Skip to content
Part 32 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Flash Back

Muhammad Hakuɗau, ya kasance ɗan kasuwa ne a da, sannan kuma ministern ƙasashen waje wanda yake zaune a Egypt, Yana da mata ɗaya da yara uku, na miji ɗaya mata biyu, iyalan nasa a nigeria suke da zama, yayinda shi yake can Egypt, sai dai yakan dawo gida ziyara.

Ana haka sai ya haɗu da wata matashiyar balarabiya ‘yar asalin ƙasar Egypt, me suna Masarrat, suka fara soyyaya, wadda ta kaisu ga aure, daga b’angaren iyayensu sam basu samu matsala ba, sai de masiffafen kishin Masarrat da ya basu cikas a zamansu.

Tun kafin suvyi aure ya sanar mata da ya na da mata harda yara, kuma ta amince ta aureshi, Duk da ba’a gari ɗaya suke da kishiyar tata ba, amma kullum cikin kishi take, sbd san da Muhammad yake mata yasa a kullum yake bata baki, yana nuna mata cewar shi ita kaɗai yake so, domin kuwa matarsa ta farko wato Mero ladan noma ce.

Ana haka har tenure ɗinsa ta ƙare, ya dawo gida nigeria da matarsa Masarrat, ya koma kan harkar kasuwancinsa domin dama ya fi ƙarfi akanta. A sanda suka dawo Masarrat tace ita baza ta zauna a gida ɗaya da Mero ba, haka Muhammad ya biye mata ya saka ta a ɗaya daga cikin gidajensa.

Duk da ba a gida ɗaya suke ba kullum sai ta haɗa Mero da Muhammad faɗa, ta koma gefe tana jin daɗi,har ta kai wata rana Muhammad ya saki Mero, Baba mahaifin Muhammad ya saka shi da ya maida ta, kuma ya ƙara umartasa da sake aure, duk da ba haka Muhammad ya so ba, amma koda wasa baya bijirewa mahaifinsa.

A lokacin Masarrat nada juna biyu, Muhammad yazo ya sameta da maganar, ta yi tsallen albarka ta dire a kan ita ba zata zauna da kishiya ba, Mero ma kaɗai ta isheta bare ace za’a ƙaro mata wata, babu yanda Muhammad be yi ba wajen ganin ya rarrasheta amma fur taƙi tace ita bata san zance ba, daga ƙarshe ma tace sai ya saketa.

Hankalin Muhammad ba ƙaramin tashi ya yi ba a lokacin, ya yi-ya yi da ita a kan ta rufa masa asiri ta bar maganar sakin nan, amma tace ita sai de a yi wacce za’ayi, amma bazata yarda ba, dama ita ba san zaman nigeria take ba, ta gaji.

Muhammad yace ya yarda zai saketa, amma ta haƙura ta haihu tukunna sai ya saketa, tace; to taji ta yarda. Abunda ya ƙara dagula zamansa da ita shine umarnin da Baba ya bayar a kan ya haɗe duk matansa gida ɗaya, haka ya dawo da Masarrat cikin gidan, bayan an aura masa Hajjo.

Masarrat ita ke juya matan, duk wadda bata bita sauda ƙafa ba saita haɗata da Muhammad, haka suka jure har zuwa sanda ta haihu, wahse garin ranar data haihu tace ita zata koma Egypt, dama ai yace ta bari ta haihu to ta haihu, dan haka ya saketa ta ƙara gaba.

Babu yadda Muhammad ze yi, duk da yana san matarsa, amma kuma ita ta buƙaci hakan, ba zai iya mata dole ba, dan haka ya saketa ta ƙara mai, ta barshi da ƙaramar jaririya sabuwar haihuwa.

Haka ya dinga bin matansa ɗaya bayan ɗaya a kan su temaka su reni jaririyar tasa amma kowace tace Allan baran bata san zance ba, duk irin yanda mahaifiyarta ta wahalar dasu kuma yanzu ace su riƙe mata ya?.

Haka Muhammad ya a je komai nasa ya shiga kula da jaririyar da ya sakawa suna Hanam, shi yake mata wanka, ya bata madarar yara, ya wanke mata bayan gari idan ta yi, komai nata shine, har yarinyar ta fara tasawa sannan ya sakata a makaranta.

Hanam ta taso cikin tsangwama ta ‘yan uwanta dama matan babanta, sai de kuma tana samun sauƙi a wajen Abbanta, domin komai take so yana mata, bata tab’a nemar abu a wajensa ya hanata ba, kullum burinsa ya faranta mata.

Da haka har ta girma ta isa shiga jami’a, Abban nata ya tambayeta me take san ta karanta ?, tace Fashion design, haka taje ta yi karatu akan fannin data zab’a, bayan ta gama shi da kansa ya buɗe mata fashion house.

*****

“Abba bai tab’a baka labarin ba ko ?”

Haris ya gyaɗa mata kai.

“Bai tab’a bani labarin ba, saide ya tab’a faɗamin cewa da ya yi zaman egypt, shine na tambaye shi ya iya larabci?, yace min; ya iya, nace masa ina san naa koya, to shine fa ya koya min, amma ni bai tab’a bani labarin ba”.

“A duk sanda akamin gori a kan cewa Masarrat ta tafi ta barni ina jin haushi, sai kuma daga baya na dena jin haushin, duk wanda zaimin magana a kanta sai nace masa ni ba babata bace, da wannan ƙaryar na samawa kaina lafiya, lakin ta’azabti katir (amma na azabtu sosai)”

“Kada ki damu Bannute(Baby girl), bayan wuya sai daɗi”

Hanam ta ɗago da kanta ta kalleshi.

“Abba ne ya faɗa naka wannan sunan ko ?”

Yana ƙunshe dariya yace.

“A’a, me kika ga ?”

“Shi kaɗai ne yake faɗamin sunan, kuma yasan cewa bana so”

“To yanzu miye laifin bannute?”

“A’a yana da laifi mana, a wurin faɗi a baki bashi da daɗi, fasararsa ce kawai me daɗi”

Kiris ya rage Haris bai ƙyalƙyale da dariya ba, tun ba yau ba idan suna hira da Abba yana bashi labarin ta, a cikin labarin da yake bashi ne ya faɗa masa cewa bata san sunan Bannuten da yake faɗa mata, kullum cewa take sunan ba daɗi.

“Gwara ma kace Binit(girl), amma wai Bannute?”

Shide be ce mata komai ba, sai murmushin da yake mata.

*****

Lagos

(Eshaan & Maryam)

So i walk into dead of night

where my monsters like to hide

chaos feels so good inside now i know

I’ve lost, I’ve lost, I’ve lost control again

always do the same and not to blame, I’ve lost control again

i don’t, i don’t, i don’t know who i am

Always do the same and not to blame I’ve lost control again.

Daddaɗar wakar I lost control ce ke tashi a cikin Mpn motar, a hankali muryar Tafida na rera waƙar tare da Alan Walker, Maryam dake zaune a gefensa kanta jingine jikin kujerar motar, ta ɗan juyo ta kalleshi, ita gaba ɗaya kiɗan waƙar hawa mata kai yake, dan har yanzu kanta ciwo yake mata.

Ɗagowa ta yi ta kai hannu ta danna next.

Yaa man sallyta bikullil anbiya

Yaa man fii qalbika rahmatul lin naas

Yaa man allafta quluuban bil islam

Yaa habiibii ya shafii’ii ya rasuulallah

Bi ummii wa abii

Fadaytuka sayyidii

Salaatun wa salaam alaikaa ya nabii

Habiibii yaa Muhammad

Waƙar rahmatun lil alamin ta shiga playing, alamun de itace next ɗin, Maryam ta koma da baya ta jingina da jikin kujera tare da lumshe ido, tana san waƙoƙin Mahir Zain.

Tafida ya yi wani guntun murmushi yana ci gaba da tuƙinsa, Neha ce ta faɗo masa a rai, dan itace take masa irin wannan, a duk sanda zasu yi tafiya a mota inde zai saka waƙa to sai ta sauya masa.

Sallalahu ala katimul anbiya

Muhammad, Muhammad

rahamatull lil alamin

rahmatul lil alamin

Fatar bakinsa ce take so ta motsa wajen bin salatin, amma ya kasa, shida yiwa fiyyayen hallita salati sai a cikin sallah, baya istigfari bare yabawa Allah, wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da kansa ya ji kamar shi me lefi ne a wurin Allah, duk da yasan cewa ba shine ya ɗorawa kansa hakan ba, amma yana jin babu daɗi sam.

Yanata saƙe-saƙe har waƙar ta ƙare, wata ta shigo, still itama ta Mahir Zain ɗin ce.

I Praise Allah for sending me you my love

you’ve found your home it’s here with me

And I am here with you

Now let me let you know.

Siririyar muryar Maryam ta shiga maimaita waƙar amma a hankali, tana yi yanda Tafida ba zai ji ba, a zatonta kenan, yau mutumin dake jin bugun zuciyarta ma har waƙar da zata yi da bakinta ce ba zai ji ba ?

Kuma yaji ɗin, sai shi kuma ya shiga rera waƙar a fili ta yanda za ta ji shi.

Finally now I’ve found my self, i feel so strong.

Yes everything was changed when you came along oh oh.

And there’s a couple of words i want to say.

Ita kuma ganin hakan yasa ta yi shiru tana sauraronsa.

Daga haka har suka ƙaraso cikin Alaro city, ba gida ya nufa ba, sai ya nufi makarantar su Maryam, a inda ya saba tsayawa ya tsaya, sannan ya kai hannu ya kashe waƙar Golden hour ta JVKE dake playing a lokacin.

Ya fuskanci Maryam, wadda itama ta juyo ta kalleshi, idonsa manne da sun glasses ta lura da yana yawan san saka baƙin glasses, ko kuma sbd idon nasa na sauya kala ne ?, Oho.

Gira ɗaya taga ya ɗaga mata alamun miye?, sai ta girgiza masa kai, ta kai hannu zata buɗe motar amma sai ya danna lock.

Ta juyo tana kallonsa, taga yama juya ya jingina da jikin kujera tare da harɗe hannayensa a ƙirji.

“Zan fita ne fa…”

Sai ya ɗago daga jikin kujerar, ya juya seat ɗin baya na motar, ya ɗauko jakarta da wata leda, ya miƙa mata jakar tare da faɗin.

“Ga jakarki ta makaranta”

Maryam ta ɗanyi murmushi tana dafe goshinta, shaf ta mance, kawai de da za su taho daga asibitin yace mata makaranta zai kaita tunda suna da exams. Sai Tafida ya ƙara miƙo mata ɗayar ledar.

“Wannan kuma abinci ne, ki tabbatar kinci shi da rana, jiya ina sauri ne shi yasa ban ɗauko miki lunch box ɗinki ba, kuma bayan kinci abincin ki sha magungunanki, suna cikin ledar su ma, and na rubuta miki yanda zaki sha kowwanensu”

Maryam ta karb’i ledar, ɗanzu kafin su bar asibitin ma saida yasa ta taci abinci, sannan ya ɗauko kuɗin da ya saba bata a kullum ya kamo hannunta ya ɗanka mata yana faɗin.

“Wannan kuma kuɗin kashewarki ne”

Maryam ta janye hannunta daga cikin nasa, ita fa har yanzu kullum idan ya bata tarawa take, dan ba komai take siya da kuɗin ba, sai abinda baza’a rasa ba, duk abinda take buƙata sai dai idan bata kirashi ba, amma daga zarar zata kirashi ta sanar masa ko baya gidan zai saka Devid ya kawo mata.

“Nagode Shona (Sweetheart)”

Tafida yaci gaba da kallonta kawai yana jin wani abu da bai san sunansa ba na yawata a zuciyarsa.

“Wifey”

“Umm!”

Sai kuma ya yi shiru dan bashi da abin faɗi.

“Am ka cire min canular nan”

Ta faɗi tana nuna masa canular, kansa ya girgiza mata.

“A’a ba yanzu ba, idan anjima zan miki wata allura”

Bata ƙara cewa komai ba, shima kuma baice ɗin ba, ya buɗe mata motar, har ta buɗe motar zata fita ya kuma kiran sunanta, ta juyo.

Kuma tana juyowar bai jira komai ba, ya saka hannayensa biyu ya tallafo fuskarta ta ko wani b’angare, sannan ya kara fuskarsa a kan tata, suka shiga musayar numfashi.

Maryam ta rintse idonta tare da matse leda da jakar dake hannunta, wata ƙila Tafida yana so ya kaita kushewarta ne, nan take jikinta ya ɗauki zafi, kamar me shirin kamuwa da zazzab’i, sannan wani sanyi ya shiga ratsawa ta jijiyon jikinta, kowace gab’a ta jikinta ta shiga rawa.

“Miriam, i am nuts about you”

Cikin wata ƙarama kuma kasallaliyar murya ya furta hakan, Maryam ta shiga cikin ƙwaƙwalwarta ta yi shawagi ko zata nemo sunan wannan abun dake faruwa da ita, amma bata samo ba, kuma kafin ta dawo daga neman abinda ta je.

Tafida ya karkatar da kansa gefe kaɗan, hancinsa ya dawo gefen nata, sannan leb’ensa ya sauƙa a kan nata, kuma beyi wata-wata ba ya yi kissing lips ɗinta, kafin ya yi bakin nata duka.

Sannan ya saki bakin nata ya ja baya yana sakin fuskar tata, ya koma yana zauna da kyau a kan kujerarsa, Da sauri Maryam ta juya masa baya, Wata kunya da taraddadi da kuma ruɗani suka lillib’eta a lokaci guda, kuma ko sakan biyar bata ƙara a motar ba ta yi fit!, ta fice.

Har ta b’ace masa da gani yana kallonta, sannan ya dawo da baya ya kwanta a jikin kujerar motar, ya lumshe idonsa yana tura sumar kansa baya, ya furta abinda ya saba furtawa a yawancin lokuta.

“Hai fagban!”

(Oh god,!)

Wani abu yake ji a kan Maryam wanda bazai iya kiransa da so kawai ba, wannan abun yafi ƙarfin so, for the first time a rayuwarsa ya haɗa baki da wata mace, abune da koda wasa bai tab’a sanin ya yake ba, bai tab’a yi ba sai yau, yau ɗinan kuma ba da kowa ba, sai da Miriam ɗinsa, halalinsa, mallakinsa.

Maryam na tafe ne kawai amma bata san ina take shiga ba, dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi can wata uwa duniya.

Hannunta na dama wanda yake riƙe da jakarta ta ɗago sannan ta mayar da jakar hannunta na hagu, wanda ke riƙe da ledar abincintabda magani, ta ɗora na daman akan lips ɗinta, tana jin labarin kiss, amma bata san ya yake ba sai yau ɗin nan, yau dlɗin da Tafida ya mata.

Tafida ? Kiransa ma kawai da tunaninta ya yi ta ji wata uwar kunya ta lullub’eta gaba ɗaya, goshinta ta daka, wata ƙila hankalinta ya dawo jikinta, ta fuskanci abunda ke gabanta.

Duk jikinta ya yi tsami, dan akwai sauran ciwo a jikinta, domin ko wuyan nata a ƙage yake, kawai dai babu raɗaɗi irin na jiya ne, sai ciwon kan da take ji, kuma shi tun bayan da wannan mara’imanin ta buga mata shi a bango yake mata ciwo har yanzu.

Wait, wait!, wait!, wacece ita ?, and me yasa ta mata haka ?, kuma Fidar Yara yace shine silar abinda ya sameta, me yasa ?, tana san sani, tabbas tana so ta sani, Sai kuma ta ture kowani tunani a sanda ƙafafunta suka tsaya a ƙofar ajinsu, tasan yau exam zata bata wahala, dan bata yi karatu ba.

Sai da ta haɗiye wani abu sannan ta saka ƙafarta a ajin.

<< Yadda Kaddara Ta So 31Yadda Kaddara Ta So 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.