Skip to content
Part 22 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

HANAM POV.

Dawowarta kenan daga wajen aiki, tun daga parlon gidan ta fara ganin sauye-sauye, duk da gidan bawai dama bashi da kya bane, yanada kyau kuma sosai, dan ko gidansu saide ya faɗa masa girma ba kyau ba.

Tsarin gidanjen estate ɗin na da kyau sosai, ɗakin data zab’awa Arya ta fara buɗewa da zummar shiga. tris ta tsaya tana kallon yanda aka sauya komai na ɗakin.

Ga uban tarin kayan wasa da aka cika ɗakin dasu, baby cot, baby cradle, da manya-manyan teddies.

Duk yawan kayan wasan sa na ɗakin na da bai kai wannan yawa ba, baki sake ta ƙarasa shiga cikin ɗakin, kafin ta sauƙe Arya daga cikin baby carrier ɗinsa, ta aje baby carrier ɗin, sannan ta ɗauka masa wasu teddies guda biyu.

Kafin ta fita daga ɗakin, ɗakin data zab’awa kanta ta shiga, taga shima an sassauya wasu abubuwan a ciki, ta aje Aryaan ɗin akan gado sannan ta bashi teddies ɗin data ɗebo, ta shiga ban ɗaki ta fito bayan ta ɗaura alwala.

Sallah ta yi sannan ta fita zuwa ƙasa dan ganin abinda zata iya samawa kanta, kitchen ɗin ma da ta shiga taga sauyi sosai, dan yau maƙil yake da kaya.

A ranta tana jinjina ƙoƙari irin na Uchenna, girki ta samu ta ɗanyi me sauƙi sannan ta zauna ta ci.

Sai wajen Bayan magariba Uchenna ya dawo, a lokacin suna zaune a parlo ita da Arya shi yana wasan sa ita kuma tana aiki a laptop, sau ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi tai mishi sannu da zuwa, bayan haka bata ƙara ce dashi komai ba.

Shima kuma bai matsa akan sai an masa maganar ba, dan haka ya yi sama abinsa.

“Nagode, naga kaya”

Sai ya tsaya da tafiyar, kafin kuma yaci gaba yana faɗin.

“Don’t mention it”

Da sauri Hanam ta ɗago da kanta ta kalli bayansa, wannan muryar, tabbas ta san muryar itace muryar wannan wanda ya temaketa a hannun ɗan daba nan, kenan shine ?, to ai dama ba taga fuskarsa ba a lokacin. Dan haka zai iya kasancewa shi ɗin ne.

R120, TRANSCORP HILTON HOTEL, ABUJA

Da misalin 12:30am

Wata baƙar budurwa ta fito daga banɗaki, sanye cikin wando leggings baƙi, sai wata baƙar half vase wadda bata ko rifi cibiyarta ba, ta kawo baƙar leather jacket ta ɗora akan half vase ɗin, gashin kanta kuma kitsan kalbar pink ɗin attachment ne, ya sauƙo har kasan mazaunanta.Hanyar ƙofar fita ta yi za ta fita daga wajen.

“HELEEN ina kuma zakije baki bani kuɗina ba?”

Wani matashi dake kwance a kan gadon dake fakin duƙunƙune cikin bargo ya faɗi, a hankali ta juyo ta kalleshi tana gyara tsaiwarta.

“Kuɗi zan baka ko ?”

“Eh mana, ai ke kika kirani kika ce nazo idan mun gama komai zaki biyani”

Ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, sannan ta saka hannunta a bayanta ta ciro bingida ƙirar pistol, tunda yaga haka ya tsorata gaba ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake, setashi ta yi da bindigar sannan tace.

“Ga kuɗinka nan zan baka, a sauƙa lafiya…”

Ta ƙarashe tare da sakin kunamar bindigar, kasan cewar akwai salansa sai ƙaran harbin bai fito ba. Meda bindigar ta yi bayanta ta sofare, tana leƙa fuskarsa.

“Au ya sheƙa, an gode Allah matsala ta kau”

Wani makeken sun glasses ta maƙala a idonta, sannan ta buɗe ƙofar ta fita, yaranta biyu suna tsaye a waje suna jiranta, suna ganinta suka matso kusa da ita tun kafin ta musu magana.

“Na aika shi lahira, kuji da securities”

“To oga”

Tana gama basu umarnin ta yi gaba.

*****

Zaune take a cikin motarta ƙirar Lamborghini, glass ɗin da ta saka ɗazu ta sauƙo da shi kan hancinta, tana zaune a wajen aka zo aka wuce da gawar yaron da ta kashe ɗazu, taja wani uban tsaki.

“Shi ji yake ya burgeni, yau ni har akwai wani wanda zai burgeni kamar masoyina TAFIDA”

Sai kuma ta yi murmushi tana jingina da jikin kujera.

“Ina kewarka masoyi”

Sai kuma ta zabura ta zauna da kyau, wayarta ta ɗauko ta aikawa ogan kungiyarsu kira, yana ɗagawa ta fara magana cike da gadara, kamar itace ogar bashi ba.

“Na gaji da Abuja, zan dawo lagos”

Daga can bangaren scorpion ya girgiza kai, ya rasa yaushe har ya yi sake fan kada ya girma, ya tuna shekaru bakwai da suka wuce, lokacin da HELEEN tazo gareshi a garin lagos.

Tana yar ƙauyenta fitik, lokacin ko bihim bata sani ba, tace masa wai wanine ya mata fyaɗe kuma ta samu ciki iyayenta suka koreta daga gida, tana so ta samu ƙarfi ta yanda zata rama wulaƙancin da aka mata.

Kuma ya tausaya mata lokacin, dan haka ya yarda ta zauna a dabar tasu, a kowani aiki ita yake ɗorawa har tazo ta shahara a daba, yanzu kuma sam ma bata jin maganarsa yanda taso haka take abunta.

“Tunda kin riga kin yanke hakan kuma miye na wani kirana, ai wannan sanar dani kike ba izini kike nema ba”

Ta sosa kanta kaɗan

“To zan ɗora laku akan aikin, zan dawo jibi, kewar masoyina nake, ina san na ganshi”

Bai ce mata komai ba ya kashe wayar. Ta koma ta ƙara jingina da jikin kujerar tana murmushi domin tinawa da sahibul ƙalbinta da ta yi, ta lumshe ido tana tuno ranar da ta fara ganinsa.

Ranar faɗa sukayi da wata daba, har aka harbeta a hannu, shine su laku suka kaita st. Nicholas hospital.

A nan ta fara ganinsa, domin shine ya ke kula da ita a asibitin.

“ I am coming for you my ESHAAN”.

*****

“Kasan Allah sai ka siya mata” cewar Khabir yana kallon Tafida, yayinda suke tsaye a cikin Admiralty mall lagos, dawowarsu kenan daga asibiti, yau motar Khabir ɗin tana wajen gyara shi yasa Tafidan ya ɗauko shi.

Kuma suna hanya yace su tsaya yau Valentine’s day yana so ya siyawa matarsa kyautar da zai bata, da suka shiga ciki ne yace Tafida ma sai ya siya.

“Wai dole ne ?, ai ba dole bane!”

“Dole ne mana, dan Allah ka siya mata, wallahi za taji daɗi”.

Ya karkatar da kai gefe yana kallon baskert ɗin da ake ce masa ya siya, sai kuma ya dawo da kansa dai-dai sannan ya gyaɗa shi a hankali.

“Na gode nawan, ni zan biya kuɗin ma”.

Kuma daga haka ya ɗaukar musu basket biyu, sannan suka fita bayan Khabir ɗin ya biya.

Saida Tafida ya kaishi garejin da ya kai motar tasa gyara sannan ya tafi gida, dan an gyarawa Khabir din motar tasa. Ya tarar da go slow a hanya, hakan ya haddasa masa makara wajen dawowa gida. Tunda ya sako motarsa cikin Alaro city, ya tsinci kansa cikin irin yanayin daya saba, duka damuwa da gajiyar daya baro wajen aiki dasu ya nemesu ya rasa.

Da haka ya isa cikin gidan nasa, parking ya yi sannan ya buɗe motar ya fito, ya zagayo gidan baya ya buɗe, ya tsaya yana kallon basket ɗin dake aje a wajen, kamar me nazarinsa, sai kuma ya kai hannu ya ɗauko shi, yaji shi da nauyi, dan haka sai yasaka karfinsa.

Ƙofar parlon ya tura sannan ya shiga abinda idonsa ya fara gane masa shine, Maryam ta taka kan coffee table ɗin dake tsakiyar parlon tana aikin goge saman tv stand, ba wannan ne yasa yake kallonta ba, yau babu hijabi a jikinta, tun ranar da suka zo garin lagos bai ƙara ganinta da hijabi ba sai yau, wata baƙar dolman dress ce a jikinta rigar bata sauƙar mata har ƙasa ba iya karta singalinta, sai farar hula a kanta,bil haƙƙi da gaskiya take aikinta, da alama ma bata san ya shigo ba.

Ear piece ne a kunnenta, tana sauraren littafin Fulani wanda abokiyar hira ta karanata, ko kaɗan bata gajiya da sauraron littafin, bayan ta gama girkin darenta ne taga har lokacin dawowar Eshaan bai dawo ba.

Dan haka ta dawo parlo ta zauna tana kallo, tana jiran lokacin shan ruwa ya yi dan yau azumi take.

Sai taga kamar saman Tv stand ɗin ya yi ƙura, sai ta shiga store ta ɗauko wata duster da take goge-goge da ita a gidan, taje ta tsaya a wajen zata goge, bisa ga mamakinta sai taga tsayinta bai kai ba, dan haka ta sauke vase ɗin dake kan coffee table ɗin parlon ta janyoshi zuwa wajen, kasan cewar ba glass bane shine ta taka shi take goge wajen.

“Miriam!”

Ya kira sunanta da ɗan ƙarfi, ganin bata ji ƙiran da ya mata da farko ba, Razana ta yi wadda ta haddasa mata zamewa daga kan coffee table ɗin, ta riga ta gama saddaƙarwa cewa ta faɗo kasa, wata ƙilama ƙashin bayanta ya karye, ko kuma ta gurɗe, gabanta banda matsanincin bugu ba abinda yake, kamar zuciyarta zata fito fili dan tsoro.

Saide kuma abinda take zaton bai faru ba, jinta kamar tana yawo a iska yasa ta buɗe idonta a hankali kamar me tsoron ganin wani abu, sai ta ganta ita ba a ƙasa ba ita ba a sama ba.

Ta kai dubanta bakin ƙofa, taga Tafida ya ɗaga hannayensa duka biyu a saitin inda take, hakan ke nuna mata cewar shine ya riƙeta, kuma har yanzu abinda take ji a kunnenta na playing, hannu ta kai ta cire air piece ɗin.

A lokacin kuma Tafeedah ya ƙaraso daidai inda take, kuma har yanzu hannayen nasa na a setin inda take, yana ƙsrasawa kusa da ita beyi wani tunanin ba ya riƙota dukanta.

Maryam ta riƙe gaban rigarsa gam, sbd abinda take ji akanta, a riƙe take a hannunsa amma ji take kamar zata faɗi, kamar bai riƙeta dai-dai ba, tana ji kamar gravity ne ke janta zuwa ƙasa, itafa bazata iya jurewa wannan kusancin nasu ba, kusan ta yi yawa.

A hankali Tafida ya sauƙe ta kan ƙafafunta, hannunsa kan waist ɗinta, ita kuma hannunta duka biyu akan gaban rigarsa, a dai-dai inda ya ɗora hannunsa yake jin abu kamar beads haka.

Sai ya yi saurin janye hannun nasa itama kuma Maryam ta ɗauke nata hannun daga jikinsa.

“Are you okay ?”

“hmmm”

Ta amsa a hankali, hannunta ɗaya ya kamo ya jata ya zaunar akan kujera, shima ya zauna a gefenta yana kallonta.

Tunani yake yanda za tayi idan ya faɗa mata abinda ke ransa, yana da tabbacin bazata so hakan ba.

Kawar da ko wani tunani ya yi, ya kai hannunsa setin inda ƙaton basket ɗin nan yake, basket ɗin ya taso ya sauƙa gabansa, yakai hannu ya ɗauka.

Sai kuma ya kafa inda-inda, yama rasa me zaice mata, to wai yace mata me ?, shifa ko a da ba budurwa gareshi ba, sau ɗaya ya tab’a yin budurwa, lokacin yana india, kuma bayan ita bai kuma ba.

Itama ɗin rai ta b’ata masa har baƙin ruhinsa ya shiga jikinsa taga abinda yake, tun daga ranar ta guje shi.

Ganin yanda yake motsi da bakinsa da kuma yanda yake inda-inda ya bawa Maryam dariya, tasan cewa yau Valentine’s day, dan taga yanda yau ƴan mata da samari suke ta shagalin ranar a makaranta, kuma abun ya burgeta sosai, bata ɗauka cewa zai kawo mata ba itama.

Kunshe dariyar ta shiga yi, harda saka hannayenta ta dafe bakinta, amma dariyar sai da ta fito, tashiga kyakyakya tata kuwa kamar bazata dena ba.

Wato ni kikewa dariya ko ?, ya tambaya a zuciyarsa, a ransa yayi kwafa, sannan ya lumshe idonsa, a hankali ya buɗe, take ƙwayar ta sauya kala zuwa ja, ya ɗan buɗe bakinsa kaɗan, fiƙar nan ta sauƙo.

Wata uwar zabura Maryam ta yi zata gudu, yayi caraf ya riƙe hannunta yana fashewa da dariya, dariya yake sosai kuma har yanzu idonsa yana jan, fiƙarma bata komaba, kuma yana dariyar hannunsa riƙe da nata.

Tunda take bata tab’a ganinsa yana dariya ba, murmushi ma sai ta ƙirga sanda ta ganshi yana yi, dariyar kuwa ta masa kyau, ta ƙara bayyana kyansa na asala.

Itama kuma sai abun ya bata dariya, suka shiga yin dariyar tare Tafida harda yarfewa hannu.

Kafin ya tsaya yana kallonta, fiƙar ya maida amma ƙwayar idon tana nan a ja.

“Gashi wifey, happy Valentine’s day”

Ya faɗi yana miƙa mata basket ɗin, Maryam tana murmushi tasa hannu ta karb’i kyakyawan basket ɗin, ta shiga fito da kayan ciki tana gani, nishaɗi take ji ta ko ina na ratsata.

Babu abinda yafi burgeta sai teddyn da taga a ciki, teddy bear ne pink color, taddyn ya mata kyau, ta tuna sanda ta yi ta santin wata teddyn Badar, wadda aliyu ya kawo mata.

Ga chocolates kala-kala a ciki, wasuma bata tab’a ganin kalarsu ba, abu na biyu daya ƙara burgeta shine wani farin kwali data ɗauko, tana buɗewa taga, peach cat ears head phones, taji kamar tayi fifike ta tashi sama dan daɗi, abun na burgeta tana ganin irinsa a tiktok.

Wani ɗan card ta ɗauko a ƙasa, rubutun ciki ta shiga karantawa a zuci.

‘I want to thank you for always being for me whenever I needed someone to complain to, whenever I needed someone to talk to, when i was at my lowest, whenever i needed soothing words, you are always there for me despite the distance.

If i am to gather al the words on earth, it ain’t to enough to tell you how much I LOVE YOU, Thanks for choosing me as your life partner, HAPPY VALENTINE’S DAY MY LOVE.

Maryam ta ɗago tana kallon Tafida, idanta na haskawa da tsantsar farin ciki, ta ƙara kai dubanta cikin basket ɗin, abu ɗaya ne ya rage a ciki.

Wani ƙaramin akwati ne, wanda tasan cewa zobe kawai ake sakawa a ciki, amma kuma wannan yana da ɗan tsayi.

Ta ɗauka ta buɗe taga zobuna biyu, daya na maza ne daya kuma na mata ne, amma ko wanne design ɗinsa da ban yake, kuma ko tantama bata yi na azurfa ne duka.

Tafeedah ya cire hular kansa yana shafa sumarsa, katin hannunta ya karb’a yana karantawa, sai kawai yayi murmushi, maryam ta nuna masa zobunan, ya yi murmushi yana karb’a, na matan ya ciro sannan yace.

“Na saka miki ?”

Ta gyaɗa masa kai, hannunsa da bai riƙe zoben ba ya kai ya kama nata sannan ya saka mata zoben, kuma kamar da aka gwada da nata, dan zoben ya zauna, maryam ta ɗaga hannun tana kallon zobunanta biyu duka na azurfa, dayan Maanmu ce ta bata, sai kuma wannan wanda yau Eshaan ya saka mata.

Tafeedah ya mika mata nasa hannun yana faɗin.

“Saka min nima, kinga mu sai yau muke engagement”

Ƴar dariya ta yi sannan ta kamo hannunsa nata hannun na rawa ta saka masa a na tsakiya, amma sak zoben ya ƙi shiga, Maryam ta haɗiye dariyarta ganin yanda zoben ya maƙale a tsakiyar hannun nasa, sai kuma ta cire shi daga na tsakiyar ta saka masa a ɗan ƙaramin ɗan yatsan nasa, sai a nan ya shiga.

Shima ɗaga hannun yayi yana dubawa, sai kuma ya ƙara meda dubansa gareta, kayan chocolate ɗin take fitarwa daga cikin jakar da aka saka su, dubansa yakai kan gefen fuskarta, kusa da kunnenta, yaga tsagu uku kamar de wanda ke kwance a gefen tasa fuskar.

“Kema kina da ƴar hadejia ?”

Maryam ta aje chocolate din data ɗauko sannan ta shafa wajen, tana faɗin

“Eh ina da ita, kowama na gidanmu yanada ita, auta ne kawai ba a masa ba, lokacin da aka haifeshi Maanmu tace baza’a masa ba, wai yanzu an dena yin zane, ya zama tsohon yayi..”

Ta ƙarashe tana dariya dan ta tuna lokacin da Maanmu ta tubure akan baza’a b’atawa autanta fuska ba.

Tafida ya gyara zamansa yana shafa doguwar sumar data fara sauko masa har wuyansa ta baya dan tayi tsayi, maganar da yake so ya faɗa yake taunawa.

<< Yadda Kaddara Ta So 21Yadda Kaddara Ta So 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.