Prologue (Thriller)
Rungumeta yayi ta baya yana mai lumshe idanu, k'amshinta yake shak'a cikeda so. Murmushi ta yi cikin shagwab'a da soyayya tace " good morning Noorie" Morning ya amsa yana juyo da ita ga fuskantar shi, a mugun tsorace ya saketa ya na mai cewa "who are you?"
Da mamakance ta kalleshi tace " Noorie!!", katseta yayi da cewa " don't call me that!, where's my wife?". Sai kuma ya juya da mugun gudu yana k'wala kiran " Hayatii!", da sauri ta biyo shi a baya tana mamakin abunda ya faru. . .