A duk sanda zan yi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutse a kaina da aka sauƙe min, kamar da a ɗaure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ƙarƙashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan ɗaurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane. . .