Skip to content
Part 26 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Har cikin gidan aka musu jagora, a wani haɗaɗɗen palour aka sauƙe su, Mami har lokacin bata daina hawaye ba, dan abubuwa da dama suna dawo mata sabo fil, musamman rashin ƴan uwanta ƴan biyu, da kuma rashin Ummanta, wa ya sani ko ƴar Adda Habiba tana nan ko ta yi aure ma, so take kawai ta kalleta, ta kalli yacce takwarar Ummanta ta girma.

Matan Sarki dukka an sanar da su, kamun ka ce me ma duka masarauta ya ɗauka da maganan dawowan Gimbiya Ramlatu, bayan shekaru ashirin da barinta gida.

Daga hadimai har dogarai, duk wan da ya san ta, to sai ya zo musu Barka, Mami dai sai zuba ido take ta ga ta in da matan Mai martaba za su ɓullo, can kuwa sai ga Umma Talatu da kuma Adda Habiba sun shigo, duk girma ya kama su, da sallama suka shigo da hadimansu a bayansu, Mami tana kallonsu ta miƙe tana faɗin, “Umma, Adda.”

Umma Talatu salati ta yi ta sanar da Ubangiji ta ce, “Da duk ɗauka na alamara ne, ashe da gaske ne, Ramlatu ke ce? Ramlatu daman kina raye, Ramlatu ina abin da kika haifa?”, Umma Talatu ta faɗa tana mai rungume Mami stam, sai kuma kuka ya ƙwace mata, Mami na kuka ita ma tana kuka.

Adda Habiba tun da ta ɗaura idanuwanta akan Mami, shikkenan sai hawaye zirr zirr, ita ma rungume juna suka yi da Mami tana faɗin, “Ramlatu ki yafe mu, Ramlatu ki yafe mana, Ramlatu ƴar uwanki kuma ƙanwanki Rahmatullah ta tafi ta bar mu, Ramlatu Rahma ta rasu”, sai ta fashe da wani kukan kuma.

Mami da matan Sarki sai kuka suke, Mami ta mance ma da rayuwan su Banafsha a palourn, matan Sarki kuma daman ba su kula da mutane da yawa ba, burinsu su kalli Mami, tun da suka kalleta kuma shikkenan sai kuke-kuke.

Mami ce ta stagaita kukanta, murya na rawa ta ce, “Adda da gaske Rahmatullah ta rasu? Adda me ya same ta? Ina Mama suwaiba?”

Adda Habiba tana kuka ko zarran ba da amsa bata samu ba, sai Umma Talatu ne ta stagaita nata kukan ta ce, “Rahmatulla kam rai yayi halinsa Ramlatu, kullum tana cikin ambaton ki, da sunanki a bakinta har ran ya fice, Mama suwaiba tana ɗakinta, tun tafiyanki ba jimawa take fama da cuta, ya ƙi ci ya ƙi cinye wa, ba irin maganin da ba’a yi ba, sai a hankali.”

Mami wani sabon kukan ne ya zo mata, a haka Sarki ya shigo ya same su, girgiza kai yayi ya ce, “Ashsha! Wannan wani irin yaranta ne da girmanku Habiba da talatu, za ku sa baƙin ku a gaba kuna kuka, ku bari mana su huta, tun da Allah yayi Allahnsa ya dawo mana da ita lafiya, ai kwa bari su huta komai mai sauƙi ne.”

Adda Habiba da Umma Talatu duk shanye kukansu suka yi, sannan suka zazzauna, Sarki ma ya samu waje ya zauna ya ce, “Bayin Allah ku yi haƙuri fa”, ya faɗa idanuwansa akan su Alhaji Mukhtar.

Murmushi Alhaji Mukhtar yayi ya ce, “Ba mastala rankashidaɗe, ai an kwana biyu ba’a haɗu ba ne.”

Jinjina kai Sarki yayi ya ce, “Yanzu dai yana da kyau ku ɗan huta, zuwa muyi sallahn azahar sai a gaggaisa kuma a ji ya bayan rabuwa.”

Alhaji Mukhtar ya ce, “To Mai martaba.”

Sarki ya dubi Mami ya ce, “Gimbiya Ramlatu masto nan kusa da ni.”

Mami mastawa tayi ta zauna a kusa da ƙafan Mai martaba, sannan ta ce, “Na same ku lafiya Baba?”

“Lafiya alhamdulillah Ramlatu, amma bari sai zuwa anjima za mu gaisa, yanzu dai ku huta, ina abokin nawa ko amaryar tawa?” Faɗin mai martaba.

Mami ƙasa tayi da kan ta, hawaye na neman zubo mata, ta daure ta mai da su, sannan ta ce, “Gata can Baba”, ta faɗa tana masa nuni da Banafsha.

Daga Sarki har matan nasa idanuwansu na kan Banafsha, murmushi yayi tare da faɗin, “Allahu Akbar! Allah mai girma wannan ce abin da kika haifa Ramlatu? Masha Allah amaryata ta girma har haka?”

Umma Talatu murmushi suka saki, suka ce, “Ikon Allah ikon gaske, Masha Allah! Yarinya kam ana ganinta an ga jinin marigayiya Rahmatullah.”

Mami ƙasa tayi da kan ta, tare da yi wa Banafsha nuni da ido na ta zo.

Mai martaba ya ce, “Zo nan raba dangi, kin raba ni da ƴa ta kin kanainaye ta, zo na kwaɗeki tukunna.”

Banafsha miƙewa tayi a hankali ta ƙarisa gaban Mai martaba, ya mata nuni da ta zauna a gefensa kan kujera, da ƙyar ta yarda ta zauna, sannan ya ce, “Masha Allah! Naji daɗin ganinku duka ba kaɗan ba, naji daɗin zuwan nan naku, kuma daman ban cire ran kamun na bar duniya zan gan ki ba Ramlatu, cikin ikon Allah sai ga ku kuma lafiya da ke da ƴar ki, to godiya ta tabbata ga Allah, yanzu ku samu ku huta, a kawo muku abun taɓa wa ku taɓa, idan mun yi sallah mun dawo sai mu gaisa kaman yan da na ce.”

Umma Talatu da Adda Habiba, miƙe wa suka, hadimai na bin su suka shige cikin gidan da Mama Hadiza da Majeeder da Mami da kuma Banafsha.

Mai martaba da General Sufyan ne da Alhaji Mukhtar suka rage a palourn, gaisawa suka yi, Mai martaba ya ce, “Sannunku bayin Allah, mun gode sosai, sannunku da ƙoƙari, ku ne mariƙan Gimbiya Ramlatuna kenan.”

General Sufyan murmushi yayi ya ce, “Rankashidaɗe eh, amma mu ma ɗin dai ba da jimawa ba, wannan yayana Mukhtar sule shi ne mijinta, sai ni kuma Sufyan sule ƙanin sa.”

Sarki jinjina kai yayi ya ce, “Masha Allah! Sannunku da ƙoƙari yarana.”

Hadimai ne suka din ga shigowa da kulolin abinci, abin mosta baki da sauransu, sai lokacin Papi ya ɗaga waya ya ƙira ACM Bunayd da ke can maƙale a mota, ba jimawa ya shigo tare da ba-faden nan, lokacin kuma Mai martaba ya riga da ya fice, saboda ya basu waje su ci abinci.

General murmushi yayi tare da girgiza kai ya ce, “Allah ya shiryeka my Man, dan kaman dai zuwanka ba shi da amfani, da mun sani mun baro ka gida kawai.”

Alhaji Mukhtar ya ce, “Ai ka ƙyale yaron nan, bansan me ke damun Bunayd ba kwana biyun nan, halin da baya yi yake son stira, amma dai nasan maganin abun auren kawai za’a masa.”

ACM Bunayd yana jin zancen su Papi, amma yayi shiru abin sa bai ce komai ba, domin shi Allah ma ya gani bai so zuwa Sokoto ɗin nan ba.

General ne ya ce, “To bismillah yaya da my Man, kunsan ba daɗi mutum ya baka abu ko albarka baka saka ba.”

ACM a cikin fruits ya jefa hannunsa, Mango da kankana kawai ya taɓa shikkenan ya ishe sa, Papi da General ne suka taɓa abu sosai, har lokacin sallah yayi suka fice suka je masallacin masarautan, an yi sallah an idar sannan suka dawo masauƙin su suna jiran zuwan mai martaba da su Mami, ACM ji yake kaman ya fire ya gan sa a Lagos.

Su Mami suna ficewa suka yi sashi Mama suwaiba, Mami da ta ga yan da Mama suwaiba ta koma sai da tayi hawaye, mama suwaiba kuwa sai ido, maganan ma sai da ƙyar take yi, ciwo jinya kusan shekaru ishirin tana fama da abu guda.

Mama Hadiza suka gaggaisa da matan Sarki, Majeeder da Banafsha duk suka gaishe su, aka kawo musu abinci suka ci, har da wasta ruwa dukkansu suka yi, amma kowa kayansa ya mayar, Mama Hadiza ne kawai bata wasta ruwa ba, ana ƙiran sallah suka tashi suka yi, sannan suka zauna zaman jiran ƙiran Mai martaba.

Mai martaba sai da aka ɗan ɗau lokaci sannan ya ƙaraso palourn, da masu taka masa baya, da ya zauna sai ya aika ƙiran su Mami har da Mama suwaiba a kawo ta.

Su Mami na zaune saƙon ƙiran Mai martaba ya iso su, nan duk suka ɗugun zuma duka suka wuce palourn, duk da sallama suka shigo, har da Mama suwaiba da ke zaune a ɗan kujeran da ake ɗaura marassa lafiya.

Sannu mai martaba ya ƙara yi musu, sannan suka ƙara gaggaisawa, Mami ta gabatar masa da su Papi, da kuma Mama Hadiza da take mariƙiyarta.

Mai martaba jinjina kai yayi ya ce, “Masha Allah! Muna godiya da ɗawainiya baiwar Allah, Allah saka miki da alkairi.”

Mama Hadiza ta ce, “Bakomai yi wa kai ne.”

Mai martaba ya ce, “To Ramlatu ya bayan rabuwa kuma?”

Mami ƙasa tayi da kan ta, tana share hawayenta ta labartawa su Mai martaba komai da komai da ya faru tun barinta gida, har zamanta wajan Mama Hadiza, har rayuwan da tayi, har auren Banafsha da aka fasa, har aurenta da Alhaji, har dai yau da suka zo Sokoto, ba abin da ta ɓoye.

Ba iya Mai martaba ba, hatta su Umma Talatu sai da suka yi hawaye, Mai martaba gaba ɗaya ji yake kaman a ce shi ya mutu ba Umman Mami ba, da ya huta da ganin irin wannan rana, shi da kan sa ya kori ƴar sa ba dogon bincike, ya kuma mata baki cikin ɓacin rai, ga shi baki ya kama ta har ta yi abin da bai kamata ba, lallai bai kyauta ba.

ACM kuwa sai yanzu ya ji zuwa Sokoto bai gundure sa ba, labarin Mami ya basa tausayi sosai, wato ashe akwai irin matan nan a duniya, lallai da ta tsaya iya haka ma tayi ƙoƙari, musamman irin tarbiyyan da ta yi wa yarinyarta da ikon Allah, da taimakon Allah, amma abu guda da ya staya masa a rai a labarin wato dai, fitsararriyan nan karya ta masa, an saka su a corner shi da Abeed, wato single take bata da aure, cijan leɓensa yayi tare da aikawa in da take zaune, da kallon za mu haɗu ne.

Mami ma kukanta take kan yi tana faɗin, “Ku yafe mini Baba, ku yi haƙuri, lokacin ƙuruciya na kai na ne, amma da ba zan taɓa zaɓan abin da ke ciki, wan da bani da tabbas da zai zo da rai akan iyayena ba, abin da bani da tabbas ɗin zan rayu da shi ko a’a.”

Mai martaba share ƙwallan da ya zubo masa yayi ya ce, “Mu ne ya kamata mu nemi yafiyanki Ramlatu, musamman ni da nake mahaifinki kuma na kasa sauƙe nauyin da Ubangiji ya ɗaura mini, domin ku ƴaƴa kiwo ne ga mu iyayenku, sannan Allah sai ya tambayi ko wani bawa akan kiwon da ya bashi, na ƴaƴa ne ko na mata, ko dai dukiya, Ramlatu ban kyauta miki ba, na jima da yafe miki, kema ki yafi mahaifinki, kuma ko kaɗan ban ga laifinki na rayuwan da kika faɗa ba, duk da bai mini daɗi ba kuma ban so hakan ba, amma dai alhamdulillah tun da ga shi har kin yi aurenki, sannan abu mafi kyau da ya mini daɗi shi ne, tarbiyyan da Nana Faɗimatu ta samu, wan da na ji daɗinsa da har ta kai matakin, da ta je musabaƙan karatun Qur’ani mai girma har Abuja, Allah ya miki albarka Ramlatu, Allah ya albarkaci zuri’anki, Allah ya saka wa mijinki da alkairi, ba ni da bakin gode musu, shi da wannan baiwar Allah Hadiza, sai dai na ce Allah ya ji ƙan mai gidanta, Allah ya masa rahama, alkairin Allah ya kai masa har makwancinsa akan riƙe marainiyar Allah da yayi.”

Duk palourn suka amsa da Ameen, Mami cikin kuka ta ce, “Baba ashe kuma Allah ya yiwa Rahmatullah rasuwa? To Allah ya mata Rahama, Allah ya sa ta huta.”

Murmushi mai ciwo Sarki yayi ya ce, “Uhmn! Ramlatu ai Rahmatullah kam sai dai fatan Allah ya sa mu yi guzurin alkairi na tarda su, rasuwa tayi wajan haihuwa kin ga kuwa mutuwa mai kyai tayi, mutuwar shahada wacce duk muke fatan ta, Allah dai ya kai haske makwancinta, Allah kuma ya sa muma mu cika da Imani.”

Nan ma duk suka ƙara amsawa da Ameen.

Mai martaba yayi gyaran murya tare da cewa, “Ramlatu mu dai bayan barin ki masarauta, komai sai a hankali kawai, amma muna godiya ga Allah a hakan, domin wani abun ni na tabbata ishara yake nuna mana, musamman maganan ɓarar da cikin jikinki a lokacin, kin ga muna ja da ikon Allah, ashe stawon rai ne ga abin da ke cikinki, wataƙila ma har da rabon ƴin ƴaƴa take da shi, tun da ga shi ana sukanta ana son hana zuwanta duniya, da yake Allah ya nufa sai da ta zo, kuma cikin ikonsa ta kasance ƴa tagari wacce ko wanne uwa da uba, za su ji ina ma su ne iyayenta, ilimin ƴaƴa mata yana da matuƙar amfani da fa’ida, sai dai mu ce Allah ƙara taimakawa, wani lokacin meyasa ake hana zubar da ciki ko da kuwa na shege ne wan da ba’a san komai game da ubansa ba, saboda baka san me za ka haifa ba, Malami ne, shugaba ne, wani wan da zai sharewa al’umman Annabi SAW hawaye ne, da dai makamantansu, amma zamani ne muke ciki wan da duk da dai haihuwan ƴaƴan shegu ya yawaita, saboda alaman tashin duniya, to har da ɓarar da yaran ana yi tun daga ciki, na sunna da waɗanda ba na sunna ba, Allah rufa asiri ya kyauta, ya ƙara shiryamu, sharri da masifan ƙarshen zamani Allah ƙara nisanta mu da su.”

Numfasawa Mai martaba yayi sannan ya kuma cewa, “Bayan barinki gida, abu na farko da muka fara fama da shi, shi ne ciwo da Allah ya jarabceni da shi, sakamon damuwa da na saka a rai na, da kuma ƙaunarki da nake yi da fushi da ke, da suka haɗe sai suka haddasa mini cutar hawan jini da ciwon zuciya, har ɓari na guda ya shanye, wan da na fi shekara uku ina fama da shi, sai daga baya na ji sauƙi cikin ikon Allah alhamdulillah, sai kuma abu na biyu shi ne cutan da ya samu suwaiba, barinki gida da watannin da ba su cika biyu ba, wasa gaske ta fara ciwo, yana cin jikinta a hankali, ana magani gida da asibti amma ba sauƙi, sai dai mu ce Alhamdulillah, tun da ga shi har yanzu da nake wannan magana tana fama, ga ta a kwance, sai an ɗaga sai an ƙwantar, an je asibitoci da dama amma ba’a ga komai da ke damunta ba, komai lafiya haka likitoci ke faɗa, har ƙasar waje an kai ta duka sai a hankali, ciwo har yau kullum gaba gaba abin yake yi, sai kuma abu na uku bayan tafiya da rayuwa ke yi da daɗi babu daɗi, cikin jarabawa da mastaloli, sannan a gefe na ina maƙale da tunaninki, to tafiyanki da shekaru biyar aka yi auren Rahmatullah, da yaron wani abokina Sarkin ƙaramar hukumar Kebbi, Rahmatullah ina ga ta kai shekaru goma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, kuma tun da aka yi aure cutan yau daban, ta gobe daban tun suna jinya har suka gaji suka kawo ta gida, muna magani dai a nan gida, sai ya zamana duk in da muka je to za’a faɗa mana aljanun jikinta sun ci ƙarfin siffanta na mutane, bi ma’ana dai ƴar aljanu ce, mun yi sa’a ma da tayi stawon rai har haka, wani magani muka amsa a yankin Nijar ta in da aka amsowa ƙannenki ƴan biyu lokacin da suka yi cuta, to wannan maganin ne muka samu jikinta yayi sauƙi kaman ba ita ke ciwo ba, har ta samu ta koma ɗakinta, tana komawa kuma sai rabo ya shiga, lafiya-lafiya tana renon ciki har ta kai watan haihuwa shiru, ciki sai da yayi shekara da rabi a jikinta, nan ma ba’a zauna ba, ba mu damu da asibiti ba tun da munsan cutanta na gida ne, aka nema magani shiru ba canji, ga ta dai lafiyanta ƙalau amma ciki ya ƙi rabuwa da ita, ƙarshe asibitin aka kai ta, ana zuwa aka ce za’a mata aiki ne a cire Yaro, aka sa hannu aka shiga da ita ɗakin haihuwa, a ƙarshe dai sai gawan Rahmatullah ne ya zo gare mu, da kuma gawan yara biyu waɗanda sam-sam ma, babu kyan kallo, kana ganinsu kasan ba lafiya ba, waɗannan yara ba mutanene ba, Allah ya so ma sun bi ta, nan aka musu sitira aka kai su gidan su na gaskiya, amma fa duk cutan da Rahmatullah ke yi to kina bakinta, hatta da za’a shiga da ita ɗakin haihuwan sai da ta ba da wasiyyan a ce ki yafe mata idan ta miki ba dai-dai ba duk ran da Allah yayi zuwanki, to daga nan kuma sai dai mu ce Alhamdulillah, waɗannan jarabawa uku mun fama da su, ko nace muna kan fama da su Ramlatu, Allah kyauta kawai.”

Mami kuka kawai take yi kaman za ta shiɗe, Rahmatullah yarinya mai hankali da nistuwa ba ruwanta, Allah sarki rayuwa lallai kulli nafsin za’ikatul maut, dole ko wani rai sai ya ɗan ɗani mutuwa, to Allah ya sa mu cika da Imani muyi kyakkyawan ƙarshe.

Mami ta ce, “Ku yi haƙuri Baba, ina mai ƙara neman afuwan ku.”

Mai martaba ya ce, “Bakomai Ramlatu, komai ya wuce ai ya zama labari kuma, yanzu kam sai dai Allah ya kyautata mana gaba ya kuma bamu ikon gyara gaba.”

Gyaran murya Alhaji Mukhtar yayi, sannan a niste ya ce, “Masha Allah! Ubangiji Allah ya yafe mu duka, Allah kuma ya kyautata ƙarshenmu, waɗanda suka riga mu gidan gaskiya Allah ya rahamce su, Rankashidaɗe ka yi haƙuri da maganar da zan yi yanzu, domin tana daga cikin dalilin zuwanmu, ba iya dawowan Ramlatu bane dalilin.”

Murmushi mai martaba yayi ya ce, “To Mukhtaru ina sauraranka.”

Alhaji Mukhtar cikin girmamawa ya ce, “Dan Allah idan da hali a cire mu a cikin duhun da muke ciki duka Rankashidaɗe, Maganan Faɗima, maganan mahaifinta, Ramlatu ta bamu labarin yan da komai ya faru kaman yan da ta faɗa yanzu, to duk sai kan mu ya ƙulle, dan Allah menene gaskiyan al’amarin? Waye mahaifin Faɗima? yana da kyau ko da baya raye ne yarinya ta san mahaifinta, domin wuce gori, ga shi dai abin da ya faru har fasa aurenta aka yi akan wannan lamari, bayan kuma maganganun da ake jifanta da shi akan mahaifiyarta, sam-sam abun babu daɗi, yarinyar nan ƙarama da ita amma ta haɗiye abubuwa da yawa, wanda wani babban ma ba lallai ya iya jurewa ba, waye mahaifin Faɗima?”

Kamun Papi ya rufe baki, tuni muryan Banafsha ya karaɗe palourn, cikin kuka take faɗin, “Kaka dan Allah waye babana? Waye wannan wan da ya mana wannan baƙin tabo ni da Mamina?”

Mami na kuka Banafsha na kuka, Majeeder kam daman tuni Papi ya korata, ya ce ta koma ciki ta jira su, shi kuma Malam Bunayd yana nan zaune hakime, a gabansa ake komai, yau dai ya ji abin da aka yi ranan da baya nan, kuma yana cike da tausayi da kuma mamakinsa a zuciyarsa, sai yanzu ma yake jin wani irin tausayin fistararriyan nan na stirga masa a ran sa, ashe da dalilin yin rashin kunyarta,(kunsan Bunayd da tausayi, ga ilimin addini ga kuma aiki da shi, abu ɗaya gare sa ku bar sa da halin ƴan duniya idan abun ya mosta.”

Umma Talatu, Adda Habiba da Mama suwaiba duk kuka suke, na labarin Mami, da kuma rasuwan Rahmatullah da Mai martaba ya tuno musu da shi, ya dawo sabo fill, dan abin sai wan da ya gani irin wahalan da ta sha ba kaɗan ba.

Ajiyan zuciya Mai martaba ya sauƙe ya ce, “Wannan gaskiya ne, ko ba don gori ba yana da kyau yarinya ta san waye mahaifinta, saboda da uba ake ado ba rigar aro ba, amma sai dai zai yiwu idan na yi wani magana ku ce ƙarya nake yi, domin har yau duk binciken da zan yi na gama bansan ya wannan al’amari ya faru ba, ni da kai na bansan waye wan da ya yiwa Ramlatu wannan aika-aikan ba, sannan abun dai abu ne mai ban mamaki, don ba ta zuwa ko ina a wannan lokacin, banma san tana da manemi ba sai daga baya nake jin ashe abokin marigayi Ahmad ɗan gidan wazirina yana nemanta, to magana ta gaskiya nima karan kai na ban sani ba, bincike nayi iya bincike, hatta hadimai da ma’aikatan gidan nan ba wan da ban tambaya ba, amma babu labari, mastalan da kenan, da ace irin rayuwan yanzu ne da ake manna maɗuka photo a ko ina(CCTV camera), ai da duk ba wannan zancen ake yi ba.”

Alhaji Mukhtar ya ce, “Rankashidaɗe ai ƙanina Sufyan, shi ne abokin marigayi Ahmad.”

“Ikon Allah ikon gaske, wato wannan shi ne abokin Ahmad ɗin, ooh sannunmu da ƙarin haƙuri Sufyanu, Allah ya jaddada Rahama a gare sa, Allah mai iko wato kai ka so Ramlatu tun farko, sai kuma Allah ya nufa wan ka ne zai aureta, to Allah basu zaman lafiya.”

Duk palourn suka amsa da Ameen.

Mama Suwaiba da ke zaune a kujeran marassa lafiya ita ce ta stagaita kukanta, cikin yin magananta da ƙyar ba ya fita sosai ta ce, “Ramlatu da farko ina mai neman yafiyarki akan labarin da zan bada, ki yafe mana domin alhaƙinki ke bibiyarmu kaman yan da Mai martaba ya faɗa, tun daga ciwon da nake fama da shi har zuwa lamarin Rahmatullah, to duk alhaƙinkin ki ne, domin Allah ba ya yafe haƙƙin wani, kuma yana sakawa mai haƙƙi tun a duniya ba sai an je lahira ba, Ramlatu ki yafe mu, ba mu kyauta miki ba, mun zalunce ki, mun ci amanan maraicinki, mahaifiyarki ta zauna zuciya ɗaya da mu lafiy lau, amma son zuciya ya rufe mana idanuwa, kwaɗayin mulki da hassada, gami da rashin tawakkali su suka ja komai, mun kasa yarda da jarrabawan da Allah ya mana na rashin haihuwa, ko da muka masta har Habiba ta zo ta samu cikin ta haihu, muna murna to daga ƙarshe ga isharan da Allah ya nuna mana, ita kan ta Rahmatullah mun ɗau alhaƙin ta, ki yi haƙuri Ramlatu.”

Adda Habiba kuka mai tsanani ta fashe da shi tana faɗin, “Ramlatu ki yafe mana, Ramlatu ki yafe mu, mun ci zalinki, haƙƙinki shi ke bibiyarmu, kiyi haƙuri Ramlatu, duk ƙullinmu ga shi daga ƙarshe kan mu ya dawo, mun yi nadama kuma mun jima da tuba, dawowanki kawai muke jira, domin mu warware gaskiyan lamari mu nemi yafiyanki, idan baki yafe mana ba bamu san da wani yanayi za mu tsaya gaban mahaliccinmu ba ranan gobe ƙiyama, Ramlatu ki yafe mana, munsan muddin kika yafe mana to alhaƙin Ummanki da na ƴan uwanki duk za su sassauta a gare mu, mun cutar da ku mugun cutarwa, ga shi yarinyar da muke taƙama da ita duka yacce Allah yayi da abin sa.”

Umma Talatu ma tana kuka ta ce, “Ramlatu ki mana afuwa, sam-sam ba mu kyauta ba, haƙƙinki ke bibiyarmu ki yafe mana.”

Mai martaba da gaba ɗaya mutanen palourn su suke kallo, musamman ACM da yake jira ya ji abin da suka yi, don tun bai ji ba zuciyarsa ke tafarfasa kaman ya fasa kan su da bindiga, Sarki ne ya ce, “Me kuka aikata Suwaiba? Talatu me kuka ƙulla? Habiba me kuka yi ne? Kada ku ce mini kuna sane da cikin da aka wa yarinyata kuma kuka taimaka wajan ganin na koreta? Ina sauraren ku maza ku bani amsa”, Mai martaba ya faɗa ran sa a mugun ɓace(kunsan tun farko na faɗa muku yana da zuciya sosai.)

Mami kukanta ne ya staya gaba ɗaya, maganganunsu take juyawa da kuma na mai martaba, a hankali ta yi ƙoƙari wajen haɗa kalmomin da suka rage a bakinta ta ce, “Mama, Umma, Adda ne kuka mini? Me kuka mana ni da Ummata da ƙannena?”

Banafsha cikin kuka ta ce, “Me kuka yi? Waye mahaifi na? Dan Allah ku faɗa mini waye babanaaaaa!”

Mai martaba rai a ɓace ya ce, “Ku muke sauraro.”

Alhaji Mukhtar cikin girmamawa ya ce, “Dan Allah Mama ku taimaka ku faɗa mana.”

Mama Suwaiba tana numfashi sama sama ta ce, “Za mu faɗa, dan alƙawari ne sai mun maimaita da bakin mu, ko da na fara ban ƙarisa ba, Talatu da Habiba za su ƙarisa, musamman ma Habiba dan ko Talatu akwai abin da muka ɓoye mata, kuma daman a rubuce yake muddin wannan rana ta zo to ranan barina duniya ta zo, dan haka shiyasa na fara neman yafiyarku, ku yafe mini dukkanku.”

Mai martaba ya ce, “Ba mai yafe ma wani anan wajan sai mun ji gaskiyan lamari, idan ya kai a yafe muku za’a yafe muku,idan ya wuce yafiya kuma to Allah zai saka ma masu haƙƙi.”

Mama Habiba tana nishi da ƙyar da ƙyar ta fara ba da labari.

GASKIYAN LAMARI.

ABIN DA YA FARU SHEKARU ARBA’IN DA ƊORI BAYA.

Kaman yan da ya ke kuma kowa ya sani, ni Suwaiba ni ce matar mai martaba ta farko, mun zauna da shi kusan shekaru uku babu haihuwa, to abin ka da yanayin sarauta ba ta ɗaukan haka, musamman ma da yake sarautan ta Sokoto ce, Mai martaba ba jimawa ya ƙara aure, ya auro Talatu, kishi halitta ce ta mata, haka Allah ya iyo mu na wata ya fi na wata, duk da acikin kishi duk wan da zai faɗa gaskiya to tabbas akwai son zuciya a ciki, dan haka sosai nake kishi da Talatu, sai dai yanayin gidan sarauta ke hanani nuna komai a fili, har talatu ta shekara biyu ita ma babu haihuwa, dan haka sai na rage kishin nawa, musamman da naji mai martaba zai ƙara aure, haɗe kan mu muka yi da Talatu, ba wajan boka muka je ba illa wajan Malaman zaure masu saɓawa Allah, waɗanda suka san gaskiya kuma suke take ta, masu saka rigan malaman kirki suna hallaka jama’a, su suke taimaka mana wajan faɗawa halaka, abun da muka fara dubawa shi ne rashin haihuwa daga mu ne ba daga Sarki ba, kuma aure zai yi sa, har da wani ma nan gaba kuma za’a samu rabo, dan haka ƙulle-ƙulle muka fara, har aka auro Habiba kuma, tana zuwa ita ma tayi shekara biyar ba haihuwa, nan muka haɗa kai da ita ma, muka labarta mata abin da za mu labarta mata, sai muka ci-gaba da shiri dukkanmu, akan kada Mai martaba ya ƙara aure balle a samun rabon da aka ce za’a samu.

Bayan wani lokaci Malaminmu ya ƙara faɗa mana, muddin muka masta wa lamarin za mu iya rasa rayuwarmu, maganan fasa aure babu dan akwai rabo, sai dai ayi abin da za’a din ga kashe yaran kada su zauna, dan haka muka yarda.

Abu na farko da ya kamata a ce ya nusar da mu ba’a ja da lamarin Ubangiji, amma muka runste ido shi ne, auren Mai martaba da Rahmatullah tun daga fari kasan nufi ne na Allah, domin ba sanarwa ba komai sai ganin Amarya muka yi, an ɗauro aure daga ƙasar Kenya, abin da ya sa ta fara stallake kaidin mu kenan, tun da bamu san da zuwanta ba sai ganinta muka yi, to cikin ikon gagara misila mabuwayi, sai ga Rahmatullah da ciki, wata tara ciff ta haifo yarinyarta mace kyakkyawa, ranan suna ta ci sunanta Ramlatu, farinciki a wajan Mai martaba babu misali, duk da shi ba mutum bane mai nuna soyayya sosai a fili, amma kana ganinsa kasan matuƙar ƙaunar Ramlatu yake yi, mu kuma a ɓangaren mu tun da an ce yaran za su dinga mutuwa, sai bamu damu sosai ba, musamman da muka ga mace ce, ai ba za mu bari ta gaji sarauta ba, za’a yi aiki a kan ta na kisa muka ce a ƙyaleta.

Daga nan kuma duk cikin da Ramlatu zata samu tana haife sa yake mutuwa, kuma duk da saka hannunmu, sai da ta yi yara kusan biyar ko shida ana abu guda, muna ta ƙulle-ƙullenmu ba mu fasa ba, daganan kuma sai ni da Habiba muka ƙara haɗa wani tuggun ba sanin Talatu, domin tamu ta fi zuwa ɗaya sosai da Habiba, dan wani lokacin zuciyan Talatu akwai rahama, wannan karon boka muka samu da maganan ciki, ya faɗa dole ɗa ɗaya za’a samu daga aljanun, dan haka ko ni ko Habiba wani dole ya haƙura, to sai nan ma ni da Habiba rashin fahimta ya shiga tsakaninmu, dan kowa na son kan sa, daman idan aka ce abu ba na na gaskiya ba dole ba kwanciyar hankali.

Sai daga baya bokan ya faɗa mana idan ni ce na riƙe cikin, to ƴar za ta ɓare kuma babu wani cikin, idan Habiba ne tayi za ta iya haife shi har ya girma, daga lokacin kuma duk abin da zai zama mana cikas za’a kawar da shi mu samu sarauta da gado, amma fa akwai hastari domin idan mace ce za’a iya samun matsala da aljanu su janye ta idan ba mu dage ba, idan kuma namiji ne wannan da sauƙi, za’a san yacce za’a yi, mun ce ya za’a yi ya zama namiji abin cikin, sai ya faɗa mana wannan kuma dole mu haƙura da abin da ciki zai haifar, tun da an samu cikin, to sanja abin ciki ko sanin abin ciki babu shi.

To shi ne fa Habiba da Rahmatullah suka fara laulayi tare, har suka zo suka haihu rana guda, Habiba ta haifi mace, Rahmatullah ta haifi maza har biyu, abun ba ƙaramin ciwo ya mana ba, hankalinmu ya tashi, musamman da muka ga yaran suna nan lafiya garau su basu mutu ba, sannan Mai martaba ya ƙara saka wa yarinyar sunan Rahmatullah, sai abu ya ƙara damun mu, nan muka ci-gaba da ƙulle-ƙullenmu, duk da kuwa rashin cikin mu ni da Talatu, amma mun yi farincikin da bai kai zuciya ba, na haihuwan da Habiba tayi.

Tun da Rahmatullah ta tafi ƙasar Kenya da yaranta, ni na koma wajan boka akan batun ƴan biyu su mutu a can yadda ba zargi, amma ya faɗa mini hakan ba zai yuwu ba dole sai sun dawo, sun dawo kuma suka kama ciwo, wannan ma duk cikin aikinmu ne ni da Habiba, saboda addu’oen mahaifiyarsu da magunguna abu ya ƙi ci, dan haka na koma na ce a kawar da Rahmatullah su a ƙyale su tukunna, idan aka gama da mahaifiyar tasu nasu da sauƙi, tun da yanzun addu’arta ke tsare su, sannan aka sa stana da rashin fahimtan juna stakaninta da Sarki, akan maitan ƙasar su ya kama ƴan biyu, amma da yake tana da haƙuri to bata biye wa Mai martaba.

Da ciwon Rahmatullah da mutuwarta duk bai shige wata guda ba, kuma kamun wannan sai da boka ya faɗa mini muddin wani al’amari ya samu tangarɗa a gaba, to zan faɗa komai da kai na kuma zan mutu, amma duk da haka sai da ta mutu hankalinmu ya kwanta, daga nan kuma muka sa aka ƙara shiga stakanin Mai martaba da yaran, duk da daman shi ba irin iyaye masu nuna tsanstar kaunar yaransu a fili ba ne, dan haka yana kula da su komai da komai, amma ba ya jan su a jiki, kuma Ramlatu bata banbance ƴan biyu da Rahmatullah ƙanwarta, Dukansu take jan su a jiki, komai da komai.

Bayan wani lokaci sai muka fahimci Rahmatullah ta fara kula wani saurayi, wajan Malamin zauren muka koma nan kuma, ya mana duba ya sanar mana tabbas akwai rabo stakaninta da wannan mutumin, ko ya za’a yi sai rabon nan ya zo duniya, dan haka kawai mu bari ta aure sa, amma idan ta aure sa to akwai alkairi a abun ba kaɗan ba, dan haka mu kuma ba za mu iya jure ganin alkairi ya sameta ba, muka ce ita ma a kashe ta, ya ce wannan kuma sai mu da shi duka mu mutu, domin duk wan da muka ga ya mutu ta haka, daman su ne silar ajalinsa kwanansa ya ƙare, da yake yana fakewa da malanta to yasan gaskiya taketa kawai yake yi, dan haka ya faɗa mana dole mubar lamarin mutuwarta, muka ce a ɓatar da ita, wannan ma ya ce ba zai yuwu ba dole sai da dalili, muka ce to wani dalili ya kamata, nan kuma ya ce bai sani ba kawai mu haƙura kuma kada mu yarda mu taɓa ƴan biyu, domin abin da ke jikinsu ma kaɗai ba zai ƙyale mu ba, sannan za su iya tona mana asiri gaba, ganin bai mana abin da muke so ba, muka wuce wajan boka.

Boka shi ya bamu maslaha akan sanadin barin Ramlatu gida, domin ya faɗa shi ɗin ma dole sai da dalili za ta bar gidan, dan ita ma kaman mahaifiyarta take tana riƙo da addini, duba mana yayi abin da zai zama dalilin barinta, nan ya ce to a haɗa ta tarayya da wani asirinsu ya tonu a kore ta akan haka, nan ma duk in da aka bi babu, bata yarda da ko wanne namiji, hatta da Ahmad yaron waziri bata sake masa, da wannan abokin Ahmad ɗin kawai take sakewa dan tana son sa, ga shi ya haɗu da soyayyan ƙuruciya dab lokacin bata cika shekaru goma sha biyar ba ma.

Da abun yaƙi sai kawai aka yanke ta aikata alfashan da wannan abokin Ahmad ɗin, idan suka aikata da shi to dole za mu iya samun daman da wani zai yi hakan da ita har a kama su, domin idan aka kama su da abokin Ahmad ɗin ma ba komai zai iya auranta a haka, ko kuwa ya taimake ta, amma idan wani daban ne to komai zai tafi yanda ake so.

Dan haka sai muka shirya komai yan da ya kamata, boka shi ya bamu abin da za mu yi aiki da shi, na gusar da hankalin mutane yacce ba wan da tunaninsa zai kai kan abin da ke faruwa, da kuma abin da zai sa abokin Ahmad ɗin da ita kan ta ba mai taɓa sanin wani abu ya shiga stakaninsa, da ɗan uwansa har abada, idan ba faɗa musu aka yi ba, saboda ko nan gaba tayi wani auren ko wani abun dai kada tayi rayuwa mai daɗi tun da ta rasa budurcinta bata kai wa miji ba.

Allah mai bawa bawansa sa’a muddin ya roƙa, ko da kuwa ba’a kan dai-dai yake ba, to muma Allah ya bamu sa’a, domin zuwan abokin Ahmad na ƙarshe nan muka aiwatar da komai, kuma komai ya tafi dai-dai, abokin Ahmad ya kusanci Ramlatu, saboda basa hayyacinsu basu san komai game da abin da ya faru ba, har suka kammala ya koma duk baya hayyacinsa, Ramlatu ma ni da kaina na ɗauko ta na gasa ta, sosai sai da ta yi kwana ukku ta dawo hayyacinta, daga nan muka din ga farinciki komai dai-dai, sai kuma kwastam bayan wani lokaci ta fara ciwo, duk mamakin ciwonta muke yi, sai muka bari akan ko dan rashin sabo da sanin namiji ne shiyasa haka, har dai Allah yayi ƙannenta ƴan biyu suka rasu, aikin da muka yi da jimawa akan mutuwar su sai lokacin ya yiwu, nan farinciki ya kuma kama mu, sai dai kuma in da gizo ke saƙar shi ne cikin da ya bayyana a jikin Ramlatu, ga samu ga rashi a wajan mu, ita kuwa mafarin ƙaddaran rayuwanta kenan.

Ganin ciki ya bayyana jikin Ramlatu sai muka tattara muka tafi wajan boka, ya faɗa mana mun riga da mun yi kuskuren da yake gudun mana aikata sa, domin yayin saduwa da Ramlatu abokin Ahmad yayi bismillah, kuma cikin ikon Allah an samu wannan cikin, an samu rabon da yake stakaninsu, sannan da ya koma gida ya koma hayyacinsa ya starkake jikinsa(wankan starki), sannan Ramlatu ma, mu da kan mu nice ma na mata wankan starkin, tun da ya mance bai faɗa mana rashin wankan ba a sharaɗinsa, dan haka Allah ya ƙaddara an samu ƙaruwa, kuma wannan cikin ko duniya za su taru a kan sa ba zai fice ba, amma bai hana mu ba muyi iya yin mu, shi dai ba abin da zai iya yi, sai dai kada mu manta da batun za mu faɗa da bakin mu, kuma zan mutu sannan ƴar Habiba komai na iya faruwa da ita, a ko wanne lokaci.

Cikin tashin hankali muka baro boka, muka wuce wajan Malam na zaure, abin da boka ya faɗa mana haka Malam na zaure ya maimaita mana, tashin hankalin da ba’a saka masa rana, domin labarin Malam na zaure ya wuce na boka tashin hankali, Malam ya ƙara da faɗa mana na sani tun farko ya hane mu da mastawa lamarin Ramlatu, amma tun da mun dage to mu sani wannan cikin sai an haife sa ko za mu yi yaya, sannan dole yan da nayi niya tun farko sai na ƙarisa, tun da na yi sanadin wannan rabon ya samu ba ta hanyar aure ba, to komai ya bar kan saiti kuma sai abin da nake gudu ya faru, dole Ramlatu za ta bar gidan sarautan, kuma tana ficewa kwanciyan hankali ya fice daga jikinmu, daga ranar da ta haihu kuma babu ni babu lafiya, sai ranar da ta sako ƙafanta ta dawo zan ji sauƙin jikina, kuma a ranar zan rasa rai na, kuma mutuwan ƴan biyu babban masifa ce gare mu duka, hatta Mai martaba sai ya taɓa kasonsa na daga abin da muka shuka, sai dai zai mana taimako ɗaya shi ne sai abin da muka yanke Mai martaba zai yi, a iya yanzu kawai, haka muka baro wajansa ba labari mai daɗi, muka dawo gida.

Rana zafi inuwa ƙuna, duniya ta fara juya mana baya tun ba’a je ko ina ba, tun bamu fara ba har tana neman ida mana, tun bamu ji daɗin ta ba tana son ƙulle mana, shiyasa ake cewa ramin ƙarya ƙurarre ne, domin namu ta jima da ƙurewa, to dai sai kuma muka rungumi asibiti, domin mun dage cikin nan ba za ta haifeshi ba balle ya zamo mana masifa, nice na bata maganin ɓarar da ciki na fiye da misali ma, wan da na tabbata ya fi ƙarfinta, za ta iya mutuwa ta haka ma, amma ba tausayi ba komai nayi hakan, ta zo jini ya ɓalle mata, a taƙaice dai tayi jinya sosai har da wankin ciki an mata duk azabar sa, bayan wata da jinyanta muka dawo gida, yanzu kuma bama batun ta sadu da wani namijin, dole barin gidan za ta yi ko ta yaya.

Muna staka da haka kuma sai ga ciki Masha Allah ya ƙara bayyana, ashe ba in da ma ya je domin ko ɓatan lissafi babu a cikinta, wannan shi ake ƙira da zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana haa maza haa mata sai yayi, ƙadangaren bakin tulu baƙin cikin mai gona, ciki ya dawo yan da yake duk da abin da aka mata a asibiti, dan haka hankalinmu ya fi tashuwa tashi, nan muka kai ta da niyan a sa mata ruwan naƙuda ta haifeshi haka ba rai, ko ana haifeshi mu kashe shi, ko kuwa su mutu ita da abin cikin nata, amma likitoci suka ƙi, ni ce na koma ga mai martaba na faɗa masa ita ta ƙi, dan haka ya sa ta zaɓa ko cikin ko mu, da yake yana kan ƙullinmu shi ma kan taimakon da Malam ya mana, sai kuwa ya yi abin da na faɗa ba daɗi ba ƙari, a ranar ya sallameta ya koreta, to tun da ta tafi kuwa nistuwarmu da kwanciyar hankalinmu ya bar jikinmu, Mai martaba shi ya fara ciwo, ba jimawa nima na kwanta, wan da muke da tabbaci duka, na hakan na nufin Ramlatu ta haifi abin da ke cikinta, cuta na yi sa har yau ina fama da shi, kuma nasan mutuwa zan yi, mai martaba kuwa ya ji sauƙi kaman yacce ya ke ga shi a zaune, sannan al’amarin Rahmatullah ma sam-sam babu daɗin ji kaman yan da kuka ji labarin rasuwarta yanzu, babu wani abin da bai faru ba, duk wani abu da muka ƙulla ya dawo kan mu, abin da muka shuka mun girbe, abu guda dai da nasan babu hannunmu a ciki, shi ne rayuwan da za ta yi idan ta bar gida, ɓacewanta da karuwancin da komai babu hannun mu, domin bamu hango wannan ba, lokacin bama wannan lissafin ma kwata-kwata, mun yi dan abin duniya da mulki ƙarshe ga yan da muka ƙare, ina wannan magana ne saboda mutanen baya su hankalta kuma kowa ya sani, gobe na da saurin zuwa, mu daina abu muna tuna iya yau ɗin kawai.

CI-GABAN LABARI.

Gaba ɗaya jama’an palourn idanuwansu na kan Mama Suwaiba, kowa da abin da yake tuna wa a ran sa, kuma kowa da abin da yake saƙa wa, sannan idan ka kalli fuskokinsu to da yawa kasan suna cikin al’ajabi da mamaki(shock).

Kamun kowa yayi magana, General Sufyan shi ne ya fara haɗo kalmomin da suka rage a kwanyansa, ba su fece ba ya ce, “Kuna nufin FAƊIMA ƳA TA Ce?

*****

<< Yar Karuwa 25Yar Karuwa 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×