Skip to content
Part 7 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

“Meema Even Center za ka kai mu.”

Muryar Anti Fati ta faɗi bayan sun fito daga gidan sun tsaya a bakin titi, sannan suka tsaida me napep.

“Ku shiga muje to”

Anti Fati ta juyo tana kallon Maryam wadda ke tsaye a bayanta sai gyara zaman gyalen dake jikinta take, ita jinta take kamar tsirara, gaba dayanta a takure take dan bata saba ba.

“Muje”

Tana ta jajjan mayafin daga baya ta shiga adaidaitar, ta kar6i Imran daga hannun Anti Fati, sai waige-waige take kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.

Da haka suka isa katafaren sabon event center din da aka bude a hadejia kwanannan, tun daga bakin gate Maryam ta tabbatar da ba bikin ƙananun mutane suka zuba, dan tun daga maka makan motocin dake parker a harabar wajen, zuwaga mutanen dake kaikawo a wajen da yanayin suturunsu zaka tabbatar da ba ƙananun mutane bane, Maryam ta kama kanta tana bin Anti Fati a baya.

TAFIDAH POV.

_🎶If this is a dream babe i don’t wanna wake up ooh yeeh !_

_This is too sweet to be real babe i don’t wanna wake up oooo yeeeh!_

_You give me life you give me vibe ooh, you be my energy i can’t deny oh_

_Super man you will be my hero what is love if you not there ?_

A hankali wakar Sweet wadda Rayvanny tareda Guchi suka rera take tashi daga cikin home theater ɗin dake katafaren falon gidan Tafida.

Daga can kan wata kujera ta zaman mutum uku kuma shine kwance, idonsa a lumshe yana bin wakar a hankali, yayi nisa a abunda yake, har Muktar ya buɗe ƙofar bema sani ba, dan hankalinsa gaba daya yana kan sauraron waƙar, saida muktar din ya ɗan daki ƙafarsa sannan ya bude idonsa, har yanzu kalar idon nasa tana nan yanda ya tashi da ita tun safe, ja har yanzu bata sauya kala ba.

Miƙewa yayi ya zauna, yayinda Muktar ya ƙarasa ya kashe waƙar, ya dawo kusa dashi ya zauna.

“Ba hakane ya kamata ba, kamata yayi ace ka kunna karatu ba waka ba, kallifa idonka har yanzu bai sauya ba”

Tafida ya yi murmushi me ciwo, ba sai ya faɗa masa ba cewa a duk lokacin dayaji karatu ji yake kamar ruhinsa zai fita tareda baƙin ruhin nan ba, shima da kansa ya san da hakan, sai kawai ya juya ga wayarsa ya dauki ɗaya daga ciki ya shiga dannawa.

“Abincine Madam ta turo maka”

Wani murmushi ya su6ucewa Tafida, a gaba ɗaya cikin abokansa babu wanda bashi da aure harda yara, amma shi banda shi, dan koda wasa bashida tsarin yin aure a yanzu.

“Ina lil me ?” (yana nufin me sunansa dan gidan Muktar ɗin)

ya faɗi yana aje wayar dake hannunsa

“Yana nan, zasuje gidan kamun ai, wata ƙila ku hadu”

Muktar ya bashi amsa yana zuba masa abincin, shi sai yanzuma da yaga abinci sannan ya tuna ashe baici abincin ba tun safe, dan yana fita daga fada gidansa ya wuto aka fito masa da dokunansa sbd hawan angwancen, ya shirya suka tafi hawan kuma basu dawo ba sai dazu, shine yayi sallah ya kwanta yana hutawa har Muktar ɗin yazo ya sameshi a haka.

“Zakaje wajen kamun ne ?”

“Shi ya zama dole, su Mairama zasu zo fa, kuma da mahaifiyar Amina ne bama shiri ba wai da ita ba”

Tafida ya faɗi yana kaiwa abincin bakinsa, kuma daga haka babu wanda yaƙara cewa komai a cikinsu har ya gama cin abincin, ya tashi ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya fito, cikin wata baƙar shadda wadda tayiwa farar fatarsa kyau, sai sheki take cikin hasken fitulin parlon, hannunsa rike da hular da zai saka, ya tako har cikin parlon sai baza kamshi yake.

Muktar ya miƙe yana kallonsa hannunsa na dama yakai ya tura gashinsa baya, wani abu daya zame masa al’ada, sannan ya saka hular a kansa

“Idanka ya dawo daidai”

Muktar ya faɗi ganin ƙwayar idon nasa ta dawo dai-dai, ma’ana ta dawo ainahin kalarta wato blue. Tafida yayi murmushi kawai, sannan ya buɗe tafin hannunsa ya mika shi saitin inda wayarsa take, nan take wayar ta taso ta sauko a kan hannunsa, wannan ba wani sabon abu bane a wajen Muktar, dan tun suna yara yasan wannan side ɗin na Tafidah.

“Muje ko ?”

Muktar ya gyada kai suka fita, saida suka fara zuwa asibitinsa wadda ya buɗeta a hadejia wato Crown Hospital, kuma Mukhtar ne yake kula da ita, bayan sun gama abinda zasuyi suka wuce meema event center.

Tunda ya isa wajen ƴan uwansa suka masa caa, kowa da nasa kalar ƙorafin, wannan yazo ya tafi wancan yazo, masu ƙorafi akan baya xuwa gidansu su sukafi yawa, shide nasa bada haƙuri ne kawai.

A wata kujera dake kusa da ta Mairama wadda take ƙanwa a wajen mahaifinsa ya zauna.

Itama saida tayi nata ƙorafin, kuma kamar sauran itama dai haƙurin ya bata. Daga nan ya shiga hira da yaranta ƴan mata dake wajen, Mairama kam kallonsa kawai take cike da tausayawa, dan abinda ya faru jiyama Fulani ta kirata ta sanar mata.

“Hamma ga ƙawar tawa”

Muryar Nadra ta faɗi daga bayansu, a hankali ya juya yana kallonsu, bama shi kaɗai ba harda mairama da yaranta, girarsa ta haɗe waje guda alamun rashin fahimta, yana kallon ƙawar tata wadda take ta washe baki, murna fal ranta yau taga Tafida kusa da kusa.

“Ƙawata da na faɗa maka jiya”

Nadra ta faɗi ganin kamar hamman nata ya manta da zancen da sukayi jiya, kuma hakaɗin ne ya manta ɗin, dan shi ba komai yake sakawa a ƙwaƙwalwarsa ba, a daidai lokacin ne kuma Muktar da matarsa da kuma ɗansa suka ƙaraso wajen, dan da tare suke kuma bayan zuwan matar tasa ya fita yace zaije ya shigo dasu.

Nan take Tafida ya manta da Nadra da kuma ƙawarta, ya miƙe yanawa me sunan nasa murmushi, yaron ɗan kimanin shekaru uku ya kar6a a hannun Muktar, yana gaisawa da matar Muktar ɗin.

“Lil me ykk”

Yaron me tsantsar kama da ubansa ya kalli Tafidah

“Lafiya”

“Wai ni da me kuke kiransa ne ?”

Muryar Mairama dake bayansu ta tambaya.

“Tafida”

Muktar ya bata amsa

“Gaskiya kun cuce shi, menene wani Tafidah? Da Eshaan ɗinsa ma kuke kiransa dashi”

Cewar Mairama, tana dubansu.

“Wallahi ranki ya daɗe baban ne yake kiransa da haka, kuma sunan sai yabi bakin mutane”.

“Ai kema da lefinki, sunan da uwa take kiran ɗa dashi ai shine suna”.

“Yanzu ranki ya daɗe menene aibun Tafida ?, nagade sunan ɗan uwanki ne”

“Sunan ɗan uwan nawa, amma kuma ai shi yarone ƙarami, sunan ya masa girma”.

Sai maganar ta bawa Tafida dariya, shi tun yanada shekara uku suke kiransa da Tafidan, amma bai musu girma ba a lokacin, sai yanzu.

*****

Maryam ta kalli Anti Fati dake ta faman hira itada dangin mijinta, zaune suke a kan wasu kujerun dake wajen, ta juya tana kallon amarya da angon da basu jima da shigowa ba, ita kwalliyar amaryace tafi birgeta, itama ta tsara abubuwa da yawa wanda za tayi idan bikin ta ya zo.

Abinda bata sani ba shine, wasu kaddararorin basa zuwama ɗan adam kamar yanda ya so, suna zuwane kamar yanda suka so.

Ita duk sai tajima wajen ya isheta, yanayin kallon da samari ke mata, ga kidan wajen dake hawa mata kai, dan haka ta ɗauki Imran ta miƙe daga wajen, ta ɗan taba kafaɗar Anti Fati.

“Za mu ɗan fita waje”

Ta faɗi bayan Anti Fatin ta juyo ta kalleta

“Ina zaku je?”

“Waje zamu fita”

“To kada kuyi nisa”

“Umhm”

Maryam ta amsa ranta fari tas, dan zata fita waje ta huta da kallon da samari ke binta dashi, gaba ɗaya a takure take, gyalen nan kwata kwata bata jin daɗinsa, tana tafiya tana gyara gyalen.Alokacin ne kuma abun ya faru, matakin farko na sauya kaddararta.

Bata ankara ba taci karo da wata tsohuwa, mayafin da take ta famar gyarawa ya faɗi kasa, kuma ɗaurin ɗankwalin dake kanta ya zame yayi baya, ta ruƙo imran dake barazanar faɗuwa batamabi ta kan gyalen nata ba ta dubi tsohuwar.

“Fan Allah kiyi haƙuri Iya, ban lura da ke bane”

Tsohuwar data tsaya tana mata kallon ƙurilla ta kasa cewa komai, ta tsirawa tawadar Allahn dake goshinta ido, da zirin farin gashin daya Dan leko ta ƙasan ɗankwalin kanta , sai kuma ta kalli wadda take wuyanta, gabanta ya buga, amma sai tayi dauriyar kallon fuskarta.

“A’a babu komai jeki kawai”

“To iya, sannu kinji”

Maryam ta faɗi tana gyara ɗaurin ɗankwalin dake kanta, tareda janyo mayafinta tafita daga wajen.

A hankali tsohuwar ta juya ga teburin da taga yarinyar ta taso, taga wata Karima wadda ta sani a cikinsu, ta kira sunan Kariman, sannan ta yafitota da hannu, Karima ta taso tazo tana gaisheta.

“Wace ce waccan wadda ta taso daga teburin ku ?”

Tsohuwar ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar Karima

“Iya jakadiya, sunanta Maryam, ƙanwar Fatice matar habib”.

Jakadiya tayi shiru tana nazarin maganar

“Karima a ganinki za tayi shekaru nawa haka ?”

Karima ta tabe baki cikin tunani

“Eh bana jin zata wuce ashirin da ɗaya…. zuwa da biyu”

Zuciyar jakadiya ta buga wani tsallen murna, dan da alama watan yin arziƙintane ya kama.

“Ina ce unguwarsu kuma waye mahaifinta ?”

“Iya jakadiya kode ɗanki zaki nemawa aurenta ne ? Naga sai tambayoyi kike jero min”

Jakadiya tayi mata wani kallo, wanda yake nuna mata cewar da gaske take ba da wasa ba, hakan yasa Karima ta tara yaɗonta gu ɗaya tace.

“Aiko da ɗan naki zaki nemawa aurenta da ya dace da mata, yar garko ce, kusa da kan matoya, sunan babanta Tijjani direba”

Wani murmushi ya subuce daga leben jakadiya, tana ƙara bin hanyar da Maryam tabi da kallo. An ce komai yanada sila, komai yanada mafari, wannan shine mafarin wasu ƙaddararorin, mafarin faruwar abubuwa da dama, silar gyaruwa wasu abubuwa, silar bacin wasunsu.

<< Yadda Kaddara Ta So 6Yadda Kaddara Ta So 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×