Skip to content
Part 35 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

MARYAM POV.

Sallah taje ta yi sannan ta zauna a ɗakinta tana tunani, tunanin da ita kanta bata san na miye ba, bisa ga dukkan alamu Tafida ya gama zautata.

“Meriuty!, Mariuty!!”

Iko sai Allah!, idan da wani me ikon ma to shi ya yi shi, yau kuma Meriuty ta koma ? Ta tab’e baki sannan ta miƙe, dama bata cire hijjabin ta ba, dan haka ta nufi ƙofa.

A ƙofar ɗakinsa ta ganshi tsaye, zuwa yanzu gashin kansa ya bushe, amma yana nan baje a kan goshinsa.

Kuma yanzu ƙwayar idonsa ta koma ja gaba ɗaya, kana kallonta yake da jajayen idanuwan nasa. Cikinsa ya shafa yana faɗin.

“Yunwa na ke ji”

Dariya ta kama Maryam, amma sai ta riƙeta, sosai take mamakin yawan cin abincinsa. Bata ce masa komai ba ta yi hanyar sauƙa ƙasa, yabi bayanta yana mata mitar yunwar da ya ke ji.

Abincin ta zubo masa sannan ta kawo masa, ya karb’a , ta yi hanyar komawa stairs ya riƙo hannunta.

“Yau ɗaya dai mu ci abinci tare pls”

Maryam bata ce masa komai ba sai kawai ta tsaya kanta a ƙasa, sannan ta miƙa hannunta alamun ya bata.

“Me zan baki ?”

Ta ɗago da kanta ta kalleshi

“Tray, gani na yi kamar abincin ya mana kaɗan mu biyu”

Shima bai ce komai ba sai ya danƙa mata, ta koma kitchen ɗin, shi ma kuma ya bi bayanta, plate ta sauya ta ƙara musu abincin, sannan ta ɗauko musu ruwa da cake parfait ɗin nan, ta ɗora a kan tray ɗin.

“Muje”

Sai ya girgiza mata kai yana karb’ar tary l ɗin daga hannun ta.

“Follow me!”

Maryam ta ga ya yi hanyar ƙofar baya, sai kawai tabi bayan nasa, Garden suka shiga, a cikin wannan rumfunan na garden ɗin suka zauna kan kujeru, ya aje musu abincin a kan table.

Maryam tabi wurin da kallo, wannan neon strip light ɗin suna ta haske a wurin, ga ruwan dake zuba a wannan water falls ɗin, ga iska me daɗi da bishiyun wurin ke bayarwa, wajen ya haɗu sosai.

Tunda suka fara cin abincin Maryam take murmushi, abu biyu ne ya saka ta murmushin, yanda Tafida ke cin abincin da kuma gida da ta tuna, cin abincin nasa a hankali yake, kamar me tsoron tauna tsakuwa.

“Me yasa ki ke murmushi ?”

Maryam ta haɗiye abincin dake bakinta sannan tace.

“Gida na tuna, yawancin lokuta, da daddare kamar haka, muna zama a kan tabarma, ni, Maanmu, Hussain, Hassan da auta, sanda Anti fati tana nan harda ita, muna saka babban tray me ɗauke da abinci a tsakiya, muna cin abincin kuma muna hira, na yi kewar cin abinci da wani”

Tafida ya yi murmushi, fitulun dake wajen suka haska mata fuskarsa, ya tura sumar kansa baya.

“Sanda na taso a fada ni kaɗai nake cin abinci na, babu wanda yake cin abinci tare da ni, me yasa ?, sbd sarauta, izza, da kuma kama kai, idan ina haɗejia kullum cikin kaɗaici nake jin kai na, babu wajen wasa, babu abokan wasa, saide idan naje makaranta, amma a duk sanda zanje india, to a sannan nake farin ciki, Daadi da kanta take min girki, sannan ta bani da hannunta, kamar de Maana, sanda Maa tana da rai ban tab’a cin abinci da hannuna ba, in dai tana kusa, kode ita ta bani, ko Appa ya bani, a wasu lokutan ma da Neha muke ci tare a gida”

Sai ya yi ‘yar dariya, alamun dai ya tuno wani abun, Maryam taci gaba da kallonsa tana sanbjin abinda ya saka shi dariyar.

“Wata rana muna cin abinci da Neha, Biryani ce Daadi ta dafa mana, a sanda ina ƙarami ina san cin yaji da yawa, sai na dauƙo yaji na shiga zubawa a iyaka inda zan ɗiba”

Yanzu kam dariya ya yi me ɗan tsayi kafin yaci gaba.

“Sai kawai Neha ta saka kuka, nayi-nayi ta yi shiru amma taƙi, sai kawai ta kama kiran sunan Daadi, Daadi ta fito daga kitchen ta na faɗin ‘Me ka mata Eshaan ?’, nide bance komai ba, sai binsu da nake da kallo, kuma inaci gaba da cin abincina, Sai kawai Neha tace ‘Daadi kinga Bhai (brother) ko?!’”

Ya kwatanta maganar cikin kuka, Maryam ta yi dariya shima kuma sai ya yi dariyar yana aje fork ɗin hannunsa, ya tura sumar kansa baya sannan y ɗauki ɗan cup ɗin da cake parfait ɗin nan ke ciki.

“Daadi tace ‘Me Bhai ɗin ya yi ?’ Neha taja hanci sannan ta nuna ni tace ‘Yana cin gun yaji’”

Daya kai karshen sai ya ƙyalƙyale da dariya, Maryam ma ta tabya shi, Idan yana raha da surutu irin haka yana bata mamaki, A koda yaushe yanayin fuskar sa babu fara’a bare annuri, saide kwarjini kawai, kuma ko a fuska bashi da yanayin yawan surutu.

Ya dauki spoon ya gutsiri cake sannan ya kai bakinsa yana taunawa yace.

“Daadi tace ‘Wato shi yake cin yajin amma ke kike jin raɗaɗi?’, Meriuty yajin india yana da zafi sosai, ba duk bakine ke iya ɗaukar yajin ba, amma haka nake iya cinsa a lokacin, ita kuma sai take kuka dan tana ganin kamar ina jin zafin yajin”

Suka kuma yin dariya a tare.

“Yaushe zakubyi final exam ?”

Muryarsa ta tambaya yana tauna cake ɗin bakinsa, Maryam ta ɗago ta kalle shi, shi ba ita yake kallo ba, plate ɗin gabansa yake kallo, wani abu da Maryam ta kula kamar hakan ɗabi’ar sace, sai ya yi maka magana ba tare da ya kalle ka ba.

“Nan da sati ɗaya”

Sai ya jinjina kansa yana ɗagowa ya kalleta.

“Allah ya amsa addu’ata, dan sati saya ne kawai zai rage min a nigeria”

Girar Maryam a haɗe tana faɗin.

“Ina kuma za ka je ?”

“Zamu je dai, bani ba, india zamu je, najima ban je ba, dan nafi shekara ba tare da na je ba, ko auren Neha ban samu naje ba, tun bayan aurenmu Daadi tace min na taho, kuma zuwana a time ɗin ba zai iyu ba, yanzu kuma lokacin da na mata alƙawari ya kusa, ga auren abokina da za’ayi a can, ga gasar world cup na cricket da za’ayi,ga sumar kaina ta isheni, ina buƙatar zuwa india, kuma de kinsa ba zan tafi babu ke ba”.

India ?, kuma wai ita ?, ita Maryam ce zata je india ?, wani iko sai Allah, a ranta ta godewa Allah sannan ta shiga masa kirari, dan Allah abun godiya ne.

HANAM POV.

“Dan Allah mana bannute”

Harees ke maganar cikin sigar magiya, yayin da yake kallon Hanam dake zaune a ɗaki, Hanam ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Nifa ba na san zuwa”

Har iyakar gaskiyarta ta faɗi, da gaske take masa cewar ita bata san zuwa wani Black Friday Fair, Kewace ke damunta, tana kewar Abba da kuma Arya, dan haka bata san zuwa ko ina, ko office ba zuwa take ba, dukuwa da yanda take bawa aikinta muhimanci.

Uchenna ya zauna kusa da ita, sannan ya kamo hannayenta duka biyu yana kallon cikin idonta.

“Bannute nasan me yasa bakya san zuwa, kewar Abba da ta Arya”

Nan take taji ƙwalla na tarar mata a ido, aƙalla de ta samu wani wanda yake iya fahimtar halin da take ciki, a cikin ranta ta yiwa Abba addu’ar Allah yaji ƙansa.

“Abba addu’a yake buƙata, Arya kuma ai ko ɗazu ma naga kunyi waya, ki aje komai Hanam, idan har muka ci gaba da waiwayar baya, bazamu tab’a ci gaba ba”

Hannu yakai ya share mata ƙwallar da ta zubo mata yana girgiza mata kai

“Abba bashi da magana data wuce, Hanam jarumace, bata kuka, tanada juriya, amma ni banga hakan ba”

Ta yi dariya cikin kuka tana kallonsa.

“Ummuahh, ta shi muje kinji?”

Ya furta ‘ummuah’ ɗin a kan bakinsa, ya miƙar da ita zai fara janta.

“Wait bari na ɗauki mayafi”

Ta ƙarashe tana cire hannunta daga nasa, wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko gyale ta ta yafa a kan Farar abayar dake jikinta.

Sannan ta kama hannunsa suka fita.

Kamar yanda yace zata buɗe ido kuma ta samu nishadi, ta samu ɗin, sai da taga wurin wasan yara ne ta ayyana cewa da ace Arya yana nan da sun kai shi wurin ya yi wasa.

Amma babu komai nan da wani watan zata je Cairo, kuma daga nan zata taho da shi.

Gada ɗaya bata jin daɗin komai, babu Abba babu Arya, duk sai take jin kanta wata iriya, dan ma akwai Harees, yana iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ba ta shiga damuwa ba.

MARYAM POV.

Yau zasu yi final exam, Ga kuma shirye-shiryen tafiyarsu india da suke, dan yace mata zasu jima a can, kamar yanda Tafida ya saba kawota kullum yau ɗinvma shine ya kawota.

“Ga lunch box ɗin ka”

Ta faɗi tana fitar masa da lunch box ɗin, tare da aje masa shi a kan cinyarsa.

Hannu yasa ya ɗauka, sannan ya mayar dashi kujerar baya.

“Sai kin dawo ?”

Ta gyaɗa masa Kai tana goya jakarta a baya, hannunta ta ji ya riƙo, dan haka ta damke hannun jakarta da ƙarfi, dan ji ta yi kamar ya saka mata shock ɗin wutar lantarki ne.

“Miriam”

Maryam ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo ta kalleshi, yana kusa da ita, kusa sosai, kuma tana juyowar ya kama fuskar ta tarebda dora tasa a kanta ta.

Har cikin ranta take addu’ar Allah yasa ba abina da ya mata rannan zai sake ba, dan wata ƙila idan ya sake ba lalle ta iya rubuta exam ɗin ba, dan gaba ɗaya zata rasa nutsuwarta ne kamar last time.

Saide addu’arta ta bata karb’u ba, dan Tafida yana ɗora hancinsa kan nata, ya shiga kissing ɗinta, wannan karon ma yabfi na farko.

Bata san yanda yake riƙe kansa ba ne, tun a ranar da ya yi kissing ɗinta yake so ya sake, amma haka ya daure, dan baya so taga gaggawarsa.

A hankali ya ja fuskarsa baya, Maryam ta yi saurin kifa kanta a gefen kafaɗarsa, gwara ta yi hakan, dan wata ƙila hakan zai sa ta gujewa kallon idonsa, dan gaba ɗaya notukan kanta sun kunce, _’yar haddar karatun da ta yi sun tashi sun bi iska, ba lalle ma ta iya tab’uka komai ba yau.

Memakon hakan da ta yi ya sa ta ji sauƙi, sai ji ta yi Tafida ya ƙara riƙeta gam a jikinsa, hakan ya ankarar da ita abun da ta ke, dan haka da sauri ta zame a jikin nasa, ko lunch box ɗinta bata ɗauka ba ta fice.

Har saida ta ƙule masa sannan ya lura da lunch box ɗin nata, ya yi murmushi sannan a hankali ya furta.

“Uwar tsoro!”

Lunch box ɗin ya ɗauka sannan ya fita, dan ya san ajinsu.

Kamar kullum yauma sanye yake cikin manyan kaya, wata green ɗin shaddace a jikinsa, kansa babu hula, dan yanzu ya tara gashi da yawa, kuma idan ya saka hular bata zama, shi yasa ya dena sakawa.

Ko da ya shiga class ɗin nasu sai yaga babu malami a ciki, ya shiga dube-dube, can ya hangota a karshen benci, ta kifa kanta a kan desk, kamar kuka take kuma kamar me bacci.

Be yi wa kowa magana ba ya shiga cikin ajin, idon ‘yan matan ajin kamar ya faɗo ƙasa dan ganin Tafida a ajinsu, shi kuma bai kula kowa ba.

Zara da Aisha ne suka juyar da kansu gefe, basa so su haɗa ido da shi, dan basu sani ba ko Maryam ta faɗa masa abin da suka yi.

“Miriam!”

Kamar a mafarki Maryam ta ji muryarsa tsaye a kanta, kai ina taya za’ayi ma yazo wajen, sai dai kuma tunawa da ta yi a mota ta barashi, bataga tafiyarsa ba, yasa ta ɗago da sauri, shiɗin ne kuwa tsaye a gefen desk ɗinta.

Ya Allahu ya Allah, wai shi be san halin da take ciki bane?, me yasa yake mata haka?, wallahi idan akaci gaba da haka zai iya zautata…. Lunch box ɗin ya miƙa mata sannan yace.

“Kin manta wannan”

Ta yi sauri ta karb’a, tana bin ‘yan class ɗin da kallo, gaba ɗaya ido ya dawo kansu, kallonsu ake daga ita har shi, wasu na mamakin alaƙar da ta haɗasu, wannan de baya kama da ita ta ya za’ayi ace yayanta ne, sai dai ko saurayi, kusan irin wannan tunan ne a kan kowa dake ajin.

Maryam ta haɗiye wani abu sannan ta juyo ta kalleshi, yana nan tsaye be tafi ba.

“Kuka ki ke ?”

Da sauri ta girgiza masa kai.

“Me yasa ki ka kifa kanki a kan table ?”

Kode ta faɗa masa cewa abinda yake mata ne yake sata take nitsewa a cikin lake chad ?,a’a ko zata faɗa masa ba’a nan ba, nan ba wajen maganar su ba ne, ita da zai temaka mata ma ya tafi, da sai tafi jin daɗin ranta.

“Babu komai, haddata ce bana so ta….ta zube”

Ita kanta sai da ta sarawa kanta da wannan ƙaryarta ta, zubewar hadda kuma ta nawa ?, ai tun da leb’ensa ya sauƙa cikin nata haddar ta zube, saide ta sake sabon lale.

Ya cije leb’ensa yana kallon ta, dariya ce take san kama shi, amma ba zai yi dariya a nan ba, dariyarsa ta makusantanasa ce kawai, ba wa al’uma duka ba, shi yasan kome take, ba hadda take san riƙewa ba, jinyar gangar jikinta take sbd ya yi kissing ɗinta.

“Ok ki kula, Allah ya temaka, Allah ya bada sa’a”.

Da fatar bakinta kawai ta amsa ameen ɗin, shima kuma yana kaiwa nan ya fice ya bar matan ajin da bin bayansa da kallo, Maryam ta kallesu takaici na san kamata.

Tafida na fita suna dawowa da kallonsu kanta, suka iyo kanta zasu tambayeta amma Zara ta dakatar su ta hanyar faɗin.

“Ba sai kun tambaya ba, mijinta ne ”

Maryam ta kifa kanta a kan desk, sbd kallon da suke mata.

R NO 147,JJ hospital, byculla, Mumbai, India

A kan gadon marasa lafiya, Galadima ne kwance, yayin da rabin jikinsa yake a rufe, ya ƙara ramewa ya yi baƙi, kansa ya langwab’e daga gefe, bakinsa sai zubar yawu ya ke, yanzu maganama ba ya iya yi, hannayensa da ƙafafunsa kam sam basa aiki, ko zama baya iyawa sai an zaunar da shi.

Da ga kan wata kujera kuma Fulani Sadiya ce, wadda idan ba kasanta sosai ba a da, to baza ka ce ita bace a yanzu, ta rame ta zama wata iriya, tsabar tashin hankali, ɗan da ta saka buri da rai a kansa, shine yake kwance yau a cikin wannan hali, sai an kwantar sai an tayar.

Bama wannan bane abun damuwar, da suka zo asinitin saida a ka masa general test, kuma a nan ne a ka asanar musu da cewa yana shaye-shaye. Sai a yanzu ta gane cewa duk abinda takewa Tafida kan ɗanta yake komowa, babu ɗaya dake samunsa duka.

Ta yi kukan baƙinciki dana nadama fiye da ƙirgenta, gashi ta yi magana da boka kan a san yanda za’ayi a warware asirin, amma bokan sai ya tunasar mata da cewa itafa tace kada ayi wanda zai tab’a karyewa, kuma shi ya mata.

Ƙofar shigowa aka turo, me martaba ya shigo, ta ɗaga kai ta kalleshi sannan ta sauƙe, takowa ya yi zuwa kan kujerar da take zaune.

“Ya me jikin ?”

Ya tambaya yana kallon Galadiman da ke kwance a kan gado, Fulani ta kalleshi itama.

“Jiki da godiya”

“Tafida ya kirani, ya faɗa min cewar nan da wani satin zai shigo india, kuma zai zo ya duba shi”

Wata ƙwallace ta kufce mata, ƙwallar nadama da kuma baƙin ciki, duk halin da ɗanta ke ciki itace sila, yanzu shi Tafidan da take komai dominsa shine ma wanda zai zo ya duba shi, bayan ko ga miciji basa yi.

A ranta ta shiga jero istingifarin da ya zame mata jiki akwanakin nan, so take ta nemi yafiyar Allah, wata ƙila ya yafe mata kura-kuran da tavyi, amma tabbas tasan cewa ita me lefi ce gareshi, shin anya ma kuwa zai yafe mata ?

<< Yadda Kaddara Ta So 34Yadda Kaddara Ta So 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.