Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Ya'yanmu by Kabiru Yusuf Fagge

Marayu Ma ‘Ya’ya Ne

Labarin Ihsan

“Abba ka ce watarana Momina za ta dawo ko?” Ihsan ta bukata cikin muryar tausayi da yarinta. Shekarunta biyar a raye.

Cikin hanzari Haris ya kalle ta, duk lokacin da ta yi masa irin wannan tambayar abin da ke faruwa kenan, ya yi saurin kallon ta sannan ya ba ta amsa da saurin sai kuma ya bar gurin.

Wannan karon kafin ya ba ta amsar ta kuma jefa masa wata tambayar.

“Abba wai Momina ta mutu, ba za ta dawo ba?”

Da sauri Haris ya bar dakin, ya shige bandaki, ya fashe da kuka. Kullum aikin kenan, Ihsan ta yi masa tambaya, ya amsa mata, ya bar inda take, ya je, ya yi ta kuka.

Bai taba samun kansa a karayar zuciya ba sai da Ihsan ta yi tsalle, ta fado cikin rayuwarsa. Tabbas sun zalunci rayuwar yarinyar, yarinya mai kyakkyawan hali da hankali da fasaha, a banza a wofi sun raba ta da iyayenta.

Daya daga cikin abin da ya sa Ihsan ta shiga zuciyar Haris shi ne yadda ta dauke shi a matsayin mahaifi, kuma wanda ta fi kauna a rayuwarta, yadda ta shaku da shi take kaunar sa, take nanukar sa ya sa, yake jinta kamar jininsa.

Sai dai kash! Da shi aka hadu aka gutsire mata kyakkyawar rayuwar da ta faro.

Ya kuma fashewa da kuka, bai ankara ba sai ji ya yi ta rungumo shi ta baya tana fadin.

“Ka yi hakuri Abbana, a makaranta ne Mardiyya ta ce min wai duk wadda Mominta ba ta gidansu to ta mutu ko kuma Abbanta ya kore ta ba za ta dawo ba. Ni kuma na san ba za ka kori Momina, ka yi hakuri Abbana idan na bata maka rai, na daina fada.” Ta fara share masa hawaye, ita ma ta fara kukan.

Haris bai san lokacin da ya rungumo ta ba, yana share mata hawaye yana cewa.

“‘Yata kar ki yi kuka, ni na ce miki Momin ki za ta dawo, kuma za ki zauna tare da ita ki yi farin ciki, ko ba ki yarda da Abbanki ba?”

Ihsan ta gyada kai, “Na yarda da Abbana, kuma na daina yarda da maganar su Mardiya.”

Ya kara rungume ta, ya ce “Yauwa diyata, ba na son ki rinka yin kuka.”

“Ni ma bana son Abbana yana kuka.” Ihsan ta fada.

Suka yi shiru, suna mayar da numfashi, “Zo mu je in wanke miki fuska, mu je shoprite.” Haris ya ce da ita.

Ihsan ta tashi tana murna, tana tsalle, “Abbana na gode.”

Duk lokacin da ya yi mata abu kamar ya wanke mata kaya sai ta yi masa godiya, ko kuma ya saya mata wani abu ko na ficika ne sai ta gode masa. Ihsan ta bude kirjin Haris wanda ta yi zaton shi ne ubanta ta dasa masa tausayi da soyayya.

Tausayi da soyayya su ne abubuwa guda biyu da a baya Haris bai san su ba, sai bayan da ya hadu da ‘yar jaririyar yarinya; Ihsan.

Wannan halin ne na tausayi da soyayya irin ta da da mahaifi ya sa Haris ya ji lallai sai ya nisanci Ihsan a lokacin da ita kuma take kara kusantar sa, a tsammanin ta shi ne silar zuwan ta duniya.

*****

Tafe suke a kan keke, Haris ne yake tuka keken yana tunanin yayin da Ihsan ke zaune a kariya tana sauraron shi.

A sanin ta kullum idan zai kai ta makaranta, to suna tafe yana rera waka ita kuma tana yi masa amshi, ko kuma ya rinka biya mata karatu tana amsawa.

Da dai Ihsan ta ji shirun ya yi yawa, kai hatta ma yanayin tukin, ta fahimci ba kamar kullum ba, don haka ta yi masa magana.

“Abbana yau ba ka da lafiya ne?”

Haris ya ji jikinsa ya dauki bari, don kuwa kalaman Ihsan na tasiri a ransa. Bai juyo ba ya ce “Me kika gani ‘yata?”

“Na ga yau babu waka, babu karatu.” Ta fada.

Ya yi sauri, ya ce “Af, mantawa na yi, sorry my daughter.”

“No problem my Dad. Ina jira.” Tana dariya.

Haris ya bude baki don fara wakar sai ya ji ya kasa, harshensa ya gaza furta komai.

Jin shirun ya sa Ihsan ta bude baki, ta fara rera waka, tana cewa:

“Abbana ina sonka,

Burina biyayyarka,

Har raina da kaunarka,

Ba na son hawayenka.

Ba shiri cikin murya mai rauni Haris ya amsa mata, kamar dai yadda suka saba.

“Ya ‘yata rabin raina,

Alkairi a ruhina,

Kin zamto cikin kaina,

Abar kauna abar bi na.

Haka suka ci gaba da tafiya, Ihsan na rerawa Haris na amsawa, abin gwanin sha’awa, gwanin tausayi.

Sun isa makarantar Kano Capital, akwai tarin motocin da aka kawo yara ‘ya’yan masu hannu da shuni da masu rufin asiri, saboda cunkuson, a haka Haris ya kutsa har zuwa bakin kofar makarantar, ya tsaya, suka sauka a tare, ya daukar mata kwandon abincinta, sannan ya rike hannunta, suka shiga ciki.

Bai rabu da ita ba kamar yadda ya saba a kullum, sai da ya kai ta kofar ajin su, sannan suka rabu, suna daga wa juna hannu, suna adabo, suna murmushi.

Ihsan ta shiga aji, tana jin matukar kwarin jiki saboda jin dadin irin yadda Abbanta ke ji da ita, sai washe baki take cikin murna, gani take ta fi kowacce ‘ya da da dace da mahaifi a cikin ajin. Ba ruwan Ihsan da irin manyan motocin da ake kawo wasu ‘yan ajinsu, ba ruwanta da abin wani ko wata ‘yar ajinsu, don ita kam Abbanta Haris yana wadata da duk abin da take bukata.

A yayin da Ihsan ta shiga aji cikin halin murna, saboda samun uba nagari, shi kuwa Haris din juyawa ya yi yana hawaye saboda tsananin damuwa. Ya san dole ko ya ki ko ya so, yau ko gobe zai rabu da Ihsan.

Daga makarantar su Ihsan, ya yanke shawarar wucewa ofishin ‘yansanda, inda zai ba da Ihsan din a matsayin wadda ya tsinta.

Ya saba duk lokacin da ya kai Ihsan makaranta, ya fito su dan yi hira da maigadin makarantar amma a wannan karon ko kallon inda yake bai yi ba, don idonsa cike yake da hawaye. Shi kansa maigadin ya yi mamaki, amma lura da halin da yake ciki ya sa, ya kyale shi, ya bi shi da kallo.

Zuciyar Haris na ingiza shi, kafafunsa na ta tukin keken, bai zame ko’ina ba sai ofishin ‘yansanda.

Haris ya zabi zuwa ofishin ‘yansanda da yake da nisa da unguwar da yake. Akwai tazarar kilimota bakwai a tsakani, ya isa City Dibision, bayan ya shiga ciki, ya nemi wuri a jikin katangar ofishin ya ajiye kekensa, sannan ya zaro mukulli ya kulle.

Duk abin da yake yi Kofur Abashe yana tsaye, yana kallon shi, sai da ya gama kullewar ya juya zai shiga cikin ofis din sannan ya yi masa magana.

“Malam a cikin folis siteshin din ma sai ka kulle keke?”

Haris ya yi murmushi “Kwarai kuwa, ai a nan ya kamata na yi hakan.”

Mamaki ya kama kofur Abashe ya ce “Me ya sa ka ce haka?”

“Saboda duk wani mutum zai yi tunanin nan ne kawai wajen da barawo bai isa ya shigo ya yi sata ba, to shi kuma barawon da yake tunaninsa ya bambanta da na masu kaya sai ya shigo, ya yi satar hankali kwance.”

Kofur Abashe ya bi shi da kallo, “Amma kai barawo ne?”

Ras! Gaban Haris ya fadi, a ransa yana tunanin ko ya san shi, amma a zahiri, ya cije ya ce “Me ka gani?”

“Gani na yi ka san falsafar barayi.” Cewar Abashe.

Haris ya yi dariya, “Ai wannan dan kadan ne daga cikin falsafofin su, ban san komai ba.”

Abashe ya ce “To albishirinka.”

Haris bai ce komai ba, kawai ya tsaya yana kallon sa.

Abashe ya dora da cewa, “Ba a fi sati daya ba wani mutum ya kawo kara aka sace masa babur. Kai me ka zo yi?”

“Na  kawo rahoton tsintar wata yarinya ne.” Haris ya amsa masa.

Abashe ya dubi gefen sa, “Ina yarinyar?”

Haris ya ce “Ban taho da ita ba.”

Abashe ya ce “Bangarenmu ne, zo mu je.” Ya wuce gaba, Haris ya bi bayan shi. Da suka shiga ofis din, Abashe ya nuna Haris ya ce “Muna tare da shi ya zo wani report ne.”

Suka wuce. A ofis din da suka shiga ba kowa, sai benci da tebur, Abashe ya ba Haris wuri ya zauna, shi ma ya zauna, ya jawo wani daddaudan fayel gabansa ya bude, ya dauko farar takarda mai layi-layi ya dora a kan fayel din, sannan ya dauki wani biro mara murfi dake gefe, kana ya dubi Haris.

“Kai nake saurare? Ka fara da gaya min sunanka.”

Haris ya kalli takardar da ke gaban Abashe, sannan ya ce “Sunan Harisu, wata yarinya na tsinta ‘yar akalla shekaru biyar zuwa shida da haihuwa, shi ne nake son na kawo ta a yi cigiya idan ba a samu iyayenta ba sai a kai ta gidan marayu.”

Abashe yana ta bin bakinsa da kallo, da ya ji ya yi shiru, sai ya ce.

“Ka yi saurin yanke hukuncin cewa idan ba a sami iyayenta ba sai a kai ta gidan marayu, me ya sa ka ce haka?”

“Saboda na yi cigiya duk inda ya kamata ba a samu inda iyayenta suke ba, kuma yarinyar da bakinta da wayonta amma ba ta iya cewa ga inda take, ba ta iya cewa ga iyayenta, sai ma cewa take yi wai ni ne babanta.”

Abashe ya yi jim yana nazarin sa, sannan ya nisa, yana kada biro, ya kasa rubuta komai yana nazartar Haris da kalamansa.

A nasa bangaren shi ma Haris din nazarin Abashen yake yi, kuma da alama ya gano abin da yake son ganowa.

Abashe ya nisa, “A ina ka tsinci yarinyar, kuma wace rana ka tsince ta? Kai kuma a ina kake da zama, mene ne sana’arka? A ina ka bar yarinyar a yanzu, me ya sa ba ka kai ta wajen mai unguwar ku ba, me…”

Haris ya dakatar da shi, “Ba zan iya amsa wadannan tarin tambayoyin naka ba.” Ya sa hannu a aljihu ya fito da damin kudi; ‘yan dari biyar-biyar, ya ajiye a gaban Abashe.

Kofur Abashe ya yi sauri ya dauki kudin yana dube-dube, kamar yana zargin wani na labe yana kallon su, kana ya kalli Haris.

“Yanzu me kake so a yi?”

Haris ya yi murmushi, “Ka fiye tambaya.”

Abashe ya yi dariya, “An sha gaya min haka, amma ni ba na damuwa saboda yanayin aikinmu ne sai da tambaya, kuma na san wannan tambayar ko ban yi ta ba, dole ka amsa min.”

“Haka ne.” Cewar Haris, ya ci gaba da fadin “So nake in kawo maka yarinyar, kai kuma ka san yadda za ka yi a kai ta gidan marayu.” Ya dan yi shiru cikin damuwa, sannan ya dora, “Ba na son ta shiga damuwa.”

“Dole kuwa za ta shiga damuwa. Amma me ya sa ba ka so?” Abashe ya bukata.

Haris bai ba shi amsa ba, ya ce “Na ji, amma kar ta wulakanta.”

“Ba za ta wulakanta ba, don su ma sauran yaran da suke gidan ba wulakanta suke ba. To yanzu, a ina zan karbe ta, nan za ka kawo ta ko kuwa?”

Haris ya gyada kai, “Na yi niyyar kawo ta nan, sai na fasa.” Ya mike tsaye, “Amma zo mu je in gaya maka yadda za a yi.”

Zumbur Abashe ya mike yana gyara aljihun da ya zuba kudi. In dai za ka ba Kofur Abashe kudi, to komai kankantarka zai mika maka rayuwarsa ka juya shi yadda kake so.

Akwai lokacin da matarsa ta ce “Abashe da wuya idan ba kudi ne ajalinka ba.”

A lokacin murmushin jin dadi Abashe ya yi ya ce “Alhamdulillahi, don kuwa idan kudi ya yi ajalina to na mutu jarumi.”

Abashe da Haris suka fito, har zuwa inda Haris ya ajiye kekensa ba tare da daya daga cikinsu ya ce uffan ba. Sai da Haris ya sunkuya zai bude mukullin keken sannan ya ce.

“Yau da misalin karfe biyar da minti ashirin zan kai ma ita Gidan Zu, bangaren wajen wasan yara.”

Abashe yana kallon Haris, yana satar kallon wasu ‘yansanda da ke bakin kofa, ya dan sunkuya.

“Me ya sa tun a ciki ba ka gaya min haka ba?”

Haris ya yi murmushi, “Saboda ka rako ni waje, idan abokan aikin ka suka ga na fito ni kadai za su tsammaci ka gaya musu abin da ya kawo ni, sai su nemi yi wa kudin da na ba ka gibi, amma yanzu idan ka koma suka tambaye ka, ka iya cewa da su ni kanin Kawunka ne na kauye.”

Abashe ya tuntsure da dariya ya doki bayansa, “Shegen bisa akwai ka da hikima. Kar ka damu da dukan, don hakan zai nuna musu kai din kamar dan’uwana ne.”

Haris ya ce “Haka ne.”

“To amma me ya sa ka zabi wannan lokaci, karfe biyar da minti ashirin, kuma ka zabi gidan Zu?” Abashe ya tambaya.

Haris ya dan hau kan kekensa, kafarsa a kasa, sannan ya ce “Mun yi da yarinyar zan kai ta gidan Zu yau, kuma na kiyasta za mu gama komai zuwa biyar mu dau hanya, mintuna sha biyar zuwa ashirin mu isa. Don haka sai mun hadu, kar ka manta akwai ninkin kudin da na ba ka.” Ya taka feda zai tafi, Abashe ya tsayar da shi.

“Akwai tambaya guda daya kafin ka tafi.”

Haris ya ce “Dole in saurare ka tun da tambaya ta zame maka cuta.”

“E wallahi.” Abashe ya amsa, sannan ya yi tambayar, “Da alama kana da kudi, kuma kai wani ne, to amma ya na gan ka a kan keke?”

Haris ya kuma yin murmushi ya ce, “Saboda basaja.”

Abashe ya kyalkyale da dariya ya ba Haris hannu suka tafa, ya ce “Shegen sama, na yarda akwai ka.”

Haris ya dan bata rai saboda yadda Abashe ya maka masa hannun da ya saba rike kulki a matsayin gaisawa, kadan ya rage, ya yi masa targade.

Abashe ya yi sauri ya dan bata fuska ya ce, “Kar fa ka damu ni ma ina yin basaja ne.”

Haris ya tuka kekensa ya fita daga ofishin ‘yansandan. Yayin da ya bar Abashe tsaye yana kallon sa, cike da murna da mamaki.

Haris na fita ya yi ajiyar zuciya don duk hankalinsa a tashe yake kar ya hadu da wani jami’in tsaron da ya san fuskarsa, asirinsa ya tonu.

*****

Tuka keken yake yi tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki. Ita kanta Ihsan da take bayan keken ba ta jin dadin tafiyar, don haka ta ce.

“Abbana me yake faruwa ne?”

Ya yi karfin hali ya ce, “Me kika gani ‘yata?”

Kafin ta ba shi amsa sun iso kofar shiga gidan Zu din, don haka ya tsaya, suka sauka a tare. Ihsan tana ta kokarin kallon fuskarsa shi kuma yana ta basarwa, don ba ya son hada ido da ita.

“Abbana na ga ba ka yin dariya, shi ya sa na nake tambayar ka, ko ba ka da lafiya ne?” Cewar Ihsan.

Haris ya kago murmushi, ba ya son ta ci gaba da yi masa irin wadannan maganganu don suna karya masa zuciya, don haka ya yi saurin ce mata.

“Mu je zan gaya miki abin da ke damuna. Zan gaya miki wata magana ‘yata.”

Ta yi murmushi, “To Abbana.”

Suka je wajen biyan kudi, ya biya, aka ba shi tikiti, suka shiga. Daga farko-farkon shiga, ya sami wurin da ake ajiye ababen hawa, ya ajiye kekensa ya kulle shi.

Ihsan tana kallon sa ta ce, “Abbana wani ba zai dauke mana kekenmu ba?” A shagwabe take maganar.

Haris ya shafa kanta, sannan ya riko hannunta, ya ce “‘Yata kenan, ai na kulle keken babu wanda zai daukar mana.”

Ya ja ta, suka fara tafiya. Wurin da suka yi alkawarin za su hadu da Abashe ya nufa. Yana wuce wata bishiyar maina kusa da kejin birrai ya hango Abashe a tsaye yana kallon wasu birrai guda uku da suke wasanni. Gaban Haris ya fadi, a take da ya tuno wannan ita ce ranar da za su rabu da Ihsan, yarinyar da ta zame masa bangare na rayuwa.

Yanayin tafiyar da yake yi, ya sauya, a yayin da kai tsaye suke durfafar inda Abashen ke tsaye. A yanzu yana sanye da shudayen riga da wando na yadi dan Kwatano, ya dankwara wata hula wadda da gani ka san bai saba sawa ba, sam shigar ba ta yi masa kyau ba, kamar wani Ladon Kauye.

“Abbana yau kuma biri za mu fara kallo?” Ihsan ta bukata.

Ya yi ajiyar zuciya a boye, sannan ya dan durkusa a gabanta, ya nuna mata Abashe ya ce “Kin ga wancan, abokina ne, za mu je wajensa ki gaishe shi, sai mun ci abinci za mu zagaya, mu yi kallo tare.”

Ihsan ta yi dariya, “Abbana ashe kana da aboki, ni ma ina da aboki a makarantamu mai suna Ahmad Abdullahi. Yaya sunan abokin naka?”

Ya yi kokarin yin dariya ya ce, “Ina da shi, ga shi ma, sunan shi Abashe.”

“Ai ban taba ganin shi ba, mu je in gaishe shi.” Ta ja hannunsa suka nufi wajen Abashe.

Haris da Ihsan suka yi masa sallama, ya amsa. Haris ya ba shi hannu suka gaisa, Ihsan ta gaishe da shi.

Haris ya ce, “Me kake kallo?”

Suka kalli birran a tare. Abashe ya ce, “Ina kallon wadannan halittun ne tare da mamakin yadda mutane ke cewa biri ya yi kama da mutum.”

Haris ya dan yi dariya, “Ta wata fuskar suke nufi. Mu je, mu zauna mana.” Ya nuna wasu kujeru.

Kai tsaye suka nufi wajen kujerun suka zazzauna, Ihsan a tsakiya. Jim, suka yi shiru irin na marasa gaskiya, ita kuma Ihsan na girmamawa.

“Mu dan yi magana mana.” Cewar Haris.

Abashe bai ce uffan ba face satar kallon Ihsan da yake yi, ya mike suka dan bar gurin.

Haris ya ce, “Ga ta nan, sai a kiyaye, ba na son in bata lokaci a nan.”

Abashe ya amsa, “Ba ka da matsala. Amma fa na lura yarinya ce tagari. Ka rike ta a wurinka mana, ka ga ko ba a ga iyayenta ba, sai ka taimaka mata.”

Haris ya bata rai, ya ce “Ba zuwa na yi ka gaya min haka ba…”

Abashe ya katse shi, “O! To kar ka damu.”

Suka koma inda Ihsan take, Haris ya ce da ita, “‘Yata bari in siyo mana cincin da lemo da ice-cream mu sha sai mu tafi kallo ko.”

Ihsan ta sauya fuska, “Abbana mu je tare.”

Haris ya yi sauri, ya ce, “A’a, ki zauna wajen abokina in dawo, ko tsoronsa kike ji?”

Ta yi sauri ta ce “A’a, ba tsoron sa nake ba.” Ta kalli Abashe tana murmushin yake. Abashe ma ya kakaro murmushi kan fuskarsa.

Haris ya juya, a zuciyarsa yana yi mata bankwana. Yana tafiya gabansa yana faduwa, gani yake wani abu zai sami Ihsan. A ransa ya ce “rabuwar dole.”  Kwalla ta biyo idanunsa, bai ankara ba sai ji ya yi Ihsan na kwalla masa kira.

“Abbana, Abbana.”

Ya kasa juyowa, don ba ya so ta ga yanayin fuskarsa. Yana tunanin abin yi, sai ya ji tana cewa.

“Ka yi sauri Abbana.”

Ya yi ajiyar zuciya, ya kara sauri. Shi kuwa Abashe baki ya saki yana kallon su, yana ta kokarin fahimtar abin da ke tsakanin Ihsan da Haris amma kudin da aka ba shi ya hana.

Haris ya isa wajen kekensa cike da tunanin ko ya koma ya dauki Ihsan ya fasa rabuwa da ita? Ya bude keken, ya hau, ya tafi. Daya daga cikin masu gadin gidan zun sai kallon sa yake yana tunanin kamar mutumin nan ba shi kadai ya shigo gidan ba.

*****

Da sauri Haris ya isa gida, gabadaya babu abin da yake bukata face ya yi sauri ya bar garin nan. Kai tsaye da ya shiga cikin gidan wata jakar goyo ya dauko, ya ajiye a gefen katifar barcinsa, sannan ya koma wajen wata dirowa ta ajiya ya bude ta, ya dauko wata karamar akwati ta karfe, akwai mukulli a jikinta, ya sa hannu ya murza mukullin ya bude, ya kalli cikinta.

Akwai kudi a ciki, sai kuma dan littafin rubutu (jotter) da wasu takardu da wata sarkar zare mai azurfa a kusa da jotar, ya yi sauri ya dauko jotar, ya dauki biro, ya yi rubutu a ciki. Rubutun da yake tunanin shi ne na karshe a ciki, domin duk tarihin samuwar Ihsan ne zuwa yau da yake ganin za su rabu a ciki.

Yana shirin mikewa ya ji gabansa ya fadi, da ya nutsu sosai sai ya ji ko kadan ba ya son rabuwa da Ihsan, take ya sake shawara, ya yi sauri ya rufe akwatin, ya kintsa kayan sannan ya dauki akwatin ya mayar da ita cikin dirowa, a lokacin ya ga wata tsohuwar wayarsa da ya ajiye, sama da shekaru biyar da kashe wayar da ajiye ta, bai taba jin ya kamata ya kunna ta ba sai yau.

Ya dauko ta yana tunani, kai tsaye ya kunna, ta kunnu, -sakonni suka rinka shigowa, ya fara dubawa. Ya san abin da zai gani a rubuce ba zai wuce na abokan aikinsa, su Tajo da Oshere da Madu ba. To amma ya yi tsammanin ganin sakon Sumayya, yarinyar da ya cukwikwiye lamuranta gabadaya ya jefa a kwandon shara, ya je, ya zubar a juji.

Yana ta murza wayar don isa ga sakon da yake son gani, ya ji wayar ta yi kara, gabansa ya fadi tare da duba lambar da kiran ya shigo. Rabon da wayar ta yi tsiwa shekaru biyar kenan.

Sunan Madu ne ya bayyana. Ya yi sauri don ya kashe wayar, sai wata zuciyar ta hane shi, ya bi fuskar wayar da kallo har ta gama burari ta katse, kafin ya gama yin ajiyar zuciya, wani kiran ya kara shigowa da lambar. A saninsa dama mutane hudu ne kawai suka san lambar. Don haka bai yi tsammanin shigowar wata bakuwar lamba ba.

Ya dauki kiran a tsorace don ya tabbatar babu alheri a ciki. Kunnensa ne ya jiyo Madu na cewa, “Harisu kana ji na.”

“E ina jin ka Mad.”

Madu ya yi ajiyar zuciya, “Na yi tsammanin ka rabu da layin. Ka yi sauri, ka bar Kano don Oga ya sa an yi masa bincike an gano inda kake, kuma ya san kai da yarinyar nan kuna raye zai zo da kansa ya nemo ka….ka san sauran.”

Haris ya yi tsaki ya ce “Madu ashe har yanzu ba ka bar fashi da satar mutane ba, kai da ka ce ba za ka dade a cikin harkar ba?”

“Harisu, abubuwa da yawa sun faru bayan rabuwar mu, abin da nake so da kai kawai ka yi abin da na ce ma, idan ya so ma yi maganar daga baya.” Kawai ya kashe wayar.

Haris ya bi wayar da kallo, sannan ya girgiza kai a ransa ya ce, “Dole in bar Ihsan.”

Ya kashe wayar, ya sa a aljihu, sannan ya mayar da akwatin cikin dirowar, ya rufe, ya zo kan jakar nan, ya dauka, ya rataya, ya fice daga gidan, ya rufe, sannan ya je can karshen katangar gidan daga kusurwa, ya haka rami, ya binne mukullin gidan, kana ya tafi.

Gidan Marayu

Abashe ya karaso daf da ofis din sakataren gidan yana rike da Ihsan wadda tun da suka baro gidan zu take yi masa tambayar ina babanta, tun yana ba ta amsar wurinsa za su je har ya yi shiru a ransa yana cewa “Lallai na hadu da yarinya mai aljanun tambayoyi, wadda ta fi ni jarabar tambaya.”

A kofar ofis din ya zaunar da ita ya ce “Bari in kirawo shi, an ce yana nan, yana aiki.”

“Wanne aiki Abbana yake yi a nan?” Ihsan ta tambaye shi.

Abashe ya kalle ta cikin damuwa a ransa ya ce “Na ci kudi da wuya.” A fili kuma ya ce “Idan ya fito zai gaya miki da kansa.” Ya shige, ya bar ta a nan tana kallon yara marayu da ke can gefe wasu suna wasa, wasu suna zazzaune kurum.

Tsawon mintuna talatin Abashe bai fito ba, har Ihsan ta fara kosawa, hawaye sun fara cika mata idanu, damuwarta ta dadu. Sai ga shi ya fito tare da Biliya; daya daga cikin ma’aikatan gidan, su biyun sai murmushi suke yi.

Abashe ya kalli Ihsan, yana fadin, “‘Yar Abba ga wannan mutumin zai kai ki wajen Abbanki, ai kuka ya kare ko?”

Ihsan ta sassauta yanayin damuwarta, ta ce “To.” Sai dai kallon da take yi wa Abashe da Biliyan akwai shakku a tattare da shi, amma ba yadda ta iya. Biliya ya kama hannunta yana fadin.

“Zo mu je ‘yar Abba. Ya sunanki?”

“Sunana Ihsan.” Ta amsa.

Sum-sum Abashe ya kama hanyar waje, yayin da Biliya ya nufi wajen wani gini rike da hannun Ihsan, wadda ita kuma take bin Abashe da kallo.

“Allah sarki, yarinya kin zo a zamanin shugabancin matsiyata, sabon shugaba Namure.” Biliya ne ke fadin haka a hankali.

“Me kake cewa?” Ya ji Ihsan na tambayar sa.

Da sauri ya dube ta, “Me kika ji ina cewa?”

“Ban ji sosai ba.” Ta ce.

Ya ce “To ba da ke nake ba, ina wata magana ne a raina.”

Ihsan ta ce, “To Malam aka ce Abbana a can yake?” Ta nuna ofis din da suka baro.

“E, shi ne ya ce a kawo ki nan din idan ya gama aikin da yake zai zo ya same ki.” Biliya ya yi mata karya don ya kwantar mata da hankali.

“Aikin me Abbana yake yi a gidan nan?” Ihsan ta bukata.

“Bai gaya miki ba?” Biliya ya tambaye ta.

Ta ce “Bai gaya min ba.”

“To za ki sani, ba dai kin shigo gidan Namure ba.” Cewar Biliya.

Ihsan ta ce, “Wane ne Namure?”

Namure Gambo shi ne sabon shugaban gidan marayu da gwamnatin jiha ta kawo – Saboda tarin almundahanar da aka sha kama shi a Hukumar Tattara Haraji, Namure ya sami sauyin wajen aiki zuwa Gidan Marayu.

Tsabar daurin gindi da yake da shi a wajen ‘yan siyasa shi ya sa ba a kori Namure daga aiki ba.

Namure kwararre ne wajen abubuwa guda biyar; gulma, bambadanci, gwara-kai, kawalci da uwa uba karya, wadanda wadannan abubuwa su ne silar kutsawarsa cikin manya da kananan ‘yan siyasa, kuma su suka zamo masa satifiket din zama darakta a Hukumar Tattara Haraji ta jiha tun a baya.

Tun da ya karbi wannan matsayi ba a taba samun kaso talatin cikin dari na abin da ake samu daga harajin ba. Akwai watannin da ta dalilin irin almundahanar sa da takurawar sa ga al’umma, har sai da jihar Kanon ta shiga wani mummunan hali na rashin kudi. Karara an sha kama shi da samun laifin ruf-da-ciki amma a karshe saboda daurin gindi sai ya haye.

Wannan karon tura ce ta kai bango aka cire shi daga hukumar zuwa shugabancin gidan marayu.

Ko sati bai yi da zuwa gidan ba ya nazarci hanyoyin da za su kawo masa kudi don ba zai iya zama ba tare da shigowar kudi ba, don haka a sati na biyu munanan ayyuka suka fara wanzuwa a gidan marayun kamar; fita da yara ‘yanmata waje, a biya shi, ta hanyar wasu alhazan birni da ‘yan siyasa masu sha’awa ga ‘yan kananan yara suke zuwa ko su aiko a daukar musu yara daga ‘yan shekaru sha biyu zuwa ‘yan sha shida ko sha bakwai, su biya, su biya bukatunsu a kansu.

Sannan kuma sai masu bukatar yara ta fuskar amfani da sassan jikinsu ko sa su aikin wahala (aikatau) da sauransu da su ma, suke zuwa, su biya, su dauke su.

Munanan halin da gidan ya shiga a cikin wannan dan lokaci ya fi gaban misali, amma da yake su hukumomi ba su cika damuwa da matsalolin talakawa ba sai ya kasance ba ruwansu, suka toshe kunnuwansu da ire-iren kiraye-kirayen da ake yi a kafafen yada labarai a kan halin da gidan ke ciki.

Washegari

Kwana Ihsan ta yi tana kuka, tana kiran Abbanta, duk yanayinta ya sauya, idanunta farare sun koma jajaye, yarinya mai kuzari ta yi lakwas, tun dare Nanny Mairo ke lallashin ta da lallaba ta, har Ihsan ta tabbatar akwai matsala ta shiga yi bilhakki.

A cikin inda yara mata ke kwana, a nan aka kai Ihsan don ta kwana, duk ga sauran yara nan marayu a kwankwance, wasu ma har sun fara barci, amma Ihsan tana zaune tana kuka, dole Nanny Mairo ta hakura da lallashin ta, ta koma wajen da take kwanciya, ta ja filo, ta kwanta.

A nan, a zaune Ihsan ta kwana tana kuka, in ka dauke wata yarinya mai suna Zainab da ke kusa da ita da ta rinka ba ta hakuri don ta yi shiru, to babu wanda ya kula ta a yaran.

Da asuba aka tashe su don su yi sallah. A tunanin Nanny Mairo Ihsan ba za ta tashi ba, amma sai ta ga ita da kanta, ta tashi, ta je inda yaran suke yin alwala, ita ma ta yi, sannan ta bi su inda suke yin sallah, suka yi tare. Mamaki ne ya kama Nanny Mairo, a ranta ta tabbatar duk inda Ihsan ta fito wanda ya rike ta ya koya mata bin Allah da Manzonsa (s.a.w), kuma yana ba ta tarbiyya, domin duk irin kukan da take yi da maganganunta na damuwa, babu rashin kunya a yanayin su face matukar damuwa da rabuwa da Abbanta.

*****

Da safe yara suka karya, da kyar Nanny Mairo ta lallaba Ihsan, ta kurbi ludayi uku na koko ba tare da cin kosai ba.

Wasu daga cikin yaran sun yi wanka, sun shirya don tafiya makaranta. Suna jiran umarni daga Nanny Mairo.

Ta tara su, ta yi musu nasiha kamar kullum, sannan ta dubi Ihsan ta ce.

“Ihsan za ki bi su kafin a dinka miki na ki kayan makarantar.”

Kwalla ta taru a idanun Ihsan ta ce, “Nanny ni ina da makarantar da nake zuwa, kuma ina da kayan makaranta.”

Nanny Mairo ta dafa kanta ta ce, “Yanzu an canza miki, wannan makarantar za ki rinka zuwa.”

“Abbana bai canja min ba, ai da ya gaya min.” Cewar Ihsan.

“To ai cewa ya yi ni in gaya miki.”

“Abbana ba ya cewa a gaya min, sai dai shi ya gaya min.”

Nanny Mairo ta sallami sauran yaran da suka tsaya suna kallon su. Bayan sun tafi kana ta juya, ta kalli Ihsan sosai.

“Ihsan ina so ki yi hakuri, ki sani cewa a nan za ki zauna, a nan za ki rinka cin abinci, a nan za ki rinka zuwa makarantar da aka saka ki har zuwa lokacin da aka gano iyayenki.”

Ihsan ta dube ta a tsanake, ta ce, “Ban gane abin da kike nufi ba. Kina nufin Abbana ya bata, sai an gano shi?”

Nanny Mairo ta girgiza kai, “Ba Abbanki ba ne ya bata ba, ke ce kika bata, aka kawo ki gidan marayu kafin a gano iyayenki.”

Damuwa ta ninku a fuskar Ihsan ta ce, “Haba, ni ban bata ba, Abbana ne fa ya hada ni da abokinsa muka zo nan, shi kuma yana aiki. Nanny ki yi hakuri, ki gaya min inda Abbana yake, na je ya kai ni makaranta, kin ga yau ma za mu yi aikin aji (classwork).”

Tausayinta ya kama Nanny, ta kasa yin magana, sai ta kama hannun Ihsan suka fito daga babban falon, suka nufi gindin wata bishiya, ta zaunar da ita, sannan ta zuba mata ido sosai, ta ce.

“Ihsan ki nutsu, ki saurari abin da zan ce.”

Ihsan ta ce, “To, amma kar ki dade don kar in yi lattin makaranta, idan ban yi aikin aji ba Auntynmu duka na za ta yi. Abbana ba ya son ya ga an doke ni.”

“Ba za ki je ba ma, bare a dake ki.” Nanny Mairo ta fada a ranta, a fili kuma ta ce, “Ihsan wanda kike cewa Abbanki ne, to ba Abbanki ba ne, shi ma tsintar ki ya yi, bai san inda iyayenki suke ba, shi ne ya kawo ki nan har zuwa lokacin da za a ga iyayenki a kai ki gurin su. Duk yaran nan da kika gani su ma hakan suke ba a ga iyayensu ba, suna zaune a nan ba sa kuka, ba sa komai suna karatunsu da rayuwarsu, don haka ke ma ki yi hakuri ki zama irin su.”

*

A ranar Ihsan ba ta je makarantar ba, duk da yawan rarrashin da Aunty Mairo ta yi mata, haka nan washegari ta tashi da idanu jajur saboda uban kukan da ta sha.

Ban da Aunty Mairo sai Zainab ne kadai suke yi wa Ihsan magana, gami da lallashin ta da kwantar mata da hankali. Haka kawai Zainab take ganin Ihsan tamkar ‘yar’uwarta, hakan kuma ba ya rasa nasaba da idan ta tuna kafin ta bata tana da kanwa, wadda suka yi yanayi da Ihsan din.

Da yammacin washegarin, bayan sun tashi daga makarantar Islamiyya da misalin karfe biyar da mintuna, Zainab ta kamo hannun Ihsan, suka nufi wajen wani lilo da ke kasan wata bishiya a gefe guda na gidan marayun.

Suna tafe ba su lura ba, Iluwa ya fallo da gudu ya bi ta tsakaninsu ya raba rikon da Zainab ta yi wa Ihsan, ya wuce fuuu! Kamar mota ba abin da ya shafe shi, daga bisani sai ga Amira ‘yar gurguwa tana cangala kafa tana bin shi tana kuka, a lokaci guda kuma tana cewa cikin tsamin baki.

“Wayyayi sai na yama.” (Wallahi sai na rama)

Zainab ta yi tsaki tana nuna Iluwa, tana fadin, “Kin gan shi nan duk gidan nan ya fi kowa fitina da barna da wasan banza, ko kadan ba shi da kirki, ya gagari kowa a gidan nan, har an saduda a halinsa. Duk wanda yake gidan nan ya san idan gari ya waye kafin yamma sai Iluwa ya yi tsokana, sai ya yi fitina sai ya bata wa mutane rai.

“Akwai watarana, wani mutum da ake tsammanin shi ne mahaifin Iluwa ya zo gidan nan, ana sa ran zai dauke shi su tafi, amma da ya ga yadda yaron yake da fitina sai ya bar shi, ya ce ba dansa ba ne.”

Ihsan ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Ni kuma kin ga Abbana ba zai ce ni ba ‘yarsa ba ce.”

Zainab ta yi murmushi, “Ita kuwa mai biye da shi sunanta Amira ‘yar gurguwa, an ce iyayenta ne suka jefar da ita saboda Allah ya halicce ta musaka.”

Ihsan ta tsaya, sannan ta kalli Zainab ta ce, “Yaya Zainab ni ma iyayena ne suka jefar da ni?”

Zainab ta girgiza kai ta ce, “A’a Ihsan, ke iyayenki suna son ki, bata kawai kika yi.”

Ihsan ta girgiza kai, “A’a Zainab, ba bata na yi ba, Abbana ne fa ya hada ni da abokinsa shi kuma ya kawo ni nan.”

Zainab ta dan damu, sannan ta kama hannunta suka ci gaba da tafiya har zuwa inda suka nufa.

A nan suka zauna, Zainab tana kwantar wa da Ihsan hankali, da ban hakuri gami da nuna mata yanayin da rayuwa ya same ta.

“Duk wanda kika gani a gidan nan to dole ce ta kawo shi, dolen da ta sa sai an yi hakuri, tun da kaddara ce, da yawa da kika gani a lokacin da aka kawo su sun fi ki shiga damuwa, amma dube su.” Ta nuna wasu yara su uku suna wasa, suna dariya, “Wancan da kika gani yana dariya, lokacin da aka kawo shi, saboda kuka kamar zai mutu, domin shi iyayensa ne suka zo Kano ziyara, suka yi hatsari a mota, gabadayansu suka kone, suka mutu, shi kadai ne ya yi rai, kuma aka nemi asalin garinsu ko wata alama da za ta kai a gano daga inda suke aka rasa…”

Da Zainab din da Ihsan duk a cikin damuwa suke, musamman da jin labarin nan.

“Amma cikin ikon Allah kalle shi, yadda yake ta wasanninsa yana dariya.”

Suka kalli wajen.

Bayan Watanni Uku

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, Ihsan ta sami watanni uku a gidan marayu, a zahiri ta saduda da tarin wasu abubuwa, don ta hakura yanzu tana zuwa makarantar da sauran yaran ke zuwa, ta shiga cikin da yawan lamuransu, a da ba ta zuwa dakin kallon talabijin da wajen wasa amma a yanzu tana dan zuwa jefi-jefi.

Ba ta da babbar kawa sai Zainab, sai kuma wani yaro sa’anta mai suna Yaroro, wanda jininsu ya hadu saboda ana cewa suna kama da juna.

Sai dai kuma har yanzu tana sa ran za ta ga Abbanta, ya zo gare ta, ko kuma ta je wurin shi watarana, don haka ta addabi ma’aikatan gidan da neman a kai ta ko a je a dubo mata gidansu ko za a gano shi.

Yanzu haka ma daga ofishin sakataren gidan ta fito, tana kuka, fuska sharkaf da hawaye. Daidai lokacin Zainab ta fito daga bangaren dakin kallo, ta hango ta, ta yi hanzari ta je gareta, ta rike hannunta.

“Ihsan yau ma ba nasara?”

Ihsan ta gyada kai tana shisshikar kuka, “Koro ni ya yi, bayan ya mare ni, ya ce kar in kuma zuwar masa ofis, wai ni na fi kowa ne…”

“Ke Ihsan zo nan.” Sakatare Isah ne ya katse mata magana bayan da ya kwalla mata kira.

Gaban Ihsan ya fadi, haka ma Zainab. Ta juya a hankali, ta kalle shi.

Sakatare Isah ya yafito su da hannu, “Ku zo nan ke da kawar ta ki.”

A sanyaye, Ihsan da Zainab suka nufi inda yake, kafin su karasa ya koma ciki, su ma suka bi shi cikin, a lokacin ya zauna a kan kujera gaban tebur, su kuma suka tsaya a gabansa.

Ransa a bace yana kallon Ihsan, “Za ki iya gaya mana kwatancen gidan naku?”

Da sauri Ihsan ta gyada kai, “E, zan iya.” Ta yi sauri ta harhada tunaninta, ta tuno lambar gidan da sunan layin.

Sakatare ya sa takarda a gabansa ya daura hannunsa mai biro a kan takardar, “Fadi in ji.”

“Lamba 224, Sarari Abenue. Gidan fari ne da akwai karfe a gaban gidan.”

Sakatare ya rubuta, sannan ya ce “Ku je, za mu sa a bincika, idan muka samo Abban naki za mu kawo miki shi.”

Da sauri ta saki murmushi, ta durkusa “Na gode Malam, na gode.”

Ya ji zuciyarsa na kiyasta masa tausayin Ihsan, ya yi sauri ya ce “Shikenan, shikenan ku je.”

*****

Washegari Ihsan ta yi ta zaman jira don ta ji an ce an ga Abbanta, amma shiru, idan ta yunkura don ta je, ta tambaye shi, sai Zainab da Yaroro su hana ta, sai ta zauna ta ci gaba da kuka.

Har ranar nan ta kare ba labari, a rana ta biyu, Zainab tana can kwance tana barci saboda masassara, Ihsan na zaune tare da Yaroro, ta yi jugum tana tunani, Yaroro ne ke ta surutu.

“Addu’a za ki yi, Allah ya sa a gan shi, ko kya koma gidanku wajen Abbanki.”

Ihsan ta ce “Ina yi.” Ta kalle shi, “Yaroro kai ba ka da Abba ko Umma ne?”

Yaroro ya yi murmushi “Ba ni da su, shi ya sa kika ga ba na kuka kamar ke.”

Ta dube shi sosai, “Kenan duk yaran da ba su da Abba ko Umma ba sa damuwa?”

Yaroro ya ce, “Watarana wasu mutanen suna zuwa su dauki wasu yaran, su zama iyayensu.”

Suka dan yi shiru.

“Ni dai na fi so Abbana ya zo, ya dauke ni.” Cewar Ihsan.

Yaroro ya yi dariya. Yana shirin yin magana Nanny Mairo ta zo wajen, ta kama hannun Ihsan, “Ki zo in ji Sakatare.”

Da sauri Ihsan ta mike, ta bi ta. Suka je ofis din Sakataren, gaban Ihsan yana ta faduwa, tana sa ran za ta ga Abbanta.

Sakatare ya dube ta, “Ihsan an je kwatancen da kika ba da, an sami kwatancen amma ba a sami Abban naki ba, kuma ba a sami inda yake ba, don haka sai ki yi hakuri, ki ci gaba da zama a cikin ‘yan’uwanki, idan Allah ya sa watarana an gan shi sai a gaya miki.”

Kuka Ihsan ta sa, ta fadi kasa, tana burguma, Nanny Mairo ce ta tallafo ta tana rarrashi.

Bayan Shekaru 6

A wani otel, a cikin daki, a kan kyakkyawan gadon dakin, Sima ce kwance ta yi daidai tana danne-dannen waya. Daidai lokacin Honarabil Iliya Ajiya ya shigo, ransa a bace yana kallon ta.

“Har yanzu ba ki dauka kin tafi ba?”Ya ce da ita.

Sima ta dago fuskarta a sake ta ce, “Wai kai Ajiya me ke damunka ne”

Ya yi tsaki, ya nufi wajen dirowa yana cewa, “Kin fi kowa sanin abin da ke damuna.” Ya ciro bandir din kudi daga dirowar na Naira dubu-dubu N50,000 ya jefa mata.

“Ki tashi, ki tafi na ce.”

Ta marairaice ta ce, “Haba Ajiya na sha gaya maka akwai matsala, ka tubure kai sai ‘yar karamar yarinya  kake so, shin ba ka san halin da ake ciki ba ne…?”

“Wanne hali ake ciki?”

“Ka manta yadda kungiyoyi suka daura damarar yaki da ire-irenku masu yi wa kananan yara fyade? Ku ne fa kuke kara karfafa musu guiwa, kwanaki har a rediyo na ji ka kana babatu…”

Ya dakatar da ita, “Kin ga dakata, babatun banza ne. Na ji kina maganar fyade, ce miki aka yi fyade zan yi? Ko ba ki fahimci irin aiki da na ba ki ba ne? Cewa na yi ki samo min yarinya ‘yar shekaru sha uku zuwa sha shida su nake sha’awa kuma ba da karfin tsiya zan far musu ba, Salamun-salamun…”

Sima ta yi tsaki, “Duk wani gyare-gyaren da za ka yi a banza, don fyade ne. Ni ina mamakin ire-irenku wallahi, a ce duk karuwai masu aji irinmu da kuke da su wadanda suka san kissa da kisisina ba su ishe ku ba sai yara kanana?”

“Sirrinsu ne ba ki sani ba Sima.” Ajiya ya ce, sannan ya kalle ta sosai, “Ki dauka su din sabbi ne, ku kuma masana kissa da kisisinar tsofaffi, ta yaya za ki iya hada nagarta da karkon sabo da tsoho? To ki sani duk sabo, sabo ne, ku daban su daban.” Ya mika hannu ya dauko wasu bandir din kudi na dubu dari biyu, ya ajiye a gabanta. “Burina ki san yadda za ki samo min abin da nake bukata, idan kika samo zan kara miki kamar su sau biyu.”

Sima ta yi shiru, tana kallon kudin, tana tunani, can ta yi ajiyar zuciya, “Yanzu har karamar yarinya ta kai matsayin wadannan kudin?”

Hon. Ajiya ya yi murmushi, “Ba yarinyar ce ta kai matsayin kudaden ba, mai aikin samo yarinyar ce.”

Sima ta yi murmushi da ajiyar zuciya, sannan ta ce, “Akwai wata dabara da na tuno.”

“Yauwa ina jin ki.” Cewar Hon. Ajiya.

“A gidajen marayu akwai yara kanana masu kananan shekaru, ni da kai za mu je a matsayin mata da miji masu neman ‘yar da za su dauka, ka ga idan muka duba, muka ga wadda ta yi daidai da ra’ayinka sai mu dauko, mu zo ka yi abin da kake so.”

Hon. Ajiya ya yi murmushi, “Shi ya sa kika zama tauraruwa a cikin ‘yanmatan da nake nema. Sai dai gyara daya da zan yi miki shi ne, ba da ni za a je dauko yarinyar ba, sai dai ko da yaro na.”

Sima ta ce “Me ya sa?”

“Saboda ni an sanni, fitacce ne, idan aka sami matsala, tawa za ta kare.”

Sima ta yi dariya, “Gaskiya kam. To sai a san da wanda za a hada ni, kuma a tsara yadda abin zai kasance.”

“Kar ki damu.” Cewar Hon. Ajiya, “Har can din ma zan sa a shiga a fita.”

“Hmn! Ai ku ‘yan siyasar nan, kun san hanyoyi da dama.”

Ya yi dariya, “Har da mara bullewa.”

Suka yi dariya gabadaya.

*****

Sima na zaune a ofishin Sakataren gidan marayu tare da Maitama, yaron Hon. Ajiya da ya turo, sun yi shiru suna kallon yanayin kuntataccen ofishin, ran Sima a bace yake da alama ta gaji da zama a ofis din da ba fanka ga teburin da suke zaune na katako ne gadardar mai dade mazaunai.

Daf da lokacin da Maitama ya yi tsaki na arba’in da uku daidai lokacin Sakatare ya shigo Ihsan na biye da shi, bai yi musu sallama ba, sai dai ban hakuri da ya bi su da shi.

“Ku yi hakuri fa, Oga ne ya tsayar da ni.” Ya ja kujera, ya zauna a gaban teburinsa.

Ihsan ta tsaya daga gefe tana kallon sa.

Sima ta kakaro murmushi tana yi wa Ihsan kallon sama da kasa, ta ce.

“A, ba komai wallahi.”

Maitama ya kura wa Ihsan ido, bakinsa a bude har sai da Sima ta fakaici idon Sakatare ta taka masa kafa, sannan ya kawar da kai yana tsaki.

Sima ta ce, “Ai ba matsala, tun da mun gama komai.”

Sakatare ya yi murmushi, “Haka ne.” Ya kalli Ihsan, “To Ihsan ga iyayen naki nan da na gaya miki, za ki zauna a wurinsu kafin a ga Abban naki, za su rike ki kamar kina hannunsa, don mun yi magana da su ba ki da wata matsala.”

Ita dai Ihsan kallon su take yi, tana tunani. A gaskiya, a yadda ta lakance su mutanen nan ba mutanen kirki ba ne, sai dai ba ta da zabi, dole ta bi su, ko don abu biyu; na farko ba ta isa ta bijire musu ba, na biyu tana sa ran idan suka tafi da ita za ta iya ganin Abbanta. Don haka ta mika kai bori ya hau, su Sima suka tafi da ita lullube da ainihin mummunar manufar da ta kawo su gidan, wato aiken Hon. Ajiya.

Sai dai a lokacin da suka fito za su tafi da ita, Ihsan da Zainab sun sha kuka, don kuwa Zainab rugowa ta yi, ta kankame Ihsan suna kuka, da kyar aka bambare ta, haka sauran yaran da suka saba da Ihsan da yawansu sai da suka fitar da hawaye saboda jimamin rabuwa.

A nata bangaren Sima sai kallon Ihsan take, tana kissima kyawunta, da yanayinta na ban tausayi, haka ta ji a ranta ta damu, za su je, su bata rayuwar yarinya a banza kuma ma marainiya. A haka suka shiga mota, suka tafi. Yara na daga mata hannu, Zainab na kuka ita ma tana kuka.

*****

A can gidan da Hon. Iliya Ajiya ya ce a kai masa Ihsan, tun da aka kai ta tun bayan karfe uku na rana har bayan magariba ba kowa, tun da dai Sima ta shigo da ita, ta nuna mata kicin da bandaki da dakin da za ta zauna, ta ce ta jira ta, ta fita har yanzu ba ta dawo ba

Ihsan tana mamakin wai wanne irin gida aka kawo ta haka? Da ta gaji da zama, cikin damuwa, sai ta tashi, ta dan kewaya, ta ga yanayin gidan, kana ta je kicin, ta bude firji ta dauki kayan marmari na kwali da tuffa ta ci, ta sha.

Da lokacin sallar La’asar ya yi, ta jiyo kiran sallah, ta je, ta yi alwala, ta zo, ta yi sallah.

Haka ta zauna tana addu’o’i irin wadanda Abbanta da malaman makarantarsu suka koya mata, har zuwa lokacin sallar magariba, nan ma ta yi sallah. Abin da ya dan kwantar mata da hankali shi ne ganin gidan akwai wutar lantarki. Sai dai hakan bai hane ta yin kuka ba, saboda damuwa da kadaici da rashin sanin makomarta. A lokacin ta ji shigowar mutum, da sauri ta bi kofar da kallo, Sima ce ta shigo.

Duk da kokarin basarwa da samarwa kai nutsuwa da Sima ta yi, sai da Ihsan ta gane ba a daidai take ba, da ta zo daf da ita sai ta ji tsami, amma ba ta san tsamin giya ba, balle ta san giya Sima ta sha, amma dai ta fuskanci akwai matsala.

Ita ma Sima da ta fahimci kamar Ihsan na neman fahimtar wani abu, sai ta yi sauri, ta kalle ta, ta ce, “Ina zuwa.” Ta fice. Bandaki ta je, ta watsawa fuskarta ruwa, sannan ta kinkintsa, ta dauki turare ta fesa, kana ta fito, ta koma wajen da Ihsan take, ta dan dafa kanta.

“Ya….ya ma kika ce sunanki?” Har yanzu da muryar mashaya giya a maganarta.

Ihsan ta ce, “Sunana Ihsan.”

“Yauwa Ihsan. Ki…ki… kwantar da hankali, ni da mijina mai…..maigidan nan tun da muka yi aure ba….mu taba samun haihuwa ba, kuma ni da shi muna matukar son ‘ya’ya, musam….. musamman ‘ya mace, kyakkyawa irinki, shi ne da muka ga ba mafi… mafita muka je gidan marayu muka ganki, muka ce muna son ki. Ihsan za mu zauna da ke, ki zamar mana ‘ya, ki saki jikinki, ki dauke mu kamar iyayenki.” Ta zaro ido, a lokaci guda tana murmushi, “Ko ba kya son zama da mu?”

Ihsan ba ta ce komai ba.

“Idan kina zaune a wurinmu ba mamaki watarana a ga iyayenki, kin ga sai mu mayar da ke wurinsu, ko ba kya son haka?”

Ihsan ta ce, “Ina so mana.”

Sima ta yi murmushi, “Yauwa ko ke fa, na ga ma ba kya murmushi. Kin ci abinci?”

Ihsan ta ce, “Na ci na rana.”

“Na dare fa?” Sima ta tambaye ta.

“Ban ci ba tukun, sai an yi sallah. Ina abincin?”

Sima ta kalle ta, a ranta ta ce “Ka ji yarinya da wayo, anya za a cimma buri ta dadin rai kuwa?” A fili kuma ta ce “Akwai a kicin.” Ta tashi, ta kunna mata talabijin, sannan ta ce “Ina zuwa.” Ta fice daga dakin. Ihsan ta bi ta da kallo.

Ba ta damu da kallon talabijin din da ta kunna mata ba, kawai ta ci gaba da nazari da tunanin yanayin Sima da gidan, ta kasa gano komai, amma dai hankalinta bai kwanta da yanayinsu ba ko kadan.

Tana cikin wannan hali na tunani, ta ji an kira sallah, ta tashi, ta yo alwala, ta zo ta fara yi. A cikin wannan yanayin ne Sima ta leko, ta gan ta tana sallah, ta cika da mamaki, don ita kam ba ta yin sallah sai idan sallar ce ta fado mata ba zato. Ta juya a sanyaye, ta koma inda ta fito.

Bayan idar da sallah, Ihsan ta je, ta duba kicin, ba ta ga abinci ba, sai abin da ke cikin firji, har za ta fita, sai ta lura da leda a ajiye, ta duba,  a ciki ta ga abinci a take-away, wannan ne ya tabbatar mata cewa ita aka ajiyewa, ta dauko hade da ruwa, ta je, ta ci.

Bayan kamar awa daya da rabi da kammala cin abincin Ihsan, tana nan zaune a kan kujera iska na kada ta, ta fara gyangyadi, sannu a hankali ta kwanta saboda gyangyadin ya ci karfinta.

Sima ta kara lekowa, ta gan ta tana barci, ta sake fita.

Can cikin barcin Ihsan ta jiyo muryar Sima da Hon. Ajiya suna magana a dakin da ke kusa da ita. Ta tashi a hankali, ta fita, ta nufi dakin, a bakin kofar dakin ta tsaya, tana iya hango su a tsaye suna tattaunawa. A zatonta za ta ga Maitama, sai ta ga wani daban, wato Hon. Ajiya.

Sima ta ce, “Ni ai na gama maka aiki tun da na kawo maka ita.”

Hon. Ajiya ya ce “Wai me yake damun ki ne, kin san irin wadannan yaran sai da lallabawa, ta yaya kike tsammanin zan je in afka mata haka sakaka….”

Gaban Ihsan ya fadi.

Sima ta yi dariya, “Ai wannan ma aiki ne mai zaman kansa, sai ka biya ni.”

“Me ya sa ke mayyar kudi ce, komai ki ce kudi.”

Sima ta ce “Ku, kuka koya mana son kudi. Kuma kar ka manta haja nake kasawa, idan na sami mai siya sai in siyar.”

Ransa a bace ya ce, “To hajar na ce zan siya?”

Ta yi dariya, “Ai hanya da yawa maganin barayin hanya, wannan hanyar ma haja ce gare ni.”

“Na ji, ki daure, ki san yadda za ki yi in biya bukatata a daren nan.” Cewar Hon. Ajiya.

“Ka matsu kenan? Kar ka damu nawan, kai dai ka kirga min.” Sima ta fada tana dariya.

Hon. Ajiya ya yi tsaki, “Da alama kin sha ta yi miki yawa, za ki yi min hauka ko? Kin manta ba sai kin yi min aiki nake kirga miki ba?”

“Au sorry nawan, na manta. Amma fa ka sani ina kishi, shi ya sa nake yi maka haka.” Cewar Sima.

“Kin ga don Allah, kina bata wa mutane lokaci, kin ce yarinyar nan ta yi barci, ki je, ki san abin yi.”

Sima ta ce, “Kwantar da hankalinka, yanzun nan zan gyaro maka komai.” Ta tashi, tana layi na ‘yan giya.

Ihsan ta yi sauri, ta bar kofar, ta koma dakin da ta baro.

Sima ta nufi kofar fita a hankali tana layi, Hon. Ajiya ya bi ta da kallo.

Ihsan tana zaune, idanunta cike da hawaye, Sima ta shigo, ta yi turus ganin Ihsan a zaune, mamaki ya kamata, ta taka a hankali, ta je kusa da ita, ta zaune.

“‘Ya na ganki a zaune, na dauka barci kike yi?”

Ihsan ta ce “Na yi barci, tashi na yi.”

Sima ta dafa kanta, “Me ya same ki, kike kuka?”

Ihsan ta dan ture hannunta ta ce, “Na tuno Abbana ne. Wajen Abbana nake son zuwa.”

“Me yake damunki ne, na gaya miki ki saki jikinki, ki dauke mu tamkar iyayenki. Wataran za mu kai ki wajen Abbanki.”

Ihsan ta kalle ta, “Wane ne na ji kuna magana da shi. Kuma me za ku yi min?”

Gaban Sima ya fadi, “Me kika gani, kuma me kika ji?”

“Na ga wani mutum da ba da shi kika je gidan marayu dauko ni ba, kuma na ji yana cewa ki shawo kaina.” Ihsan ta fada.

Sima ta kura mata ido, “Wannan shi ne mijina, wancan yaronsa ne, lokacin da muka zo ba ya gari ne, shi ne ya hada ni da shi, ya ce mu je, mu dauko ki. Kuma cewa ya yi a kwantar miki da hankali don ki ji nan kamar a gidan iyayenki.”

Ihsan ta kalle ta kawai, ba ta yi magana ba.

Sima ta ci gaba da magana a sanyaye, “Ki kwanta mana.”

Ihsan ta girgiza kai, “Ba yanzu zan kwanta ba.”

“To ni bari in kwanta.” Sima ta sami wuri a kusa da Ihsan ta kwanta lamo. Tsawon mintuna talatin Sima na kwance kamar mai yin barci, ita kuwa Ihsan tana zaune ta yi tagumi, tana kukan zuci.

Can jimawa da Sima ta gaji, ta mike zaune tana kallon Ihsan, ta ce “Bari in je, in dawo.” Ta fice, ko kallon ta Ihsan ba ta yi ba.

Hon. Ajiya na zaune a falon, ya yi tagumi, Sima ta shiga ko sallama ba ta yi masa ba, ya yi zumbur, ya zauna sosai yana kallon ta. Tana zuwa kusa da shi, ta zube a kan kujera.

“Ka hakura da yau kurum, na gaji, don yarinyar nan ba za ta yi barci ba, bare ka cimma burinka.” Cewar Sima.

“Ke Sima!” Ya daka mata tsawa, “Me kike nufi?”

Sima ta harare shi, ta yi tsaki, “Na yi duk yadda zan yi don ta yi barci amma ta ki, ga shi ni barcin nake ji. Ka mayar da maitar ka zuwa gobe….”

“Idan ba haka ba fa?” Hon. Ajiya fada a fusace.

Sima ta yatsina fuska, “Sai a yi abin kunya, don ina mai tabbatar maka idan ka ce za ka haike wa yarinyar nan to za ta yi maka tonon silili.”

Ya koma cikin kujera ya yi ragwaf, yana huci hadi da tsaki.

Sima ta lumshe ido don barci ya ci karfinta.

A can inda take, Ihsan ta tashi, ta rufe kofar dakin, ta sa sakata, sannan ta je, ta ci gaba da zama cikin takaici.

*****

Washegari haka Ihsan ta wuni ba Sima bare Hon. Ajiya a gida, da alama asubanci suka yi, suka fice daga gidan.

Ta zauna cikin tunane-tunane, da farko dai ta tabbatarwa kanta mutanen nan karya suke yi ba miji da mata ba ne, sannan kuma ba gaskiya suke gaya mata ba da suke cewa za su rike ta a matsayin ‘ya. A take ta fara tunanin yadda za ta gudu daga gidan.

Can bayan sallar Isha’i tana kwance a kan kujera ta ji shigowar Sima da Hon. Ajiya, ta yi lamo tana sauraron su. Cikin wannan hali Sima ta shigo, ta dan tattaba ta don tana tunanin barci take yi, Ihsan ta ki tashi, ta yi kamar barcin take, ba ta yi magana ba, Sima ta juya, ta fita. Tana fita, Ihsan ta tashi a nutse ba tare da sanin Sima ba ta bi bayanta.

A falo, Hon. Ajiya yana zaune yana shan lemo, Sima ta shiga, ita kuwa Ihsan da take biye da ita, ta makale a bakin kofa tana hango su tare da jin abin da suke fada.

“Ya aka yi?” Hon. Ajiya ya tambaye ta.

Sima ta yi murmushi ta ce “Ta yi barci.”

Hon. Ajiya ya ce, “Alhamdulillahi, sai ki hanzarta, ki je, ki shaka mata hodar.”

Sima ta yi masa gatsine, “Saurin me kake yi? Ka bari in huta mana, in sha lemo.”

Zumbur ya mike, “Kin ga malama hutu bai same ki ba, ki bari idan kika gama, sai ki zo, ki huta ni kuma kin ga a lokacin ina can.”

Ta yi tsaki, ta fada kan kujera, “To maye, bari in dan jika makogarona.”

A lokacin Ihsan da ke tsaye a kofar falon ta juya a hankali, ta bar wurin, ba ta koma dakin da take ba, ta nemi kofar fita daga gidan.

Hon. Ajiya bai zauna ba, sai da  ya ga Sima ta kurbi lemon, ta shanye kofi daya, ya azalzale ta, dole ta fita, ta nufi dakin da Ihsan take. Da ta je, sai ta yi tsaye cikin mamaki, ganin Ihsan ba ta nan, amma sai ta yi tunanin ko bandaki ta shiga, ta yi sauri, ta je bandakin ta duba, ba ta gan ta ba, ta shiga kicin, nan ma ba Ihsan ba alamarta, wasa-wasa Sima ta karade duk inda ya kamata ta shiga a gidan amma babu ita, ba labarinta, hankalinta ya tashi, ta nufi falo.

Hon. Ajiya na zaune, jin shigowar Sima ya mike zumbur cikin fara’a, sai dai ganin yanayin da take ciki ya sa fara’arsa ta rikide ta koma damuwa.

“Me ya faru?” ya fada murya na rawa.

Sima ta yi ajiyar zuciya, ta ce “Yarinyar nan ta gudu!”

“Ta gudu?!” Hon. Ajiya ya maimaita.

“Na duba ko’ina a gidan nan ban gan ta ba.” Sima ta yi masa bayani.

“Shitt!!” Ya fada tare da zaro waya, ya yi sauri ya lalubo lambar Maigadi, ya kira, sannan ya kara a kunne.

“Maigadi kana ina?”

Muryar Maigadi ta bayyana a kunnensa yana fadin, “Ina kofar geeett.”

“Yarinyar da aka kawo gidan nan ta fita?”

Maigadi a waya ya ce, “E, yanzu ta fita, ta ce an aike…”

Hon. Ajiya ya katse shi da tsawa, “Yi sauri ka kamo ta, duk inda ta shiga, kar in gan ka ba tare da ita ba…” Ya kashe wayar yana yi wa Sima wani irin kallo.

Sima ta ce “Me ya sa ka ce a kamo ta?”

“Ba ki da hankali Sima, na ce ke mahaukaciya ce, tun da kika ga yarinyar nan ta gudu to ta ji duk abubuwan da muka tattauna, kuma ta san shirinmu, me kike tsammani idan muka kyale ta, ta gudu? Ai tona mana asiri za ta yi.”

Sima ta girgiza kai, “Haka ne. To me za ka yi mata idan an kamo ta?”

Ya harare ta a fusace, “Zan iya kashe ta don asirina ya rufu, kin manta yau saura watanni mu gama wannan mulkin mu nemi tazarce…?”

Sima ta gyada kai, “Ban manta ba.”

“To me kike zato idan ta tona min asiri?”

“Gaskiya ne, akwai matsala.” Sima ta fada.

“To don haka sai an kamo ta zan san hukuncin da zan yanke mata.”

Wayarsa ta yi kara, kafin ya dauka ta tsinke, ya duba, ya ga filashin ne daga Maigadi. Ya yi sauri ya kira shi yana fadin, “Matsiyaci!” Kafin ta shiga. Da ta shiga, Maigadi ya daga ya ce, “Yaya ka kamo ta?”

Maigadi ya ce, “Yallabai wallahi yarinyar nan ta bace min…”

Hon. Ajiya ya daka masa tsawa, yana cewa “Yi min shiru sakarai, ka fice min daga gida, kar ka dawo sai tare da yarinyar nan in dai har kana son aikinka.” Ya kashe wayar, sannan ya yi jifa da ita kan kujera.

Sima na bin shi da kallo cikin mamaki.

****

Washegari

A karkashin teburin wani mai sayar da kayan miya Ihsan ta kwana, ba ta bar wurin ba sai da gari ya waye sosai, sannan ta kara mike hanya tana tafiya, tana dube-dube ko wani ya biyo ta.

A daidai wani masallaci ta sami buta, ta debi ruwa, ta wanke fuskarta, sannan ta yi alwala, ta je can bayan masallacin daga cikin farfajiya ta yi sallah.

Bayan ta bar masallacin ne ta fara jin yunwa, da ta tuna ba yadda za ta yi sai ta fara hawaye, a ranta tana tunanin yadda za ta sami abinci ta ci, ta yi tunanin ko ta yi roko? Haka ta ci gaba da tafiya ba ta san inda za ta ba ko inda ta nufa, ga shi ta yi doguwar tafiya, ga yunwa, take kanta ya fara ciwo, duk ta galabaita.

A cikin wannan yanayi ne ba ta san ta hau kan titi ba, haka shi ma wani mai haye da babur irin na zamani da ake cewa ‘roba-roba’ ya buge ta. Abin ya zame mata goma da ashirin, ta suma.

Mai tuka babur din saurayi ne da yake dauke da shekaru ashirin da shida, yana sanye da rigar shet da wando, duk ya rude, ya tsaya a kanta, ya rasa abin da zai yi.

Daya daga cikin mutanen da suka zo wurin don ganin abin da ya faru, shi ya kwantar masa da hankali, “Kar ka tada hankalinka, ba ta mutu ba, suma ta yi, bari mu yayyafa mata ruwa.”

Wani almajiri da ke gefe ya miko ruwan leda, mutumin ya karba, ya yayyafa mata sannan ya shafa mata a goshi. Ihsan ta farfado tana yin ajiyar zuciya, sannan kuma tana motsa baki.

Da mutumin ya dube ta sosai, sai ya kalli saurayin ya ce, “Yi kokari ka samo lemon kwalba ko na roba, da dan wani abinci mara nauyi, yunwa take ji.”

Saurayin ya bazama da sauri, jim kadan ya dawo, lokacin Ihsan ta bude ido sosai, har an dan jingina ta da bango. Aka ba ta lemo da cincin, ta hau ci, bayan ta gama, ta sha ruwa, tana gamawa ta dawo hayyacinta.

A yanzu ‘yan kallon sun ragu, daga wasu mutane biyu ‘yan gwanin kwaf, sai mutumin nan da saurayin.

Mutumin ya dubi saurayin, “Yaro ya sunanka ne?”

“Sunana Amadu Sha’aibu.” Cewar yaron.

“To ga yarinya dai ta farfado, garin yaya haka ta faru?”

“Baba ni dan jarida ne, ina sauri ne zan je dauko wani labari a Gidan Zu, ban lura ba ta shigo min na kade ta.” Cewar Amadu.

Mutumin ya kalli Ihsan, “Yarinya ya sunanki? Kuma daga ina kike, me ya faru kika hau titi haka?”

Ihsan ta fashe da kuka. A lokacin wani dansanda ya iso wajen. Ihsan ta ba da labarinta tun daga zamanta da Harisu, da kai ta wajen abokinsa Abashe da ya yi Gidan Zu, zuwa kai ta gidan marayu da rayuwarta a gidan marayu, zuwa daukarta da Sima ta yi a matsayin za su rike ta zuwa gudowarta, ta gaya musu gabadaya.

Gabadaya, da Amadu da mutumin da dansandan da mutane biyun ‘yan jin kwakwaf babu wanda bai tausaya mata ba, Amadu har da hawaye a idonsa.

Ihsan ta ce cikin muryar kuka, “Don Allah kafin ka mayar da ni gidan marayun ku fara kai ni gidanmu in duba ko Abbana ya dawo.”

Amadu ya ce, “Ki kwantar da hankalinki. Yanzu za ki gane gidan naku idan aka je unguwar?”

Ihsan ta gyada kai, ta ce, “E”, dansandan ya riga ta da cewa.

“Ka ga dan jarida sai mun fara zuwa asibiti an tabbatar da lafiyarta, sannan mu je ofis a rubuta abin da ya faru (report).”

Zumbur Ihsan ta mike, “Ni lafiyata kalau, kujewa kawai na yi. Don Allah ku kai ni gidanmu, in ga Abbana.”

Dansanda ya ce, “Za a kai ki, amma sai hukuma ta san da duk wannan lamura naki.”

Amadu ya kalle ta ya ce, “Kar ki damu Ihsan, zan tsaya in tabbatar da an kai ki gidanku, ki daina kukan.”

Ta kalle shi kawai tana share hawaye.

*****

Ihsan da Amadu da Kofur Zaidu suka je unguwar da Ihsan ta sanar da su, sannan sannu a hankali da kwatance ta kai su har cikin layin da suke, to amma duk da sun je har kofar gidan, sai ta gaza gane gidan kai tsaye saboda a da gidan babu babbar kofa (gate), babu katangar haraba bare shuke-shuke, amma a yanzu duk an samar da su.

Ihsan ta tsaya a gaban gidan, ta ba shi baya tana kallon saitin gidan, inda kai tsaye take kallon wurin teburin mai shayi da bishiya a gefensa, ba za ta taba mantawa da wajen ba a ranta ta ce “Ga wajen Saleh Mai-shayi.” Sannan ta juya, ta kuma kallon gidan, sai kuma ta kalli su Amadu.

“Ina ganin nan ne gidanmu.”

Kofur Zaidu ya ce “Kina kokwanto ne?”

Ihsan ta amsa, “An sauya masa abubuwa da dama shi ya sa na fadi haka.”

Amadu ya ce, “Tsawon shekaru bakwai dole za a iya samun sauye-sauye. Idan har kin tabbatar za mu iya neman wadanda ke cikin gidan.”

Ihsan ta daga kai, “Na tabbatar nan ne gidanmu.”

Suka yi ta buga kofar gidan, amma babu wanda ya zo bare a bude musu, har suka fara saduda sai ga Saleh Mai-shayi ya tsallako zuwa gare su, yana fadin.

“Bayin Allah, masu gidan nan ba mazauna ba ne, daga mijin har matar ma’aikatan gwamnati ne da kamfani, idan neman su kuke sai dai ku yi amfani da wayar tangaraho.”

Tun da ya iso Ihsan ke kallon sa, don ta san shi, ta gane shi, Saleh Mai-shayi ne, ta sha shan shayinsa. A cikin maganarsa, abin da ya sa ta damuwa shi ne yadda yake fadin wasu mutane sun riga sun mallaki gidan. To ina Abbanta? Hawaye ya biyo kuncinta.

Amadu ya kalle ta, ya ce, “Ba kuka za ki yi ba, ki tuna ko akwai wata mafitar.”

Ihsan ta dan sarara, kana ta dubi Malam Saleh ta ce, “Malam Saleh ba ka gane ni ba?”

Malam Saleh ya kalle ta sosai, ya girgiza kai “Yarinya ban gane ki ba, kin san ganin ya ragu, haka aikin kwakwalwar ma ya karanta.”

Ihsan ta ce, “Ni ce Ihsan da muke gidan nan ni da Abbana…”

Malam Saleh ya kura mata ido baki a bude, sannan ya yi zumbur ya ce “Allah mai iko, Ihsan ce na ko gane ‘yar Harisu, yaro mai kirki. Ihsan ke kika girma haka, kika zama budurwa?”

Ihsan ta gyada kai tana share hawaye, “Ni ce.”

Malam Saleh ya ce, “To ina Abban naki? Allah ya sa ba mutuwa ya yi ba? Ai da mutane nan za su tare a gidan nan, komai na ku ni aka ba ajiya, duk na jibge su a dakin zaure, duk da kayan ba yawa gare su ba, fatan za ki tafi da su?”

Ihsan ba ta iya yin magana ba, Amadu ne ya ce, “Za mu dai ga kayan kafin mu tafi da su.”

Malam Saleh ya kalle shi, “Ina ta zuba ba ku gaya min me yake tafe da ku ba? Na ga har da dan doka kuke tare.”

Kofur Zaidu ya ce, “Za ka ji komai, mu je wajen kayan nasu.”

“To, to, ba matsala mu je.” Malam Saleh ya ce da su, sannan ya juya don jagorantar su.

*****

A dakin zauren, suna zazzaune akan wasu kujerun tsugunno na katako. Bayan bincike da dudduba wani abu da zai nuna musu inda Haris yake, ba su gano komai ba, sai littafin jotar da a yanzu Amadu ya fara karanta musu, wanda ke kunshe da asalin samuwar Ihsan da rayuwar ta tun tana jaririya, wanda Haris ya rubuta da hannunsa.

Bayan da Amadu ya kammala karanta rubutun da Haris ya bari na asalin Ihsan, wanda ya nuna asalin iyayenta ‘yan garin Gombe ne. Idanun Ihsan cike da hawaye, ta dube shi, muryarta cike da tausayi.

“Don Allah ina son ka yi min wata alfarma.”

Amadu ya dube ta, “Ina sauraron ki.”

“Ina son ka raka ni Gombe.”

Amadu da ‘yansanda suka dubi juna, daya dansandan ya yi gyaran murya, “Ai ba matsala, za mu je ofis mu dauki bayanai, sannan a ga yiwuwar zuwa neman mahaifin naki, idan yana raye.”

Ihsan ta yi saurin kallon sa, shi kuwa ya kawar da kansa.

Gombe

Gidan kerarre ne na karshe, ta ko’ina ya hadu da kayan kawa, a harabar gidan akwai shuke-shuke da tarin motoci, wasu mazauna gurin sun ce gidan shi ne na biyu ko na uku a keruwa, wasu kuma na kiran gidan da ‘aljannar duniya’.

A harabar gidan akwai ma’aikata, tun daga kan masu ban-ruwa, masu gadi, direbobi da masu tsaron lafiya.

Dr. Mansur ya yi ajiyar zuciya ya dubi Alhaji Habu ya ce, “Amma Alhaji ya aka yi har Alhaji ya kai wannan lokacin ba a gaya min da wuri ba, ko don matarsa ba ta raye?”

Alhaji Habu ya harare shi, “Wai sau nawa zan gaya maka mu ma ba mu sani ba.”

Dr. Mansur ya ce “Ina mamakin wadannan kalamai naka, shi ya sa nake ta maimaita tambayar. Kuma ina son in san su waye abokan gabar Alhaji.”

“Me kake nufi?” Hajiya ‘Yar-Bala ta bukata.

Dr. Mansur ya nuna Alhaji Audu ya ce, “Wannan cutar, ba ciwo ba ne na Allah da Annabi ba, akwai wanda ya yi masa irin abin nan da ake cewa sammu.”

Suka kalle shi a tare, “Me kake nufi? Kana zaton za mu yi wa dan’uwanmu sammu ne?”

“Ban ce ku ba, ai tambayar ku na yi ko yana da sabani da wani.” Cewar Dr. Mansur.

“To wa ya sani.” In ji Hajiya ‘Yar-Bala.

Dr. Mansur ya kuma kallon Alhaji Audu, “Yanzu ina ganin zan sa a dauke shi a kai shi asibiti.”

Alhaji Habu ya yi murmushi ya ce “Ai tun farko ma da abin da ka ce kenan da ya fi wannan surutun.”

“Wane ne zai yi jinyarsa a cikinku”

Suka kalli juna. Hajiya ‘Yar-Bala ta ce “To a gaskiya ni ina da wata tafiya a gabana, kuma zan dade.”

Alhaji Habu ya ce, “Ni kuma akwai tarin ayyuka da suka sha min kai, yanzu ma da kyar na iya zuwa nan.”

Dr. Mansur ya dube su, “Shikenan zan sami wanda zai yi jinyarsa sai a rinka biyan shi.”

“Hakan ya yi, kafin lokacinsa ba.” Cewar Alhaji Habu.

Alhaji Audu dake kwance duk yana jin su amma ba zai iya motsi ko magana ba, amma zuciyarsa cike take da tsananin tsana ga ‘yan’uwan nasa, shi kadai ya san irin abin da suka yi masa, kuma yana neman damar da zai sanar da wani damuwarsa da halin da yake ciki da kuma irin kulle-kullen da ‘yan’uwan nasa ke yi don su cinye dukiyarsa.

*****

Da misalin karfe biyu da mintuna goma sha uku, Ihsan da Amadu suka isa Gombe, suka sauka a tasha, su uku ya kamata a ce sun zo, su da dansanda daya da aka hada su, amma dansandan ya yi musu duk irin karyar da zai iya ya zille, ya bar su, amma ya ba su lambar wayarsa ya ce idan suka sami abin da suka zo nema ko suka dawo su kira shi.

Amadu ya dubi Ihsan, ya ce “Bari mu fara yin sallah tukunna, sai mu nemi gidan, don da alama ba zai yi wahalar ganowa ba.”

A wajen tashar suka sami masallaci, Amadu ya shiga ciki ya yi sallah, ita kuma Ihsan ta sami wani zauren gida a jikin masallacin ta yi tata sallar.

Bayan idar da sallar suka nemi abinci suka siya, suka ci.

Duk wani motsi na Ihsan, Amadu yana kula da shi, yanayi da halayyar yarinyar ya sa shi matukar tausaya mata, kuma ya ji yana son taimaka mata gwargwadon iyawarsa. Har suka gama, suka tafi neman abin da ya kawo su.

Kamar yadda suka zata, ba su sha wahala ba, mutum daya suka tambaya, ya gaya musu inda gidan yake. Amma sai da suka hau mota.

Lokacin da suka je inda gidan yake sun sha mamaki, duk yadda suka zaci gidan; girmansa da haduwarsa ya wuce nan.

Sakin baki suka yi suna kallon gidan, Ihsan ta dubi Amadu, “Anya nan ne gidan?”

Amadu ya yi ajiyar zuciya, “Tabbas nan ne gidan kamar yadda bayanin Haris ya nuna.”

“Ni gaskiya ina tsoro.” Cewar Ihsan.

“Tsoron me? Kina tunanin Abban naki zai yi miki karya ne? Ai yadda kika ba da labarinsa zai yi wuya ya rubuta karya.”

A hankali Ihsan ta ce, “Haka ne. To ya za mu yi?”

“Zuwa za mu yi, mu tambaya, mu yi bayani.”

Amadu da Ihsan suka karasa jikin kofar gidan suna dubawa ko za su gano maigadi, a daidai lokaci Alhaji Habu ya karaso a cikin tsohuwar Marsandinsa, ya yi fakin, ya fito yana dakawa su Ihsan tsawa, “Kai, kai ‘ya’yan talakawa, maular ce haka, ya aka yi ne?”

Suka rissina masa, Amadu ya ce, “Mun zo neman mai wannan gidan ne.”

Alhaji Habu ya ce “Ai ka ji! Ni na san maula ce, to maigidan nan ya mutu sai a koma wani wajen matsiyata, ‘yan maula.” Ya wuce fuuu, ya bar su nan suna kallon bayansa.

Ihsan ta fashe da kuka. Amadu ya dube ta yana fadin, “Hakuri za ki yi, ki yi shiru, don kukan ba shi da amfani a yanzu, ko mene ne ma ki fara bari mu samu, mu yi bayanin dalilin zuwanmu.”

Suka dan yi shiru, Ihsan tana shisshikar kuka, “Dole in yi kuka, ya zan yi da rayuwata?”

“Kin ga ni fa ban yarda da abin da wannan mutumin ya fada ba.” Cewar Amadu.

Ta daina kukan, ta dube shi, “Me ya sa ka fadi haka?”

Amadu ya kwantar da muryarsa, “Yadda ya gaya mana maganar ba ta nuna cewa maigidan ya mutu ba, ya yi mana haka ne kawai don ya kore mu.”

Ihsan ta tattara hankalinta gare shi, ta kasa magana.

“Bari mu sami wani a makwabtan nan mu tambaye shi.” Amadu ya fada.

Akwai wani gida mai babbar kofa dake can tsallaken gidan Alhaji Audun Gombe, a bakin kofar akwai wani maigadi buzu, yana tufka igiya, Amadu da Ihsan suka karasa gare shi, suka yi masa sallama.

Ba ya jin Hausa sosai, amma ya amsa yana kallon su. Amadu ya ce “Don Allah Malam tambaya muke yi.”

Buzu ya ce “To namiji yi sauri ka yi tambayar ka, don maigida basshi bidar irin wanga tsayuwa a kofar gida nai, shi ya hana ni kawo mata ta.”

Amadu ya nuna kofar gidan Alhaji Audun Gombe ya ce, “Don Allah wai maigidan can ya mutu?”

Buzu ya zaro idanu ya ce “Yauhe? Yau ya mutu kenan don mu nan ba mu sani ba.”

“Wani mutum ne ya gaya mana, yanzu ya shiga ciki.”

Buzu ya dan yi jim, “Kai wallah da wuya, don da tuni unguwar ga ta cika da batun, ni dai na san an kai shi asibiti.”

Suka dan yi shiru.

“Don Allah ina ne asibitin?” Ihsan ta tambaye shi a kagauce.

Buzu ya dan yi shiru, sannan ya ce, “Akwai wani likita da yake duba shi, mun taba zuwa wajen shi duba shi, sai in kwatanta muku asibitin da yake ku je, ku tambaye shi.”

Ya kwatanta musu asibitin, suka yi godiya, suka tafi.

*****

Ihsan da Amadu da Dr. Mansur a zaune a ofis dinsa, sun yi shiru bayan Ihsan ta gama ba da labarinta. Dr. Mansur ya yi ajiyar zuciya bayan da ya gama nazari, sannan ya kura wa Ihsan ido.

“Bisa dalilai guda biyu zuwa uku zan iya yarda da labarin da kuka zo da shi. Da farko, kin yi kama da matar Alhaji Audu, Hajiya Saudatu, wadda Allah ya yi mata rasuwa.”

Kwalla ta biyo idon Ihsan.

“Sannan yadda kuka ba da labarin abin da ya faru da Alhaji da sace ‘yarsa babu kuskure, amma kafin in ce muku komai ya kamata in kara samun madogara.”

Amadu ya ciro katin shaidarsa, ya mika masa. Dr. Mansur ya karba yana dubawa. Sannan Ihsan ta dauko daurin kayanta lokacin da aka sace ta, ta mika masa.

“Idan yana raye ka ba shi wannan.”

Dr. Mansur ya duba kayan sannan ya kara kallon Ihsan. Ya tuno wani hoto na Ihsan a lokacin tana karama sanye da wadannan kayan. A iya saninsa, duk lokacin da Ihsan ta sa sabbin kaya, to sai Alhaji Audu ya sa an dauke ta a hoto.

To amma nan da nan zuciyarsa ta raya masa wani abu, ta darsa masa ba yanzu ya kamata, ya nuna wa Alhaji zuwan su Ihsan ba, yanzu ana bukatar samun lafiyarsa ne.

“To amma kuma ba mamaki idan har Ihsan din ‘yarsa ce, ganin ta na iya sa ya sami sauki.” Dr. Mansur ya raya a ransa.

A lokacin da yake wannan tunanin, Amadu kuma yana nazarinsa, kuma tabbas ya gano abubuwa guda biyu, na farko da alamun ya gamsu Ihsan din ‘yar Alhaji Audu ce, na biyu kuma kamar hakan ba zai yi wa Ihsan kyau ba, domin da alama zai ki hada ta da mahaifin nata.

Dr. Mansur ya kalle su, “Kuna da masauki?”

Ihsan ta kada kai alamun a’a, ta ce, “Ba mu san kowa ba a garin nan.”

“Shikenan, ku zo mu je in ba ku masauki a gidana.” Dr. Mansur ya ce da su.

*****

Idan ka ga yadda Alhaji Habu da Hajiya ‘Yar-Bala suka bararraje a gidan Alhaji Audun Gombe sai ka rantse ya mutu, an mallaka musu gidan. Don shi Alhaji Habu ma yana gab da tattaro iyalansa ya dawo gidan kamar yadda ya tsara.

Sai dai a yanzu da suke zaune a falon gidan bayan da suka sa ma’aikatan gidan su hado musu abinci, ransu a bace yake. Hajiya ‘Yar-Bala tana kallon Alhaji Habu da jajayen idanunta.

“Kai nake sauraron fa, ka yi shiru.”

Alhaji Habu ya yi tsaki, “Na gaya miki na sa a binciko min inda Dr. Mansur din ya boye Alhaji. Idan bai mutu ba, sai in sa a taimaka masa a karasa shi, ya huta, idan kuma ya mutu shi kenan ya hutar da mu, sai ki zo mu raba kowa ya kama gabansa.”

Suka yi shiru, kafin daga bisani Hajiya ‘Yar-Bala ta dora da tambayar, “Yaya batun ma’ajiyar takardun nasa?”

Alhaji Habu ya harare ta, “Wai sau nawa zan gaya miki duk suna banki, ko ba ki san sai karamin mai kudi ne yake ajiya a gida ba? Ki bari a tabbatar da rasa mai dukiyar tukun, ai wannan ya fi wuya, idan ya so samun komai duk mai sauki ne.”

“Ai gani na yi kana bori da sanyin jiki.” Cewar Hajiya ‘Yar-Bala.

“Haba Malama, na fa fi ki damuwa da wannan abu, ko kadan ba na son in ga wani ko wata ta rabi gidan nan, ko almajirai ma korar su nake, ba ki ga yadda dazu na yi fata-fata da wasu yara ba, wadanda ya kamata a ce na tausayawa.”

Hajiya ‘Yar-Bala ta ce, “Ka tausaya musu yanzu watarana su ma sa tausaya ma.”

“To ai shi ya sa ban tausaya musu ba.” Cewar Alhaji Habu yana dariya.

*****

Hankalin Dr. Mansur da ma’aikaciyar asibiti (nurse) ya yi matukar tashi, domin gabadaya sun gama saduda cewar Alhaji Audu da ke gabansu ya mutu, wani irin numfashi da yake yi na karshen zangon rayuwa shi ya kara ruda su, sannan ga shi duk wani abu da ya kamata su yi masa don ceto rayuwarsa sun yi, amma abin ya gagara, tun Dr. Mansur yana sa rai har ya fara saduda, ya zuba wa Alhajin ido yana kallon sa, yana jiran ya mutu, ya rufe masa fuska.

A daidai lokacin ya tuno Ihsan, ya tuno da kayan da ta ba shi, da sauri ya mike, ya fita daga dakin, nurse ta bi shi da kallo ba tare da ta yi magana ba. Bayan fitarsa ta ci gaba da kura wa Alhaji Audu ido cikin tausayi.

Jim kadan Dr. Mansur ya dawo dauke da kayan Ihsan, ya zo daidai kan Alhaji Audu ya tsaya, yana bude kayan. A daidai lokacin Alhaji Audu yana nishi, yana rufe ido ya bude, da ya bude, ya kalli abin da ke hannun Dr. Mansur, sai ya kasa rufe idon, ya tsaya cak, yana kallon sa, sai kuma ya fara motsa baki yana furta wasu kalamai da babu sauti. Da sauri Dr. Mansur ya kara kunnensa a daidai bakinsa. Ita kuma nurse sai bin sa take yi da kallo.

Da kyar yake yin maganar, hakan shi ma Dr. Mansur din da kyar yake iya jin abin da yake cewa.

“A…a ina…ka…ka sami…kayan nannn….”

Dr. Mansur ya ce, “Ihsan dinka aka gani.”

Alhaji Audu ya zaro ido, sai kuma ya suma. Nurse ta matsa da sauri a rude, “Dakta yi sauri, ya mutu.”

Dr. Mansur ya dube ta, “Kar ki damu, suma ya yi.” Suka kalli juna.

Mintuna hamsin da doriya suka shude, Alhaji Audu ya farfado a yanzu yana kishingide hannunsa rike da kayan da Dr. Mansur ya ba shi, yana hawaye, yana sauraron labarin da Dakta din yake ba shi na Ihsan.

“Ina Ihsan din take?” Alhaji Audu ya bukata a kagauce.

“Tana nan. Akwai matsala ne shi ya sa ban kawo ta ba.” Cewar Dr. Mansur.

Dr. Mansur ya dube shi, ya ce, “Ka yafe min, amma akwai wadanda suke barazana ga rayuwarka, don haka idan aka kawo maka Ihsan za su iya sanin inda kake da halin da kake ciki…”

Alhaji Audu ya ce, “Na san wadanda kake magana, amma ganin ‘yata ya fiye min komai, ko da zan rasa rayuwar tawa.”

Dr. Mansur ya kura masa ido cike da tausayi.

*****

Alhaji Habu da Hajiya ‘Yar-Bala suna zaune, Tajo ya shigo falon yana duddukar da kai kasa. Alhaji Habu ya dube shi da sauri, “Ya aka yi?”

Tajo ya ce, “Alhaji akwai matsala. Don mun gano gidan da Dr. Mansur din ya boye Alhajin. Sannan kuma mun gano, ‘yar Alhajin da aka sace shekaru da suka wuce, ta dawo.”

Zumbur Hajiya ‘Yar-Bala da Alhaji Habu suke mike tsaye suna kallon juna, kana kamar a tare suka dubi Tajo.

“Me kake nufi?” Hajiya ‘Yar-Bala ta bukata.

“E, ‘yarsa da kuka sa aka sace don a kashe ta, tun tana karama, ita ce ta dawo.” Tajo ya jaddada musu.

“Kana nufin Ihsan?” Alhaji Habu ya bukata, yanzu gumi ya fara yawaita a kan goshinsa.

“E.”

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! La haula wa la…” ‘Yar-Bala ta fara sallallami cikin marairaicewa, “Asirinmu zai tonu Alhaji,  yanzu ya za mu yi kenan?”

Suka dan yi shiru.

Alhaji Habu yana huci, “Ki nutsu, ba mu makara ba.” Ya kalli Tajo, “A gama da su gabadaya, kar su wuce yau, kar a bari in ga fuskar Ihsan.”

Suka dan yi shiru, kafin Hajiya ‘Yar-Bala ta nisa, ta ce “Alhaji wadannan yaran har yanzu ka yarda da su?”

“Kina nufin su Tajo? Ki kwantar da hankalinki, wancan karon ma yaron nan ne Harisu ya yaudare su, ya gudu da yarinyar, kuma shi Oshere, shi ya tabbatar min an kashe su. Yanzu kuma, tun da a wancan lokacin hakanmu bai cimma ruwa ba, ai kin ga yanzu sai ya karasa aikinsa, kuma ya dauki fansa.”

“Haka ne.”

*****

Alhaji Audu yana kishingide a gefen gadon, duk ya dokanta Dr. Mansur ya zo masa da diyarsa. Motsi kadan sai ya dubi kofar shigowa, haka ya kasance tsawon lokaci, kafin ya ji an murda kofa tare da sallama.

Dr. Mansur ya shigo, Ihsan na biye da shi, gabadaya hankali da idanun Alhaji Audu yana kan Ihsan da ke bayan Dr. Mansur, ji ya yi tamkar ya sauko a guje ya rungume ‘yarsa, amma bai zai iya ba.

Idanunsa da zuciyarsa sun gama yarda ‘yarsa, ya rasa abin da zai yi, sai hawaye ya shiga fitowa daga idanunsa, har suka karaso, suka tsaya a bakin gadon da yake, ita da Dr. Mansur suka kalli juna.

“Ihsan wannan shi ne ainihin mahaifinki.”

Cikin rawar jiki Ihsan ta karasa, ta rungume mahaifinta tana kuka.

“Abba an raba ni da kai, an bar ka cikin wannan halin.”

“Ayya ‘yata, kar ki damu, duk wani bakinciki da halin damuwa ya kare a yanzu, ganinki ya sanyaya min idanuna da zuciyata.”

Shi ma ya ci gaba da kukan.

Kamar daga sama, Tajo da Oshere suka fado cikin dakin. Hankalin Alhaji Audu ya tashi da ya hada ido da Tajo da Oshere, kafin su tantance abin da ke faruwa, sai jin karar harbi suka yi, Tajo ya harbi Dr. Mansur.

Faduwar Dr. Mansur kasa ya yi daidai da rikicewar su Alhaji Audu da Ihsan, Ihsan din ta kwallara kara. Dr. Mansur ya dafe wurin da jini ke fita daga kafarsa.

Tajo ya tsaya a gabansu, yana yi musu kallon daidai.

“Wancan karon kun tsallake tarkonmu, saboda an munafurce mu, amma wannan karon ba ku isa ku tsallake ba.” Ya saita Ihsan da bindiga. “Wannan yarinyar ta dalilinta aikinmu ya lalace, ake kallonmu a matsayin ragwaye, zan fara da ita, zan kashe ta, kafin in…”

Wani mugun duka da aka yi wa hannunsa da katako ya tilasta katsewar maganarsa, bindigar da ke hannunsa ta fadi kasa.

Haris da ya yi dukan, ya yi sauri, ya zari bindigar, ya yi gefe yana kallon Tajo, suka yi wa juna kallon-kallo.

Ran Oshere a bace, ya dubi Tajo ya ce, “Ka ga butulun da muka dade muna nema, ya kawo kansa ko? Na gaya maka, idan kere na yawo, zabo na yawo watarana za su hadu.”

Haris ya yi murmushi, “Oshere, ashe har yanzu kunnenka bai yi laushi ba.”

Oshere ya kalli Tajo, sannan a tare suka sake kallon Haris, kafin su yi magana, Haris din ne ya yi magana, yana daga murya.

“Ku shigo!”

‘Yansanda DSS su uku suka shigo kowannensu rike da bindiga, suka ritsa Tajo da Oshere. Tajo ya kalli Haris.

“Wane ne kai?”

Alhaji Audu ne ya yi magana.

“Harisu Umar yarona ne, kuma jami’in ‘yansanda ne mai mukamin sifiritanda na ‘yansanda, ni na ba shi wannan aikin saboda tserar da rayuwata da ta ‘yata da matata.” Ya dan fitar da hawaye, “Duk da kun yi nasarar kashe min mata, shi ya cece ni, ya ceci ‘yata, yanzu kuma ya yi sanadiyyar kawo karshen zaluncinku, musamman wadanda suka saka ku wannan mummunan aikin.”

Daya daga cikin jami’an ‘yansanda ya mikawa Dr. Mansur wani farin kyalle, shi kuma Dr. din ya daure wajen da aka harbe shi.

Ihsan ta tashi da sauri, ta rungume Haris, “Allah Sarki Abbana, ashe zan sake ganinka, ka wahalar da ni Abbana.”

Alhaji Audu ya ci gaba da magana.

“‘Yan’uwana su ne silar wannan mummunan aikin. Abin da ba kowa ba ne ya sani, shi ne, tun kafin a haifi Ihsan ina da ‘ya’ya guda biyu mace da namiji, Iman da Saifullah, su suka sa aka kashe su, aka kashe mahaifiyarsu.” Ya dan sarara, “Ba su san, na san shirinsu ba, na son ganin bayana da duk wani jinina, kawai don su cimma burinsu, na mallake duk wani abu da na mallaka.”

Ya ci gaba da hawaye.

Haris ya dan janye jikinsa daga Ihsan, ya dubi yaransa, “Ya ake ciki?”

“E, suna can, suna jiran wayar su Tajo, su ji cewar sun kashe Alhaji da Ihsan da kai, sai su zo.”

Haris ya girgiza kai, “Da kyau, kun yi daidai. A aiwatar da abu na gaba.”

Tun kafin ya rufe baki, jami’an nan suka buga su Tajo da kasa, suka sa musu ankwa a hannaye.

“Ku yi amfani da wayar su wajen kiran Alhajin, muna nan zai kawo kansa.”

Daya daga cikin jami’an ya sa hannu a aljihun Tajo, ya dauko wayarsa, ya kira Alhaji Habu.

“Alhaji an gama aiki, za ku iya zuwa gidan da muka gaya muku.” Bai jira abin da za su ce ba, ya kashe wayar. “An gama Sir, kuma za su zo.”

Haris ya ce, “Da kyau, yanzu ku fita da wadannan, ku kai su mota, ku boye, ku dawo.”

Cikin mintuna bakwai suka yi abin da ya sa su, suka dawo, suka sami wuri a falon, suka boye. Ihsan dai cikin mamaki, ta koma kusa da mahaifinta, ta zauna, ta kura masa ido, shi kuma ya kwanta, ya lumshe idanunsa.

Jim kadan Alhaji Habu da Hajiya ‘Yar-Bala suka shigo, kai tsaye hankulansu suka tafi kan gadon da Alhaji Audu ke kwance.

“Da kyau Tajo, kun cika aiki, za ku karbi ladanku har da kari.”

A daf da gadon, suka tsaya, suna kallon Ihsan.

“Ya aka yi, ita wannan ba su kashe ta ba?” Cewar Hajiya ‘Yar-Bala.

Haris da yaransa suka fito, suna dubansu.

“Shi ma Alhajin ba su kashe shi ba!”

A razane suka dube su cikin mamaki, Hajiya ‘Yar-Bala, ido ya raina fata, kamar za ta yi kuka, Alhaji ma a razane yake, yana ta bari. Suka kasa magana.

A hankali Alhaji Audu ya bude ido, ya mike zaune. Su Alhaji Habu suka dube shi cikin kaduwa.

“Shekara da shekaru kuna saka da mugun zare, kuna haka wa kanku ramin mugunta, yau kun zo tikewar da ramin ya rufta da ku.” Haris ya fada yana matsawa zuwa gare su.

“Harisu ashe kai munafuki ne?” Alhaji Habu ya fada.

“Ba munafuki ba ne, mai kama munafukai da masu laifi ne irinku.” Haris ya mayar masa da martani. “Saboda son rai irin naku, babu abin da Alhaji ba ya yi muku, amma dole sai kun ga bayansa, kuna kokarin raba shi da duniyar saboda dukiyarsa, bayan kun kashe masa ‘ya’ya da mata.” Ya dan yi shiru, yana kallonsu.

“Karshenku ne ya zo, za ku girbi abin da kuka shuka.”

Alhaji Habu da Hajiya ‘Yar-Bala suka durkusa a gaban Alhaji Audu suna rokon shi, suna ba shi hakuri.

“Yaya don Allah ka yi hakuri, wallahi sharrin zuciya.”

Alhaji Audu ya girgiza kai, “Yanzu sai ku je, ku girbi sharrin zuciyar taku. Ku da jami’an tsaro ba ni ba.”

Jami’an nan suka kifar da su, suka sa musu ankwa, suka yi waje da su.

*****

Haris da Ihsan suna zaune, Ihsan ta kura masa ido cikin mamaki tana murmushi akwai jin kunya a tare da ita.

“Kin kura min ido, mene ne tambayar ki?” Haris ya bukata cikin murmushi.

“Ina da abubuwa da yawa da nake son sani a game da kai, da yadda ka rike ni, na yi tsammanin kai mahaifina ne tsawon shekaru.”

Ya yi dariya, “Sannu a hankali za ki ji komai, kafin mu rabu in bar kasar nan za ki san komai.”

“Kai daya za ka tafi, ko tare da ni?”

“A wajen mahaifinki za ki zauna, tun da an kawo karshen masu barazana da rayuwar ku.”

“Tare za mu tafi dai, a wajenka zan zauna.”

Ya girgiza kai, “Mahaifinki yana raye, ba za ki zauna a wurina ba.”

Suka dan yi shiru. Sannan Ihsan ta dora.

“Na gaya wa mahaifin nawa, kuma ya yarda idan na gama karatuna zai aura min kai.”

Haris bai san lokacin da ya mike tsaye ba, yana kallon ta cikin matukar mamaki.

Ta kalle shi, “Abbana, ba za ka aure ni ba kenan?”

Ya dan yi shiru yana kallonta. Ta fara hawaye.

“Ba zan iya rayuwa da kowa ba sai kai, ba ka san irin kunci da wahalar rayuwar da na shiga ba lokacin da ka tafi, ka bar ni a gidan marayu. Allah ne ya yi ina da sauran rayuwa a gaba.” Ta ci gaba da kuka.

Ya dan sunkuyo kusa da ita.

“‘Yata ban taba jin dadin rabuwa da ke ba. Sannan ban taba zaton zan rayu da ke a matsayin matata ba, wanda wannan abu kuma shi ne abin da na fi komai so a rayuwa ta. Don Allah da gaske, za ki zauna da ni a matsayin mace da miji?”

Ta kalle shi, tana murmushi cikin hawaye.

“Shi ne abin da na fi komai so idan ka amince.”

“Tashi mu je wajen mahaifin naki.”

Ta tashi cikin doki da farin ciki, suka jera gwanin sha’awa.

*****

Kafin Haris ya tafi kwas na watanni shida, shi da Ihsan suka je har Kano, gidan marayu, ta kai musu kayayyaki da kudi masu yawa, sannan ta riski Zainab kawarta tana nan, amma Allah ya yi wa Yaroro rasuwa, ta dauki Zainab din da wasu yara su bakwai da suka zauna tare, ta dawo da su Gombe, ta sa mahaifinta ya dauki nauyin komai na su na rayuwa.

Karshe

Alhamdulillahi

Kabiru Yusuf Fagge (anka)

07030319787

<< ‘Ya’yanmu 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×