Skip to content
Part 22 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Banafsha na ci gaba da kukanta, cikin kukan ta ke faɗin, “Me yasa sai ni? Komai ni? Daga wannan sai wannan, ina farin cikin komai ya zo ƙarshe mahaifiyata ta yi aure, nima na yi, ashe ba haka ba ne, Allah idan wani abun na aikata, na tuba ka yafe mini” ta faɗa tana sakin kuka mai tsanani, ga wani irin sarawan da kan ta ke yi, kaman ta cire kan ta huta.

Mami cikin damuwa ta ce, “Banafsha meyasa bakyason aiki da karatunki ne? Sau tari idan kika yi abu ina dukanki ne dan haushin da kike bani, na abu da kike yi watarana kaman wacce bata je makaranta ba kwata-kwata, Banafsha bakisan jarabawa ba ne? ko kuwa baki san komai sai Allah ya ƙaddara ba ne? Lafiyan da kike da shi yanzu da rayuwan da kike yi, wai wayonki ne ya baki ko Allah?”

Banafsha tana kuka ta ce, “Mami abin akwai ciwo fa?”

Mami kwantar da murya ta yi ta dinga rarrashinta, har ta daina kukan da ƙyar sai ajiyan zuciyan da take jerawa, sannan Mami ta tashi ta fice dan ita ma daurewa kawai take yi, amma tana tausayin Banafsha, sai dai ba yan da aka iya da abin da Allah ya ƙaddara, a ko wanni hali sai dai mu ce Alhamdulillahi ala kulli halin.

Banafsha kuwa Mami na fita ta ci-gaba da kukanta, har mugun ciwon kai da zazzaɓi suka rufe ta bata sararawa kan ta ba, sai da ɓarawon baccin wahala yayi gaba da ita.

Mami haka ta kwana cikin tausayin yarinyarta, ko da Alhaji Mukhtar ya ƙira ta ma ba su wani jima suna waya ba suka yi sallama, dan ya fahimci abu na damunta, sai dai bai kawo damuwan Banafsha bane, ya ɗauka ko dai irin abun al’ada na matan nan ne, idan mace za ta yi aure duk girmanta, sai taji wani iri na komawa gidan wani da za ta yi da zama, kuma zaman na din-din-din.

Washegari da safe Mami ta shiga wajan Banafsha, ganin halin da take ciki ba ƙaramin ɓaci ran ta yayi ba, tasan abin da ya sameta ba daɗi kuma na tausayi ne, amma kuma rashin jin Banafsha yayi yawa sai ana stawatar mata, zama tayi fiska a haɗe ta ce, “Banafsha wai kam kin kai ni damuwa ne da wannan al’amari ni mahaifiyarki? Me yasa bakya ji? Yanzu ciwon kan da kika jawa kanki maganin me kenan? Me zai ƙara miki?.”

Cunna baki Banafsha tayi tare da marairaicewa, amma ba ta ce komai ba.

Mami ta ce, “ki sani, a ko wanni hali bawa so ake ya kasance mai godiya ga Allah, la’in shaƙartum la’azidanna lakum, wa in kafartun fa inna azabi la shadidan, a halin daɗi da rashin daɗi ka godewa Allah, domin idan ka gode masa zai ƙara maka, amma fa idan ka kafurce masa bi ma’ana kaƙi yin haƙuri, to azabar sa tabbatacciya ce, abu idan na daɗi ne ya same ki godewa Allah ki yi hamdala, abu kishiyan daɗin ma ki gode wa ki yi hamdala, domin komi da ya samu bawa ko da a wajansa mara daɗi ne, to a wajan Allah hakan ne alkairi ga bawansa, domin Allah ya fi mu son kanmu, kuma ya fi mu sanin abin da ya ke alkairi a gare mu, Banafsha ki yi haƙuri ki cire komai a ranki, na tabbata Allah zai ba ki wan da ya fi Aliyu, nesa ba kusa ba.”

Ajiyan zuciya na sauƙe, na langwaɓar da kai na, sannan na ce, “ki yi haƙuri Mami, in Allah ya yarda zan cire komai a raina.”

“Yauwá ƴar albarka gudalliyan Maminta, yanzu maza tashi muje mu karya, sai ki zo kiyi wanka ki shirya, anjima kaɗan mutanen Kano za su iso, kuma suna zuwa za mu tafi.”

Kallon Mami nayi na tura baki na ce, “Karatun nawa kuma fa Mami?”

“Idan muka je can duk za’a yi abin da ya kamata, yanzu dai tashi maza ki wanke fiska, ki tabbatar kin fito kin karya, bana son zama da yunwan nan.”

Sai da na tashi na shige toilet sannan Mami ta fice, tana jin dama-dama a ran ta, tun da Banafsha ta haƙura ta daina kukan.

Wanka na iyo, na fito na shirya kawai, ko ta kan abin gyaran jikin ban bi ba, tun da ba aure ai basu da amfani, haushinsu ma nake ji, haka na saka kayana mai kyau na fice, abin karyawa na ɗiba na ci ɗan dai-dai, na koma na sha magani, sannan na wuce wajan Aunty A’isha na ɗauki Emaan muka fice a gidan, tun da ba wani aure ba zan ci-gaba da takurawa kai na ba.

Gidan Abbaa muka shiga, da shi muka fara haɗuwa, durƙusawa nayi har ƙasa na gaishesa ya amsa yana murmushi, ya ce, “Allah ya miki albarka ko Faɗima, a ta haƙuri da rayuwan duniya, komai mai wucewa ne, watarana sai labari.”

“Insha Allah Abbaa”, na faɗa kai na a ƙasa.

Murmushi yayi ya ce, “To yayi kyau Faɗima.”

Abbaa na wucewa nima na miƙe muka shige ciki, Ummu na samu zaune a palourn, ganina sai ta yi murmushin jin daɗi tun da na sake har na iya fitowa waje, gaisheta nayi ta amsa, ita ma ta ƙara bani haƙuri, muna zaune sai ga Umaima ta fito tana faɗin, “wai daman da gaske muryanki nake jiyowa Masoyiya, na ɗauka ai mutanen Kano basa zuwa ko ina kuma sai ɗaki.”

Hararanta nayi na miƙe na bi ta ɗaki, ta ja hannun Emaan tana faɗin, “Ƴar beauty, wallahi masoyiya yarinyar nan kyau take mini.”

“Uhmñ”, kawai na ce na samu waje na kwanta, ina kallon Umaima da ta gama shirya jakanta na tafiya Kano, murmushi kawai na yi, dan ni ba wani son zuwa Kanon nake ba, kawai dai ba wani dabaran ne.

Umaima ta ce, “ki yi haƙuri fa masoyiya, Allah ne bai nufa ba, wataƙila ke rabon ya Danish ne shiyasa, shi zai more wannan kayan.”

Hararanta nayi na ja guntun tsaki na ce, “Za ki ji da shi ne ai, ban da lokacinki balle na yayanki.”

Zolayana Umaima ta ci-gaba da yi, dan dole na ɗan sake, tana gamawa kuma ta miƙe tare da cewa, “To tashi mu tafi, yau kwana sai Kano ba zama.”

Miƙewa nayi na ɗauki Emaan da ta fara bacci, mun fito muka faɗawa Ummu mun tafi, ita ma tana murmushi ta ce sai ta zo, dan da ita za’a yi tafiyan, mu dai mun wuce da Umaima.

Da azahar kuwa sai ga motoci a ƙofan gidanmu, Umaima ce ta fita ta yiwa baƙin iso, manyan mata ne biyu kawai, nan aka cika musu gabansu da abinci da kayan tarba, su Mama Hadiza suka fito suka gaggaisa, matan fiskansu a sake sai fara’a suke, Hajiya Huraira da Hajiya Nafisa, kaman yan da suka gabatar da kan su.

Mamina wanka tayi ta shirya cikin shiganta na alfarma, ba ƙaramin kyau Mami tayi ba, kana ganinta ka ga matar manya, ko da ta fito matan da suka zo sai da suka koɗa kyawunta, Hajiya Huraira ne ta ce, “Masha Allah, amaryanmu sai sam barka yaya ya iya zaɓe.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “Nagode sannunku da hanya.”

Hajiya Nafisa ta ce, “Tun da Amarya ta fito, sai mu ɗau niyan tafiya, tun da gurin ba nan kusa ba.”

Duk kowa ya fito da kayakinsa, duk abin buƙata Mami ta haɗe su waje guda, kayan auren Malam Abbo da komai da suka kawo, an ajiye a gidan Abbaa, idan sun zo za su karɓa a can, Mami ta kulle gidan aka kai wa Abbaa key.

Aunty A’isha da Emaan ƴar ta, Mama Hadiza, Ummu, Nana bealkysou, Umaima, Banafsha, sai Mami Amarya Uwar gayya, su suka shige motocin, suka juya kuma aka ɗau hanyan jimeta.

Tafiyan awa uku suka yi suka iso jimeta wajan ƙarfe biyar, airport suka nufa, suna isa kuma suka samu Nusaiba a can, dan tun da suka iso Abeed ya ƙira aka kawo ta, komai da komai na tafiya Abeed yayi, suka shige jirgi sai kanawan dabo, Abeed mamaki yake, yasan dai mutum bakwai ne suka fito a gidan Mami, amma sai ganin fan’s na ƳAR KARUWA yake yi a jirgi, ga su Queen, Habiba, Hafsah, Fatima, A’isha, ɓingel kabi, Sarah lawal etc, duk kun maƙale a jirgi, sai fatan Allah sauƙe mu lafiya, domin uwar batoorl ma ba’a bar ta a baya ba.

Dare-dare jirginsu yayi landing, nan aka zo da zugan motoci ɗaukan amarya da mutanenta.

Railway estate aka yi da su, Umaima sai baza idanuwa take tana bai wa maganenta abinci, Kano ta dabo tumbin Giwa ko da me ka zo an fi ka, dan ma shigowan dare ne, kallo kuwa bai koma sama ba sai da suka iso gidan Alhaji, ai su Ummu sai washe baki kawai suke yi, Aunty A’isha sai da ta kasa haƙuri ta ce, “Aunty Ramla tun da mu kaɗai ne a motan nan bari na faɗa rai na, dole ki din ga ganina a gidanki, daman Daddyn Emaan ya ce za’a musu transfer zuwa Kano, shikkenan na samu wajan zuwa, irin wannan aljanar duniyan.”

Mami dai tana jin su, murmushi take dan ita addu’a ne kawai a bakinta, tun da suka iso Kano take karanto addu’oenta, har suka shiga gidan, aka parker su a gaban tankamemen part na Papi.

Momsee ne ta fito tana hamdala, sannan ta zo motan da su Mami suke ta ce, “bayin Allah, sannunmu da gajiya, ku fito mana da amaryanmu mun iso.”

Su Mami duk fitowa suka yi, Mami bakinta ɗauke da addu’a.

Umaima sai washe baki take kawai ganin gidan ƴan gayu haɗaɗɗe, ita kuwa Malama Banafsha ba za ka iya faɗin ga halin da take ciki ba, an ce labarin zuciya a tambayi fiska, to ita nata fiskan shiru ne, ba abin da za ka fahimta, farincikin ta ɗaya shi ne Maminta tayi aure.

Su Majeeder da tun da suka ji labarin an iso da amarya tuni suka fito jiran isowansu, suna isowa suka ƙariso wajan Momsee suna tambayan ina Mami amarya, Momsee kallonsu tayi ta ce, “Ku dai ba za ku girma ba, idan kuka yi haƙuri zuwa gobe ai za ku gan ta, yanzu ku ƙyale baiwar Allah ta huta.”

Majeeder shiru suka yi, suka wuce wajan da su Ummu ke staye, gaishe su suka yi tare da sannu da hanya, Majeeder ne ta fara magana, cikin sansanyar muryanta ta ce, “Ina Maminmu da Banafshata?”

Mami tana jin muryan da sunan da aka ƙira ta gane Majeeder ce, murmushi kawai tayi, dan tun asali tana jin ƙaunar yarinyar.

Umaima kuwa jin Majeeder na tambayan Banafsha, wai Banafshanta, harara ta aikawa Majeeder, sai lokacin kuma jikin Umaima yayi sanyi, tun-tuni damuwa da halin da Banafsha za ta shiga idan ta ji an fasa aurenta, shi ya hanata saka damuwan rabuwa da Banafsha a ran ta, amma yanzu sai ta ji wani iri kaman tayi kuka, shikkenan kuma ita da ganin Banafsha sai Allah yayi.

Banafsha ma a nata ɓangaren tana jin muryan, ta san ba zai wuce Majeeder ba wacce Alhaji ya bata labarinta, ita ma sun yi musabaƙa ta zo na daya, murmushi kawai ta saki tare da cewa, “Sannunki.”

Majeeder wajan Banafsha ta iyo kaman ta san ta, tayi hugging nata ta ce, “sannunku da hanya, sis sannunku da hanya”, ta faɗa tana yi wa Umaima murmushi, Umaima kuwa hararanta tayi.

Momsee ce ta musu iso, sannu a hankali Mami ke tafiya cikin nistuwa, su Majeeder an shige cikin masu kawo amarya kaman tare suka zo.

Da bismillah Mami ta sanya ƙafanta a haɗaɗɗen babban palourn gidan, Momsee kuwa jagora ta musu tiryan-tiryan har suka haura sama, nan ma wani babban palourn ne, ƙofan part da yake na Mami ta tura suka shige, nan suka stinci kan su a wani haɗaɗɗen palour da ya sha ɗima-ɗiman kujeru Arsh color da black.

Momsee tana murmushi ta ce, “To amaryanmu ga sashinki nan, duk abin buƙata akwai, idan akwai abin da babu ma kuna buƙata to ku mini magana, a huta gajiya, za’a kawo muku abinci.”

Mama Hadiza ne ta ce, “Ƴar nan Allah miki albarka, mun gode sosai sannunki da ƙoƙari, ku ma ku huta gajiya.”

Momsee ta amsa tana murmushi ta miƙa hanyan fita tana faɗin, “Majeeder, Ramla ku wuce mu tafi ku bari su huta, sai zuwa safiya kwa ga Mamin taku.”

Mama Hadiza ta ce, “a’a ke kuwa ƙyale su mana.”

Momsee ta ce, “Mama baki san yaran na bane da fitina, balle da suka damu kowa da maganan Maminsu, kun ga ku wuce muje sai da safe ku zo ku gaisheta.”

Majeeder na tura baki ta tashi, suka bi Momsee suka fice, a Gaba ta sa su har part nata, sannan ta musu faɗa akan su ƙyalesu su huta, idan suka yi haƙuri ai nan da kwana biyu za su waste, su bar musu Mamin tasu.

Momsee masu aiki ta ƙira ta sa suka shirya abincin da aka saka su dafawa, sannan ta ce su ɗauka su tafi, su Majeeder suka ce za su kai, amma ta hana su, tana gaba ƴan aikin na bin ta a baya har suka isa sashin Mami a sama.

Mama Hadiza ganinsu da kuloli ta ce, “ohh! Ba ki zauna hutawan ba kika kuma shigowa wani ɗawainiyan? To sannunki Allah yayi albarka ya kuma ba su zaman lafiya.”

Momsee ta amsa da Ameen, sai da aka ajiye musu komai da komai, sannan ta juya ta fice, duk zirga-zirgan da take yi ko mostin Hajiya Sa’adatu bata ji ba, tana komawa nata ɓangaren ta wasta ruwa ta bi lafiyan gado ta kwanta, dan daman sun yi waya da General sun fita da Papi.

Mama Hadiza waje ta samu ta zauna ta ce, “Masha Allah! Ramlatu kin ga asalin abin da ake ƙira da jinkirin alkairi, sai dai mu ce Allah sanya albarka, sannan ki yi haƙuri da komai za ki ji ko za ki gani, ki toshe kunnenki ki yiwa mijinki biyayya.”

Murmushi mai kyau Mami ta saki ta ce, “Insha Allah Mama Hadiza.”

Ummu ce ta miƙe ta ce, “To duk mai buƙatan abinci ya ɗiba ya ci, sannan ɗakunan kuma ku duba wan da ba na mijinta ba, sai ku shige ayi alwala ayi salla.”

Aunty A’isha shumfiɗe Emaan tayi akan kujera, sannan ta miƙe ta buɗe ɗakunan, guda uku ne ɗakunan, kuma ko wanne da banɗakinsa a ciki, amma guda biyu ne kawai akwai gadaje da su Sip da komai, ɗayan empty yake a share kawai.

Wan da yake empty nan suka shiga da kayakinsu, masu alwala suka yi, masu yin wanka suka yi, masu cin abinci ma suka ci, sannan kowa ya nemi wajan kwanciya ya bi lafiyan haƙarƙarinsa.

Mami sam bata yi bacci ba, alwala ta ɗaura ta shiga karatun Alkur’ani mai girma da nafilolinta.

Hajiya Nafisa daman tun da suka iso dirver ya juya da ita gidanta, tana zuwa kuwa ta samu su Papi da General duka a can, sannu da hanya suka mata, cikin zolaya ta ce, “Alhaji dole ka dage, ashe zanƙaɗeɗiya ka samo a Adamawa, gaskiya amarya fa Masha Allah, Allah dai ya bada zaman lafiya, mun kawo maka ita sai ka hanzarta zuwa.”

Papi kam bakinsa ya ƙi rufuwa, sai washe sa kawai yake yi, gani yake kaman ba gaske bane, ba zai koma ya ga Ramla a gidansa ba.

Abeed tattaran matarsa yayi su ma suka wuce nasu gidan, ɗakinsu kawai ta karkaɓe musu, suka wasta ruwa, suka ci abincin da ya musu takeaway sannan suka bi lafiyan gado kuma, sai huce gajiya, amma fa ta soyayya, kunsan soyayya ta fi saurin tafiyar da gajiya.

Papi sai da lokaci ya ɗan ja sannan suka koma gida shi da General, Papi yayi sashinsa shi ma General yayi nasa.

Papi ji yake kaman ya je ya ga masoyiyarsa tukunna, amma kuma dare tayi kuma ga gajiya yasan ma sun yi bacci, shiyasa ko ƙiranta bai yi ba, ya wuce sashin Hajiya Sa’adatu, ya sameta zaune tana ta surutu ita kaɗai, amma da alama waya ta gama.

A gefen Mom ya zauna yana murmushi ya ce, “Uwar gida ran gida sannu da aiki.”

Hajiya Sa’adatu banza ta yi da shi, Alhaji ya kuma magana shiru, ganin haka sai ya murmusa tare da rungumeta, ai a hasale Mom ta fara kiciniyar ƙwacewa tana faɗin, “ka ƙyale ni, ina jin dai Amarya aka kawo maka ba? To jeka wajanta na yafe mata kai.”

Murmushi Alhaji yayi ya ce, “Ni kuma a yanzu dai ke nake buƙata.”

Hajiya Sa’adatu staki ta ja, ta miƙe ta bar wajan, Alhaji gajiya yayi da zama ya miƙe yana murmushi ya wuce ɗakinsa, ya wasta ruwa ya kwanta.

Washe-gari da sassafe Momsee ta shiga kitchen da kan ta, ita da su Majeeder suka yi abin kari, sannan duk suka je suka yi wanka, ta sa su Majeeder suka jida abincin suka kai wa su Mami.

A palourn ƙasa suka haɗu da Papi, gaishesa suka yi ya amsa, ya ce, “Wannan abincin kuma daga ina?”

“Momsee ce ta dafa, wai mu kawo wa su Mami”, faɗin Ramla.

Washe baki yayi, tare da saka wa ƴar ƙanwarsa kuma matar ƙaninsa albarka, su kuma suka wuce da abincin suka kai musu.

Da sallama suka shigo sashin, Mama Hadiza da ke hakimce akan kujera ne ta amsa musu, suka shigo suka gaisheta da Ummu da ke zaune a gefe, sannan suka ce ga abincin nan wai su kawo inji Momsee.

Ummu ta ce, “To an gode sannunku da aiki.”

Tambayan Banafsha suka yi, aka faɗa musu tana bacci, sannan suka tambayi Mami, wacce dai-dai lokacin ta fito, ta ci wanka da kwalliyanta sai ƙamshi ke tashi a jikinta.

Mami zama tayi tare da sakin murmushi ta ce, “Yaran Mami gani nan, me aka kawo mini, ya kuke?”

Majeeder ce ta yi magana, ta ce, “Muna lafiya Mami, ya gajiyanku na hanya?”

“Alhamdulillahi, to duk sai ku faɗa mini sunayenku dan na gane ku ko”, cewan Mami tana murmushi.

Majeeder ta ce, “Ni ce Majeeder, sai wannan Nabeela tana da twin bro Nabeel su ne ƴan autanmu, wannan kuma Suhaila tana da twin bro Suhail, sai kuma wannan mai sunanki ce in ji Papi.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “Masha Allah, ashe har da takwarata Ramla, to yayi kyau, sannunku ko.”

Miƙewa suka yi za su tafi, Mami ta ce su dawo su zauna mana, su karya a nan duka, amma suka ce sai Banafsha ta tashi za su zo, suka yi tafiyansu.

Mama Hadiza ta ce, “halan ko a ina suka ji sunan Banafsha da suka riƙe haka oho, tun jiya Banafsha-banafsha kaman wata selebiruti.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “a bakin mai gidan suka ji.”

Ummu ta ce, “Ah lallai sunan Banafsha ya rigata zuwa Kano, yaran kuwa ga hankali.”

Sai da hansti tayi, sannan Alhaji ya shiga ya gaisar da su Mama Hadiza, ya musu sannu da hanya, sai bin Mami yake da wani haɗaɗɗen kallo, ita kuwa sai murmushi take masa, tambayan su Banafsha yayi, aka faɗa masa suna bacci, ya murmusa kawai ya fice, dan yasan da gaskiyansu, hanyan ba sauƙi dole sai ka huta gajiya, shiyasa ma ya tura masu ɗauko Amarya tun asabar dan su huta kamun su kuma juyowa.

Ɓangaren Abeed kuwa da sassafe ya doka wa Dr Arshan ƙira, suna gaisawa ya ce, “Malam kana ina na zo har Mubi na cicciɓo amaryanka na kawo ta Kano.”

Dr Arshan a nasa ɓangaren ya ce, “ban gane ba Captain?”

“To ina nufin yanzu haka mutumiyarka na Kano, jiya mun ɗauko Amarya”, Abeed ya faɗa yana dariya.

Dr Arshan miƙewa yayi daga zaunen da yake, ya ce, “Amma dai gaskiyan ACM, ashe sam-sam ba ka da kirki captain, za’a tafi wa mutum da matarsa ba izninsa, ina ma laifin ka staya ka ɗauke ni mu kai amaryan tare, yanzu so kake samarinku na Kano masu bleaching su gane mini mata.”

Abeed dariya ya dinga yi, ganin Dr Arshan ya dage wai matansa, stagaita dariyan yayi ya ce, “To sai ka yi gaggawan zuwa ai dan dama yau akwai walima gobe kuma family and friends, duk da dai bamu da masauƙin gauraye sai na masu iyali.”

Dr Arshan ya ce, “tun da akwai na masu iyali da sauƙi, bari ka ga na shirya yanzu na kamo hanya.”

“Ok idan kun sauƙa sai ka ƙirani, zan zo na ɗauke ka a airport ɗin.”

“Okay captain thanks.”

Sallama suka yi Abeed ya kashe wayansa yana dariya, sannan yayi dialing numbern ɗan gidan General, amma har ya gama ringing ba’a ɗauka ba, kuma yasan ba zai wuce da gan-gan ACM ya ƙi ɗaukan ƙiransa ba, ajiye wayan yayi.

A ɓangaren ACM Bunayd, dawowansa kenan daga aikin da aka ƙira sa yi, ya sauƙa a jirgi yan da ya saba ta cikin gidansa kawai a zura igiya ya sauƙo, ya shiga palourn ko zama bai yi ba ƙiran Abeed ya shigo, yana kallo yaƙi ɗagawa dan yasan ba zai wuce wani neman maganan Abeed ya ƙira ya masa ba, ga gajiya zai ƙara masa gajiya da surutunsa.

Dr Arshan a nasa ɓangaren da yake babban likita ne, tuni yayi duk abin da ya kamata ya miƙa kula da komai a hannun na ƙasa da shi, ya shirya ya kamo hanyan jimeta, yana isa nan ma yayi arranging na komai jirgin ya ɗaga zuwa Kano, suna isa ya dannawa Abeed ƙira, ya zo ya ɗauke sa.

Suna tafiya a mota Abeed ya ce, “Dr wato ba ka tsayawa kallon ruwa, balle kwaɗo ya maka ƙafa, irin isowannan haka kaman daman a hanya kake na faɗa maka.”

Murmushi Dr Arshan yayi ya ce, “kana wasa Captain, idan baka yi bani waje ato, yanzu dai kai ni na kalleta tukunna.”

“A’a lokacin waliman ya kusa ai, ba lallai ka samu hankalinta ba yanzu, kasan mata da maganan kwalliya.”

Dr Arshan jinjina kai yayi, Abeed ya wuce da shi gidan Bunayd, ya ce ya samu ya shirya, shi ma bari ya je ya shirya zai dawo ya ɗauke sa su tafi waliman.

ACM Bunayd kuwa ya wasta ruwa ya kwanta yana hutawansa, sai ga ƙiran Papi, yana ɗauka ya ce, “Papi ango ba ya laifi ko ya kashe ƴar masu gida.”

Papi murmushi yayi tare da girgiza kai ya ce, “To Allah ya shiryaka Bunayd, tun da ka dawo kam ba za ka zo bane, ko ka yafe zuwa waliman ne bayan kai ka ce a yi shi.”

Shafa kai ACM Bunayd yayi ya ce, “sorry Papi, na manta ne amma yanzunnan ina hanya.”

“Allah kawo ka lafiya”, faɗin Papi a nasa ɓangaren, suna gama magana kuma ya daste ƙiran.

Bunayd sai da ya yi baccin 1 hour, sannan ya kuma ɗaukan wanka ya shirya abinsa ya kamo hanyan Kano, yana isowa ya ƙira driver ya zo ya ɗauke sa, ya kai sa gidansa, tun da gate man ya faɗa masa Abeed ya zo, ya taɓe baki yana faɗin ko me ya kawo sa oho, shi da yake da nasa gidan har da mace.

Bunayd na shiga ya ci karo da Dr Arshan, da mamaki yake kallonsa, wato shi Abeed ya kawo, murmushi kawai ya saki ya ce, “Dr Arshan kai ne a Kanon namu.”

Hannu Dr Arshan ya bai wa Bunayd suka yi musabaha, sannan ya ce, “Ni ne ACM, na biyo matata ce, da ita aka kawo amarya.”

Murmushin gefen baki ACM yayi ya ce, “Mata ikon Allah, mata masu Palace, wato yanzu baro patient’s ka yi bayin Allah saboda wata, and kuma ba matarka ba balle ka ce mini Palace ka biyu, dan da matarka ce ba zan ga laifinka ba, ko ni ina samun dai-dai ni to idan na bar ta tayi tafiya wan da za ta yi nesa da ni to kamawa ta yi, ko ta haihu muna jone, ba ruwana da jinin haihuwan.”

Dariya Dr Arshan yayi ya ce, “Wato fa ACM kai mayen gaske ne, to daɗin me ma za ka ji idan mace na jini, Allah ni likita ne amma jinin nan bana ƙaunarsa, musamman ƙarnin sa.”

Taɓe baki Bunayd yayi ya ce, “Dan na patients ne ba na matarka ba shiyasa, ai matan ma ba ko wacce jininta ke ƙarni ba, ko wacce da irin halittanta, kuma da irin yacce take kula da abun, ni fa ko bata kula da shi indai na samu dai-dai ni, to ni zan dinga kula da Palace in and out.”

Dr Arshan ya ce, “Ba ka da dama ACM, kuma fa kasan indai mace jininta na ƙarni sosai, to irinsu ne idan suna breast-feeding za ka ji nonon na ƙarni, amma wan da jininsu ba ƙarni ko tumbuɗi yaronsu yayi to ƙarnin da sauƙi.”

Lumshe ido Bunayd yayi tare da lasan lip’s ya buɗe baki zai yi magana, Dr Arshan ya dakatar da shi, wai su je su shirya, dan idan ya biye masa za’a fara waliman ba su yi komai ba, ba zai samu kallon matarsa yan da ya kamata ba.

Wucewa suka yi, Bunayd ya shige ɗakinsa, shi ma Dr Arshan ya shige ɗakin da ya zaɓawa kansa zai shirya a ciki.

Banafsha ba su tashi da wuri ba, dan Umaima ma ta rigata tashuwa, suna farkawa kuma suka karya tare da yin wanka, ba jimawa mai kwalliya ta zo ta fara gwangwaje su na shirin walima dan lokaci ya kusa.

Haraban gidan Papi an ƙawata shi ya sha kyau, kaman ba walima za’a yi ba, an saka rumfuna ko ta ina, ga wajan zaman maza ga na mata, ga na Amarya da jama’an ta, haka Uwar gida, haka kuma ga wajan zaman malami, shirye-shirye kawai ake yi, dan lokacin waliman ya riga da ya yi.

Lokacin da Malami ya iso, ko wanne tawaga sun fito, idan kaga yan da aka cika abin mamaki, duk da dai daman Alhaji Mukhtar mutum ne mai jama’a, abun mamaki rumfar Uwar gida da mutanenta, babu ko ɗan stunstu balle ɗan mutum.

Mami ta haɗe cikin kayanta na alfarma da mayafinta, ta rufe har fiskanta ta sha kyau.

Umaima da Banafsha kaya iri ɗaya suka sa, dogayen rigunan su wan da ya amshe su sosai, Mami ce ta musu shi.

Su Ummu duk kowa ya sha kyau ya haɗe, Aunty A’isha ma da Emaan nata sun yi ankonsu, kyau kam kowa yayi sa Masha Allah, duk sun samu waje sun Zazzauna a gefen Mami.

Momsee ta haɗe ita ma cikin wata dakakkiyar yadi, mayafinta ɗan dai-dai ta yafa, suna zaune tare da su Majeeder da sauran matan abokanaye, da dai jama’an da suka halarci waliman.

Majeeder, Ramla, Suhaila da Nabeela duk kaya iri ɗaya suka saka da Momsee, sosai suka yi kyau su ma, Majeeder ta dage za ta koma rumfan su Mami, amma Momsee ta hana ta, wai tana takura wa su Mami, dan dolenta ta zauna.

Su Suhail da Nabeel da sauran abokanan Papi da na General da su kan su masu gayyan, duk suna rumfan maza, Papi ya haɗe cikin gare yadinsa iri ɗaya da na General.

Ba iya Papi ke mamakin kasancewan rumfan su Mom empty ba kowa ba, kusan jama’an duka mamaki suke.

Malami ya fara wa’azi mai matuƙar shiga jiki, musamman akan yacce wasu ke ɗaukan rayuwa da zafi, bayan kuma yanzu duniyan ma duka gaba-ɗaya kaɗan ne ya rage mata balle mu ƴan adam, tun da alamomi dai na tashin duniya manyan ne kawai ba su bayyana ba, kaman zuwan dujjal, yajuju wa majuju, ɗauke Alkur’ani mai girma da Allah zai yi, zuwan Annabi Isa..etc, manyan alamomin ne kawai tukunna, amma ƙananun alamomi duk wan da ya duba da idon fahimta, to ya san sun jima da bayyana, don hatta wannan tsadan rayuwan alama ce ta duniya ta zo ƙarshe, sai dai Allah ya kyauta, ga kuma yaƙi da ƙasashe daban-daban ke yi, wan da sannu a hankali zai juye ya koma yaƙin duniya duka, fatan mu dai Allah azurta mu da mutuwan shahada idan mun riski lokacin, idan kuma mutuwanmu ta zo a yanzu Allah sa mu cika da imani, domin yanzu ana mutuwar fuji’a, sai addu’an gamawa da duniyar lafiya.

Papi jin shiru-shiru har an yi nisa da wa’azi, sai ya miƙe ya shige cikin gidan, gaba-ɗaya sashin Mom ya duba sama ko ƙasa amma babu ita ba alamanta, ran shi ne ya ɗan sosu, to ina ta je ana hidima kuma, waya ya ɗaga ya ƙirata amma layukanta a kashe, girgiza kai kawai yayi ya koma ya zauna ya ci gaba da sauraran tunatarwan Malam mai wa’azi.

Banafsha da bata son idon jama’a sosai, tana maƙale a bayan Mami, ba za ka ma kalleta ba ko ka zo wajan, da ta gaji ma miƙewa tayi ta ce, “Mami bari na ɗauko abu a ciki ina dawowa.”

Mami tana ji ta girgiza kai dan ta san Banafsha so take ta gudu, cewa tayi kawai, “a dawo lafiya, saura ki zauna kuma, ana wa’azi mai amfanarwa kina son guduwa.”

Cunna baki tayi ta ce, “Ba fa gudu zan yi ba Mamina, Allah kuwa zan dawo.”

“To naji, jeki amma maza ki dawo yanzun nan.”

“Uhmñ! to Mami”, ta faɗa tare da barin wajan, dan daman ta riga ta faɗawa Umaima, kuma ita ma Umaiman ta san halin ƙawartata.

Nusaiba tana shiryawa, Abeed ya sa driver ya kai ta wajan waliman, shi kuma ya wuce gidan ACM Bunayd dan su wuce tare da Arshan, bai san ma da zuwan Bunayd ɗin ba.

Dr Arshan wani irin haɗewa yayi na mamaki, gàskiya Dr Arshan kyakkyawan gaske ne, kaman Balarabe haka yake, yana fitowan palourn ya ga wayam, Bunayd bai fito ba tukunna, zama yayi jiran fitowansa.

ACM Bunayd kuwa yana fitowa a wanka ya fiddo kayansa jamfa, yana sakawa ya ji ya takura ya cire ya ajiye, ko wani kaya ya saka sai ya ji bai masa ba, ƙarshe wata fitted jallabiya ya saka, fari tass ya karɓesa kuma ba kaɗan ba, kyau yayi kaman a ƙasan labarawa, ga kistonsa kuma da ya ƙara masa kyau, sai da ya gama feshe-feshensa sannan ya fito ya nufo palourn, cikin takunsa na ƴan gayu.

Dr Arshan ya jima da zama sannan ya jiyo ƙamshi, yana ɗagowa suka yi ido huɗu da Bunayd, murmushi ya saki ya ce, “ACM da ku mata ne, to irinku ne masu saka maza su shaƙi haram, irin wannan turare haka kaman za ka tashi hancin mutum a aiki.”

Murmushi ACM yayi, yana isowa in da Dr Arshan ke zaune, sai ga Abeed ya shigo, Abeed da mamaki yake kallon Bunayd ya ce, “Musulmin ɗan jagaliya yaushe a gari? Na ɗauka ba za ka zo waliman ba bai, ɗan Amarya guda.

Dr Arshan ya ce, “tun da ka iso mu wuce, idan kuka tsaya magananku da ba ya ƙarewan nan sai a hankali.”

Bunayd kallon banza ya yiwa Abeed sannan ya ce, “Kai saboda ka nuna wa duniya, kana chaje Palace shi ne sai yanzu za ka iso.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “Wai to na hana wani yin permanent Palace ɗin ne, ba dai ka ce ƴar jagaliya kake so irinka ba, to za ka sha jira.”

Banza Bunayd ya yiwa Abeed suka fice, Mota guda suka shiga, Dr Arshan ne ya ce zai tuƙa su, shi yana driving sai Abeed zaune a kujeran gefensa, Oga kwata-kwata kuma yana hakimce a baya kaman wani Sarki.

Suna tafiya suna hiransu suna dariya, dan Bunayd ba’a raba sa da abin dariya, musamman idan da abokanansa yake zaune, shi sai yayi magana ya tsare kaman ba shi yayi ba, amma kai kuma sai maganan ya saka dariya kaman wan da ya fito daga Zariya.

Abeed shi ke nunawa Dr Arshan in da za su bi, har suka iso gida, aka buɗe musu tangamemen gate ɗin suka shige, ya samu waje yayi parking duk suka fito.

Dr Arshan ya ce, “captain kasan abin da ya kawo ni fa musamman, ba ƙarya ba waliman nayi niyan zuwa ba, wajanta na zo, ita na biyo, jininta ne ya jawo ne, dan tun da na ganta na foller, yarinyar tana da kyau ko ba powder.”

Dariya Bunayd yayi ya ce, “A IG ka fara ganinta.”

Duk sai suka saka dariya, shi dai Bunayd murmushi yayi, ya ce, “Idan Palace nata ba wuta ka yi a banza fa, kuma idan ustaziya ce an sha ka wasa wallahi, duk zaucewan nan ba wani abin da ya kamata.”

Dr Arshan ya ce, “Ko ma mecece ni fa a haka ta mini ACM, kuma ka ƙyale ustazan nan, matan da mazan sun san ta kan rayuwa wallahi, a waje suke ustazanci, a gida musamman gidan miji to su karuwai ne.”

Abeed ya ce, “faɗa masa dai ko zai gane, amma shi ya ce sam-sam ba haka ba, sai ƴar jagaliya.”

ACM ya ɗage kafaɗa irin ko a jikinsa ba za su taɓa saka shi ya yarda ba, yayi gaba abin sa ya nufi wajan su General, tun da Papi ya hangonsa ya girgiza kai kawai, yana cewa General, “kalli yaronka dan neman magana da jallabiya ya zo taron jama’a.”

Murmushi kawai General yake saki ganin irin haɗuwa da kyawun da yaron nasa yayi domin gaba-daya sai da ya haske wajan, cewa yayi, “Masha Allah, Allah ya azurta yarona da samun mace ta gari yau ɗin nan, wanka ta biya kuɗin sabulu, alfarman ayoyin wannan ƙur’ani mai girma da ake karantawa ana fassarawa.”

Papi ya ce, “Ameen”, dai-dai lokacin ACM Bunayd ya ƙariso, cikin takunsa na ƙasaita, tafiyan ba sauri ba ne a niste yake yin sa, amma kana ganinsa ka ga tafiyan zaratan jaruman maza.

Abeed ya ce, “To Danmusa newprince sai mu je wajan kalar shiga gaban motan taka.”

Murmushi Dr Arshan yayi, suma suka nufi wajan taron cikin takunsa mai ɗaukan hankali, wajan su Papi suka fara zuwa suka gaishe su tukunna, sai Abeed ya fara kalle-kallen rumfan su Mami, yana hangota kuwa ya taɓa Dr Arshan ya masa nuni da ita, a kunne ya raɗa masa, ga can ajebotan taka, shi kuma Dr Arshan har da dafe saitin zuciyansa a siyasance, wai irin sai da zuciyar sa ta buga da yayi tozali da matarsa(To Umaima tun Abbaa bai ba da ita ba, har Arshan ya ɗaura wa kan sa aure da ita.)

ACM a hankali ya ce, “Sir ina Mom fa? Na ga rumfant empty ba kowa.”

Ƙwafa Papi yayi ya ce, “Wannan Maman taku sai a hankali, jiya fa har aka kawo amarya tana nan, amma yau na nemeta na rasa kuma tasan za’a yi waliman.”

Bunayd ya ce, “Bari na dubo ta ko wani abun ne.”

Papi ya ce, “Na duba ta bata nan.”

General ya ce, “barshi dai ya je ya ƙara dubota, my man je ka ko wani abun ne ya faru, yaya idonsa baya gani da kyau wataƙila tun da ya ga amarya, ya daina kallon kowa sai ita.”

Murmushi kawai Papi yayi, ACM Bunayd kuma ya juya ya nufi sashin Papi.

Umaima kaman an ce ta ɗago ai kuwa idanuwanta suka sauƙa akan Dr Arshan, waro idanuwan tayi tana tambayan kan ta me ya kawo sa Kano kuma, shi kuwa a nasa ɓangaren ɗaga mata gira yayi, ita ko ta cunna baki, daga nan fa magana da ido da signa ta ɓalle tsakaninsu, duk abin da suke Abeed ya kalli Umaima ya kalli Dr Arshan, sai maste dariyansa kawai yake yi, yana faɗin yau kuma ya ga sabon sample na soyayya.

Banafsha tana shigewa sashin Papi, ta zauna a nan palourn ƙasa, kujera ta samu ta lume ciki ta kwanta abin ta, a zahiri tana ƙarewa palourn ne kallo, amma a baɗini gaba-ɗaya tunaninta ma ba ya garin Kano, Malam Abbo da take ƙoƙarin yakicewa a ran ta ne, ko da yaushe take tunaninsa, ta rasa haushinsa za ta ji ko tausayinsa, tun da ta san yana ƙaunarta.

ACM Bunayd palourn ya shigo yana danna wayansa, wani ƙamshi ne ya ji ya doki hancinsa, wan da shi dai yasan bai taɓa jin sa a palourn ba, kuma ba shi ne a jikinsa ba, dan haka tunani yayi ko akwai wan da bai je waliman ba yana cikin palourn, ba tare da ya damu da duba halittan da ke palourn ba ya wuce sama abinsa, sashin Mom ya shiga shi ma ya duba sama ƙasa babu ita, ba alamanta, taɓe baki yayi kawai ya juyo ya fito, yana mamakin hali irin na Mom, yana isowa palourn ƙasan kuma sai idanuwansa suka sauƙa, a kan wacce ke kwance a kan kujeran, fiskanta na kallon kan kujeran, ta bai wa cikin palourn baya.

Bunayd kawar da idonsa yayi, amma kuma sai ya samu kan sa da son ƙara kallon bayanta, wani yawu ya haɗiye ƙwattt!, shi tun da yake a rayuwansa bai taɓa kallon mace mai shape da haɗaɗɗen sura irin wannan ba, duk da ba wai ya cika kallon mata ba ne, sai ya ji yana son kallon wacece wannan ɗin.

Banafsha kuwa tana kwance a kan kujera ta juya baya, ta juya gaba duk tunaninta take yi, bata ji shigowan mutum ba har ya haura sama ya dawo duk bata ji ba, yanzu ma gajiya tayi da fiskantan kan kujeran ta kuma mirginawa ta juyo, duk abin da take a kan idon Bunayd da ya staya kallonta ya kasa ko mosti, sai da ta juyo gaba-ɗaya sannan yayi mutuwan staye, “what??”, ya faɗa a hankali, kallonta yake da kyau yana tunanin me wannan ke yi a gidansu? Ita da aka ce tayi aure me ya kawo ta Kano? Ai ko dangin amaryan Papi ce, tun da ta yi aure last Friday ita ma, ai bai kamata ta fita ba balle har ta zo Kano, gaskiya wasu mutanen akwai ƙarancin ilimi, mijin nata ma soko ne bai san me yake yi ba..

Bunayd bai ida zancen zucinsa ba, ya stinkayi haɗaɗɗiyar muryan Banafsha tana sumbatu, wan da jin muryan nata ya ƙara tabbatar masa ita ce, sai dai ba ya jiyo abin da take faɗa sosai, guntun tsaki ya ja tare da takawa a hankali ya ƙarisa gabanta, rasa ma me zai mata yayi, dan daman ya faɗa muddin ya gan ta ba ruwansa da tana da aure, dole sai ya mata hukunci.

Bunayd na tsaye yana tunanin me zai mata, tun da bata san yana wajan ba har yanzu, wani abu ne ya faɗo masa a rai, da ya tuna yawancin mata suna tsoron kule(Mage), dan haka a take ya shige wayansa ya nemo in da zai samu kukan kule, yana samu ya kawo wayan dai-dai kunnenta sannan ya kunna.

Banafsha na duniyan tunaninta, kawai ta ji kukan kule a kunnenta, wan da sabo da tsabar storo har ji tayi kaman yanan bin jikinta ne, ai da mugun sauri ta tashi a firgice ta yi tsalle ta dira a ƙasa, kamun ta kuma yin wani mosti Bunayd ya saka takalminsa ya murje mata ƴan yastu.

Banafsha ga kukan kule bai daina ba, ga azaba, ai a tamanin ta nemi hanyan ficewa a palourn har tana tun tuɓe, goshinta kuwa kaɗan ne ya hana sa haɗuwa da ƙofa, ficewa tayi ko ta kan takalminta bata bi ba, ta yi wajan su Mami a birkice.

Bunayd murmushi yayi wan da har haƙoransa dai da suka bayya, dimple nasa one side ya losta, ganin murmushin ba zai kai sa ba, bakinsa ya buɗe yayi dariya ɗan dai-dai, sannan ya seta kan sa ya fice shi na yana murmushi, farin ciki da nishaɗi yake ji a ransa, ko ba komai ta amshi hukuncinta, sannan kuma ya gane maganinta da kukan kule, idonsa idonta to sai ya kunna, dan haka adana application ɗin yayi a wayansa, wajan su Papi ya wuce, yana murmushi ya faɗa masa ba Mom, Papi ya ce daman ya sani ai ba kallonta zai yi ba, dan shi ma ya duba bata nan.

Abeed kallon Bunayd na ta murmushi shi kaɗai tun ɗazu, taɓa shi yayi ya ce, “Ya aka yi ne ɗan jagaliya? Sai washe talatin da biyunka kake kai kaɗai”

Haɗe fiska Bunayd yayi ya ce, “Kai dai ka so jin gulma kaman mace”, yana faɗa dai-dai an fara addu’an tashuwa, suka shafa addu’a ya tashi yayi part nasa, dan yasan part na Momsee yanzu haka ƴan biki za su cika.

Su Abeed da Dr Arshan kuma Majeeder suka jawo, tare da nuna mata Umaima wai ta ƙira musu ita, ta ce mata inji Dr Arshan, Majeeder ta amsa, ta nufi wajan su Umaima, dan daman ta mastu ta je wajan su.

Banafsha tana fitowa a birkice ta ƙarisa wajan su Mami ta nemi waje ta zauna, Umaima ce ta kalleta ya ce, “kina lafiya kuwa masoyiya?”

Ajiyan zuciya ta sauƙe ta ce, “Wani lafiya kuma, ai babu lafiya, ba ki ganni bane.”

Umaima ta ce, “To me ya faru, ga shi dai ko takalmi ba ki fito da shi ba, kaman an biyoki da gudu.”

Banafsha ta ce, “ai in da gudu aka biyo ni da sauƙi, da na shiga cikin gidan, sai na tsaya a palourn ƙasa ban ƙarisa sashin Mami ba, saboda na ga babu kowa a gidan, kekam ina kwance a palourn har bacci ya fara ɗauka na, sai kule na ji a jikina yana kuka, ina tashuwa a rikice ya kuma ƙwarzane mini ƙafa da farcun ƙafansa.”

Umaima kallon Banafsha tayi tana maste dariyanta, ta ce, “ki dai faɗa gaskiya wallahi Masoyiya, kule ta ina a wannan gidan? Ke de wani abun daban ne ya sameki.”

Banafsha haushi taji wai Umaima ta ce ƙarya tayi kuma tana mata dariya, sai ta haɗe fiska ta juya kawai, ana yin addu’a ta tamke hannun Mami suka wuce ciki tare, ko kallon Umaima ta ƙi yi.

Umaima kuwa Majeeder ce ta ƙariso wajanta ta ce, “sis wai inji su ya Abeed suna miki magana, ga su can amma na ce miki wai inji Dr Arshan.”

Umaima har za ta juya kuma sai ta fasa, ta ce da Majeeder su je, tare suka jera suna tafiya har suka iso wajan su Abeed.

Abeed murmushi yayi tare da yiwa Umaima sannu da zuwa, sannan ya ce Majeeder ta tafi sun sallameta sun gode, ita kuma ta juya abin ta.

Dr Arshan ya ce, “Hajiya barka da zuwa.”

Umaima ta amsa tana tura baki, Abeed ƙarshe barin su Dr Arshan yayi su sha hiransu, tafiyansa yayi wajan Bunayd dan ya ga lokacin da ya shige part nasa, ya shiga yana dariya, Bunayd yana kallonsa ya ja staki kawai, wai mutum kullum dariya kaman wan da kan sa ba ƙalau ba, Abeed dai bai kula Bunayd ba, Nusaibarsa ya ƙira a waya, duk da tana cikin gidan amma hiransu suke a waya.

Dr Arshan da Umaima kuwa sun sha dramansu, kuma bai faɗa mata son ta yake yi ba har suka gama hiran, ta koma ciki abin ta shi kuma ya koma wajan su Abeed.

Washe-gari kuma family and friends, yau ma kowa ya haɗu ya kuma sha kyau abin sa, su Bunayd duk sun sha wanka sun haɗe, sun halarci taron da wuri, yau ma dai babu Mom, kuma layinta ba ya shiga, har layukanta na ƙasar waje da Papi ke da su, ya ƙira amma ba sa shiga, dan haka tattara kashinta yayi ya ajiye a gefe suka ci-gaba da hidimansu.

Umaima da Banafsha tare da su Majeeder wajan zamansu guda, sun sha kyau su ma, duk ƙoƙarin Banafsha na kada ta yi tunanin Malam Abbo, amma muddin ta yi shiru to sai ta faɗa duniyar tunaninsa, ta rasa me ke mata daɗi.

Duk abin da Banafsha ke yi idanuwan Bunayd na kan ta, amma ita bata kula da shi ba.

Dr Arshan ko da ya kalli Banafsha shi ma ba ƙaramin mamaki yayi ba, ya ce ko dai mai kama da ita ne, Umaima ta ce masa an yi auren Faɗima, amma kuma ga ta nan yana kallon ta, ikon Allah.

Abeed ne ya ce, “Dr Arshan ka ga wata dalleliyar haɗɗaɗɗiyar Chika kuwa, a gefen mutumiyarka? Ni ina ganin fa naga second wife tawa kenan”

Dr Arshan dariya yayi ya ce, “matar wani fa kake kallo, ita ce nake faɗa maka mutumiyar ACM.”

Abeed haɓa ya riƙe, ya ce, “Ba ka ce wai tayi aure ba ranan.”

“Yeah! May be tare da ita aka kawo amaryan Papi, ko ita ma danginsu ce, idan kuma ba ita ba to tabbas mai mugun kama da ita ne.”

Abeed ya ce, “Amma idan har ita ne to lallai da alama, mijin da ya aureta bayan sokanci, to har da jahilci yana damunsa, wannan haɗaɗɗiyar zinaren yake bari ta fita sakaka haka, kuma ma abun haushin tana amarya ko sadakinsa bai more ba, Allah sarki wataƙila Soja ne irinmu ko an yi bikin ma baya nan”, haka Abeed ya din ga mitansa shi kaɗai, ji yake kaman ya ga mijin Faɗima ya rufe sa da duka.

Bunayd da ya bai wa su Banafsha baya, ba sa kallonsa, yana sauraran su Abeed bai ce musu komai ba, hankalinsa na kan wayansa yana ƙulla ƙullalliyansa.

Ana hidima kowa da kowa na zaune, Papi, General, Momsee da Mami duk wajan zamansu ɗaya, sai sauran jama’a su Alhaji Idris da sauran abokanan Papi ma wajan zamansu ɗaya.

Papi da General suna zaune shiru, har lokacin Mami da Momsee ba su iso ba, ga shi dai ana hidima ana ci ana sha, ana ta shagali dai, General ne ya ce, “Wai su Dear kam ba za su fito bane, ta koyawa amarya maƙalewa a cikin gida.”

Murmushi Papi yayi ya ce, “ai harka da mata sai a hankali.”

Papi bai gama rufe baki ba sai ga su Momsee sun ƙariso, Momsee kayanta irin na General, ita kuma Mami irin na Papi, yau kam mayafin bata rufe fiska da shi ba, ta yafa sa a kafaɗa irin na manyan hajiyoyi.

Momsee ce ta ja kujera ta ce, “To amarya bismillah”, sai da Mami ta zauna tana murmushi, sannan ita ma ta ja nata ta zauna.

Papi yana murmushi ya ce, “Ramlatu ga ki ga General yau kam, tun da aka yi aure ya dameni bai kalli amarya ba.”

Momsee ta ce, “ai kam sungullolin sai a hankali yaya, amfanin taron ma kenan a ga juna.”

Mami idanuwanta a ƙasa sai murmushi kawai take yi, ita gaba-ɗaya abin da ake yin nan kunyan yake saka ta ji, hidiman biki kaman na budurwa, Alhaji ya koɗa abun sosai, ai ko auren farinsa albarka.

General yana dariya ya kai kallonsa kan Mami yana faɗin, “Amaryan……”, maganan bakinsa ne ya ɗauke, lokaci guda kuma da murmushin da ke fiskansa, zaro idanuwan yayi bakinsa a buɗe yake nuna Mami, da ƙyar ya tattaro kalmomin bakinsa ya haɗe su wajan cewa, “Gim..bi.ya..Ra..Ram.latt..ke ce..na..nake gani?”

Mami jin sunan da aka ƙirata da shi, ai a ɗari da sittin ta ɗago kan ta, dan ta yi mugun storita, zaro ido ta yi ita ɗin ma, kaman wacce ta ga abun storo, ta ce, “Ya Sufyannnn kai neee?”

Gumi ne ya fara sharto wa General, duk da kuwa iskan da ke kaɗa wa a wajan.

Momsee da Papi kuwa suman zaune suka yi na wucen gadi, ikon Allah suke kallo, me ke faruwa haka stakanin General da Ramla kaman wan da suka kai shekara da shekaru da sanin juna.

Papi ne yayi ƙarfin halin cewa, “General ka san Ramla ne daman? Ramla a ina kika san General?”

Momsee ta ce, “Dear ba dai ita ce Gimbiya Ramlat da ka taɓa bani labarinta ba?”

General Sufyan gaba-ɗaya ma ya rasa abin faɗa, sai dai kawai ɗaga kai da yayi na tambayan da Papi ya masa akan daman ya san Ramla, da kuma Momsee da ta yi nata tambayan.”

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Allah mai iko”, faɗin Momsee.

Mami na ƙoƙarin miƙewa, Papi ya dakatar da ita, dole ta koma ta zauna, tana jin wani irin gingimemen abu na tinkaro ta, lallai a yau dole daga ƴar ta har mijinta, su san wacece ita, hatta Mama Hadiza da ta ɓoye musu gaskiya.

Papi ganin General ya ɗaga masa kai, alaman eh, sai ya sauƙe ajiyan zuciya tare da faɗin, “Ku yi haƙuri to a samu a gama wannan taron, anjima sai mu zauna a yi magana, please General ka sai ta yanayinka, ke ma Ramlatu ki yi haƙuri har mu samu a sallami jama’a.

Mami dai kaman wacce ruwa ya cinye haka ta zama, shi kuwa General gaba-ɗaya ji yake kaman akan ƙaya yake zaune.

<< Yar Karuwa 21Yar Karuwa 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.