai faɗa miki ba, to mijinki dai su Hussain yasa aka kira masa ya yambayi ko wannensu wani aiki yake so, dan yace aikin gareji bai dace dasu ba, Hussain yace shagon PS 5 yake so, shi kuma Hassan yace jari yake so zai fara sai da wayoyi, yanzu dai haka zancen da nake miki ya buɗe musu shaguna kusa da kusa, shi Hussain na PS5, Hassan kuma ya cika masa shago da wayoyi da su covers, kayan dai harkar waya, ai in faɗa miki shagon Hussain yafi kyau, inda kika san a waje, kinga shagon ne ?”

Kamar wata sokuwa haka Maryama ta girgiza mata kai, itama Anti Fati kamar me jiran girgiza kan nata ta ci gaba.

“Wallahi shagon ya haɗu, a taya mu godiya”

“To zan faɗa masa”

Kuma daga haka wayar ta ƙare, Maryama ta yi shiru ta na jujjuya abun a ranta, wai ita kam wa take aure ne ?  Ta kasa ganewa kan wannan bawan Allahn.

Sauƙa tayi daga kan gadon da take zaune tayi sujudi shukr, sannan ta ƙara godewa Allah a bayyane, dan sai da godiya, Allah ya gama mata komai.

Kalaman ɗazu ne suka dawo mata a rai, dan haka ta koma inda ta bar wayarta ta ɗauka, ta shiga Google ta rubuta ‘ Meri aakho ka taara hai tu’.

are the star of m’You y eyes’.

Itace amsar data samu, Maryam ta kusa kaiwa ƙasa dan daɗi, kenan yana nufin tana da muhimanci a rayuwarsa haka?

“Oh Allah”

Ta furta a bayyane, murmushi kwance a kan fuskarta, kuma har yanzu tana kallon wayar, ita kuwa me za ta yi dan ta sakawa wannan bawan Allahn.

Da sauri ta aje wayar ta fita, bata samu kowa a ƙasa ba dan haka kanta tsaye ta wuce kitchen. Abun da idonta ya fara arba da shi shine.

Tafida tsaye a jikin fridge yana shan ruwa a roba, shima jin an buɗo ƙofar yasa ya juyo hannunsa riƙe da gorar ruwan. Kallonsa kawai take, tana jin wani abu na yawatawa a kanta, ji take kamar taje ta rungumeshi ta faɗa masa cewar ta gode, amma ba zata iya hakan ba sam. Faɗa kawai take.

“Sannu da dawowa”

Da kai ya amsa mata yana ci gaba da shan ruwan.

“Ka ci abincin ne ? Naga kana shan ruwa”

Ta faɗi tana ƙarasa shigowa cikin kitchen ɗin, sai ya juyo ya kalli warmers ɗin.

“Da naga ba ki ajemin akan danning ɗin ba, shi yasa nayi zaton baki girka komai ba”

“Baka duba wanna ba?”

“Ummm”

“To ai shine abincin naka”

Ya ɗan cije leb’ensa yana me da gorar cikin fridge ɗin, ya rufe fridge ɗin nasu me ƙofa biyu, sannan ya juyo ya kalleta.

“A ina kika siyo kayan nan ?”

Ya tambaya ne dan yaga kayan da ba shi ya siyo ba a cikin fridge ɗin, kuma dama so yake ya sha ruwa sai ya buɗe warmers ɗin, dan ya san nasa ne, ƙishin ruwan yafi ji shi yasa. Tana ɗaukowa plate da ta bashi amsa

“Ɗazu a super market ɗin nan”

“But ai wannan na kayan buƙatar ki ne na makaranta”

Ta juyo tana aje plate da ɗin akan island ɗian sannan muryarta ta fito ba tare da ta kalleshi ba.

“Na sani, kawai ina buƙatar kayan ne, kuma kuɗin yamin yawa shi yasa na siya”

Ya ƙaraso inda take tsaye, hakan yasa ta tsaya da ƙoƙarin buɗe warmers ɗin da take shirin yi, gabanta ya shiga bugu, ashe da gaibu take, da tace zata iya rungumeshi, wasa ne kawai, a yanzu da yake tsaye a gabanta ma ta kasa ƙwaƙwaran tunani, ina kuma ga ace tana cikin jikinsa ne, sai yanzu ta kalleshi da kyau.

T-shirt ce a jikinsa, da sweat pants wanda ya bayyana baƙin zaren dake ɗaure a ƙafarsa ta dama, sai crocs sanye a kafarsa, gashin kansa na gaba kwance a goshinsa, duk da yana kawai hannu ya kawar time to time.

“Last time na faɗa miki cewar if you need anything, just talk to me, zan bawa Devid ya kawo miki, anything Miriam, i mean anything”

Da ƙyar Maryam ta gyaɗa kanta, ta san Devid shine drivernsa, drivern da baya tuƙa shi a mota sai dai aike. Ya lumshe idanuwansa yana sauraron bugun zuciyarta, wani abu da a yanzu ya zame masa rabin jiki, da baya iya sukuni idan bai ji shi ba.

Ƙamshin spices ne ya daki hancinsa, irin spices ɗin da yasan a girki ɗaya ake saka irinsa, biryani, dan haka ya buɗe idonsa dan yaga shin ita ɗince Daaso ta dafa masa ? Ko dai ta saka ne a wani girkin daban.

Sai ya ga kuwa ita ɗince, sai da ya haɗiyi wani yawu, shida yaci biryani sai idan yaje india, da akwai wani restaurant ɗin indians da yake zuwa yaci a can, amma yanzu me wajen ya rufe, hakan tasa ya daɗe baici ba.

Kuma shi ba wani samun time ɗin dafata yake ba. Ya dawo da dubansa kan Maryam, me yasa take da nasarar yin duk abinda yake so ne ? Hai fagban’ (Oh god).

Ya faɗi bayan a zuciyarsa, yana kallo har ta zuba masa a cikin plate. Ya kalli abincin sosai, biryanin ta ji kwai ta ji kaza.

Kamar yanda yake sonta, sai yake jin kamar yana india ne, Daadi tayi masa ta saka shi a gaba tana faɗin maza cinye Eshaan, kuma kamar yana Abuja gidan kawunsa Imran Neha ta dafo masa tana faɗin sai ka cinye tas Bhai.

A hankali yaja kujerar island ɗin ya zauna, yaja plate ɗin gabansa, kawai sai ya tsura musu ido yana kallo, kamar me nazarinsa, to ita wai a inama ta iya girki haka ?.

Maryam ta ɗebe sauran kayan data b’ata ta saka a dish washer, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko masa milk shake ɗin da tayi ta zuba a cikin wata jar. ta aje masa a gabansa, sai taga har yanzu bai fara cin abincin ba, ya saka a gaba yana kallo, kamar me san gano inda tayi kuskere.

“Baka so ne ?”

Ya juyo ya kalleta, sai kuma ya kalli milk shake ɗin nan.

“No ba so ne ba nayi ba, biryani is among my favorite food, kawai dai tambayar ki nake san nayi tun kafin na fara cin abincin, dan kar ki ce santi nake”.

Dariya ta so kwacewa Maryam, amma kawai sai ta yi murmushi.

“Ina jinka”

“A ina kika koyi girki ?”

Yanzu kam dariya ta ɗan yi, shi kuma bai tab’a ganin dariyarta ba sai yau, sai ya kafeta da ido yana sauraren bugun zuciyarta wanda yake bugawa cikin nishaɗi.

“Maanmu ce ta koya min, kuma ina ƙara sanin sabbabin girke-girke through social media, more especially tiktok da instar”

Ya gyaɗa kai yana jan plate ɗin gabansa.

“Me zai hana ki zama food blogger, tun da kinga course ɗinki na makaranta ma na yan tuwo ne”

“Inji wa ?”

“Inji Eshaan”

Yanzu ma murmushin ta yi, a ranta take faɗin ashe yana magana haka.

“Haka mutane suke cewa wai home and rural economic na ƴan tuwo ne, amma ba haka ba ne, sana’o’i da dama ake koyarwa, kamar calabash decoration, tie and dye, fishing, farming ga kuma shi kansa girkin da dai sauransu”.

Ya gyaɗa kai yana kai loma wajen ta uku, dan shi baiji wani banbanci da na indian ba, kamar Neha ko Daadi ne suka dafa.

“Back to our business, ki zama food blogger, ina ga wasuma zasu ƙaru da abinda kike”

Ta gyaɗa kanta ita ma, sun tab’a maganar ita da Badar, amma a lokacin dariya kawai ta yi mata, bata bawa abun muhimanci ba.

“Amma fa ba zaki nuna fuskarki ba, babu muryar ki kuma duk abinda zaki faɗi saide ki rubuta, waƙoƙi koma dai wani abun dabam zaki ɗora a kai”.

Mamaki ya kusa kama Maryam, wai kishinta yake ? Dama ita takai namiji kamar Tafida ya yi kishint?

To yanzu kawai tana tafiya a hanya ta haɗu da wani ta nuna masa Tafida tace shine mijinta ta tabbatar da dariya zai mata, dan ko kaɗan basu dace ba, Tafida irin mazan nan ne da ba’a ganin irinsu sai a film ɗin india, na film ɗinma idan har ya kasance director ɗin ya zab’o kyakyawa a matsayin actorn.

“Yaushe zaki fara ?”

“Ummm duk time ɗin da zanyi girkin gida”

“Wanne daga ciki zakiyi, tiktok ko inster ?”

“Duka biyu”

Ya gyada mata kai, ganin kamar hirar ta ƙare kuma yana cin abinci ta tsaye masa a kai tana saka shi managa yasa Maryam ta ɗauki flask ɗin data zuba rice stick ɗinta, ta buɗe ta juye a plate, sannan ta ɗauki milk shake ɗin itama ta ɗora komai a tray ta fice.

Shima bai hanata ba, to idan ya hanata yace mata me?.

A parlo ta zauna ta fara ci, dan tasan yadda yake cin abincin sa cikin yanga, ba da wuri zai gama ba sai ta gama ma shi bai gama ba.

<< Yadda Kaddara Ta So 17Yadda Kaddara Ta So 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×