Skip to content
Part 13 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Uku

Yayin da wadancan dakaru suka makale a makarantar Malam Kunkuru, a nan fadar Sarki Zaki an hade zaman fadar, inda manya da kananan dabbobin duk suka taru, shirye-shiryen tura dakaru ne yake ci gaba da tafiya. Sabanin wancan zabi na farko, a wannan karon kowace dabba an ba ta dama ne ta bayar da shawarar wace dabba ce ta fi dacewa a saka ta a cikin dakarun, kuma ta yi bayanan dalilan da suka sa take ganin ya kamata a dauki wannan dabbar. Wato wane irin amfani take ganin idan an tafi da ita za ta bayar.

A yinin jiya an ambaci dabbobi uku, wadanda kuma aka lissafa kwarewarsu a fannoni da dama, da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa. A yau ma a kan wannan aka dora, inda a halin yanzu Guza yake bayyana dalilan da suka kamata a yi la’akari da su wurin sa Karkanda a cikin ayarin. Wanda yana gamawa kuma shi Karkandan ya nemi izinin yin magana.

Bayan an ba shi wannan damar, sai ya fara da godiya ga fadar, da kuma shi Guza da ya bayar da shawarar a hada da shi a cikin ayarin: “Na cika da mamaki kwarai, domin sam ban taba tsammanin wata karamar dabba tana da masaniya akan abubuwan da zan iya na dabarun yaki ba. Abin da dai kawai na yarda a baya shi ne dukkansu sun  san ina da karfi.”

Mafi yawan dabbobin wurin suka yi dariya. Sannan ya kara cewa. “To idan fada ta ba ni dama ni ma akwai wanda nake so in ambato, saboda matukar alfanon da zai iya yi a irin wannan gaba.”

Dila ya ce. “Bisimilla.” A madadin Basaraken.

Karkandan nan ya ce. “Wato ba don kankantar jiki ba, samun wata dabba mai alfano a yaki kamar Zabiyar Jaba, ba karamin aiki ba ne.”

“Zabiyar Jaba kuma?” Wasu daga mazauna fadar suka tambaya, cike  da mamakin jin sunan.

“Zabiyar Jaba kuwa.” Ya amsa tare da dan waiwayawa bangaren da ya ji muryoyin sun fi karfi.

Zakin wanda yake zaune bisa karaga yana murmushi ya ce. “Ka san da yawa ba su san ta ba fa.”

“Ba mamaki,” In ji Karkanda, “ka san dayake kwanan nan sun yi nisa ba kamar da ba.

Kahuhu ya ce. “Ai an ce sun fi son wuri mai yalwar bishiyoyi ne, watakila shi ya sa suke matsawa gaba.” Ya dan dakata, sannan ya kara cewa. “Kodayake duk da hakan ma dai ana tsoron yanzu sun tasar ma karewa a duniya baki daya, domin sun ragu, gayar raguwa.”

Dila ya kalle shi cikin mamaki: “Wai Alaramma kai ma ka san ta dama?”

Ya yi dariya: “Yallabai na dai karanta labarinta daga takardun Mahaifina.”

Karkanda ya ci gaba: “Abin da ya sa na ga dacewar a gayyato wannan Jaba, ba komai ba ne illa kaiwarta makura wurin juriya da sadaukarwa da karfi da kuma makamin yaki da take tattare da shi. Amma tun da wasun mu ma ba su san ta ba, ina ganin ya kamata in fadada bayaninta sosai. Yadda ko ganin ta aka yi za a iya shaida ta: Da farko dai ana kiranta Zabiya ne saboda tsananin fari ko jar fatarta, sababanin gama-garin Jaba. Bayan suffa da idan ka gani za ka ga tabbas kirar jiki ne da ita irin na Jaba, kafatanin al’adu da tsarin zamantakewarta sun sha bamban da na Jaba.

Domin ita daga kallon ta za yarda lallai wannan mayakiya ce. Tana da manyan fikoki guda biyu a sama da kasan bakinta, wadanda kuma suka fito waje karara, ba irin na sauran dabbobi da sai sun bude baki ake ganin su ba. Babu wani abu da za ta ciza da wannan hakoran komai girmansa face sai ya gijita. Tana kuma da zafin nama kwarai. Don haka da wuya abokin gwabzawa ya cimma ta, sai dai in tazarar girmansun ce ta yawaita kwarai.

Haka nan wani abu da zai kara tabbatar mana da dacewarta a wannan rundina, ita ce dabi’arta ta sadaukarwa. Domin a kowane garke na Zabiyar Jaba Sarauniya ce kawai take haihuwa. Sauran ba sa ko kusantar juna, balle su haihu. Wannan sarauniya tana nan zaune wuri daya da kananan ‘ya’yanta. Su kuwa kafatanin majiya karfinsu su ne suke bazama, su yi ta haka a karkashin kasa suna hako musa saiwoyin bishiya, wanda yana daya daga cikin mafiya dadin kalaci a wurinsu.”

Lokacin da ya kawo nan, sai ya lura kusan kowa da ke wurin ba bin da yake yi sai faman gyada kai. Don haka ya dakata tare da cewa: “Ina sa ran dai ko a nan na tsaya fada za ta gamsu cewa wannan Jaba abokiyar tafiya ce.”

Zakin ne ya fara cewa “Kwarai da gaske.”

Sannan Dila ma ya ce. “A sahun gaba ma kuwa.” Ya dan dakata, sannan ya kalli Kahuhu ya ce. “Wato dole ma wannan  Jaba ta yi karanci ai a doron kasa.”

Kahuhun ya dube shi ya ce. “Uhm?”

Ya ce. “To ba ka ji yadda tsarin nasu yake ba, wai dukkan garke babu wanda zai haihu sai sarauniya kwaya daya tak?”

Kahuhun ya dan yi dariya, sannan ya ce. “Sarkin Azamci kenan, ai ita haihuwa daban, ba ta hanyar ta ake auna albarka ko yaduwar abu ba, a ilmance. Kodayake dai haka ake ayyanawa a lissafi irin na gama-garin wasu jama’a.”

Dila ya kalle shi cikin mamaki: “To idan kuwa ba ta hanyar haihuwa za a auna albarka ko yaduwar abu a bayan kasa ba, ta ina za a auna?”

Zakin, wanda sau da dama yakan so irin wannan tattaunawar ta barke tsakanin ‘yan gaban goshin fadar biyu. Shi ma bin su kawai ya ci gaba da yi da kallo, yana murmushi. Kahuhu ya ce.

“To bari in yi maka wasu ‘yan tambayoyi kadan.”

“Ina ji.” In ji Dilan.

Ya ce. “Ka san lokacin  da karya take dauka kafin ta haihu? Ina nufin daga haihuwa zuwa wata.”

Dila ya ce. “Ai Karya tana iya haihuwa sau biyu a duk shekara.”

Ya ce. “Madallah, ‘ya’ya kamar nawa take haifa a duk haihuwa daya?”

Dila ya ce. “Za ta iya haifar daga shida har zuwa goma sha.”

Ya ce. “To da kyau. Saniya fa, sau nawa take haihuwa a shekara?”

“Sau daya mana.” Dila ya amsa.

Kahuhu ya ce. “Ita kuma kamar ‘ya’ya nawa take haifowa in ta tashi haihuwa?”

Dila ya ce. “Daya, sai ko sa’ar gaske ta haifi biyu?”

Kahuhun ya yi dariya, sannan ya ce da shi. “To sau nawa kana ganin garken Shanu?”

Dila ya ce. “Sau barkatai.”

Sai ya kara cewa. “Shi kuma garken Karnuka fa?”

Sai Dila ya fashe da dariya, ya ce. “To, to, na san inda ka nufa.”

Haka kuma Zakin ya yi dariya, sannan kafatanin dabbobin wurin suka ci gaba da dariya.

Zakin ya kara da cewa. “Kuma ka ga su shanu kullum yanka su bil’adama suke yi, amma Karnuka ba kasafai ba. In ka ga sun mutu da yawa to kawai wata annoba ce ta afka musu.”

Mazauna wurin suka ce “Tabbas.”

Haka dai aka ta yin hira cikin raha a karashen zaman na wannan yinin. Har zuwa lokacin da Sarkin ya shiga gida, sauran mukarrabai da jama’ar fada suka kama nasu hanyoyin.

<< Yini Sittin Da Daya 12Yini Sittin Da Daya 14 >>

1 thought on “Yini Sittin Da Daya 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×