Skip to content
Part 31 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Washegari.

Da misalin 04:00am

“Miriam!”

Kamar a mafarki ta ji ana kiranta, sunan da aka ƙara kira yasa ta buɗe idonta a cikin hasken ɗakin, har yanzu suna asibitin nan, idonta yaci gaba da yawatawa a cikin ɗakin, kafin suka sauƙa akan Tafida dake riƙe da hannunta, ɗayan hannun nasa kuma yana shafa sumarta data baje akan pillown da take kwance.

Duk abinda ya faru jiya ya dawo mata sabo, ta tuna yanda bayan ya mata wannan abun ta nemi ciwon ta rasa, bayan nan kuma ya samu waje ya zauna a ɗakin yana gadinta.

Amma kuma ba’a ɗakin ya kwana ba, dan ta farka cikin dare taga baya ɗakin.

Kuma sau biyu tana farkawa bayan nan, duka bata ganinsa a ɗakin, sai yaunzu da yake tashinta. Ƙwayar idonsa taga ta sauya zuwa ja, hakan yasa ta kauda nata idon daga cikin nasa.

“Ki tashi ki yi sallah…”

Kanta kawai ta gyaɗa masa, tana jira taga ya fita daga ɗakin ta koma baccinta, dan fashin sallah take, amma sai taga ya samu kujerar dake ɗakin ya zauna yana kallonta.

Maryam ta kasa ko motsi, duk da ciwon da take jinsa babu, saide wuyanta dake mata ciwon shima kaɗan.

Tafida yaci gaba da kallonta da shanyayyun idanuwansu, dan bacci yake ji sosai, jiya bayan ya tabbatar da ta yi bacci ya gyara mata kwanciya haɗi da mata kiss a goshi, sannan ya fice, ya tafi can saman rufin asibitin ya yi jinyar kansa, dan duka ciwon jikinta baƙin ruhin nan ya shanye, sannan kuma yake sakar masa a nasa jikinsa.

Bai damu ba, indai har Miriam ɗinsa zata samu sauƙi, burinsa shine samun sauƙinta, ko da kuwa shi zai cutu, ganin an shafe kusan minti goma sha ba tare da ta tashi ba yasa ya gyara zamansa da kyau yana kallonta.

“Ko ba zaki iya tashi ba ?”

Maryam ta girgiza masa kai

“Zan iya mana…”

Tun jiya sai yanzu muryarta ta fito, kwata-kwata ta rasa magana jiya sbd azaba, dan ji take kamar idan ta yi maganar wani ƙashi zai karye a wuyanta.

“To ki tashi mana“

“Umhm, zan tashi ai“

Sai kuma ya koma ya jingina da jikin kujerar yana ci gaba da kallonta,wani tunani ya haska a cikin kansa, dan haka kawai sai ya yi shiru, ya lumshe idonsa dan yana buƙatar komawa bacci.

Maryam ta ɗan juyo ta kalleshi jin ya yi shiru, sai ta ga kamar bacci ma yake, idanunsa a rufe, ga yanda numfashinsa ke fita a hankali.

Sai ta samu kanta da kasa dena kallonsa, ya ƙara ƙiba a kan yanda ta san shi da, dan yanzu har ɗan wani kumatu ta ga ya yi, kamar yanda ta saba ganinsa, yauma sanye yake cikin ƙananun kaya, wani plane brown yadi ne a jikin nasa, kansa babu hula, dan yanzu ta lura da baya saka hula sosai, wata ƙila sbd gashin da ya tara ne, dan yanzu ma gashin ya sauƙo masa, daga gaba a kan goshinsa, daga gefe a kan kunnuwansa, daga baya kuma a kan wuyansa.

Hannunsa na dama ɗore a kan cikinsa, wannan stamped bracelet ɗin ɗaure a hannunsa kamar kullum, rubutun dake jiki an rubuta shi da manyan baƙi ‘TAFEEDAH’, shine abinda aka rubuta ɗin, idonta ya kai kan ƙafarsa, wannan baƙin zaren da ta lura baya rabo da shi ɗaure a ƙafarsa ta dama.

Sai kuma idanuwanta suka yi sama zuwa kan fuskarsa, taci gaba da kallon yanda fuskar tasa ta yi yayin da yake baccin, kamar wani baby me jan kumatu haka ya koma.

Sai taji inama su dawwama a haka, yana baccinsa yayin da ita take kallonsa.

HARIS POV.

“Iza ana bi kun zaujek, la takriji min hun!”

(inde har nine mijnki, kada ki fita daga nan!)

Haris ke maganar cikin wani iko, yana kallon Hanam, wadda ta juya zata fita daga falon Abba.

Hanam ta rintse idonta, tare da juyowa, Yau ake kwana bakwai da rasuwar Abba, kuma tana zaune a ɗakinta na gidansu ita da su Falaƙ, wayar Haris ɗin ta sameta, yace tazo falon Abba yana san ganinta, shine ta sa’ba hijabinta ta nufi falon, tana shiga falon idonta ya sauƙa a kan mutanen dake falon, gaba ɗaya ‘yan uwanta wanda suke uba ɗaya ne, matan babanta guda biyu, Baba kakansu da kuma ƙannen Abba, a takaice de duka ‘yan uwanta akwaisu a falon, saide ba wannan bane abinda yasa ta yi yunƙurin fita ba, Massarat da ta gani ita da yaranta uku ne yasa ta juya.

Ta zuba idonta a kan Haris wanda ya haɗe girar sama da ta kasa.

“Ki dawo ki zauna”

Yanda yake mata maganar cikin iko yasa ta haɗiye wani abu, bazata iya masa musu ba, dan haka ta dawo a hankali ta zauna a kusa da shi, domin shi a ƙasa kan carpet yake zaune.

Babane ya soma magana, ya yi musu nasiha da kuma ta’aziyya, kafin ya kawo musu maganar yanda gidan zaici gaba da tafiya bayan rasuwar Abba, sun yanke cewa Kamal ne zai ci gaba da kula da Hakuɗau group of industries, tunda shine babba, kuma Baba ya umarce shi da ya yi aure.

Daga nan ya shiga ƙoƙarin sallamar su, amma sai Haris yace aa kowa ya zauna, suka zauna ɗin suna binsa da kallo dan jin abinda zai faɗi, Hanam ya kalla sannan ya kalli Masarrat.

“Hanam, atazri min immik, Ki nemi yafiyar mahaifiyar ki”

Ya faɗi cikin harshe biyu, Hanam ta kalleshi sannan ta kalli Masarrat ɗin, wadda a cikin kwanaki ukun ta rame, sai ido ga fuskarta jawur da ita, Haris ya bawa kowa mamaki, musamman ma Baba, dan wannan shine abinda ya kamata ace ya yi tun farko.

“Ba kiji bane, nace ki nemi yafiyarta!”

Bata ce komai ba, sai kallonsa da take, bisa ga dukkan alamu baisan abinda matar nan ta mata bane, amma babu komai zata zauna ta bashi labari dalla-dalla, kuma tana da tabbacin zai goyi bayanta idan har ya ji abinda Masarrat ɗin ta mata.

“Masima’ati ? (Bakiji bane ?), Kome zata miki tana nan a mahaifiyar ki, koda zata ɗauko wuƙa tana yankar naman jikinki, bazata tab’a canjawa daga wannan matsayin ba, kisani idan fa har tana fishi da ke to Allah ma fishi yake da ke, kuma duk abinda zata miki ke baki isa kin yi fishi da ita ba, sai de ma ke ki bata haƙuri, ba dan ni ba, ba dan na isa ba, ki bata haƙuri”

Maganar ta doketa, bama ita kaɗai ba, harma da kowa dake wurin, nan take ta fara hawaye, babu abinda ya faɗa wanda yake ba dai-dai ba, dan haka ta ɗago da kanta tana sharar hawaye, ta kalli Masarrat wadda take a tsallakenta, sannan tace.

“Ana asfe immi, bitmanna inik tisamihini”

(ina me baki hakuri Mamana, kuma ina fatan zaki yafemin).

Masarrat ta fashe da kuka ta miƙe tsaye ta ƙaraso kusa da ‘yarta ta rungumeta, Hanam ta saki wani kuka a lokacin da tajita a jikin mahaifiyar ta, haƙiƙa ɗumin uwa da ban yake, ashe haka Arya yake ji a duk sanda yake hannunta ?, da ace tana samun irin wannan ɗumin to da duk wata damuwa ta duniya bazata dameta ba, me yasa Masarrat ta rabata da wannan ɗumin ?, me yasa ta nisance ta ?.

“Ana yalli rah uɗulubu samah minnik ya binti, anal galɗane”

(nice zan nemi yafiyarki ‘yata, nice me laifi)

Ta faɗi a lokacin da ta saketa, Hanam ta girgiza mata kai.

“A’a immi, baki da lefi, Allah ya yafe mana”

Kowa saida ya share ƙwalla, dan tsabar tausayi, Masarrat tabi kishiyoyinta ɗaya bayan ɗaya tana neman yafiyarsu, haka ma Baba, kuma duka sun yafe mata, su Mero ma sun nemi yafiyar Hanam, itama kuma tace ta yafe musu.

“Ya walad ta’al ila hina”

(kai yaro, zo nan)

Hanam ta faɗi tana kallon ƙanenenta, gaba ɗayan su suka taso zuwa wajenta, ta rungumesu tana kuka kafin ta sake su tana kallon su.

“Shu ismiki inti ?”

(menene sunan ki?)

Macen me tsananin kamarta ta tambaya, yarinyar na kallonta tace.

“Salwa”

“Wa inti ? (kai kuma fa?)”

Ta tambayi babban.

“Ana Al’amin”

“Wa ana Khalil”

Ƙaramin ya amsa mata tun kafin ta tambaya.

“Wa ana bi kun…”

(ni kuma suna…)

“Hanam”

yaran suka katseta a tare, ta yi dariya cikin kuka tana shafa kansu, ɗaya bayan ɗaya tabi ta sumbaci kawunansu.

“Ammi ƙalat na inik uktina”

(Ammi ta fada mana ke yayarmu ce)

Macen me zaƙin murya ta faɗi, Haman ta gyaɗa musu kai.

“Ana ukutukuml kabira”

(Ni yayar ku ce)

“Haz bi kun ibnik ?”

Wannan ɗan ki ne?

Al’amin ya tambaya yana nuna mata Arya dake hannun Rafi’a, Hanam ta kalli wurin da yake nunawa, Arya sai sabgar gabansa yake, tunda Abba ya rasu bata ƙara ɗaukarsa ba, jiya ba ma ta ganshi ba kwata-kwata, sai yau ta ganshi a wurin maman Uchenna da ta zo ta mata ta’aziyya, kuma Uchennan ya faɗa mata cewar Arya ɗin yana wurin maman tasa ne, sai ta juyo ta kallesu tare da gyaɗa musu kai.

“Bishbahani mu ?”

Yana kama da ni ko?

Khalil ya dungurewa Salwa kai.

“La, huwa bishbahani ili”a’a dani yake kama

“Ya kazzab kras wulaik, huwa ibni wa bishbahani ili mu intim”

(Kai taron makaryata kumana shiru, wannan fa ɗana ne, dani yake kama ba ku ba).

Cewar Al’amin, Hanam ta yi dariya, dan musun nasu ya bata dariya, irin wannan farin cikin take buƙata, ta daɗe tana nemansa kuma bata samu ba sai bayan rasuwar Abba, inama a ce yana raye, ya ganta cikin yan uwanta, tana dariya da raha, sai kuma ƙunci ya mamaye fuskarta, a cikin zuciyata ta ƙara nemawa Abba rahamar Allah.

Ɗaya bayan ɗaya aka shiga watsewa daga falon, bayan da su Al’amin suka gama musun su akan da wa Arya yake kama a cikin su, Kuma har suka fice musun bai ƙare ba, dan Arya ɗinma a hannun Salwa yake.

Ya rage daga Haris sai ita sai Baba, Baba ya shigayiwa Haris godiya akan yanda ya haɗa kan iyalin ɗan nasa, kafin shima ya tashi ya fice.

Hanam taci gaba da kallon Haris, wani abu na yawatawa a kanta, wai me Abba yace mata ne ?, cewa ya yi bai tab’a zab’a mata abunda yake mara kyau a gareta ba, yanzu gashi tana gani.

Wannan ɗin da Abba ya aura mata shine ya zama silar shiryawarta da mahaifiyar ta, da ‘yan uwanta ma baki ɗaya. Shima ɗin juyowa ya yi ya kalleta, Hanam ta saka hannunta na dama a cikin nasa.

“Na gode Harees, Allah ya biya ka abinda ka min”.

Kansa ya girgiza mata sannan yace.

“Duk abinda zan yiwa Abba ban faɗi ba Bannute (baby girl), Abba ya yi min komai, ya zamemin uba a sanda nawa ya ƙini, burinsa shine yaga kan iyalansa a haɗe, kuma shine abinda yake ta ƙoƙarin yi a sanda yake da rai, amma haƙarsa bata cimma ruwa ba, ni kuma na cika masa hakan, wata ƙila ruhinsa zai samu salama”.

Hanam ta kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Kasan me yasa muka b’ata da immi ?”

Tana jin sanda ya girgiza mata kansa dake kan nata, sai ta ci gaba.

“Ok zan ba ka labarin…”

<< Yadda Kaddara Ta So 30Yadda Kaddara Ta So 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.