Skip to content
Part 24 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Haɗejia Emirates

Da misalin 04:00pm

“Kina jina ko Husaina?, kada ki bari a ganki, idan kuma aka ganki to kadama ki ambaci sunana”.

cewar Jakadiyar Fulani Sadiya, tana danƙawa Hassana asirin da Fulanin ta sakata ta karb’o ɗazu a wajen bokanta, Hasaina ta riƙe abun da kyau, a ranta tana faɗin ai dole ne ma ta je ta yi aikin, kodan ya dawo kansu.

“Inshaallah Jakadiya, baza’a samu wata matsala ba kamar sauran”

Jakadiya ta gyaɗa kai, tana waige-waige irin na marasa gaskiya.

Hasaina ta bar wajen, a ranta tana raya koma miye wannan tana fatan ya zama sannadiyyar zuwan sharrinsu ƙarshe akan Tafida, dan temakon da Tafida ya mata ita da ƴar uwarta ba me mantuwa bane a gareta.

Sai ta tuna sanda Tafida ya temaketa, ranar Fulani Sadiyace ta aiketa b’angaren Galadima, ta shiga har wajen nasa ta bashi saƙon da Fulanin ta aikota.

Ta zo zata fita Galadima ya riƙe mata hannu, yana faɗa mata kalaman banza, daga haka suka shiga kokuwa yana san haike mata, ihu ta ƙwalla a lokacin, ita de bata san ya aka yi Tafida ya san abinda ke faruwa a ɗakin ba, sai ganinsa ta yi ya fasa windown glass ɗin dake ɗakin.

Kallonsu ya shiga yi a lokacin, hannunta riƙe a cikin na Galadima, a lokacin ita kuma sai kuka take, hakan yasa ya fahimci abinda ke faruwa, dan yasan halin Galadiman tun ba yau ba.

Ya rufe Galadima da duka a lokacin, kuma saida ya masa lilis, sannan ya dawo wajenta tana ta kuka a lokacin shi ya ɗauko mata hijabinta da Galadima yacire mata.

Kuma shine ya rakata har b’angarensu na bayi, ya sadata da ƴar uwarta, kuma ya shawarce su da akan zeyiwa me martaba magana a yanta su su bar zaman fadar, suka faɗa masa cewar basu da kowa sai junansu iyayensu sun rasu, ya temake su sosai a lokacin.

Kuma har wa yau basu mance alkairinsa garesu ba, sannan zata iya yin komai domin Tafida, tun kafin ya temaketa ake bata asiri akansa take binnewa, wannan kuma bana binnewa bane, na jefawa a rijiya ne, kuma zata jefa ɗin, dan tana so taga ƙarshen sharrinsu akan jaruminsu.

Ta tsayar da tunaninta a lokacin da ta kawo gaban wakekeyar rijiyar da aka dena aiki da ita a yanzu, kakarsu wadda suka taso a gunta, wadda ta kasance baiwa ce a gidan sarautar, kuma ita ta basu labarin cewa rijiyar tafi shekara hamsin da dai na amfani.

Ta ɗago abin da ke hannunta, ƴar karamar kwalbace, sai wasu baƙaƙen abubuwa a ciki, ga wani abu kamar takarda, hannu ta kai ta ture murfin da aka rufe rijiyar da shi, tun daga sama har ƙasa yanace ta baibaye wajen, amma babu ko tsoro a ranta ta cilla kwalbar a ciki, inde akan Tafida ne komai ta fanjama-fanjam.

“Inshaallah wannan shine ƙarshen sharrinki fulani, ba zaki ƙara cutar da Tafida ba”.

***** 

House No 122, B3, Alaro city Lekki, Lagos

Da 09:30pm

Maryam ta fito daga kitchen hannunta riƙe da wani glass bowl, wanda ke cike da yoghurt, wanda ta ƙawata shi da, kwakwa, apple da dabino.

A hankali ƙafafunta wanda babu takalmu suke takawa zuwa cikin parlon da babu haske sosai, ƙananun fitilun dake sama ne kaɗai suke ci dan Tafida ya kashe sauran.

Mamaki ya kamata lokacin da ta gama shigowa cikin parlon, ta ga babu kowa a falon, ita de tasan ta bar Tafida zaune a wajen.

Bakinta ta tab’e a ranta tana faɗin wata ƙila ɗakinsa ya koma, zama tayi a inda ta tashi ɗazu.

Hannunta na dama ta kai tana taba kanta, Ɗazu suka fita ita da Tafida, kamar yanda ya faɗa mata zai kaita saloon idan ya dawo ya kaita ɗin, kuma an mata saloon ɗin, saloon ɗin daya bata mamaki.

Dan an mayar da gashinta very smooth, kamar na fararen fata haka ya koma, abun ya bata mamaki sosai, tana ta mamakin dama gashin africans da yake da ƙarfi yana iya komawa haka ?, kuma dama can gashin nata ba ƙarfi ne da shi ba, kuma ba wani laushi ya cika ba, bakuma shi da tsayi sosai, dan yanxuma da aka miƙar mata dashi kaɗan ya sauƙo kafaɗarta.

Kanta take tambaya yanzu haka zata ci gaba da zama da kanta a tsefe kullum ?, dan matar da tai mata gyaran kan ta bata mayuka wanda zata shafa su ƙara mikar mata da gashin, da wanda zasu riƙa saka gashin yana sheƙi…

Tunaninta ya katse, sakamakon Tafida da taga yana sauƙowa daga kan stairs hannunsa riƙe da wata jaka, tana kallonsa har yazo ya zauna kusa da ita.

“Gashi Neha ce tace na kawo miki, ni na manta ma yanzu ma cable naje ɗauka a jakar shi yasa na ganta”

Maryam ta sa hannu biyu tana karb’ar jakar tare da faɗin.

“Wacece Neha ?”

Tambayar da takewa kanta kenan, tun bayan da taga lambar Neha ɗin a wayarsa, da kuma kiran da Neha ɗin ta masa a ranar nan.

“Ƙanwata ce, da Mamata da Babanta uwa ɗaya uba ɗaya suke, aiki da aure sune suka zaunar da ita a abuja, kuma dama Babanta a can yake kasuwanci”

Maryam ta gyaɗa kai tana zaro faffaɗan kwalin dake cikin jakar siyyayar, kwalin ta buɗe wani kyakyawan pakistan ta gani, rigar da wandon peach color ne, da mayafinsa sea green color, ɗaga shi ta shiga yi baki buɗe cikin murna.

“Pakistan ?”

Muryarta ta fito cike da ɗoki, Tafida ya girgiza kansa yana shafa dogon gashinsa.

“Ba pakistan ba, chickankari sunansa a india”

kai ta gyaɗa masa tana aje shi a gefe, ɗayan kwalin dake ciki ta ɗauko, ta buɗe, shi kuma silk saree ne a ciki a ciki, wannan ta san sunansa a indian ma, maroon color ne shi an masa printing ɗin jajayen filawowi, sai blouse ɗin saree din, ita kuma fara ce, kunyace ta hanata ɗagawa, dan a ganinta blouse ɗin bata da banbanci da halp vase, duk da hannun rigar dogo ne.

“Kai mata godiya, kace mata nagode sosai”

Ta ƙarashe tana buɗe wani kit na sarƙa da dankunne, ga kuma sarƙar kai a ciki, Maryam ta kama baki, wato de so ake ta koma ba’indiya.

“A’a bazan ɗau wannan nauyin ba, na baki de ki mata godiya”

Ya faɗi yana buɗe wayarsa, Maryam ta gyaɗa masa kai, lambar Neha ɗin ya lalubo, sannan ya miƙo mata, Maryam ta kara a kunnenta.

“Mera bhai, aap kaise hain? ( yayana, ya kake ?)”

Abinda muryar ba’indiyar ta faɗi kenan, bayan an ɗaga kiran, Maryam ta gane me take cewa, dan irin waɗanan kalaman na indianci tana tsintarsu a kallo, sai dai bata san da ya zata amsa mata ba, bata sani ba ma ko bata jin hausa dan haka ta ce.

“It’s not him, it’s his wife”

Sai taji budurwar tana dariya.

“Surukata ya kike ?…”

Mamaki ya ɗan kama Maryam, ko da yake, ai ba abun mamaki bane, tunda yayan nata ma yana jin hausa.

“Lafiya, kema ya kike ?”

Maryam ta tambaya.

“Ina lafiya sosai, kin ɗauka bana jin hausa ko?”

Maryam na ɗan yaƙe ta gyaɗa mata kai, kamar da aka ce mata Neha ɗin tana ganinta.

“Ina jin hausa sosai, wata ƙilama nafi mijinki iyawa”

“Chup tum, yeh choot bulawu (Ki mana shiru, wannan ai ƙarya ce)”

Maryam ta juya ta kalli Tafida dake wannan batun, wanda yana sauraron abinda suke cewa, duk da wayar ba a speaker take ba, sai Maryam ta sauƙe wayar daga kunneta ta saka a speaker.

“Woh kaun hai ? (waye wanna ɗin?)”

“Au, bama ki gane ni ba kenan”

Ya amsata da hausa, sab’anin ita da ta masa hindi.

“Bhai kaja baya kawai, wannan maganar ba taka bace, ƙarya nayi ?, ai nafika iya hausan”

“Kiyi istingifari yarinya, kinsan de ni hausa ce ta haifeni, ke kuma daga sama kika koya”

Sai faɗan nasu ya bawa Maryam dariya, kamar ba Tafida ba, wannan me kama kan, me ji da aji, me magana cikin ƙasaita, ya koma Yaya wanda yake nishaɗi da kanwarsa.

“Naji duk da daga saman na koya nade fika”

“Ki kiyaye nifa Nik(Neha Imran Khan), ki bar ganin ke soja ce, ni har yanzu ina miki kallon wannan yarinyar wadda na ɗauketa sanda tana jaririya”

“Surukata manta da wannan, idan muka biya shi ba zamu zanta ba”

Maryam na dariya ta cire wayar a speaker, sannan ta mayar kunnenta, hira suka ɗan tab’a kaɗan, kafin Maryam ta mata godiya daga haka wayar ta ƙare.

“Naga itama tana jin hausa sosai”

Tafida na murmushi yace.

“Mijinta ai ɗan nigeria ne, shima bahaushen ne, kuma gata sojar nigeria”

“soja kuma ?”

ya gyaɗa kai yana ɗauko bowl ɗin yoghurt ɗin nan.

“Eh soja ce”

maryam ta gyaɗa kai cikin gamsuwa, ƙwaƙwalwarta na hasko mata wannan hoton nasu da ta gani shida ita, wanda jta ɗin kesanye cikin kayan sojoji.

“Shima mijin nata soja ne”

“Lalle kam”.

“Tare muka taso da ita, duk da ba sosai muke haɗuwa a india ba, amma muna haɗuwa a abuja, dan ina zuwa hutu a gidansu, kuma itama da ta gama secondary a nan india ta koma taci gaba, sosai na shaƙu da ita, kamar wata ƙanwata da muka fito ciki ɗaya haka nake ɗaukarta”

Wayarsa ce ta yi ƙara dan haka ya kai haannu ya ɗauka, a lokack guda yana aje bowl ɗin hannunsa, Khabir ne ke kiransa ya ɗaga da sallama a bakinsa.

“Kaifa baka san zaman lafiya, yanzu sbd Allah jiya fa na dawo, amma shine kake wannan magamar”

Shine abinda ya faɗi bayan ya gama sauraron Khabir ɗin, ya kuma yin shiru yana sauraren nasa.

“Shikenan Allah kai mu goben”

Daga haka ya sauƙe wayarsa, ya kalli Maryam da take kallon tv.

“Gobe da yamma ki shirya, zamu fita”

Kalmar ‘fita’ ita tafi yiwa Maryam daɗi, dan tun da ta sako ƙafarta a Alaro city bata ƙara fita ba, ko saloon ɗin da suka je a cikin Alaron yake.

Taji dadi sosai, ko ba komai ta samu dalilin da zata saka chickankari ɗinta, dan shi yafi mata kyau fiye da saree ɗin, ta ƙudirce a ranta cewa bazata saka saree ɗin nan ba, to a wani dalili ma?, haka kawai, ita bama ta iya ɗaura shi ba, kuma bazata iya saka shi ba da wannan gajerar blouse ɗin da bata kai cibiya ba.

Birnin taraiyya, Abuja

Da 09:00pm

Heleen ce tsaye a ƙofar wani tsohon gini, bayan ta kuma yaranta ne guda biyu, gabaɗaya ranta a b’ace yake dan ita ta yi niyyar komawa lagos jiya, amma ogansu Ya roƙeta da kada ta dawo ta bari su gama aikin tukunna, dan haka ta haƙura, amma ta yi alƙawarin sauƙe bacin ranta akan wanda suka zo farmaka.

Sanye take da baƙar tank top, sai wani baƙin legging, wannan kalbar attachement din ta ɗaureta da ribbom, ƙafarta sanye cikin takalimin timberand boot, hannunta na dama riƙe da bindigarta ƙirar pistola.

“Zamu iya shiga Oga”

Ta gyaɗa masa kai tana saka bullet a cikin bingidar, sannan muryarta Ta fito cike da umarni.

“Muje!”

Itace a kan gaba, su kuma suna bayanta yayinda suma suke riƙe da bindigar. Kan me uwa Da wabi kawai suka shiga yi a cikin wajen, duk wanda su ka yi karo dashi sai sun sammasa alburishi.

Da haka har suka ƙarasa gaban Ogan nasu, wanda yake pointing ɗin Heleen da bindiga, babu ƙwayar tsoro a idonta ta tunkareshi, an jima da wuce lokacin da za ta ji tsoro, sanda zata shiga ƙungiyarsu ta aje tsoronta.

Hannunsa sai karkarwa yake yana nunata da bindigar a lokaci guda kuma yana ja da baya, Heleen bata fasa tunkararsa ba, da haka har saida ta cimmasa.

Kuma tana ƙarasa gabansa bata jira komai ba, ta ɗago da ƙafarta ta daki hannunsa, bindigar ta faɗi can gefe, Ya juyo ta kalleta bayan ya kalli bindigar dake yashe a ƙasa, babu alamun rahama ko imani a idon ta, kallonsa take cikin ido.

Hannunsa Ya ɗaga zai roƙeta kan ta yi haƙuri ta masa afuwa, bata bashi damar magana ba, ta sakar masa naushi a fuska, sannan ta masa wani a ciki, kafin ta riƙe wuyansa da hannunta ɗaya ta ɗaga shi sama.

Ya shiga kakarin mutuwa yana riƙe hannunta dan Ya shaƙu sosai, sakinsa ta yi tana dukansa a ƙafarta. Ya faɗi ƙasa timm!, ta gyara tsaiwarta tana zaro bullet haɗi da lodawa a cikin bindigarta, dan ta ƙarar da wanɗa ta loda ɗazu.

“Me yasa kaci amanar mu ?”

Muryarta ta fito cikin wani irin b’acin rai, kuma bashi take kallo ba, bindigarta data ɗaga sama bayan ta loda bullet take kallo, cikin shaƙaƙƙiyar muryar da taci azaba yake faɗin.

“Na roƙe ki Heleen, kiyi min…”

Ji kake tass!, ta sakar masa bullet a ka, bindigar tata har hayaƙi take.

“Oga ai bai gama bayani ba kika sheƙe shi”

“Bana buƙatar bayaninsa, shine ya zama katanga tsakanina da ganin Tafida, ba shi kaɗai ba, duk wanda yaso Ya raba tsanani da Tafida irin sakamakonsa kenna”.

Abuja

“Mom lafiya kuwa ?”

Mero ta ɗago ta kalli Kamal dake tsaye a gabanta, Kamal kam kawai ƙare mata kallo yake, ta rame ta yi wani baƙi, gaba ɗaya basa gane mata a cikin kwanakin.

Zama ya yi akan kujerar da take, kusa da ita yana ci gaba da kallonta.

“Mom, ki faɗa min, meke damunki wai ?”

Mero ta sauya hannunta na dama da na hagu wajen tare hab’arta, sannan muryarta ta fito cike da damuwa.

“Hanama ce Kamal”

Hanam ?, wai yaushe yarinyar nan zata barsu su huta ne ?, ta bar gidan ma amma bata bari sun huta ba?.

“Mom Ya kamata a ɗauki mataki, dan shima mijin nata Ya takura min a wajen aiki”

“Shi arnen ?”

“A’a Mom, uche musulmine, yana sallah”

Ta tab’e baki, dan ita wannan ba matsalarta bace, Uche ko me kamarsa basa gabanta.

“Yanzu miye abin yi ?”

Ta ɗan juyo ta kalleshi kaɗan.

“Babu Kamal, babu abinda zamu iya”

Girarsa na tattarewa waje guda yake faɗin.

“Ban gane ba, babu ?!”

Itama ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa.

“Babu, mu barsu da balinsu, kaga akan Hanam ɗin nan aurena ke gil-gilwa, dama an yanke min igiya ɗaya sbd uwarta, sauran biyun ma gasu suna shirin tsinkewa”

“Yanzu me Ya faru ?!”

“Abban ku baya min magana, ya yi fushi da ni, ko nice da girki idan na kai masa abinci baya ci, na kasa gane kan bawan Allahn nan, kaga fa da duk abinda nake mata tun tana ƙarama bai tab’a cewa komai ba, sai de ya ɗanyi b’acin ransa na kwanaki, daga nan komai Ya wuce, amma, banda yanzu”

Kamal Ya sauƙe wani numfashi.

“To wai ni taya ma a ka yi Ya sani ?”

“Jabeer ɗin ne ya faɗa masa mana, kaga fa saida na gargaɗeshi da kada Ya ƙira sunana amma, dan sh**yar sai da ta faɗa”

Ta ƙarashe da ƙwafa, Kamal ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba, yana tunani.

*****

<< Yadda Kaddara Ta So 23Yadda Kaddara Ta So 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.