Skip to content
Part 20 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

A duk sanda zan yi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutse a kaina da aka sauƙe min, kamar da a ɗaure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ƙarƙashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan ɗaurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane akaran kai na, rayuwata akwai wahala Wifey, shi yasa nake ganin lefin su Fulani da suka sakoki a cikin rayuwata, rayuwata bata da alƙibla, rayuwa nake ba irin ta sauran mutane ba, na banbanta da sauran mutane, sam bana farin ciki, duk dariya ko murmushin da zan yi yakan tsaya akan lebena ne kawai, baya kaiwa har cikin zuciyata, ko kaɗan bana farin ciki, saide kuma inasan naga na saka wasu farin ciki, tunda ni bazan samu ba me zai hana na bawa wasu, amma kuma Maryam shigowarki rayuwata ya sauya wasu abubuwan, a da baƙin ruhina baya kusanta ta sai raina ya b’aci, amma a wattanin nan da muke ciki sai abun yayi ƙamari, ya dawo yana tashi kullum, saide tun daga ranar da aka ɗaura mana aure bai ƙara tashi ba, sai dai ko nayi wannan…”

Ya ƙarashe yana nuna mata ƙwayar idonsa.

“Kuma ke ce kaɗai kike sakani naji cewa bani kaɗai ba ne, ina da wani, duk da ina da ƴan uwa amma kullum cikin kaɗaice nake jina, abubuwa sunmin yawa akai na, banajin daɗi jikina kullum, ko kaɗan wanna ba rayuwata ba ce”

Sai yaji wani nauyi dake zuciyar sa ya sauƙa, kamar wani dutse aka ɗora akan kirjin sa kuma aka sauƙe haka yake ji, yaji shi free domin ya amayar da abinda ke damunsa tsawon shekaru, bai tab’a zama ya bajewa wani ciwonsa haka ba, ko Neha da yafi kusancin da ita fiye da kowa bai tab’a magana da ita irin haka ba, bai tab’a ba, amma kuma kullum abun na ci masa zuciya, har yana barazanar hanashi numfashi, kuma duk abinda ya faɗa mata haka ɗin ne, baya jinsa daidai, baya farin ciki, yanajin kamar rayuwar tasa ba tasa bace, kamar ana sarrafashi ne, yanzu haka sai da yayi kokawa da wani abu sannan ya iya amayar da wannan maganganun.

“Ke kalleni nan”

Maryam na goge hawaye ta kalleshi, har idonta ya sauya kala zuwa ja, matsowa kusa da ita yayi ya kai ɗan yatsansa ya goge mata hawayen, a tarihin zamansu karo na farko daya fara tab’a jikinta kenan.

“Ki dai na kuka is not good for you”

Maryama ta gyaɗa masa kai, wayarsa dake tsallaken island ɗin ta shiga playin waƙar Teri meri khani, hakan ke nuna wa Tafida cewa kira ne ya shigo, dan haka ya miƙe, ya dafa kan maryam sannan ya ɗauki wayar tasa da glasses ɗinsa ya fita.

Bayan Maryam ta iya ƙarfafa kanta ta dena kukan ta ɗauki sauran cake ɗin da bai ƙarasa ci ba, dama wanda ta haɗa ɗin duka ta saka a fridge, ta tattare duk abinda ta bata ta saka a cikin dishwasher na cikin dishwasher ɗin kuma wanda ta wanke ta ɗebesu ta sakasu a inda ta saba ajewa.

Ba tajin ko cake ɗinma zata iya ci, dan haka ta fita daga kitchen ɗin, fitowar tata ta yi dai-dai da shigowar Tafida daga Ƙofar waje.

Ido suka haɗa sai ta ganshi da baƙin glass har yanzu, taji tausayinsa ya ƙara kamata, hannunsa ta kalla taga ledoji har biyu, bata ce masa ƙala ba ta yi hanyar hawa sama.

“Wifey tsaya mana”

Maryam ta tsaya da tafiyar da take, a hankali ta ɗaga kanta sama tana so ta hana hawayen dake san zubowa sauƙa. Sai da ta tattabar da bazasu sauƙo ba sannan ta juyo, a lakocin Tafida har ya zauna akan kujera, da hannu ya yafito ta, dan haka ta dawo cikin parlon.

Gefensa ya nuna mata alamun ta zauna, sai ta zauna ɗin tana kama hijabin jikinta, yayin da shi kuma yake fitowa da wani kwali daga cikin leda.

“Desktop led ring light ne, tunda zaki fara food blogging”

Ya faɗi a lokacin da yake ciro kwalin, Maryam kawai kallonsa take, tana mamakin yanda yake iya b’oye abunda ke ƙarƙashin ransa.

Shi da kansa ya haɗa ring light ɗin, ya jona da wuta hasken ring light ɗin ya haske fuskar Maryam dan a setinta ya ajeshi, Maryam ta kai hannu ta tare fuskarta.

“Ha kawo ko ?”

“Umm”

Ta amsa shi da ƙyar, sai kuma ya zare shi daga socket ɗin, sannan ya dawo ya zauna a inda ya tashi.

“Kinga yadda yake working ko ?”

Maryam ta gyaɗa masa kai, sai kuma ya janyo ɗayar ledar, ita kuma bai buɗe ta ba ya miƙa mata kawai.

“Kije ki, a ina zan aje miki ring light ɗin?”

Maryam ta karb’i ledar tana miƙewa, bata amsa shi ba, sai kama ring light ɗin da ta yi ta aje shi a kusa da TV stand sannan tayi sama.

A kan gadonta ta zazzage ledar daya bata, hijabaine kusan kala goma, Maryam ta zauna a bakin gadon tana kallon hijaban hawaye na cika mata ido, ya kamata ace tayi wani abu akan rayuwar bawan Allahn nan.

Bai kamata ace ta barshi cikin wannan halin ba, ya zama dole ta temaka masa, kamar yanda ya temaki rayuwarta, sam bai kamata ta zuba ido tana ganinsa haka ba, she need to do something.

Hadejia Emirates

Sashen Bayi

Da ƙarfe 05:30pm.

“Ke? Wai ina kika je ne ?”

Cewar Hassana tana duban Husainarta, Husainar ta zauna tana sharce gumi.

“Ke dai bari, wannan mara rabon ce tasani binne mata wani asirin da suka ƙara yi akan Tafida”

Ido waje Hasana take kallon yar uwar tata.

“Ke inji dai baki binne ba ?”

Husaina ta girgiza kai.

“Na binne mana, me zai hanani binnewa”

“To amma Hassana me yasa ?”

“Saboda inaso na nunawa Fulani Sadiya cewa mugunta sayin faƙo ce, idan baka iya ba ka b’ata jikinka, ita har yanzu Allah bai sa ta gane cewa abinda take ba daidai bane, ta yi, ta yiwa bawan Allahn nan asiri amma bai ci shi ba taƙi ta haƙuri”

Hasana ta yi ƙasa da murya tana faɗin

“Ai wannan addiƙu mina diƙu inna hu ɗiɗif ce”

Suka saka dariya suna tafawa

“Har yanzu fa bata lura da cewa duk asirin da ta masa kan ɗanta ya ke dawowa ba, kinga na neman mata data saka aka masa kan ɗanta ya dawo, ta saka a masa na shayeye shima ya dawo kan ɗanta, yanzu haka Allah ne kaɗai yasan name ta sa aka masa wannan karon”

“Allah sarki bawan Allah Tafida,yana can yana fama da kansa ita kuma tana nan tana shirin ƙara masa wani zafin”

Husaina ta dan daki cinyar Hasana tana faɗin.

“Me dallah nace miki asirin baya cinsa, wata ƙilama daya tafi bakinsa ƙofar garin Hadejia yake dawowa”.

Suka ɗan dara kaɗan kafin Hassana ta ce.

“Kome ya tsare mata? Oho.”

“Wataƙila dan tana ga yafi ɗanta halin arziƙi ne, saboda kinga shi bashi da wani hali na kushe, amma ɗanta fa ?, yafi kowa lalacewa, wata ƙila tana ganin kamar idan sarki ya sauƙa shi za’a ɗora, ita kuma da ɗanta su tashi a tutar babu, shi yasa take wannan abubuwan”

Hassana ta tab’e baki.

“Amma fa Husaina lamarin Tafida abun a duba ne, bisa ga dukkan alamu akwai wani a bayan lamarinsa”

Husaina ta gyaɗa kai tana nazari.

“Ƙila hakane, to amma ke a ganinki waye ?”

“Yaya zan yi nasani, Allah shi ya barwa kansa sani”

Husaina ta aje kofin ruwan data sha tana faɗin

“Koma de waye muna fatan Allah kub’utar da shi daga sharrinsa, dan Tafida mutumin kirki ne”

“Ameen ƴar uwata”.

Hanam Pov. 

Sai da sukayi sati ɗaya a Hakuɗau sannan suka dawo abuja, Hanam saida tayi nadamar zuwanta hakuɗau wannan karon, dan basu tahoba sai da Abba ya ce kada ta haura watan nan ba tare da ta nemi mijin aure ba.

Ta rasa yadda za ta yi ita bata da wanda take so, Jabeer ne kawai ta tab’a soyyaya da shi, bata da wata mafita dan Abba ma haka ya  sata agaba da nasa faɗan, ta laluba ta lalubo bata da wani tsayyaye sai Jabeer ɗin, shi kuma har yanzu yana santa.

Dan haka kawai ta cewa Abba ta amince da auren Jabeer ɗin, Abba yayi murna sosai kuma a ranar data faɗa masa cewa ta amince ɗin ya kira Jabeer ɗin ya sanar masa, Jabeer yazo suka yi magana basu wani ja abun da tsawo ba dan dama tun farko an fara maganar bikin.

Saboda haka suka yanke biki sati biyu, Hanam sam ba haka taso ba, ita bata ƙi a barta daga ita sai Arya da Abba ba, amma babu yadda za ta yi, ko kaɗan bata san Abba ya yi fishi ko ransa ya b’aci, tafi so a kullum ta ga yana farin ciki, inde har auren nata shine farin cikinsa to za ta yi auren.

*****

“Wai yanzu mom bari za ki yi tayi auren nan?”

Muryar Kamal ta faɗi, yayin da yake zaune a ɗakin mahaifiyarsa, suna facing juna, Mero ta yi wani murmushi wanda za a iya kira dana makirci.

“Kamal kenan, ai bazan tab’a bari ta yi auren nan ba, ba dai Jabeer bane ? To ita da Jabeer sai a lahira idan ana haɗuwa, amma babu ita babu shi, bazan tab’a bari ta auri Jabeer ba”

Kamal ya bushe da dariya harda buga ƙafa.

“To yanzu mi ye shirinki ?”

“Kai dai ka zuba ido ka gani, Allah ya kaimu ranar ɗaurin aure, ba dai ita wannan shashashar taƙi yarda mu haɗa kai ba? Ni ɗaya zan yi abuna na gama”.

“Wa ke nan?”

“Hajjo mana, wai ita me tsoron Allah”, ta ƙarashe da kwafa.

“Auren yar lele, bari muga to idan za’ayi”, gabaɗayansu suka saka dariya.

Uchenna Pov.

Zaune yake a ɗakinsa, guitar yake kaɗawa cikin wani kiɗi me taushi da sanyaya ruhi, waƙar daya rubuta yake rerawa tareda ƙidan.

Waƙa na ɗaya daga cikin mafarkansa na rayuwa, kuma tun yana ƙarami yake so ya yi waƙa, dan haka yake rubuta waƙar yana ajewa, idan ya samu free time kamar haka sai yazauna yana rerawa, wata ƙila ya kore ƙunci damuwa da b’acin rai dake cikin zuciyar sa.

Labarin ɗaura auren Hanam a gobe ya dake shi, hakan yasa yake cikin duhu, dan har yanzu yana santa, kuma dama bai tab’a dai na santa ba, ita kaɗai ya so, kuma ya ƙudircewa ransa ita zai ci gaba da so har zuwa lokacin da zai rasata, wataƙilla Allah baisa ta kasance tasa ba, wataƙila ba shi da rabon samunta, wata k.

Wayarsa da ta yi ringing ta dakatar da tunani da kuma kiɗan da ya ke lokaci guda.

Uchenna ya juyo ya kalli wayar tasa dake aje a gefensa ‘MOM’ shine abinda ya fito b’aro, b’aro akan screen ɗin, ya aje guitar ɗin yana murmushi kafin ya kai hannu ya ɗauki wayar.

“Mom”

Ya kira sunanta, kuma yana jin sautin murmushin ta ta cikin wayar, kafin ta amsa

“Na’am Haris, ya kake?”

“Ina lafiya, and you ?”

“I am fine also”

“How is Zakiyya?”

“She is fine, she went to school”

Yayi murmushi, yana shafa sumar kansa

“Zaki zo bikin ne?”

“Me zai hana Haris?, mutumin nan ya yi maka komai daya kamata ace mahaifin ka ne yayi maka, ya zama dole nazo na taya shi murnar auren ƴarsa”

Ya gyaɗa kansa kamar tana ganinsa.

“Yaushe za ki zo?”

“Gobe in shallah, i call to inform you dama”

“Ok mom see you tomorrow”

“Take care of yourself, Allah ya maka albarka”

“Emeen”

Daga haka wayar ta ƙare, ya lumshe idonsa yana jingina da jikin gado, yana azabtuwa, Allah ya sani yana azabtuwa sosai.

Maryam Pov.

Tsaye take a jikin lokarta tana shirya kayan data wanke kuma ta goge yau da rana, dan gobe monday, tun shekaran jiya take cikin damuwa, sam bata jin daɗin ranta, gaba ɗaya lamarin Tafida ya dagula mata lissaffi, tarasa wani mataki zata ɗauka akai, kuma gashi bata san kowa yasan halin da yake ciki, dan wannan sirrinsa ne, da ta nemi shawarar Anti Fati.

Wutar da aka ɗauke ce tasa tunaninta yankewa, tunda tazo garin kusan sati biyu amma bata tab’a ganin wutar gidan ta yi koda fari ba, balle a ɗauke, abun ya bata mamaki, tsoro ya mamayeta ganin duhun da ɗakin yayi.

Allan Ya yi ta da wani bala’in tsoro, tana da tsoro sosai musammanma na duhu, tana tsoron duhu shi yasa ma bata kashe wuta idan zata kwanta, yanzu gashi ita ɗaya ce a ɗakin bazata iya tuna inda ta aje wayarta bama balle taje ta ɗauko.

Taji kamar ana tab’a balcony ɗun ɗakinta, ta zabura ta yi waje, wajen ma babu haske, ko ina yayi duhu a gidan, dan wajejen karfe 10 ma ne na dare.

Maryam ta ci gaba da takawa tana bin corridor ɗin a tsorace, ji take kamar ta fasa ihu, sai kuma gashi ta fasa ihun, saka makon karo data ci da abu kamar mutum, hannunta taji an ruƙo, ta kara rudewa tana fasa ihu, sai kuma taji ance

“Ssssshhhhhh!”

Ta ƙara ruɗewa tana ƙoƙarin ƙwatar hannunta daga ruƙon da aka mata, tsabar ta kiɗime sam bata gane muryarsa ba.

“Ke !! Miriam nine ”

Inaa, sam bata ta gane yaren da yake, tsoro ya cika mata ciki, tsalle kawai take da ihu tana haɗawa da kiran sunan Allah.

Tafida yaga abun nata bana ƙare bane, shima yana waya da Fulani yaga wutar ta ɗauke shi yasa ya fito dan ya duba me ke faruwa, shine ya ci karo da ita.

Tafin hannunsa na hagu wanda be riƙeta dashi ba ya buɗe, nan take wuta ta bayyana tana ci, kuma ba tare da ta tab’a tafin hannunsa ba, Maryam ta ƙara fasa ihu tana fadin.

“Wayyo Allah wayyo Maanmu, dan Allah karka ƙonani aljani, ka yi haƙuri kaji, dan Allah kayi haƙuri, to wai ni me na maka ma?”

Tafida yana murmushi ta ya ɗago da hannun setin fuskarsa ta yadda zata samu damar ganin fuskarsa, sai kuma tayi shiru ta tsaya da tirje-tirjen da take, yana murmushi har hakwaransa na bayyana yace

“Main hoon na (nine), nine Eshaan, Tafida”

Ya faɗa mata sunayen har guda biyu duk dan ta gane, babu abinda ya bashi dariya sai ganin yanda fuskarta take sharkaf da hawaye.

“Eshaan ne ?” Ta tambaya kamar wata sokuwa, yana murmushin dake barazanar komawa dariya ya gyaɗa mata kai

“Eh nine”

Har yanzu wutar na setin fuskarsa, yayin da yake riƙe da hannunta daya

“Ki koma ɗakinki ki zauna, zanje na duba wutar”

A kiɗime ta ƙankame shi daga gefe kamar side hug amma duka hayyaneta biyu kewaye daya shi, ita kanta bata san ta yi hakan ba, dan gaba ɗaya ta tsure ta ƙidime, ta shiga girgiza masa kai tana kuka.

“Ni a’a, bazan koma ɗakin ba, tsoro nake ji Eshaan, i am scared, Eshaan…Eshaan”

Dariya tana so ta kifcewa Tafida ya kai hannunsa ya ciro nata daga jikinsa, ya riƙo hannun nata.

“To muje tare”

Ya faɗi yana jan hannunta, a hankali suke taka stairs ɗin, ya riƙe hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma har yanzu wutar na ci, yana haska musu hanya har suka shiga garden ta kofar dake parlo, kasan cewar makunnar wutar gidan gaba daya a garden ɗin take.

Koda ya buɗe wajen sai yaga layin wutar ne ya sauƙa, dan haka ya mai da layin, nan take haske ya gauraye ko ina a gidan, Maryam ta sauƙe wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali.

Bata ankara cewa hannunta na cikin na Tafida ba saida suka shiga parlo, aiko tana ganin haka ta yi saurin zame nata daga cikin nasa, ta kalle shi da idonta da har yanzu akwai sauran ƙwallar data taru mata a ciki.

Sai kuma ta ruga da gudu ta haye sama ta faɗa ɗakinta tare da banko ƙofa. A jikin ƙofa ta jingina tana maida numfashi kamar me asthma, hannunta akan kirjinta, idanuwanta a lumshe, sai yanzu duk abinda ta yi yake dawo mata daki-daki, da ace wani ne ya faɗa mata cewar zata iya riƙe Tafida kamar yanda tayi yau to da kuwa ko qur’ani ne zata dafa akan hakan bazata faru ba.

Hannunta na dama daya rike ta ɗago ta kalla, sai kuma ta yi murmushi sannan ta bar jikin ƙofar tana goge hawayen idonta, sannan ta koma ta ci gaba da saka kayanta a wardrobe.

Tafida ya bi bayanta da kallo yana murmushi har sanda ta shige dakinta, sannan ya tako zuwa saman shima ya shige dakinsa, gabaɗaya ta gama bashi dariya yau ɗin nan, ga yadda yaji zuciyarta na bugawa a ɗazun, ya saka shi cikin nishadi.

<< Yadda Kaddara Ta So 19Yadda Kaddara Ta So 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.